KOMAI NISAN DARE

18.

by @zeeykumurya

KOMAI NISAN DARE 


18.


Zeey Kumurya 



Ta yi nasarar lalubo wayar ta riƙe a hannunta, ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi tare da faɗin. "Inna ana kira ki zo ki ɗaga kar ta katse." Karɓar wayar Inna ta yi da niyyar ɗagawa, kafin ta ɗaga wayar ta saka Battery shutdown ta ɗauke. 

"Yawwa, ba ni in kin ɗaga."


 A'isha ta faɗi haka tana yawo da hannunta a cikin iska tamkar za ta cafki babu. 

A sanyaye Inna ta ce. "Ban kai ga ɗagawa ba ta mutu, ina ji chaji ne ya ƙare." A gigice A'isha ta ce. "Innalillahi! kunna dai mu gani ko batir ɗin ne ya goce." Inna ba ta yi musu ba ta kunna wayar, ƙara mutuwa wayar ta yi alamun dai babu chajin. Cikin damuwa na ganin samu da rashi A'isha ta miƙe tana faɗin. "Bari na kai ta wurin chaji." 


"Idan kina ganin hanya ba, mene haka ne wai A'isha kike yi? Duk kin bi kin gigice saboda an kira waya, shi ne ma ko ba shi ba ne wanda kike ta ƙulafucin kiran nasa oho? Kin ga A'isha ki raba kan ki da abin da ya fi ƙarfin ki, ki cire damuwar yaron nan daga ranki." 

Komawa ta yi ta zauna tare da saka kuka, cikin raunin murya ta ce. "Inna shi kaɗai ne fa wanda ya so mu a cikin garin nan bayan Innar Ma'u, shi ne abokin hirata, tunda ya tafi na koma halin zaman kaɗaici, idan na damu da kiran shi laifi ne? Idan kuma laifi ne ki yi haƙuri na daina." Wani irin sanyi jikin Inna ya yi, tausayin A'isha ya cika mata zuciya. Tabbas idan kana cikin hali na ƙunci da kaɗaici ka samu mai ɗebe maka kewa, lokaci ɗaya kuma ya tafi dole ka damu. Cikin kwantar da murya ta ce. "Ko kaɗan abin da kika yi ba laifi ba ne, kawai dai ina so ki rage damuwar da kika saka a ranki ne, kawo wayar yanzu na kai ta gurin caji, kar a kuma kira a ji a kashe." Share hawayen fuskarta ta yi ta miƙa mata wayar.


Sai bayan isha'i Inna ta je karɓo wayar, ta cewa mai cajin ya kunna ya duba gurin kira ya kira mata lambar da aka kira. Bayan ya duba ya ce. "Babu lamba ko ɗaya a gurin kira fa." Da mamaki Inna ta ce. "An kira fa tana ta ringing, kafin a ɗaga ta mutu babu chaji."

"Shi ya sa ba za a ga kiran ba, ai indai aka kira ba a ɗaga ba har waya ta mutu a haka to kiran ba zai nuna ba."

"Yanzu kenan ba za a ga lambar da aka kira ba?"

"Eh." Ya ba ta amsa a tak'aice.

Zuciyar Inna babu daɗi ta karɓi wayar bayan ta biya shi kuɗin cajin ta koma gida. 

Ihu ne kawai A'isha ba ta yi ba da Inna ta sanar mata ba a ga lambar da aka kira ba, amma ta sha kuka mara sauti. Washegari tun asubar fari suka shirya don tafiya, sai dai a karo na biyu Inna ta nemi kuɗi sama da ƙasa ta rasa, ga shi ba ta ko ficika da ya yi saura, gabaɗaya kuɗaɗen hannunta ta haɗe guri ɗaya ta ajiye a tare.


"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Inna ko dai aljanu ne suka makarantar da ni? Ba sa son a mini magani shi ya sa duk sanda muka shirya da niyyar tafiya asibiti suke sace kuɗin." A'isha ta faɗi haka cikin matsanancin kuka.

Kasa magana Inna ta yi, saboda abun ba ƙaramin dukan zuciyarta gami da ɗaure mata kai ya yi ba. Sunayen Allah kawai take ambata a cikin zuciyarta, wannan wanne irin bala'i ne da jarabta? Waye yake musu wannan satar rainin hankalin? Ta tambayi kanta tare da ɗaga hannu cikin hawaye ta ce. "Allah kai ne sarki, kai ka san me kake nufi da wannan yarinya, Allah duk wanda yake zaluntar mu Allah ka saka mana, ka toni asirin duk wanda yake daukar kuɗin nan, ka ba wa wannan baiwa taka lafiya." 

Kuka sosai A'isha ta wuni tana yi ranar, rarrashin ta Inna ta dinga yi tare da yi mata nasiha akan Ubangiji yana sane da su, su cigaba da addu'a kawai ita ce mafita.


Rayuwa ta koma musu tamkar ta da kafin zuwan Umar, rayuwar rashi da ƙunci da fuskantar ƙyara da tsana daga mutanen gida da na gari. Kullum Inna a tafe take yawon nema musu abin da za su ci, rayuwa dai ta tsananta a gare su.


Yau ta kama Monday, da safe suna cin gayen dafaffen dankalin hausa Inna ta dubi A'isha ta ce. "Ya kamata ki koma makaranta yau, kin ga ni yanzu ba zama nake ba, kuma duk inda na je hankalina ba a kwance yake ba, saboda ina fargabar kar wani abun ya same ki na bar ki ke kaɗai a gida, na dinga tafiya da ke kuma duk inda za ni ba mai yiyuwa ba ne, amma idan kina makarantar sai na fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali." A sanyaye ta ce. "Shikenan Inna zan koma yau insha Allahu, amma fa kullum na je sai Form master ɗinmu ya ce mini har yanzu lokacin da za a mini aikin idon bai yi ba?" 

"Ki shirya sai mu je tare na roƙi alfarmar su bar ki ki cigaba da zuwa kafin Allah ya hore a kai ki asibitin."

"To, Allah ya sa su yarda." 

"Amin."


Kamar yadda Inna ta faɗa tare suka je makarantar, ta samu malamin su A'isha ta yi masa bayanin matsalar da aka samu na sace musu kuɗi, cikin tausayawa ya ce babu komai ta cigaba da zuwa, abin da ya sa suka damu har suke magana saboda A'ishan tana da ƙoƙari, kuma rashin ganin da ba ta yi zai iya sawa ƙoƙarin nata ya ragu, tunda ba ta rubutu ba ta ganin abin da aka koya musu. Godiya Inna ta yi masa ta dawo gida. Tunda ta shigo layin su ta san da akwai wani baƙon al'amarin da yake faruwa a gidansu, ganin mutan gidan kusan dukan su a waje, ga wata ƙaramar Mota fake a ƙofar gidan yara sun yanyame ta. Ƙarasowar ta gurin ya yi daidai da boɗo murfin motar da Yawale yayan Malam ya yi ya fito, karaf suka haɗa ido da Inna, wanda hakan ya haifar mata da faɗuwar gaba. Haɗe fuska ta yi sosai ta wuce cikin gidan ba tare da ta bari sun haɗa ido da kowa a gurin ba, yayinda shi kuma ya bi ta da wani irin kallo, sauran matan gidan kuma suka raka ta da harara. Tana ji yo su zagayensu ana ta murnar dawowar su bayan sun shigo cikin gidan, anata ɓangaren kuma fargaba ce fal ranta, na rashin sanin da wanne kalar cin mutunci mazan gidan suka dawo musu da shi wannan karon ba. Har A'isha ta dawo ba ta fita ba, tana zaune tana ta tunane-tunane, Sallah ce kawai ke tashin ta.

"Inna sannu da gida." 
A'isha ta faɗa bayan ta yi sallama tare da laluben gurin zama ta zauna.


Numfashi Inna ta sauke tare da janye tagumin da ta yi ta ce. "Yawwa, har kun taso?"

"Eh, me ya sa yau ba ki je kin ɗauko ni ba?"

"Wallahi shaf na sha'afa ne A'isha, ban ma san lokacin ya yi ba, wa ya dawo da ke?"

"Wani malaminmu ne, ya ga duk za a tafi a bar ni, shi ne ya ce bari ya rako ni."

"To an gode Allah ya saka da Alkhairi, ki je ki cire uniform ɗin kar ya yi datti, kin san ba mu da omo."

"To, ina abincina yunwa nake ji." Ta yi maganar cikin marairaice fuska.

Cikin damuwa Inna ta ce "Ba mu da komai na ci a gidan nan, kuma ban san inda za mu samo ba, tun ɗazu nake tunani amma na rasa ina zan je." 


"Yau ma haka za mu kwana ba mu ci komai ba?"

"To ya za mu yi? Sai dai mu yi ta addu'a Allah ya kawo mana mafita." 


Cikin karaya A'isha ta ce. "Inna me zai hana mu siyar da wayar da Yaya Umar ya ba mu, mu siya abinci da kuɗin, tunda babu abin da muke da ita, shi bai kira ba mu ma ba ma kiran kowa." Shiru Inna ta yi cikin nazari, a ranta tana mamakin kaifin basira da hankali da A'isha ta yi bayan tafiyar Umar, ta koma so silent, kamar ba ita ce wadda ba ta zama guri ɗaya ba a da, ta daina sangarta da abubuwan yara. Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta ce. "Kin kawo shawara, amma kuma kar sai mun siyar ya yi ta neman mu ba ya samu."

"Ba ma zai kira ba." 

Ta yi maganar cikin jin zafin rashin kiran nasa a cikin ranta, zuwa yanzu ta fitar da rai daga tsammanin kiran shi ko dawowar shi kamar yadda ya ce mata, ta ba wa zuciyarta haƙuri tare da ƙoƙarin cire shi daga cikinta, gami da ɗaukar ƙudirin mantawa da shi gabaɗaya a cikin rayuwarta, duk da ta san yiyuwar hakan na da matuƙar wahala, amma tana addu'a da fatan hakan ta kasance.

Shawarar A'isha Inna ta bi, ba tare da jinkiri ba ta je ta siyar da wayar, bayan Magriba kuma ta tattara wasu daga cikin takalman A'isha masu tsada da agoguna da Umar ya siya mata ta kai gidan wata dillaliya dake nan ƙofar fadan wadda ke siyan tsoffi kaya ta sayar. Da wannan kuɗin ta yo musu sayayyar kayan abinci da sauran abubuwan amfani wanda za su musu kwanaki.




Bayan kwana uku da daddare suna zaune a tsakar gida A'isha tana muraja'ar Alkur'ani, ɗaya daga cikin ƴanmatan gidan ta faɗo musu zagaye babu ko sallama, cikin fitsara ta dubi Inna ta ce. "Asabe ki zo ke da makauniyar ƴarki yanzu in ji babanmu." Kafin su ba ta amsa ta juya ta fita. Cikin tsantsar ɓaci rai A'isha ta ce. "Ba za mu je ɗin ba." Inna dake danne nata ɓacin ran ta ce. "Mu je mu ji neman me yake mana."


"Ni dai gaskiya ba za ni ba, kin san fa Baba Yawale ba ya ƙaunar mu, in mun je ma na san zagi da cin mutuncin mu kawai zai yi kamar yadda ya saba." 

"Mu dai je A'isha, kin san na fi ki ƙin son haɗuwa da mutumin nan, amma saboda gudun magana da fitina mu je ɗin mu ji kiran me yake mana." 

"Amma Inna...."

"Ki tashi mu tafi kawai, ba na son jan maganar nan taki."

Ba ta kuma magana ba ta tashi kamar za ta yi kuka ta zira takalmi Inna ta kama hannunta suka tafi. Sashen matansa suka je, suka tarar da su zaune har da Iya. (Yawale Yayan Malam mijin Su Inna ne, Babansu ɗaya, ɗan Iya ne shi, duk mazan gidan a yanzu shi ne Babba.) Bayan sun yi sallama suka nemi guri suka zauna duk da ba wanda ya amsa musu sallamar, cikin ladabi Inna ta gaishe da Iya, ba tare da ta amsa ba ta fara magana cikin masifa.

"Sannu Asabe, yanzu tsabar mugun hali da tsiya a ce ɗannan ya dawo har ya yi kwana uku amma ke da ƴarki ku kasa zuwa yi masa sannu da zuwa?" 


Shiru Inna ta yi ba ta ce komai ba, A'isha kuwa dama ɗauke kanta ta yi kamar ba ta gurin, sai turo baki gaba take." 

"Ai ban isa ba Iya, kina ganin yanzu ma sun shigo ko arziƙin gaisuwa ban samu daga gare su ba." Yawale ya faɗi haka yana jifan da Inna da mugun kallo.


Wani kallo Inna ta watsa masa, amma still ba ta yi magana ba. Hangame baki Iya ta yi ta ce. "Iyee, samun guri, lallai Asabe, muna magana kin mana shiru, wato ga yan iska marasa aikin yi ko?"

"Ai su ɗin ne."


 A'isha ta faɗa ƙasa-ƙasa. Hararar ta Inna ta yi don ta ji ta sarai, ba yabo ba fallasa ta ce. "To Iya ku yi haƙuri." Ƙwafa Iya ta yi tare da jan tsaki. Cikin gadara Yawale ya ce. "Na dawo na samu wani labari da sam bai yi daɗi ba Asabe, wato har yanzu ba za ku daina bin mutane kuna ci musu sassan jiki ba ko?" Kafin Inna ta yi magana A'isha ta fashe da kuka tare da faɗin. "Mu ba ma cin mutane, kuma......" 


Marin da Iya ta wanka mata ya sa ta yin shiru tare da dafe ƙuncinta, da sauri Inna ta kalli Iya, duk haƙuri da kawaicinta amma kana kallon fuskarta ka san yau an kai ta bango, don ɓacin rai ne kwance a cikinta.

"Ko za ki rama mata ne da kike kallo na haka?" Iya ta faɗi haka kamar za ta kai mata marin ita ma.


Ɗaya daga cikin matan Yawale ta ce. "Ai sai ta aikata, kin san su mayu ba kunya gare su ba, mu dai muna ta li'ilafi, aniyar mutum ta bi shi, kuma naman jikinmu ɗaci gare shi ba ciyuwa za mu yi ba, ato." Wani abu mai ɗaci ne ya zo ya tokare wuyan Inna, magana take so ta yi amma ɓacin rai ya hana ta, rungume A'isha dake kuka kawai ta yi tare da ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi. 

Cikin karkaɗa ƙafa da muzurai Yawale ya ce. "Abin da ya sa na aika a kira ku ba komai ba ne sai don na sanar da ku cewa na karɓi kuɗin baikon A'isha daga hannun Tsoho Makawo ɗazu da yamma, mun kuma tsayar da ranar ɗaurin Aure ni da shi sati biyu masu zuwa, ranar juma'a bayan an sakko daga masallaci za a ɗaura auren, don haka sai ku fara shiri." Ya yi maganar cikin sigar bayar da umarni.........✍️