TAMBAYOYI DA SANARWA.
by @hafnancy
*MUHIMMAN TAMBAYOYI MASU TSAYAWA A RAI:*
•*Bayyanar DON KB ya nuna Jidda da Saffy basu haɗa alaka ta jini ba tunda FANSA yake neman ɗauka kan rayuwar Saffy da aka lalata ita kaɗai.*
*•Shin DON KB zai samu damar aiwatar da FANSARSA kan Samha?*
*•Ya batun AUREN Jidda da Yallabai? Kuna ganin haka zasu ci gaba da rayuwa a duhu ko kuwa zasu bayyanawa duniya auren da suka yi?*
*•Wacce JARABAWA ce mutanen Yallabai ke yi ma Jidda? kuna ganin zata lashe JARABAWAR har ta samu karɓuwa a wurinsu? kuma su karɓi juna biyun da take ɗauke da shi? Ko a ƘARSHE suna raba auren tun kafin duniya ta san da aurensu?*
*•Me zai faru idan Iyalen Yallabai suka gano alakar Jidda da Yallabai?*
*•Iyayen Jidda na nemanta ko kuwa sun yafewa duniya ita? Kuma wani kalar mataki kuke ganin zasu ɗauka kan Abba Habibu daya aurar da ita ba da saninsu ba?*😰
*•Kuna ganin Haj. Nafeesa za ta tsaya kan ƙudirinta na cutar da Saffy? Sannan wani FANSA kuke ganin Saffy za ta ɗauka kanta?*
*•Haj. Haire fa? Shin maganin da ta karɓa daga Malam Shagala zai yi AIKI ko kuwa za a samu MATSALA?*
*•Hadiza ta koma gefe, shirun ya yi yawa. Me take ƘULLAWA?*
*DUKA AMSOSHIN TAMBAYOYIN NAN NA CIKIN BOOK 2 IN SHA ALLAH.*
Littafin HARAMTACCIYAR GADA BOOK 2 na kudi ne ba free ba. BOOK 2 zai fara sauka ranar litinin (05-10-2026) in sha Allah.
*Nagode.*
*Hafnancy.*