CHAPTER 1
by @prettys01
*KADUNA STATE*
_MILINIUM CITY_ _ROYAL MERCY HOSPITAL_ On 18/October/ 2007 5:45pm “Inyaaaaaaa!…........ inyaaaaaaa!!........ Inyaaaaaaa!!!” sautin kukan jaririya ya cika ɗakin asibiti.
Doctor Zulaikha, wacce ke riƙe da jaririyar, tana yanke mata cibiya cikin kulawa.
Murmushi ne a kwance akan fuskar ta, yayin da take kallon yadda jaririyar ke kuka da ƙarfi, tana wutsil-wutsil da fararen ƙafafunta masu taushi.
Doctor Zulaikha, ta ɗan juyo ta kalli ma’aikatan jinya, cikin nutsuwa ta ce.
“Ku miƙo towel, a rufe mata jiki.”
A hankali ta ɗaga jaririyar sama, kukan ta na ƙara ƙarfi yana cika ɗakin. Wata ma’aikaciyar jinya ta karɓe ta da sauri, tana goge jikinta cikin kulawa.
A gefe, mahaifiyar jaririyar tana kwance cikin gajiya, numfashinta yana fita a hankali, idonta a rufe. Hawaye masu ɗumi na bin gefen fuskarta—ba na ciwo kaɗai ba, har da farin cikin samun abin da ta dade tana jira ita da mijinta wato Haihuwa.
“Alhamdulillah…” Doctor Zulaikha ta furta a hankali, tana duba halin da mahaifiyar take ciki.
“Sannu Hajiya, sannu! Ga ƴar, an samu mace." Ta faɗa tana ɗaura mata yarinyar da har lokacin kuka take yi.
Cikin soyayya Hajiya Fatima ta buɗe idanunta da suka sauya launi ta zuba akan ƴarta gudan jininta dana mijinta, lokaci guda ta wasu sabbin hawayen farin ciki suka gangaro daga cikin idanunta, murmushi take tana hawaye, tare da addu'a a cikin ranta.
Sun jima suna neman haihuwa Allah bai kawo ba, babu irin walahar da ba su sha ba, sune wannan waƙar sune wancan kasar ɗan duba lafiyarsu, sai dai ko ina ace musu lafiya lau suke, daga nan suka falwala wa Ubangiji suka dage da addu'a, suka kau da kai daga zancen dangi gaba ɗaya........... _Mahaƙurci mawadaci_ sai gashi bayan shekara 10 da aurensu Allah ya azurtasu da samun ƴa mace.
★ Idanunta na kan jaririyar dake zuƙan ruwan Nononta a hankali, hannunta na dama na kan gashin jaririyar tana shafawa a hankali. Sunyi wanka dukkansu, suna jiran sallama ne da kuma Alhaji Nura, wanda ya bar asibitin yana hawaye, ganin matarsa cikin halin nakuda mai tsanani, hakan yasa ya fice yana ta kuka sai kace ƙaramin yaro.
A ɗan wannan lokacin da take shayar da yarinyar har ta lissafa daga fara Shayarwa, yaye, tafiya, makarantar da ƴar za ta yi, da duk wani gatan da za ta yi mata har zuwa aurar da ita.
Ita kaɗai ke ta lissafinta tana yi tana murmushi, lokaci guda ta kalla ƙofa jin yadda aka buɗe da sauri, zabura ta ɗan yi sai kuma ta yi murmushi mai sanyi tana kallon Mijin nata dake tsaye ya kasa shigowa ciki.
Hannu ta miƙa mai alaman ya kama, da ɗayan kuma tana nuna mai yarinyar da barci ya ɗauke ta yanzu.
A hankali Alhaji Nura ya shigo ciki kaman mai tsoron wani abu, yana isa bakin gadon ya ɗauki ƴar ya jijjiga da ƙarfi, take ta calla ihu ta fara kuka, shi kuwa tsabar farin ciki sai ya fashe da kuka, ya aje ƴar sannan ya yi sujoodul-shukrh ɗan miƙa godiyarsa ga Allah.
Bayan ya ɗago ya saki murmushi sannan ya zauna gefan matarsa, cikin sanyi hali ya ce.
“Fatima! Alhamdulillah, alhamdulillah, a ƙarshe dai ga ƴar mu, mace Allah ya bamu, insha Allahu za mu kula da wannan kiwon da Allah ya ba mu, insha Allah babu irin gatan da ba za mu yi mata ba, gata sai ta ture da yardan Allah” Fatima ta yi murmushi.
“Wani suna ka zaɓa mata?.” sai ya yi murmushi.
“Kinsan ba zan sauya ba." Lumshe ido ta yi.
“Na gode sosai, na za ci za ka sanya sunan Hajja ne!.” ya ɗauki ƴar yana kallon fuskarta sosai.
“Hmmmm sunanta SAKEENAT! Wato natsuwar ruhinmu.” ya faɗa idanunsa kan na Jaririyar, Fatima ta shafa cikinta dake ɗan mata zafi, ta kalla mijinta nata cikin kulawa.
“Abu Sakeenat, ina so na tambayeka wani abu guda ɗaya tak.” daɗin sunan da ta kirasa yasa ya zauna gefe guda yana zumuɗi.
“Ina jinki Ummu Sakeenat." Sai ta riƙe hannunsa dana Sakeenat da idanunta suke a buɗe tana kallon fuskar Alhaji Nura.
“Ki faɗa mana!.” ya faɗa jin ta yi shiru.
“Hmmmm alfarma nake nama akan Sakeenat.” a tare suka kalla Sakeenat cike da kulawa jin ta yi ɗan sauti ‘Ƴarh’
“Fatima ki faɗa kanki tsaye." Ya faɗa cike da kulawa.
“Ba wani abu bane face..........uhmmm.....uhmmmm..........nasan cewa idan gatan da ake ma yara sun kai Ɗari (100), to kai dubu za ka mata.........to Ni, a cikin Dubun ina so na yi mata abu guda ɗaya tak.........."
“Ɗaya cakal!?.” ya tambaya yana mata murmushi, itama murmushin ta yi.
“Eh ɗaya tak ya ishe Ni a cikin dubu." Ta kai nan tana kallon fuskar Sakeenat da ta kwaso haskenta da manyan idanunta kaɗai sauran kamannin kuwa duk na Alhaji Nura ne.
Alhaji Nura da hankalinsa ke kan ƴarsa ya ɗan ja hancinta yana cewa.
“Na baki wannan daman, Allah ya bamu tsawon rai Fatynah." Rungumesu ya yi dukkansu cike da soyayya da ƙauna.
★ Da misalin 8:30pm aka sallame su, Alhaji Nura da kansa ya yi driving ɗinsu har zuwa gida, da yake ba wanda suka sanar ma haihuwan daga danginta harna nasa saboda kowa haushinsu suke ji, ita Fatima anyi-anyi ta rabu da shi ta aura wani haka shima anyi da shi ya sake aure ko ya ƙara aure amma ya ƙi, sai gashi rana ɗaya Allah ya azurtasu da samun rabo, rabon da suka ɓoye ma duniya dan ba mutane mamaki.
A bakin wani danƙareren gidan ya danna horn, mai gadi ya buɗe gidan cikin fara'a.
Motar Alhaji Nura murza hancin motarsa zuwa cikin katafaren gidansa, har kuma lokacin murmushi ne kwance akan fuskansa kaman wanda aka yi ma bushara da gidan Aljanna.
Ma'aikatan gidan mata uku duk suna sanye da Hijab sai rigar da suka ɗauka akan Hijab ɗin wanda uniform din aiki ne, ɗaya mai girki, ɗaya gyaran gida ɗaya wanke-wanke.
A gefan parking lot suka tsaya suna jiran arba da Madam tare da abinda aka haifa.
Alhaji Nura ya fito yana washe musu baki, su kuma suka tsugunna suna gaishesa cike da mutumtawa.
Babyn ya fara miƙa musu suka amsa suna zagaye fuskar yarinyar, kafin Alhaji Nura ya fiddo kayan da suka je da shi asibiti ya nemesu ya rasa, duk sun shige da yarinyar ciki, murmushi ya sake yi sannan ya kira ɗaya daga cikin masu aikin.
“Salma! Salma!! Salma!!.” da sauri Salma ta fito fuskarta a haɗe ba kaman ɗazu ba. Kayan dake hannunsa ya miƙa mata yana cewa.
“Mai ya same ki?." Yarinyar da ba za ta wuce 23yrs ba ta ɗan saki ranta.
“Sun hanani ɗaukar yarinyar, dan Allah kace subani na mata wanka."
“Ah ƴar gold ce ba za ki mata wanka ba, wankanta sai manya su Maman Daddy...........ga Madam na kallon ku, ai duk tasan zaman da za ta yi daku, kun nuna baƙwayinta sai Sakeenat." Kallon cikin motar ta yi suka haɗa ido da Hajiya Fatima dake mata murmushi.
“Madam ki yi haƙuri, zo na taimaka miki." Hajiya Fatima ta yunƙuro tana dafa Salma.
Da taimakon su ta shiga ciki har bedroom ɗin ta, ta zauna gefan gado tana rintse ido saboda zafin da take ji duk kuwa an mata wanka a asibiti.
Bayan ta zauna da ƙyau Alhaji Nura da kansa ya kawo mata abinci, ya zauna kusa da ita ya fara bata a baki, cikin ƙauna da soyayya, amsa ta fara yi tana ci idanunta na kansa.
Sai da ya tabbatar taƙoshi sannan ya mai da kwanukan, a lokacin ya dawo ɗauke da Sakeenat dake kuka mara sauti, ya kwantar da ita jikin Hajiya Fatima yana cewa.
“Na rasa ina zansa kaina saboda farin ciki, duk a zatona ba mutum za ki haifa ba, duk na fidda rai zan ga gudan jinina sai ga shi Allah ya ban Sakeenat, zan kira na sanar ma family na kema ki sanar musu, nasan za su yi farin ciki da ƙaruwar nan." Da haka ya ɗauki wayarsa ya fara latsa number mahaifiyarsa Hajja.
Tana kallonsa ya fara gaishe da Hajja, sannan ya sa a speaker.
“Nura ya kake ya aiki?.”
“Lafiya lau Hajja."
“To masha Allah, ina mara zuciyar matarka?.” sai ya kalla Fatima, murmushi suka yi sannan ya ce.
“Tana Lafiya Hajja, uhmm dama zan faɗa miki ta sauka ne.”
“Ba ta yi Saukar Alqur'ani ba? Ko sakewa ta yi.”
“Hajja ba wannan ba, Ta sauka mace, ɗazu an samu Sakeenat." Dariyarsa ya danne jin irin zaburar da Hajja ta yi.
“Nura bansan shirme, yaushe Fatima ta samu ciki balle ta hai....." Sautin kukan Sakeenat ne yasa ta yi shuru tana sauraran kukan dake tashi a hankali.
“Nura ba dai ƴa kuka sato ba!?." Ta yi maganar cikin raɗa.
“Wallahi haihuwa ta yi, ki sanar ma sauran." Da haka ya kashe wayar yana jin tana ƙwalama yaran gidan kira.
Fatima ta yi murmushi sannan itama ta ɗauki wayarta ta kira number Babbar yayarta wacce ta zama mata uwa, tana sonta fiye da misali, bayan haka ita ce kaɗai mai ƙarfafa mata gwiwa akan rayuwarta da Nura.
Ɗaukar wayar aka yi daga can ɓangaren, ta yi sallama sannan aka amsa cikin natsuwa.
“Ina wuni Aunty."
“Lafiya lau Zahrah, ya gidan?."
“Aunty Alhamdulillah.” ta faɗa tana jin soyayyar Auntyn na ta.
“Ke yanzu rayuwar da kika zaɓa ma kanki kenan, dan Familyn mu sun samu Banbancin Ra'ayin akan rayuwar aurenki shine kika watsar da kowa, hatta Ni kin dena nema gaba ɗaya, hmmm ai kin ƙyauta.” murmushi ta yi mai sanyi tana ɗan matsa hannun mijin na ta dake cikin hannunta.
“Aunty ba haka bane......"
“To yane? A ganinki Nura ne ba maso ko mene?........... Kinsan Ni banda matsala da hakan, amma ki dinga nemansu dan sauke haƙƙin, su gani suke gata suke miki dan rayuwarki suke hange, amma..............”
“Na haihu." Ta katseta da sauri.
“Me............kin me?." Murmushi ta yi.
“An samu mai sunanki, Sakeenat." Take.......... Yadda kasan an tsungule Jaririya ta fara ƙananun kuka.
Aunty ta katse wayar lokaci guda ta kira ta Video call.
Ɗauka ta yi tana haska mata fuskar Sakeenat dake calla kuka.
Aunty ta fashe da kuka tana kallon jaririyar Fatima.
“Ya.....yanzu haihuwa kika yi baki faɗa ma kowa ba Fatima...........wayyo Allah...........Fatima kin haihu..............Ya Salam kalla duk kin kumbura, innalillahi gobe zan so Kaduna, ina zuwa." Ta faɗa tana share hawaye take da nufan ɗakin yaranta.
Ta faɗa musu tana miƙa musu wayar da har lokacin fuskar Sakeenat ke bayyana tana kallon screen ɗin.
Yaran su hau ihu suna jin daɗi harda ƴam mata, take Fatima itama ta fashe da kuka, tana jin sanyi na ratsa mata zuciya.
Bayan sun gama waya, danginta da na Alhaji Nura suka fara jera kira, kowa sai ɗauki yake, kuma duk wanda ya kira sai ya ma Fatima ya jiki, ƴan uwansa da ba sa mata magana suke ta kiranta suka gaisheta cikin ƙauna.
Idan suka ce a yau ba su ga soyayyar dangi ba sunyi ƙarya, haka Hajja a daren ranar suka zo, dan ganin Sakeenat.
Wasu ma a gidan suka ce za su kwana, Alhaji Nura ya ya ba kowa ɗaki.
Badan ya so ba ya ba yara Sakeenat suka dinga jaƙwalƙwalawa, har sai da suka gaji ya amso ta, ya mai da ma Fatima ita.
Part ɗinsa ya nufa dan Yayarsa za ta kwana tare da Fatima, da yake ta zo hutu gidan Hajja shine suke zo dukka, yanzu kuma ana za su kwana da yaranta..................
*Hayin Ɗan Mani*
La'asar sakaliya, rana ya yi zafi sosai, yayinda ɗakuna suke dum babu rahma, a hankali take tura cikinta gaba har ta isa kan taburma, ta zauna da ƙyar tana sauke ajiyan zuciya, yanzu tafiya kaɗan sai ta ji a jikinta, gashi ko waje ba ta leƙawa umarnin Mijinta ne, ga tsohon ciki, duk ta bi ta kumbura amma har yau ko asibiti ba ta taɓa zuwa ba, kuma a lissafinta lokacin haihuwa tuni ya wuce, gashi ko ta yi mai magana baya mai da hankali akan komai da ya shafeta. Ta gaji da zaman ciki ne, hakan yasa ta fito ta zagaye ƙaramin tsakar gidan nasu, daga nan ta zauna kan taburma ta miƙe ƙafafunta.
Matar ba wata babba bace dan ba za ta wuce 25yrs ba, tana da tsayi sosai, sai dai baƙa ce, irin ɓakin da kafin a samu ana daɗewa, baƙin mai duhu kaman gawayi, amma yana da ƙyalli, hakan yasa ake ganin kalar a mai ƙyau, tana da manyan idanuwa farare wanda suka ƙara daidaita fuskarta mai cike da annuri.
Gidan ba babba bane, mai ɗan girma, sannnan part biyu ne, kowanne ciki da falo sai Kitchen, yayinda bayika biyu suke daga gefe guda.
Gidan ba yabo ba fallasa, ko ina tsaftsaf, gaba ɗaya cikin gidan ya sha cement ta ko ina.
Lokaci guda ta kalla inda ta jiyo shewa da dariya.
Mijinta ne da sabuwar Amaryarsa, sune dukkansu ɗaure da towel, Amarya ta riƙe kwandon wanka da ke dauke da soso da sabulun GIV, shi kuma ya rike bokitin mai hannu.
Suna riƙe da juna suke ɗan waƙe-waƙen masoya wanda suka riƙa a soyayya, da yake bayin gidan duk a waje suke, tasan wanka suka fito su yi, tana daga inda take, tana kallonsu.
Yana taran ruwa daga panpo waje, Amaryar na kai musu cikin bayi tare da zubawa a wani bawo wanda a ciki suke wanka, za ta iya rantse wa da Allah tunda ya auro Amaryarsa mai suna Zulee Baby, yake wanka sau biyu a rana, kuma duk tare suke yi, su shiga bayi, su yi wanka da wasan banza har maƙota suna jin su, kuma ba ta isa ta ce ko ƙalaba.
Bayan bucket ɗin ƙarshe ya cika, da kanshi ya dauka ya bi bayan Zulee Baby duk kuwa da sun haɗa ido da A'isha.
Yana shiga bayin suka rufe ɗan ƙyauren tare da sagalo towel biyu, nan suka fara wasan da suka saba, suna yi suna shewa.
A'isha dake zaune ta girgiza kai, tunda tana damuwa da salon iskancin nan har ta dena, ta zuba musu ido kawai.
“Baby ka dena, bana so Wayyo caculculi, bana.......bana.........sooo......." Cewan Zulee Baby cikin dariya, yadda kasan a tsakar gidan suke wanka, haka kuma duk sun watso ruwa waje kaman wasu yara.
Bayan sun gama sheƙe ayarsu, suka fito kowa daure da towel, Zulee ta ruga da gudu ta shiga ɗakinta, shi kuma ya yi ƙwafa biye da ita tare da cewa.
“Zan kama ki, sai na rama." Ya faɗa dai-dai yana tsayuwa kusa da A'isha dake sakar mai murmushi, wanda haka fuskantar yake ko da kuwa ranta a ɓace yake za ka ga tana murmushi.
“Aishatuna, Bara na sanya kaya ina zuwa.” ya faɗa yana nufan ɗakin Zulee.
Bayan shigarsa a ƙalla ya ɗau 20mnt sannan ya fito sanye da farar jallabiya, inda take zaune ya isa ya zaune gefenta yana naɗe hannun jallabiyar.
A'isha da har lokacin fuskarta ɗauke da murmushi amma cikin ranta tsanarsa ce ta mamaye ko wani lungu da saƙo na zuciyarta.
“Ya fama da wahala?." Ya faɗa yana kafeta da ido.
“Hmmm lafiya ba lafiya ba, kana gani kullum cikin ciwo nake, ga bayana dake yawan riƙewa, kuma cikin nan watansa 10, ina jin tsoron ko akwai matsala, gashi kaƙi bari naje asibiti, ina tsoron halin da zan shiga idan haihuwar ta zo." Ta kai nan hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, amma fuskarta a sake take.
Tsaki ya ja mai tsayi.
“Hmmm Aisha, waya aike ki ɗaukan ciki? Na ce waya aike ki? Sanin kanki ne na ce bana son haihuwa, hakan yasa na dinga baki ƙwayoyin hana ɗaukan ciki na tsawon shekara biyu, sai daga baya kika dena sha, saboda neman ma kai walaha, kika ɗau ciki kika ƙi faɗa min, bayan na sani babu irin dukan da ban miki akan cikin nan ba, amma kika yi watsi da ni, hakan yasa na zare hannuna daga komai naki, na zuba miki ido, gashi yanzu wa gari ya waya!?........ uhmm." Ya kai nan yana kau da kansa daga kallonta.
A'isha ta share hawayen sannan ta ce.
“Tabbas laifi na ne, sai dai banyi tsammanin ba za ka zama min abin dogaro ba, duba da da dukiyata kake rayuwa, da dukiyata kake komai hatta auran Zulaikha da shi ka yi, ina kallonka ina sane da komai, ba wai dan ina zaune da kai shike nuna banda wata mafita akan rayuwata ba, ina da shi, kuma zan ɗauka, a karo na ƙarshe na ce ka kaini asibiti ko kuma kasan sauran." Ta yi ƙwafa tana lumshe idanunta.
“Barazana kike min ko gori? hmmm ai ba abin mamaki bane, tunda iyayanki su kansu kafin su rasu ba ki musu biyayya, suka ce zasu aura miki wani, ke kika rufe ido sai Ni, babu irin rashin kirki da baki musu ba, daga ƙarshe suka sallama ma ki ni, hmmmm to ko me za ki yi bazan ga laifin ki ba." Ya faɗa hankalinsa Kwance kaman ba shine ya hure mata kunni ba.
“Hakane, amma komai da ya faru laifin kane, kai ka dinga min kalaman yaudara wanda suka na makance a soyayyarka, Iyayena suka nuna min hanya mai ƙyau da fitila mai haske, kai kuma ya rufe min ido da baƙin yadi, yayinda ka kamin hannu ka ce za ka min jagoranci, sai dai mai.........muna isa kan gada ka saki hannun nawa ka yi tafiyarka hmmmm." Ta faɗa tana mai wannan murmushin wanda yake ganin ya fi kuka ciwo.
“Kema sarai kinsan na riƙe ki da amana, na baki dukkan gata, kuma da zuciya ɗaya nake sonki, duk kuwa da ɓakin fatarki, kawai wannan ne bana so." Ya faɗa yana nuna tulelen cikinta.
“Na ce bana son haihuwa, amma kinƙi ji, shi yasa na auro wata mai jin magana na, yanzu haka saboda Ni an cire mahaifarta...........” ya faɗa yana miƙewa tsaye.
“Duk da bansan cikin, haka na ɗauke miki girki, kullum nike kawo miki abinci sau uku a rana, wanda nake siyo miki a Restaurant, ko Ni bana cin abinda kike ci, saboda nasan darajar riƙe amana.” ya faɗa cike da alfaharin yana ciyar da ita abinci mai ƙyau da dukiyarta.
A hankali ta buɗe baki ta ce.
“Ka shirya zuwa gobe za ka samu sammaci daga kotu, dan a gobe zan kai ƙararka, a ƙwatar min haƙƙi na, dukiyata duk ka dawo min da su, sannan wannan gidan a bani kayana, hmmmm ka kaini ƙarshe Bashir, duk da banda kowa amma Allah yabani ilimi, nasan kuma ta yadda zan kaika ƙasa a ko wani Shari'a, ina sane da komai nawa." Ta kai nan tana miƙewa da ƙyar, sannan ta fara dafa bango tana nufan ɗakinta.
“Ki shirya da safe na kaiki asibiti." Ya faɗa cikin borin kunya, ba ta tsaya ba ta shiga ɗakin nata cikin takaicin rayuwar da take yi, kuma ta yi shiru ta kasa magana.
Bashir da zai fita sai ya kasa, hakan yasa ya koma ɗakin Zulee.
Zulee zaune take gaban mudubi tana feshe jikinta da turaruka masu ƙamshi.
Daga sama har ƙasa ya kalleta, take ya ji rabin damuwarsa ya bi iska, yana sonta sosai balle da ta kasance fara mai manyan dukiyar Fulani, duk kuwa da bawa ni ƙyau gareta a fuska ba, kuma da za su tsaya da A'isha, duk da baƙin A'isha ita za'a ɗauka.
Kallonsa ta yi tana murmushi, sannan ta tako har zuwa gabansa tana wani karairaya, hannusa ta riƙe tana cewa.
“Baby meke damunka!?.” maimakon ya bata amsa, sai ya zauna gefan gado yana zaunar da ita kan jikinsa.
“Aisha.....A'isha ce matsalata." Ya faɗa lumshe ido.
“Me ya haɗaku?.” ta faɗa cike da salo, shi kuma ya kwashe komai ya faɗa mata cikin rauni.
“Kinsan Babanta irin mi kuɗin ƙauye ne, wanda bai da kowa sai ya dawo birnin, ana ya aura mahaifiyarta wacce ƴar gudun hijira ce, yana da kuɗi sosai, kuma ƴarsa daya A'isha, yana ji da ita fiye da misali, haka na rabata da su na aureta, saboda ina sonta kuma tana da kuɗi, bayan bikin mu da shekara 1, gidansu ya yi gobara, iyayenta duk suka mutu, hakan yasa gaba ɗaya dukiyarta ya dawo hannunta, sai ta bani gaba ɗaya a jiya, yanzu haka babu komai a hannunta duk na ƙarar da su, manyan shaguna guda biyar na sai da, gidaje da abubuwa da yawa, duk babu su sunbi iska, yanzu idan maganar nan ya fita akwai matsala, da babban gida muke a Gomna Road, na sa mu dawo nan na siyar da wancan..........Kuma Ni bana son tana fita ne, ba wai kuɗin asibitin ne banda shi ba, kawai na tsana kashe kuɗi........ yanzu idan maganar nan ya je wajen hukuma Akwai babbar matsala.........” ya kai nan kamar ya yi kuka..
Zulee Baby ta yi dariya tana rungumesa.
“Ina da shawara Baby.”
“Ina jinki My Love.” a hankali ta raɗa mai kalaman da yasa ya zaro ido.
*“Idan ta mutu kafin gobe ba!?.”* ya kalleta da sauri bayan ya raba jikinsu, sai ta ɗaga mai kai.
“Uhm in ta zama gawa kafin gobe shike nan, ka huta kuma komai ya zama namu.”
“To wa yace miki ta za ta mutu yanzu?.” sai ta ɗan yi dariya.
“Ai a haka ma matacciya ce, kawai mu ƙarasa turata kabari, hakan ma zai zama hutu a gare ta." Kansa ya mai nauyi, yasan Zulee Baby sosai, zai iya cewa duk rayuwa iri ɗaya suke yi, shi neman kuɗi yake da mata, yayinda irinsu Zulee yake musu hanya ga manyan masu kuɗi, aurensa da A'isha ne yasa ya dena wannan aikin ya kama business.
“Ba zan iya kashe rai ba, gaskiya ba zan iya ba.” ya kai nan yana girgiza kai.
“Ni zan taimaka maka, da dai ta kai ƙarar mijina ƙwanda a gama da ita." Ta faɗa cike da bariki.
“Za ki iya!?.” ta ɗaga mai kai.
“To ya zamu yi da mutane, kinsan halin jama'a?.” ta yi wani shu'umin murmushi.
“Karka damu da wannan, kai dai ka kwantar da hankalinka, komai zai tafi yadda muke so." Da haka shima hankalinsa ya kwanta, ya biye mata suka fara aikin da basa wanda basa gajiya da shi, su tai maƙalƙale juna kamar mayen ƙarfe da ƙarfe ................✍️ END.
THE BEGINNING, FANS... 🤸📚🌹 Wannan labari ne mai ɗauke da murmushi da hawaye, farin ciki da baƙin ciki. Za ku ci karo da wani salo na daban daga cikin littattafaina, domin ƙaddarar da ke tattare da wannan labarin ba kaɗan ba ne.
Ku shirya domin tafiya mai cike da darussa, soyayya, ƙalubale da kuma abubuwan da za su girgiza tunaninku.
Tashin kai fa? Ayyy... sai kun biyo ni a hankali! 🤸🗣️🔥
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 8126151523
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ * BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
*THE SHIDORIA WRITER'S TEAM*
> “Karka damu da wannan, kai dai ka kwantar da hankalinka, komai zai tafi yadda muke so." Da haka shima hankalinsa ya kwanta, ya biye mata suka fara aikin da basa wanda basa gajiya da shi, su tai maƙalƙale juna kamar mayen ƙarfe da ƙarfe ................