ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 6

by @ibtisamwrites01

………………….
                  ZAREN ZUMUNCI
            (The thread of family bond)

   
                     WRITTEN 

                            BY

                  IBTISAMWRITES ✍️

  



PAGE 6
 
Shiru ne ya wanzu a wurin na kusan minti talatin haka.
 
Ita Hajiya Zuwairah da ’yan uwansa ba su taɓa kawo wa a ransu wai a cikin su za a samu wanda zai iya yin magana a gaban Inne ba. Idan ta yanke hukunci irin wannan, sai dai su yi biyayya kawai, ko da ba sa so.
 
Ga baki ɗaya Hajiya Zuwairah ta yi shiru ta zuba masa ido. Tana son ta gani, shin da gaske ne wai Aliyu ne yake ce mata yana da wacce yake son aura kuma ya zauna da ita har abada, kuma wai a gaban idonta, bayan ta zo ta ce musu ga tsarin ta, ga yadda take so ayi?
 
Ta yi ɗan jim, sai ta ce,
 
“Aliyu, wace ce kake son ka aura? Kuma waye ubanta a ƙasar nan?”
 
Dukkan su ba su yi tsammanin cewa Inne za ta yi tambaya akan abin da Aliyu ya zo da shi ba, amma sai abin ya ba su mamaki matuƙa.
 
Shi kuwa Aliyu, cikin jin daɗi da farin ciki, ya ce,
 
“Sunanta Amna. Ba a ƙasar nan suke ba. A India take, inda na je karatu muka haɗu a can. Sannan babanta babban mai kuɗi ne a ƙasar India, sannan kuma ana ji da shi a can kuma—”
 
Sai kawai cikin tsawa ta ce,
 
“Rufe min baki!”
 
“Nan dama da kake maganar kana da wadda kake so ɗin, ba a ƙasar nan take ba ma, a wata ƙasa take? To, ba zai taɓa yiwuwa ba. Kana jina ko? Ka buɗe kunnuwanka da kyau ka ji ni. Ba kai, babu ita! Na gaya maka ka cire wannan tunanin a cikin zuciyar ka. Na faɗa maka!”
 
Tana gama faɗin wannan maganar, Inne ta ce wa kowa ya tashi ya bata wuri. Ita ta gama magana, kawai su fara shirye-shirye.
 
Ta tashi ta basu wuri, suka dai kowa na kallon ɗan uwanda ya kasa cewa komai, sai kawai suka tashi suka tafi ɓangaren su. Kowa yana da bukatar ya yi tunani.
 
Haka suka kwana cikin wani yanayi da ɗayan su ba zai ce ga shi ba.
 
Washegari suka amso suka gaida Inne, amma ta amsa musu kaɗan-kaɗan, a cewar ta kar ta sake su zo su fara mata ƙorafi.
 
Kowa ya fita babu daɗi dai. Shi ko Aliyu da ya shigo ko “Sallama” ma ba ta amsa ba, bare gaisuwa. Haka ya ƙaraci zaman sa ya tashi ya tafi aiki.
 
Ta kai ta kawo, an yi 2 weeks Inne ba ta amsa wa Aliyu gaisuwar sa.
 
Da ya ga abin ba na kare bane, sai ya zo bata haƙuri ya ce,
 
“Inne, na san na yi miki laifi. Ki yi haƙuri ki yafe min. Amma kin san ban taɓa tsallake maganar ki ba, ko da kuwa abin nan bai min daɗi ba. Ban taɓa saba miki ba. Amma Inne, don rana ɗaya na faɗi abin da ke raina sai ace ya zama laifi?”
 
“Ya kike so in yi da rayuwata? Na faɗa miki ra’ayi na ne saboda bana son ko wace za a haɗa ni da ita ta cutu, nima na cutu, tun da bana son ta. Ina da wadda nake so.”
 
“Sai kuma ki daina kula ni. Inne, an yi min adalci anan.”
 
Shiru Inne ta yi tana sauraron sa, tana tunanin a ina Aliyu ya koyo mai da magana ne.
 
Sai kuma wata zuciyar tata ta ce, kin ba su damar su faɗi zaɓin su ne, ballantana ki gane waye mai iya faɗan ra’ayin shi da wanda ba zai iya ba.
 
Sai ta girgiza kai ta ce,
 
“Na ji Aliyu. Duk abin da ka ce, zaɓin nawa ne. Ba ka so ta shi ka fita.”
 
Ya ce,
 
“Inne, ki yi haƙuri.”
 
Sai Inne ta ce,
 
“Aliyu, ni can ce mun zaɓa maka mata, amma ka nemi ka bata min kan wata can da ban santa ba. To, shikenan na haƙura, amma ka ƙwana da cewa wannan aure babu faɗi. Tashi ka fice min daga nan.”
 
Haka jiki ba ƙwari ya tashi ya tafi.
 
Yana tunanin ta ina zai fara maganin matsalar da ke tunkaro shi.
 
Ibtisamwrites✍️