ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )
PAGE 5
………………….
ZAREN ZUMUNCI
(The thread of family bond)
WRITTEN
BY
IBTISAMWRITES ✍️
PAGE 5
Abban ya kurɓi ruwa kana ya ce,
“Ina da niyyar dama,in faɗa miki abin da na yanke, amma ga shi kin kasa haƙuri sai da kika tambaya.”
Inne ta yi murmushi dai ta ce,
“Tun da ka yi niyyar faɗa ɗin kawai ka faɗa min in san yaushe zan fara shiri.”
Can ABBA ya ce,
“Na yi tunani a kai, akan abin da kika faɗa. Kin yi tunani mai kyau.”
Sai ya ɗan tsaya. Ita ko Inne tana ta murmushi, ma burin ta ya kusa cika.
Sai Abban ya kuma cewa,
“Amma ya kamata kafin a kai kan matsaya sai an fara tuntubar yaran tukunna, a ji ta bakin su kafin ayi komai.”
Buɗe baki da Inne ta yi sai ta ce,
“Aa Abba, ai ba sai an nemi shawarar su ba. Sun san dai ba za mu yi musu zaɓan tumin dare ba.”
Abban ya girgiza kai ya ce,
“A’a, kin san bana son yi wa yara na dole. Ki kira su duka nan sai mu ji ta bakin su duka.”
Inne ta yi jimm, sai ta ce,
“Haba Abba, ka bari. Ni zan yi musu magana kawai, kar ka damu.”
Ya dago ido ya kalleta zai yi magana, ta ce,
“Ba ka yarda da ni din zan yi abin da ya da ce bane, Abba?”
Sai ya ce,
“Me ya kawo wannan maganar kuma?”
Sai kawai ya girgiza kai ya ce,
“Shi kenan, amma kar ki musu dole.”
Ya yi mata sai da safe ya tafi ɗaki.
Washegari da safe ta kira su a waya ta ce after sun dawo daga office tana son ganin su duka.
Suka amsa mata da,
“Toh, Inne.”
Daga nan ta ɗaga waya ta kira autar ta Fauziyya ta ce tana son magana da ita, ta zo ɗaki yanzu.
Ta ce,
“Okay, Inne. I’m coming right away.”
She came to the room, knocked and waited for permission to enter.
Sai Inne ta amsa daga ciki ta ce,
“Shigo, auta.”
Fauziyya ta shiga cikin ta ce,
“Here I am, Inne.”
Her face full with smile.
Inne ta ce,
“Samu wuri ki zauna. Fauziyya, ina son nayi magana da ke.”
Fauziyya, sensing the seriousness on her mother’s face, sai ta zauna tana jiran jin abin da za ta faɗa.
Inne ta ce,
“Da, ina son sai duk kun haɗu sai in yi maganar, amma kuma na kasa in jira. Na ce bari in fara yi miki albishir ɗin kafin sauran su dawo.”
Ita ma da dan murnar ta, ta na jiran ta ji me inne din zata ce.
Anan ne Inne ta saki bomb ɗin nan.
Fauziyya jin wannan zance sai tayi sak, tana kallon maman nata.Saboda bata taba tsammanin cewar abin da zata fadi kenan bah.
Kafin tayi magana sai Inne ta ce,
“Tun ranar da na je gidan na gan su, sai na kwaɗaita ta tarbiyyar da suka samu. Shi yasa nake muku kwaɗayin su.”
Fauziyya za ta yi magana sai Inne ta ce mata ta tashi ta tafi, kuma kar ta ce za ta kira brothers ɗin ta ta gaya musu.
Ta bari in sun dawo da kansu za ta faɗa musu.
Haka ta tashi jiki ba ƙwari ta bar ɗakin ta koma nata.
Tun da ta koma ta kasa yin komai. Ta yi shiru tana tunani, sai dai tana jiran brothers ɗin nata su dawo ta ga waye zai fara yi wa Inne gardama, daga nan ita ma sai ta faɗi nata ƙorafin.
Da dare ya yi sai ga su Yaya Kabir sun shigo ɓangaren Inne saboda su ji me yasa ta kira su da safe ta ce tana neman su in sun dawo.
Suna zaune a parlor suna hira sai ga Inne nan ta shigo. Duk suka yi mata gaisuwar dare kafin kowa da nashi tunanin na yau.
Inne na cikin farin ciki saboda ya bayyana a fuskarta.
Suka ce ko ma mene ne, yana da nasaba da maganar da za ta faɗa musu.
Bayan ta zauna sun gama gaisawa sai ta nemi wuri ta zauna. Ta duba ta ga ba ta ga Fauziyya ba, ta ce wa Larai, mai aikin ta, ta kira mata ita, kuma ta taho tare da ita.
Duk suka zuba mata ido suna jin me take faɗa. Ba wanda ya ce komai, duk da deep down suna son su san me ke faruwa, don zuciyar su ta tiga da ta ba su. Akwai wata matsala, amma ba su san mecece ba.
Suna haka sai ga Fauziyya nan ta fito, amma kuma sun lura kamar ba ta cikin kuzarin ta da suka san ta da shi.
Za su tambaye ta me yake damun ta, sai suka ji Inne tayi gyaran murya ta ce,
“Ku bani hankalin ku nan da tunanin ku.”
Duk suka dago da kansu suka zuba mata idanu.
Inne ganin haka sai ta fara cewa,
“Ni da mahaifin ku mun zauna, mun duba, mun bincika, kuma mun ga hakan ya dace. Ya kamata kuma a sanar da ku.”
Duk sai suka shiga cikin ruɗu da jin wannan magana.
Kafin su gama processing ɗin ta sai suka ji ta ce,
“Mun yanke hukuncin cewa za mu haɗa ku da ’ya’yan Baba Lawal aure.”
Inne ta saki bomb ɗin kuma ta haɗe rai, kar ma su ce za su yi ƙorafi.
Suma ganin babu fuska sai suka kasa cewa komai. Kowa yana saka yana warwarewa.
A cikin thought ɗin da suke, wani na cewa aure, wani na arranged marriage, wani yana kai, amma duk ciki babu wanda zai iya ja da maganar Inne.
Sun san ma in sun yi maganar, ba abin da zai canza.
Ana wannan zaman sai kawai suka ji Aliyu, ƙanin su, ya yi gyaran murya ya ce,
“Ina da magana, Inne.”
Kowa sai da ya dago kai ya kalle shi har Inne ɗin, amma kafin wani yayi ƙoƙarin hana shi ya ci gaba da cewa,
“Ba wai ba zan bi abin da kika ce ba ne, ba kuma zan yi gardama da ke ba akan hakan. Amma ni ina da wadda nake so, kuma ita nake so na aura, kuma na zauna da ita har abada.”
Ibtisamwrites✍️