19.
by @zeeykumurya
KOMAI NISAN DARE
19.
Zeey Kumurya
Cikin rashin fahimta Inna ta ɗago kai ta dube shi ta ce. "Ban gane ba Yaya? Wacce A'ishan kake nufin ka karɓi kuɗin Auren ta?"
"A'isha nawa muke da su a gidan nan da kike da iko da su wanda zan saka a kira ki don na sanar miki batun auren su? Wannan dai makauniyar dake gabanki ita nake nufi."
"Tabɗijan! Tatsuniya ma kenan, to wallahi ba zan aurar da ƴata ba a yanzu, kuma babu wanda ya isa...."
"Ke Asabe saurara!"
Iya ta katse ta cikin tsawa sannan ta cigaba da magana. "Don ma kin samu Tsoho makahon ya taimake ku ya ce zai aure ta shi ne za ki yi wa mutane iskanci? Ƴar taki Shegiya mara asali za ki yi wa mutane firfita a kan ta? To wallahi wannan auren tamkar an yi an gama."
Cikin bushewar zuci da tsantsar ɓacin rai Inna ta ce. "Ni kuma babu wanda ya isa ya aurar mini da ƴa ko wanene." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannun A'isha suka miƙe, wadda kukan da take na marin da Iya ta yi mata ya sa ba ta fahimtar abun da suke cewa. Wata dariya Yawale ya yi ya ce. "Me za ki iya in an aurar miki da ƴar? Wa kike da shi? Ƙarƙari ki ce za ki kai ƙara gurin Sarki ko? To Sarkin baya nan ya tafi umra, sai mu ga wa zai tsaya miki."
"Allah, shi ne zai mini katangar ƙarfe da duk wani mummunan ƙudirin ku a kan mu."
Inna ta faɗa a fusace, yau kam sun kai ta bango, duk haƙuri da kawaicin da take musu a yanzu ta ji ba za ta iya ba.
"Ni kuma in dai sunana Yawale sai an yi auren A'isha makauniya da Tsoho makaho."
Sai a yanzu A'isha ta fahimci abin da ake magana akai, da wannan kalaman na Yawale. Wata irin bugawa zuciyarta ta yi, ƙara volume ɗin kukanta ta yi cikin rawar murya ta ce. "Inna me na ji Baba Yawale yana cewa? Ni za a yiwa Aure?" Hawayen fuskarta Inna ta fara share mata tare da faɗin. "Ki kwantar da hankali, in dai ina raye babu wanda ya isa ya miki Auran dole, tunda babu wanda ya haifar mini ke." Ba ta jira sauraren tijarar Iya da Matan Yawale suke taya ta ba, ta ja A'isha suka fice daga ɓangaren.
"Inna don Allah mu bar garin nan, mu bar musu gidansu, kin san tunda Baba Yawale ya dawo rashin mutuncin da ake mana sai ya ƙaru."
A'isha ta faɗi haka cikin kuka.
Girgiza kai Inna ta yi cikin ɗacin rai ta ce. "Na fi ki gajiya da zaman gidan nan A'isha, dan dai babu yadda zan yi ne, kuma ina tunanin idan mun bar nan ba mu san ina za mu ba, ba mu san da waɗanda Allah zai ƙara haɗa mu ba."
"Ƴan'uwanmu mana, ko da gaske ba mu da su?"
"Muna da su, amma wani babban dalili ya sa ba zan koma gare su ba."
"Wanne dalili ne? Don Allah Inna ko sau ɗaya ne ki kai ni na gan su, tun ina ƴar ƙarama ake mini gorin rashin asali, tun bana damuwa har na fara damuwa duk da ban san me hakan yake nufi ba, yanzu na gane me ake nufi da rashin asali, na fuskanci me kalmar SHEGIYA take nufi, kamar yadda na gano ba Baba Malam ne ya haife ni ba."
Cikin tsantsar mamaki da damuwa Inna take kallon A'isha, a shekarunta ba ta yi tunanin za ta iya gane waɗan nan abubuwan ba a yanzu, musamman da har yanzu ɗabi'un yara sun fi yawa a tattare da ita a kan na manya, cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Wa ya faɗa miki ba Malam ne ya haife ki ba? Na ce ki daina mini wannan zancen ko, don ba gaskiya ba ne, Malam shi ne mahaifinki." Cikin matsanancin kuka ta ce. "Ki daina ɓoye mini Inna, na riga na gane gaskiya, amma don Allah ko ba za ki kai ni na ga ƴan'uwanmu ba ki taimaka ki ba ni labarin su, da dalilin baro su da kika yi."
"Zan faɗa miki, amma ba yanzu ba, domin har yanzu ke yarinya ce, ƙwaƙwalwar ki ba za ta ɗauki labarin ba balle har ta ba ki damar fuskantar shi, amma da sharaɗin ba za ki kuma tambaya ta ba har sai lokacin da na ga ya dace na faɗa miki da kaina."
Gyaɗa mata kai kawai ta yi tare da kifa kanta a kan cinyarta ta cigaba da kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar duk mai sauraren shi.
Washegari da ciwon kai ta tashi, hakan ya sa Inna ta ce ta zauna kar ta je makaranta, ranar Monday idan ta kai ta sai ta sanar da Malaman ba ta da lafiya ne ya sa ba ta zo ba. Da Yamma Inna tana ramuwar baccin da ba ta yi ba daren jiya ta ji muryar Namiji yana magana a kanta.
A firgice ta tashi tare da rarumar hijabinta dake kusa da ita ta saka, Yawale ta gani ya ƙura mata ido yana bin ta da wani irin kallo. Haɗe rai ta yi cikin ɓacin rai ta ce. "Mene ne haka Yawale? Ya za ka shigo mini har ɗaki babu neman izini, a kan me?"
"Saboda gidanmu ne ina da ikon shiga duk inda na ga dama."
"Ko kai ka gina sashen nan ka ba ni haya ba ka hurumin faɗo mini har cikin ɗaki ba tare da neman izini ba, don haka kar ka ƙara yi mini irin wannan ba na so, idan kuma ba haka ba wallahi hukuma ce za ta raba mu!" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. Dariyar rainin hankali ya yi ya ce. "To hukumar ta raba mu mana Asabe?"
Tsaki Inna ta ja tana ƙara gyara hijabin jikinta ta ce. "Ka tashi ka fitar mini daga ɗaki Yawale." Gemunsa ya shafa cikin shigar duniyanci tare da faɗin. "Ba ke kika saka na shigo ba, don haka ba ki isa kin sa na fita ba, A'isha na zo kira dama, Tsoho makaho ne yake jiran ta a soro za su yi taɗi."
Kallon ba ka da hankali Inna ta yi masa ta ce. "Dama a kan wannan shirmen ka shigo mini har cikin ɗaki ina bacci? ban da, da wata manufar a ranka da ka shigo gidan ba ka ga A'ishan kwance a tsakar gida ba? Yawale ka ji tsoron Allah, ka tuna za ka mutu fa, duk abubuwan da kake yi Ubangiji yana kallon ka."
"Har kura ce za ta ce wa kare maye? Ke har kin isa ki yi mini wa'azi Asabe? Ke da kike tattare da abin kunya, SHEGIYA fa kika ajiye, ai ke kika cancanci wa'azi ba ni ba."
Miƙewa Inna ta yi ba ta kuma magana ba, don ta fuskanci neman magana kawai yake da ita. Ficewa ta yi ta bar masa ɗakin zuciyarta na mata wani irin zafi, ta gaji da cin zarafin mutanen gidan nan, rashin dajarar ta har ya kai ƙaton mutum ya shigo mata ɗaki ba excuse tana bacci ya gama ƙare mata kallo, Gaskiya dole ta san abin yi, ba za ta ɗauki wannan akuyancin da jahilcin ba, musamman da ta daɗe da gane ƙudirin Yawale a kanta.
"Ke A'isha tashi mu je tsoho makaho yana jiran ki, ko ba kya ji ne? Ƴar bantan Uba kawai."
Yawale da ya fito daga ɗaki ya faɗi haka cikin masifa.
Ko motsi A'isha ba ta yi ba, duk da tana jin shi sarai, Hararar shi Inna ta yi ta ce. "Babu fa inda za ta, Yawale tun wuri ina shawartarka da ka ruguje wannan maganar Auren mara ma'ana, ban da zalunci yarinyar da ko shekara goma sha biyar ba ta cika ba ita ake ƙoƙarin aurawa Tsohon da ko ni ba zan aure shi ba? Tsohon ma mara mutunci da rashin sanin darajar ɗan Adam, ya mayar da aure ba a bakin komai ba, waye bai san Auri saki yake ba kaf garin nan, wato yanzu an gane halinsa an daina ba shi Auren shi ne zai zo nan, ni kuma da ban san ciwon kaina ba sai na ɗauka na bayar, to wannan ɓatan basiran ba da ni za a yi ba."
"Duk rashin mutuncin shi amma ai yana da asali ko?"
"Wannan ku ta shafa ba ni ba."
Jinjina kai Yawale ya yi ya ce. "Kuma yarinya tunda tana zaune a cikin gidanmu tana cin arziƙin mu muna da ikon aurar da ita ga duk wanda muka so."
"Tunda wata tsiyar kuke tsinana mata ba, gata nan ga ka, ka daura mata Auran mu gani."
"To mu zuba mu gani, ni da ke ɗan halak ka fasa." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa da sashen, Inna ta raka bayansa da harara.
Cikin jin daɗin yadda Inna ta yi wa Yawale tatas A'isha ta ce. "Gwara da kika yi masa haka, gobe ba zai dawo ba."
Sai dai maganar A'isha ba ta tabbata ba, don kullum sai Yawale ya zo kiran A'isha akan ta fita gurin tsoho makaho, Inna kuma ta murje idonta ta ce bai isa ba, ba za ta je ba. Tun mutanen gidan ba sa fuskantar abin da yake Faruwa har suka fara fuskanta, nan fa suka yi caa a kan Inna, suna cewa don ma sun samu Tsohon ya taimake su ya ce zai auri ƴar tata take ƙi? Har da masu cewa ba ƙaramin jihadi Tsoho makahon ya yi ba da ya ce zai auri A'isha. Ba ta kula su, ta dage da kaiwa Ubangiji kukanta, don zuciyarta cike take da fargaba da tsoro, sanin halin Yawale ta san dagaske yake zai aura wa A'ishaTsoho makaho, a haka har kwanaki goma suka shuɗe.
Da yamma Inna ta ɗauko A'isha daga makaranta, suna tafiya tana ba wa Inna labarin wani sabon Malami da aka kawo musu daga Kano.
"Yawwa ga su nan ma sun dawo."
Muryar Yawale ta doki dodon kunnansu da faɗin haka lokacin da suka shiga zauren gidansu. Su tsoro ma ya ba su, saboda yadda ya yi maganar a hanzarce.
"Sannun ku da zuwa, ina A'ishushuwan tawa?"
Tsoho makaho dake zaune a kan tabarma ya faɗi haka yana shafa tumbinsa.
Tsaki Inna ta ja cikin takaici ta kama hannun A'isha suka yi gaba.
"A'a, Asabe ya za ki ja ta ku tafi kuma? Kin san daɗewar da muka yi muna jiran ku kuwa? Ki zo magana Malam Tsoho ya zo mu yi fa." Ko waigowa Inna ba ta yi ba balle ya saka ran za ta tsaya. Giwa a saɓule ya ce. "Ka yi haƙuri Malam, haka nake ta fama da su, daga uwar har ƴar taurin kai gare su, amma bari na je na saka su fito." Murmushi tsoho makaho ya yi, cikin washe dafaffun haƙoransa ya ce. "Babu komai ka ƙyale su, rashin fahimta ne, da zarar mun fahimci juna komai zai wuce, wuyarta a ɗaura mana Auren a kawo ta gidana." Ya ƙarashe maganar yana lalubar sandarsa. Bayan ya miƙe ya zira hannu a aljihu ya zaro kuɗi ya miƙa wa Yawale, hannu na rawa ya karɓa tare da washe baki ya ce. "Malam ba ka gajiya da abin arziƙi, Allah ya saka da Alkhairi ya ji ƙan mahaifa."
"Amin, babu komai, ai ni ka gama yi mini komai tunda ka ba ni Auren yarinyar nan, don yadda na ji ana faɗar kyawun surarta na san zan mori kuɗina."
Cikin dariya Yawale ya ce. "Za kuwa ka mora, don yarinyar a dire take dumurmur, sai dai an kai mata ita za ka tabbatar da abin da nake faɗa." Murmurshi Tsoho ya yi ya ce. "Madalla, haka ake so, yanzu bari na wuce gida, anjima su Nalami za su kawo kayan lefen, su kuma masu jere za su iya zuwa gobe, an gama gyara gurin amaryar."
"Toh Allah ya kai mu, bari na kira maka Mamman ɗin ko?" Yawale ya faɗa tare da fita ƙofar gida, inda ɗan jagoran Tsoho yake zaune yake jiran shi.
Tunda suka shiga gida A'isha take kuka, cikin kwanakin nan ta mayar da shi sana'arta, gabaɗaya ta lalace ta yi baƙi saboda damuwa da saka a ranta, a kodayaushe cikin rarrashin ta Inna take da nuna mata wannan Auren ba mai yiyu ba ne, amma ta kasa yarda da hakan, saboda ta san in dai suna cikin gidan nan to babu abin da zai hana Yawale aiwatar da abin da ya yi niyya, dama da Sarki yana nan ne zai iya tsawatar masa, shi kaɗai ne suke da tabbacin zai hana shi kaf cikin garin ya hanu.
Da daddare kamar yadda Tsoho makaho ya faɗa sai ga kaya an kawo a cikin leda Viva, atamfa Leda guda biyu da shadda wanke kuɗinka guda ɗaya, pant da shimi bibbiyu, da takalmi soso guda ɗaya, sai ƙullin su powder da man shafawa a wata baƙar leda daban. Yadda aka zube kayan a tsakar gida matan gida na gani haka Inna ta tashi ta bar su a gurin cikin tsananin baƙin ciki, ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba da ganin kayan, don hakan ya tabbatar mata dagaske fa Yawale yake aurar da A'isha zai yi. A'isha kuwa tsabar kuka har shiɗewa ta dinga yi, yadda suka ga rana haka suka dare, don jikinta rikicewa ya yi da zazzaɓi mai zafi gami da ciwon kai.
Washegari ta tashi jikin nata ya tsananta, hakan ya ƙara tayar da hankalin Inna, ga ba ta da kuɗin siyo mata magani, abun ya taru ya yi mata yawa, so take ta samu space ɗin da za ta yi tunanin mafita akan ganin auren nan bai yiyu ba, amma yanayin jikin A'isha ya sa ba ta da nutsuwar hakan....