THE THRONE OF THORNS

THE DARKNESS BENEATH

by @maryam730

Numfashi mai nauyi ta sauke tana nufar ƙofar ta buɗe, buɗewa tayi tana fita da ƙafar ta ta dama bakin ɗauke da bismillah.
‎
‎
‎‎Wacce tayi mata knocking ɗin ce ta fara yin gaba ganin ta fito.Bin bayan ta tayi tana danna kiran wayar Ummu, Husna ce ta ɗaga kiran sakamakon tashin ta da ringing ɗin wayar yayi,inda Atti ta umarce ta da ta kaiwa Ummu.Itama Husnar cikin hanzari ta nufi gurin Ummu da ta fito da ga toilet,miƙamata tayi ta cewa Adda ce,cikin hanzari Ummu ta yi saurin ɗora wayar a kunne ta tana cewa "Maleekah"
‎
‎
‎Amsawa Atti tayi da murmushi akan fuskarta tana cewa,"Ummu a taya mu da addu'a yanzu zamu shiga".Murmushin ƙarfin hali Ummu tayi daga can tana cewa "Allah ya tsare ya dawo min da ke lafiya, ki kula da kanki, ki kula da lafiyar ki banda wuce gona da iri banda shiga abinda be shafe ki ba nasan ki".
‎
‎ƙaramar dariya Atti ta saki tana cewa "toh Ummuna sai kuma mun fito ko an fito da mu ta faɗa da zulaya tana saurin katse kiran sakamakon ƙarasowar su dai dai wani ɗaki, dan tasan yanzu Ummu zata balbaleta da faɗa.
‎
‎
‎Matar ce ta tsaya a gurin alamar iya nan ne zata iya zuwa.Murɗa ƙofar Atti tayi tana shiga ciki,ɗakin shiru ko sautin numfashi da taka tsantsan suke fitarwa.Gaba ɗaya duk an hallara ita kaɗai ake jira,ƙarasawa tayi ta zauna kusa da wata wacce suka zauna guri ɗaya ɗazu.
‎
‎
‎Batayi minti talatin da shigowa ba sai ga wasu dogaye murtuka-murtukan ɓaƙaƙen samudawa,sun kame cikin suit ɓaki da wani tambarin kan zaki maƙale a gefen aljihunsa.
‎
‎
‎
‎Babu ko ɗigon rahama ko sauƙi a tare dasu.Wani ƙaton akwati da suka zo dashi ne suka buɗe suna fito da dogayen siraran ɓaƙaƙen ƙyallaye ne da kuma wannan tag ɗin da ke jikin su.
‎
‎Hajiya Jamila da Mr Samuel ne suka shigo cikin sauri dan sun san cewa su Atti ba susan hatsarin mutanen da suke ciki ba gashi basason tun yanzu a fara samun matsala,shiyasa suka zo a rikice dan kula da komai.Tsayawa suka yi a gefe bayan sun shiga.
‎
‎
‎Wannan tag ɗin aka fara rarraba musu,inda aka umarce su da su maƙala shi jikin rigar su.Cikin hanzari kowa ya maƙala kamar yacce mutanen suka umarata.
‎
‎
‎Bayan sun saka ne aka jera su a layi. Idan layi yazo kanka zaka saka wayarka da duk wani abu harda agogo,zobe da ɗan kunne a cikin wannan akwatin,sannan ayi scanning ɗinka da wata na'ura (metal scanner).Ana gama caje ka sai kayi gefe.Haka aka gama caje su gaba ɗayansu.

‎
‎Cikin wata tsawa mai firgita zuƙata wanda yake kamar ogan su ya fara yin magana cikin kaushin murya yace,"Ku sani inda zaku shiga gurine na rai ko mutuwa,gurine na iyayen shegu dan haka in ma zaka shiga da wani mugun ƙuduri a zuciyar ka ka cire ka yar tun anan dan ba inda zai kaika sai gadar dana sani,kuma a kashe ka an kashe banza ko gawar ka baza'a gani ba ".
‎
‎
‎Tuni jikin wasu a cikin su ya ƙara dau kar kyarma ,eh sun sani in da zasu ya na da hatsari sosai amma yacce a tsakanin yau ake ta maimaita zancen mutuwa ne ya tashi hankalinsu sosai,amma ba yacce suka iya dan NO WAY BACK.
‎
‎
‎Wacce suke zaune guri ɗaya da Atti ce tun meeting ɗin farko ce hannun ta keta mazari,gaba ɗaya jikin ta ya jiƙe da gumi tun kafin a je ko ina.
‎
‎Atti ce ta ɗora hannun ta akan hannun yarinyar, saurin razana yarinyar tayi inda Atti ta ɗan ƙara riƙe hannun ta ɗan ƙarfi,tana ɗan jijjiga mata kai alamar ta kwantar da hankali ta, tare da lumshe idonta wanda yau ya ƙara wani haske sai sheƙi yake kamar diamond.A hankali jikin yarinyar ya daina rawa,kafin ta jiyo ta sakarwa Atti murmushi,itama ta mayar mata.
‎
‎
‎
‎Bayan ya gama maganar ne aka ɗakko wannan baƙaƙen ƙyallayen.Sai a sannan ne suka gane me ake shirin yi misu wato rufe musu ido za'ayi (blindfolding),abunda ya sosawa zuciyar wasu daga cikin su wanda ya haɗa har da Atti.
‎
‎Saboda ƙarara an ɗauke su kamar bayi,bata tsinkewa al'amarin ba sai data ga an ɗakko wata igiya doguwa kamar wacce ake ɗaure shanu da su.Kuma da alama ɗaure musu hannaye zaa yi kamar wasu dabbobi da ake tsoron guduwar su.
‎
‎
‎Haka aka zauna aka fara daure hannayensu gaba ɗaya da igiya ƙwalli ɗaya, wannan yarinyar ce ta ɗazo yanzu ma a gaban Atti idonta ya cika taf da ƙwalla.Zuwa akayi aka fara ɗaure musu ido da wannan ƙyallayen inda haske ya gushe musu duhu na mamaye shi.
‎
‎
‎Ganin sun gama komai ne yasa suka kuma ƙirgasu su ashirin ne cif.Har haɗe kayan su su kayi suma .
‎
‎
‎Ogan su ne ya fito da wata ƴar box ta kan zaki itama,Hajiya Jamila ce ta miƙo mai wani key ya saka ajiki,kafin shima ya ɗakko wani key ɗin kalar wancan san ya kuma sakawa,yana ajje ta akan tebur ɗin.Motsi ta fara da kanta tana buɗewa har ta gama buɗe wa wani card ♦️ya fito.
‎
‎
‎Card ɗin ya ɗauka yana nuna shi jikin bango,nan da bangon ya fara tsagewa kamar almara ƙofa ta bayyana.Gaba yayi yana ɗaukar wannan igiyar ya fara jansu kamar wasu awaki ya nufi ƙofar dasu inda yaransa suka take musu baya,kuma anan ne su Hajiya Jamila suka ja birki ita da Mr Samuel dan iyakar su kenan.
‎
‎
‎Wani ƙaton daki su ka shiga babu ko tsinke a cikin sa kafin su ja wannan ƙofar suka rufi ta ƙofar na ɓacewa kamar bata taɓa wanzuwa ba bango ya bayyana .
‎
‎
‎
‎Bayan sun shiga ɗakin ne ogan again ya ƙara danna wani maɓalli nan danan ɗakin ta fara girgiza yana yin ƙasa dirrr dirrr,tuni suka fara ihu.Ogan nasu ne ya juyo yana kallon Atti wacce ko ɗaga ɗan yatsanta batayi ba da sunan tsoro,ƙure ta yayi da kallon al'ajabi na ya ce ko kaɗan bata nuna alamar ko ɗar ba,har daƙin ya daina jijjiga alamar sunzo.
‎
‎
‎ƙofar ɗakin ce ta kuma wangalewa amma wannan karan a wani duhu baƙiƙirin suka sauka,sai da suka fita na gane ashe elevator ce mai kamar ɗaki suka shiga.
‎
‎
‎Wani surƙuƙin dogon lungu ne kamar a daji mai duhu da ko tafin hannun ka bazaka iya gani bane suka shiga .
‎
‎
‎ Amma dake su dama a cikin duhun suke sai basu lura ba,sai su ogannin ne suka kunna wasu fitila amma duk da haka duhun bai gushe ba suna dai iya gannin inda suke takawa.Tafiya miƙaƙiya kamar ba zata ƙare ba suke,duk sun galaɓaita tun ba'a fara komai ba sun fita hayyacin su.
‎
‎
‎Bayan sun kwashe sama da minti 40 suna tafiya a wannan lungun, sannan suka zo wata doguwar ƙofa da akayi da narkakken ɓakin ƙarfe.
‎
‎
‎Ogan bai yi wata wata ba ya ciro wata aska yana yanka tsakiyar hannun sa nan da nan jini ya bayyana.Jikin wani circle a ƙofar yasaka kamar tsafi ƙofar ta fara juyawa har ta buɗe kanta.
‎
‎
‎Wani haske ne ya musu sallama da tashin kiɗe-kiɗe daga ɗan nesa da su kaɗan,alamar sun kusa ƙarasowa.......end of chapter 13..... written by Muraimaa Naabba ✍️✍️✍️.....
‎