Introduction
by @prettys01
★ SAKEENAT ★ ★ BANBANCIN RA’AYI ★ Written by SAKINA ABDULLAHI 😍 PRETTY SK CE 😍
*❤️ GODIYA* Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (SWT), wanda Ya bani ikon fara rubuta wannan littafi. Ina miƙa godiya ta musamman ga iyayena, malamaina, abokaina da duk masu goyon bayana. Haka kuma ina godewa dukkan masoya karatu da masu bibiyar ayyukana..
⚠️ GARGAƊI ⚠️ Wannan littafi mai suna “SAKEENAT (Banbancin Ra’ayi)” mallakar marubuciya ce, kuma littafi ne na kuɗi (₦500 kacal). Dukkan rubutu, labari, sunaye da tsarin wannan aiki an tsara su da fasaha da wahalar tunani. Don haka an haramta kwafi, satar rubutu, gyara ko yaɗa shi ba tare da izini ba. Duk wanda ya karya wannan doka zai fuskanci hukunci bisa dokar kare haƙƙin mallaka. Please respect the writer’s effort. Support original content.
START POSTING 📅 DATE: 01/08/2026 ✍️📚🌹
📖 GABATARWA Rayuwa cike take da ƙalubale da gwagwarmaya. Wasu lokuta banbancin ra’ayi kan shiga tsakanin mutanen da suka fi kusanci da juna, har ya haddasa rarrabuwar kai tare rikici na musanman. Wannan labari na SAKEENAT zai nuna yadda yarinya mai natsuwa da haƙuri ta fuskanci ƙalubale masu yawa saboda banbancin ra’ayi da ya taso a rayuwarta.
★SAKEENAT★ * BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_
📖 🕊️ Ma’anar “Sakeenah” a Al-Qur’ani Kalmar “Sakeenah” (سكينة) tana nufin: NATSUWA kwanciyar hankali zaman lafiya a zuciya saukar rahamar Allah da nutsuwa. Allah Ya ambaci Sakeenah a wurare da dama....... Surah At-Tawbah (9:26) Allah ya saukar da natsuwa (sakeenah) ga Manzon Allah ﷺ da muminai a lokacin wahala. * Ma’ana: Allah ne ke saukar da kwanciyar hankali a lokacin tsoro.
Surah Al-Fath (48:4) Allah Ya ce Ya saukar da sakeenah a cikin zukatan muminai domin su ƙara imani. 🌸 Ma’anar sunan “Sakeenat” Idan a ka ambaci “Sakeenat” a matsayin suna, yana nufin: 👉 “Wacce ke kawo natsuwa” 👉 “Mai kwanciyar hankali” 👉 “Alamar zaman lafiya”
Dan haka sunan SAKEENAT yana da amana mai ƙyau, ku sanya ma ƴaƴanku domin su zamo muku natsuwar ruhi.