ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 4

by @ibtisamwrites01

***

https://www.arewapen.com/book?id=6ab8fc22c237adaad549e3a2


***

………………….
                          ZAREN ZUMUNCI
                 (The thread of family bond)

                               WRITTEN 

                                    BY

                       IBTISAMWRITES ✍️







PAGE 4
 
Yaran gaba ɗaya kusan a ɓangaren Mammi (Haj. Lubna) suke rayuwa saboda ita ba ta hana su yin duk abin da za su yi. Ba ta saka su aiki ko ta ce su tashi su shiga kitchen don su daura girki.
 
Duk masu aiki ke yi musu, so sun fi son zaman can ba takurawa. Amma ɓangaren Mami (Hajiya Zainab) kam ba a cewa komai, don ita ba za ka shigo ɓangaren ta ka ce za ka zauna haka kurum ba. Dole ne ka yi aiki. In a time ɗin ma ka shigo an gama girki, to fa sai ta saka ku gyaran ƙwaba, shara, mopping, har wanki toilets.
 
Shi yasa ba sa zama a side ɗin ta. Gari na waye wa suke komawa ɓangaren Mammi. Ita ke biye musu su yi duk abin da suke so, ba ta takurawa.
 
Ita Mammi ma, in taga mood ɗin su is off, ita ce mai ba su kuɗin su je shopping ko su sha ice cream.
 
Haka rayuwar su take gudana tun bayan dawowar su daga Spain.
 
Bayan komawar Hajiya Zuwairah gidanta, bayan ta yi duk wani abu da ya kamata ta yi, sai ta nemi wuri ta zauna, sai ta ɗan faɗa tunani na abin da ya faru ranar.
 
Ta kula da yadda yaran suka tarbi juna cikin mutuntawa. Duk da Fauziyya ce kawai suka je da ita, amma kuma sun ɗauke ta kamar tasu.
 
Sannan ta yaba da hankali da nitsuwar su, sai kawai wani tunani ya darsu a zuciyar ta, sai wani murmushi ya kubuce mata kamar wadda ta ci lottery.
 
Sai ta ji magana daga sama ta ɗan firgita ta dawo reality. Ashe mai aikin ta ce ke mata magana akan ta gama girkin kuma ta jera a dining.
 
Haj. Zuwairah na cikin mood ɗin da ba za ta yi fada ba, sai ta ce mata ta fi, shikenan.
 
Amma da mood ɗin ta is off, ai kafin ta gama maganar ma ta sauke mata nata rabo.
 
Ya ki jinin in tana zaune ita kaɗai ka shigo ka yi sallama ba ta amsa ba, kuma ka shigo ba ta bada izini ba. Shi yasa kowa ma yake taka-tsantsan a gidan, saboda rules ɗin ta suna da yawa.
 
Wannan ɗin ma mai aikin ce ta ga kamar ba ta motsi, shi yasa ta shiga. Amma ashe tunani take yi.
 
Bayan ta sallami mai aikin nata, sai ta tashi tana zirga-zirga tana tunanin ta yaya za ta fara yi wa mijin ta wannan magana and ta yaya zai karɓe ta?
 
Duk ba ta sani ba. A haka dai ta yanke hukuncin za ta yi masa maganar in ya dawo daga office.
 
Alh. Aliyu ya dawo daga office da yamma, amma ba ta yi masa maganar ba sai in za su kwanta bacci tukunna.
 
Haka lokacin sallah ya yi, ya tafi masjid, bai dawo ba sai da aka yi Isha sannan ya dawo.
 
Wajen 10 sun gama shirin bacci, sai Inne ta ce wa mijin nata tana da wata magana da take da ita, amma ba ta san ta yaya zai ɗauki maganar ba.
 
Ya ce ta faɗa ya ji menene, tukunna kar ta yanke hukuncin ba zai karɓa ba kai tsaye.
 
Haka ta faɗa masa tunanin da ta yi a kan ra’ayin ta, ko in ce burin ta, na son haɗa ’ya’yan su da na Alh. Lawal aure.
 
Ta ce ta yaba da hankalin su da nitsuwar su, shi yasa take da burin haɗa zuri’a da su.
 
Alh. Aliyu yayi shiru, ya ce ta je zai yi tunani akan maganar.
 
Wajen sati biyu kenan da Inne ta yi wa Abba magana, amma be ce mata komai ba har yanzu.
 
Ita kuma dai ta yi ta ƙoƙarin ta kar ta tuntube shi, amma abu ya ci tura.
 
Yau dai ta ce za ta tambaye shi ta ji ina maganar ta kwana.
 
Abban na zaune a falo yana cin abinci bayan ya dawo daga fitar da ya yi. Inne kuma na daga gefen shi a zaune.
 
Ta ɗan yi shiru, sai ta ce,
 
“Abba, daman ina ta jiran na ji ka yi min magana akan zancen da muka yi kwanaki, amma kuma na ji har yanzu shiru. Ba ka ce komai ba.”
 
Ibtisamwrites✍️