His Rose

Calculated Dominance & Homecoming

by @northernangel

Few hours back...
Lokacin da Yemma ta shiga wing ɗin Baffa tare da Rahama, sun tarar da shi zaune shi kaɗai a lounge ɗinsa yana kallon TV. Sai dai ya ci gayu na alfarma ya sha lafiyayyar babbar riga tamkar wanda ke shirin fita ɗaurin aure—nan kuwa driver ɗinsa kawai yake jira ya ƙaraso ya kai shi private majalisarsu. Da sallama a bakin Yemma suka shigo, yayin da Rahama da ke biye da ita tayi sallama ita ma tana kalle-kalle, dan shi ne karo na farko da ta taɓa jefa ƙafarta a cikin wing ɗin Baffa. Amsa musu ya yi, sannan ya ɗan ɗago kansa jin wata bakuwar murya daban a bayan Yemma. Ganin Rahama ya sanya shi ɗan dakatawa gami da ƙanƙance idanunsa kan Yemma, yana mamakin ko lafiya. Sam bai gane kowace ce Rahama ba, domin iyakacinsa da ita dining hall ne na gidan, shi ma kuma ba kowace rana take samun zuwa ba. Ita kuma Rahama, saboda tsangwama da taunts ɗin da take sha a hannun su Salma, ya sanya ba ta cika zuwa wajen ba sai idan ta tabbatar Zafar zai je—don bas yi mata ɗigon rashin mutunci a gabansa. Yemma ta ƙaraso ta zauna a kusa da Baffa tana ƙare wa yanayinsa kallo. Ita ma Rahama ta sami waje a ƙasa ta zauna, kanta a sunkuye. Gaishe da Baffa ta shiga yi cikin murya mai rawa, yayin da shi kuma ya amsa mata cikin nutsuwa gami da tambayarta ko tana lafiya—duk da cewa yana zargin matan Zafar ɗin ce, amma bai ƙarasa tabbatarwa ba. Yemma ce ta dauko maganar kai tsaye: "Ke, ba shi labarin abin da ya faru ya ji da kunnensa!" Rahama ta ɗago ta kalle su, sannan cikin hanzari ta sake sunkuyar da kanta ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai ban tausayi. Cikin mamaki Baffa ya kalli Yemma, yana cewa,  "Subhanallahi! Lafiya?!" Cikin haɗe rai da murtuke fuska Yemma ta ce, "Ina fa lafiya?! Daga abin arziki sai ya koma na tsiya! An act of goodwill has turned into total destruction! Takanas iyayenta suka shiga gidan waccan yarinyar to show support and congratulate her, amma ba ka ga ɗiban albarkan da suka yi musu ita da danginta ba! The toxic disrespect they received from them is totally disgusting! That ungodly girl calculatedly lured Rahma into her bedroom under a false pretense. Ka ga dai yanayin jikinsu ba ɗaya ba, and she took advantage of Rahma’s submissive nature. She trapped her in her soundproof inner room and used shears to completely butcher her hair, all out of pure, malicious hassada!" Daga haka ta maida kaifaffen kallonta kan Rahama tana umartarta, "Ke, buɗe masa gashin ya gani! Take off that veil right now! Let him see the actual damage with his own eyes!" Rahama, da jikinta ke ta faman wani irin mugun tsuma, ta cigaba da kuka yayin da al'amarin ke dawo mata sabo fil. Wani irin matsanancin baƙin ciki ne ke lulluɓe mata zuciya idan ta tuna irin cin mutuncin da Zara ta yi mata da kuma kalaman da ta gasa mata kafin wannan aika-aikan. Hannunta na ɗan rawa ta sanya shi ta janye mayafin kanta—inda sai ga guntulallan, dan tsugul din gashin kanta ya bayyana a fili. Ita kuwa Yemma, idanunta na kan Baffa tsaye don jiran ganin reaction dinsa. Sai dai shi sam Baffa idonsa ba ya ma wajensu; wayarsa kawai yake daddannawa yana ƙoƙarin kiran driver ɗinsa da ya ga ya ɗan ja lokaci! Haɗe rai Yemma ta yi tamau tana cewa, "Nuna maka fa ake yi, Baffa!" Ba tare da ya ɗago kansa ba, kai tsaye ya amsa mata cikin sanyi da ko in kula. "Aziza... ai wannan zancen naku ne na mata. You carry the title of matriarch in this household for a reason, and I am entirely certain you possess the fortitude to navigate this crisis on your own. After all, you have always chosen to orchestrate and manage every single dynamic of your son's marital affairs independently, completely bypassing my counsel. Since you chose to steer his life in this direction without my consensus, I am confident you can fully absorb and handle the consequences of whatever unfolds under your watch now. I am leaving this completely in your hands, as I always have." Daga haka ya sanya wayarsa a kunne tare da miƙewa tsaye, yana fara magana da wanda ke ɗaya ɓangaren kiran yayin da ya doshi ƙofar fita waje. Da kallo suka bi shi su duka biyun har ya fice daga wing ɗin. Wani marayan kuka Rahama ta fashe da shi tana jin gaba ɗaya auren ma ya fita daga ranta. Ita kuwa Yemma, hanyar da Baffa ya bi ya fita kawai take bi da kaifaffen kallo tana gyaɗa kanta a hankali—lallai Umar! Wato ita zai ƙankanta gami da disga ta a gaban wannan yarinyar?! Miƙewa ta yi a fusace tana faɗin, "Tashi mu je, ke! Honestly, I don’t even know what kind of absolute fool you are! Since when is a co-wife someone you trust?! How on earth did you let her get close enough to touch a single strand of your hair?! To this day, I cannot comprehend how you have completely failed to secure Zafar's attention! Honestly, at this point, I see absolutely no purpose in this entire marriage. It has been an absolute waste of time, wollahi!" Daga haka ta fice, Rahama na biye da ita a baya tana gundarin kuka, yayin da Yemma ta ke ta zazzaga masifa mara ƙarshe. Suna isowa wing ɗinta, ta haɗa Rahama da iyayenta ta riƙa balbale su da fada ta ko-ina, sannan ta yi wucewarta ciki ta hau sama abinta... Wajen ƙarfe biyar na yamma Yemma ta kira Zafar bai yi picking ba. Da ta kira PA ɗinsa, shi ne ya sanar da ita suna Ibadan; nan ne ta umarce shi da ya mika wa Zafar wayar.  Sai dai ko da PA ɗin ya ƙaraso inda suke, sun riga sun shiga meeting din da ya kaisu, don haka ya sake sanar da ita. Ba ta ce masa ko ƙala ba, kawai ta datse wayar. Ba ta same shi ba har sai da ya kammala ya dawo gida, ya ɗauki wayarsa daga motar Mu'azzam sannan ya kira ta. Tana picking, kai tsaye cikin muryar izzar nan Yemma ta ce masa, "It is your wife I want to see. Call her immediately and instruct her to report to my wing!" Ba tare da wata-wata ba, Zafar ya amsa mata cikin nutsuwa. "With all due respect, Yemma, I cannot allow that. The last time she exited your presence, it culminated in a severe medical crisis that nearly cost us everything. I have firmly drawn a line keeping her away from your wing for her stability. Yemma, ɗan Allah, ɗan Allah, I am pleading with you, with the absolute highest respect for your standing, to preserve your dignity as my mother and respect this boundary. I am begging you, do not allow yourself to be dragged into these petty domestic disputes. They are far beneath you." Yemma, da ke zaune, ta miƙe tsaye a fusace! Idanunta a zare take sauraronsa har ya kammala. Cikin wata low, dangerous voice ta ce masa: "Fine. If that is the stance you have chosen to take against your own mother... so be it." Daga haka ta katse wayar gaba ɗaya. Kiran wayar tata ya riƙa yi amma sam ba tayi picking ba—har ya ƙaraso cikin gidan Zara, wanda a lokacin ne kuma ya kira Zaran ta fito suka wuce asibiti domin duba baby Jasmine…



A ɓangaren Zafar da Zara kuwa, tuni suka shirya tamkar ba su ne suka gama masifa da sa-in-sa a cikin mota ba lokacin da suka shiga sashen ganin baby Jasmine. Sai wajen ƙarfe sha ɗaya na dare suka dawo gida, inda kai tsaye suka wuce wing ɗin Zafar. A can ta kwana, sai da Asuba da zai tafi masallaci ita kuma ta tattara ta koma ɓangarenta. Sai washegari da safe ta sadu da su Susan da Sam saboda a gidan suka kwana, ita dai Vicky komawa gida ta yi tun daren jiya. Misalin ƙarfe 9:00 na safe, suka fita ita da Zafar zuwa asibitin. Bayan dawowarsu kuma suka wuce sashensa saboda weekend ne yana gida ranar. Haka suka wuni tare—masallaci kawai ke fitar da shi, sai kuma da yamma da suka sake wucewa asibiti tare. Bayan sun dawo, ya wuce ɓangaren Yemma daga nan kuma ya sake fitowa ya dawo gida. Ranar ma a ɓangarensa ta kwana, kuma haka suka sake wuni tare a ranar Lahadi. Sai ranar Monday da daddare, bayan sun dawo daga asibiti, ya ce mata ta shigar da motar ciki shi kuma zai wuce masallaci. Haka kuwa aka yi. Sai dai abin da ba ta sani ba shi ne, gidan Rahama ya ke da niyyar kwana a ranar. Bayan ta yi parking motar, ta fito ta nufi ciki inda Ghost ya tare ta kamar yadda ya saba kullum. Sama ta hau ta yi dinner ɗinta, sannan ta gudanar da duk wani night routine ɗinta na alfarma. Bayan ta kammala, ta sanya kayan baccinta ta ɗaura after-dress a kai, sannan ta fito ta nufi part ɗinsa. Ko da ta shiga wajen ƙarfe goma saura ne na dare amma ba ya nan. Sai kawai ta yi tunanin ko yana ɓangaren Yemma ne, dan haka ta zauna a lounge ɗinsa tana jiran dawowarsa. Sai da agogo ya buga ƙarfe 11:00 na dare, sannan gaskiyar al'amarin ta fito fili kuma ta tabbatar da abin da hakan ke nufi... Kiransa ta hau yi a waya sam bai yi picking ba, ɗan haka kawai ta miƙe gami da ƙara saka wannan after-dress ɗin a jikinta, ta sauko ƙasa sannan ta fice daga wing ɗin nasa gaba ɗaya. Kai tsaye ta doshi babbar harabar gidan har ta ƙaraso gate. Fita ta yi daga gidan gaba ɗaya, ta soma takawa ita kaɗai cikin wannan sanyayan daren har ta ƙaraso ƙofar gidan Rahama. Ɗaya daga cikin securities ɗin da ke zaune a tsallaken hanyar ne ya taso a guje ya tsallako, sannan ya buɗe mata ƙaramin kofar gate ɗin. Shiga ta yi ta doshi main entrance ɗin gidan kai tsaye. Tana ƙarasawa babbar ƙofar shigar, ta ji ta a rufe gam. Ba wani jira ta zagaya ta back door ɗin gidan—da yake tsarin ginin gida ɗaya ne sak da na Mu'azzam, ya sanya ba ta sha wata wahalar gane inda back door yake ba. Tana ƙarasawa ta tura ta shiga ta hanyar, sannan ta ringa tafiya har ta wuce katoton kitchen ɗin gidan—wanda har a lokacin akwai maids a ciki suna ta faman jibgar aiki bil-haƙƙi. Saboda yau ɗin nan gaba ɗaya wasu yan uwa da ƙawayen Rahama sun kai su goma sha a nan suka baje suka wuni! Yanzu shi ne sabon salon da ta tsiro da shi tun kwanaki— wato tara ƙawaye da wasu sabbin matan  manyan kasa datayi befriending har da kwana wasu, tun lokacin da Zafar ke asibiti. Circle din kanta take dashi yanzu na mata sa yayan manya masu ji da kansu. Tun dawowar su Zafar daga asibiti ya ɗan taɓa samun su a gidan kusan sau biyu amma bai ce mata ko ɗigon ƙala ba, don kuwa sam hakan ba damuwarsa ba ne, shi yama dauka duk yan uwanta ne. Maids ɗin gidan kawai ne ke cin kaniyarsu da masifaffen aiki—su ma kuma ba a daɗe da kawo mata su ba, saboda tun farko cewa tayi ba ta buƙata, sai da kawayen nata suka wayar mata da kai. Maids din ba su ma lura da Zara ba har ta shige ta wuce parlour ɗin gidan kai tsaye, inda ta shige elevator ta harba zuwa penthouse ɗin Zafar. Tana tafiya kuwa, tunawa kawai take yi da lokacin da Salma ke cikin gidan—tana ji a ranta har gwara lokacin akan yanzu. Zafar yana zaune a living room ɗinsa da waya a kunnensa yana magana cikin nutsuwa, yayin da Rahama ke kwance kan wata lafiyayyar sofa tana danna wayarta ita ma hankalinta a kwance. Kai baka ce sun san juna ba, ko taya ake a haihu a ragaya? oho! Kwana biyun nan har wani mugun zazzabi Rahama ta yi, sai yau ne ma da ƙawayenta suka shigo ta ɗan samu wani sa'ida a jikinta da ranta—har ta tsula ƙwalliya cikin wadansu yan iskan sleepwears ɗinta na alfarma, kanta na sanye da wani tsadadden human hair da ya yi mata kyau ba kaɗan ba. Kamar daga sama kawai suka ji an turo ƙofar an yi musu dirar mikiya! Wani irin zabura Rahama ta yi ta miƙe zaune a razane ganin wadda ta gilma ta gabanta. Zafar da ke magana a waya ya ɗago kansa yana kallon Zara tamkar a mafarki; kawai sai ya kashe kiran ba tare da ya yi sallama da wanda yake maganar da shi ba. Zara kam ko a jikinta wannan kaifaffen kallon da suke jefa mata! Kai tsaye ta doshi inda Zafar ke zaune tana faɗin: "Interesting... You omitted the detail that our sleeping arrangements had moved to this side of the estate." Wani nauyayyen shiru ne ya biyo bayan maganar tata, idanunsu su biyun na kanta. Cikin wata nonchalant, unbothered voice Zafar ya jefa mata tambaya. "What exactly do you think you're doing here, Zara?" Ita ma cikin irin wannan muryar tasa mai ko-oho ta amsa masa, "I'm just here to spend the night with my husband. Problem?" Wani short, clinical chuckle ya saki yana girgiza kansa a hankali. Sannan ba tare da wata-wata ko musu ba, ya miƙe tsaye, ya ɗauki laptop ɗinsa da ke kan table din gabansa, ya fito yana doshi hanyar fita gaba ɗaya gami da cewa mata, "Muje." Ita ma ko kallo Rahama bata samu daga gurinta ba, kawai ta bi bayansa tana wata ƙasaitattar ƙwafa. Daga haka suka sauko su biyun suka fice daga cikin gidan ba tare da wani ya sake cewa ɗan uwansa uffan ba. Ko da suka koma gida ma bai ce mata uffan ba; sai ma janyo ta da yayi tsaf zuwa jikinsa bayan sun kwanta a gadon, harda showering dinta da kisses. Baccinsu suka yi peacefully tamkar babu wani al'amari da ya taɓa giftawa a tsakaninsu. Yayin da a ɓangaren Rahama kuwa, ta kwana cikin tsantsar kuka, nadama, da zafaffen takaicin da ke cin zuciyarta. A ranar cikin tsakiyar daren, ta kira mahaifiyarta suka gudanar da magana mai tsawon gaske, sannan suka tsara wata gagarumar shawara da za su aiwatar a tsakaninsu... Daga ranar kuwa sai aka samu wani asalin daidaita da tsantsar kwanciyar hankali tsakanin Zafar da Zara; gaba ɗaya ya daina kwana a gidan Rahama. Sai dai abin da Zara ba ta sani ba shi ne, kullum da Asuba idan ya fito daga masallaci, maimakon ya shiga gidan Yemma sai ya wuce gidan Rahama kai tsaye ya sauke duk wani azabar jarabarsa a can. Rahama kam ko complain guda ba ta yi, saboda tuni ta hango hanyar ɓullewa sakamakon shawarar da suka yanke da mahaifiyarta, kuma suna nan suna ta shirye-shiryen abin da suka ƙulla za su aiwatar ɗin. A ɓangaren Zara kuwa, hankalinta a kwance yake tamau, komai yana tafiyar mata smoothly daidai yadda take so—musamman a ɓangaren ɗiyarta. Bayan dawowarta gida da sati ɗaya, aka fara sanya ta tana practicing ba wa ɗiyarta nono, sakamakon respiratory stability da ta samu tare da ƙwarin suck-swallow reflex ɗinta. Da ta yi one to two sucks ake cire ta domin kar ta gaji, har ta kai ga tana iya yin sama da hakan a sati na biyu. Ranar da suka shiga sati na uku kuwa, aka ba su ɗiyarsu aka sallame su daga asibitin. Idan ka ganta ba za ka taba cewa daga kwalba (incubator) ta fito ba saboda girmanta da kibarta—sai kawai ace Tabarakallah, Masha Allah! Farin ciki a wajen Zara da Zafar ba ya misaltuwa, haka zalika a wajen Yemma da Baffa. Hasali ma suna shigowa cikin estate ɗin, Zafar ya wuce da su kai tsaye Galado Manor, ya kai su wing ɗin Baffa—wanda daga shi sai Yemma ne kawai a ciki. Nan aka mika musu ƴar suka ganta for the first time. Zafar kuma ya sake jaddada musu cikakken sunanta, wanda har da traditional Igbo name ɗinta sai da ya bayyana musu dalla-dalla. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa Baffa ba, musamman da ya lura gaba ɗaya yanayin Yemma ya sauya lokacin da ake ambaton Igbo name ɗin yarinyar. Shi dai Baffa ba abin da yake yi sai dariyar ƙasa-ƙasa—wadda ƙiri-ƙiri suka fahimci ta da matarsa yake. Shi ma dai Zafar dariyar yake yi a tsanake yana ɗan satar kallon Zara, yayin da ita kuma Zara ko ɗigon kula da yanayin Yemman ba ta yi ba; ita dai Alla-Alla take kawai a mika mata ɗiyarta su tattara su wuce gida, yayin da Yemma ta kankame a kirjinta kamar bata son bada ita…