SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER2

by @prettys01

> “Karka damu da wannan, kai dai ka kwantar da hankalinka, komai zai tafi yadda muke so." Da haka shima hankalinsa ya kwanta, ya biye mata suka fara aikin da basa wanda basa gajiya da shi............

★★★★★★★★★★★

Aisha baiwar Allah, haka ta kwana cikin mawiyacin hali, ba ta taɓa haihuwa ba amma tasan naƙuda take yi, shiru ta yi tana tuna irin rayuwar da ta yi a baya, rayuwa ne mai cikin gata da walwala, haka ta taso har girmanta, iyayenta sun raineta cikin kulawa, sai dai kash, ta saɓa musu, ta bujire musu ta aura wanda ba sa so, amma ta dage sai da ta aureshi.

Bashir mutum ne mai fuska biyu, da fuskar kirki ya yaudareta har ta auresa, duk kuwa da mutane suna da maganganu akansa, wasu suna cewa ‘Daga ƙauye aka koreshi' wasu suke. ‘Barawo ne, shine ya sauya gari.'

Komai da abinda ake faɗa a kansa, duk dai ta share, kuma ko da suka yi aure, dukiyarta baya gabansa, hatta idan ta yi girki mai rai da lafiya, sai ya ƙi ci, ya ce da iya cefanen da ya yi za ta dinga girki.

Haka ya dinga nuna mata na kirki ne shi, bai bayyana ɗayan fuskarsa ba, sai da dukiyarta gaba ɗaya ya shiga hannunsa, daga nan ya sauya mata, abu kaɗan duka, zagi, haka take rayuwa a cikin gidan saboda tana sonsa, so na gaskiya.

Hawaye ne suka gangaro daga cikin idanunta, ta share tana shafa cikin jikinta, tana fatan ta haihu lafiya, ta kuma raina abinda za ta samu, sai dai a kowani raka'a takan roƙa Allah ya bata Mace, ita dai kawai tana son mace, sannan tun ba yanzu ba ta zaɓa suna idan har ta samu mace, wato *Sakeenat*, badan komai ba, sai a baya, mai aikinsu sunanta Sakeenat, yarinyar akwai ladabi, ga natsuwa, sannan ita kaɗai take ma kallon ƙanwa, duk kuwa da ƴar aiki ce, amma tana ji da ita sosai, sai dai mai rabawa ya raba, dan harda ita gobarar nan ta ci tare da iyayenta.

A'isha haka ta ɗau dogon lokaci tana cikin halin ciwo, tun tana motsi har ta kasa, sai zufa dake tsatstsafo mata na wahala da azaba, ga mararta dake wani irin juyawa, haka abinda ke cikinta nan take ya fara juyawa.

Ta galaɓaita sosai, hatta kai tana fizgan nunfashi cikin wani yanayi, a daidai lokacin aka fara kiran sallar asuba, a kuma dai-dai lokacin, ta jiyo masu wankan asuba sun fito suna shewa da wasanni, kamar yadda suka saba.

Ji tayi wani kuzari ya zo mata, hakan yasa ta fara jan jikinta tana nufan ƙofa, cikin ikon Allah ta isa bakin ƙofa ta buga da iya ƙarfinta, sai dai ba ta wani ƙarfi, hakan yasa sautin kaɗan ne, sai wani gurnani take yi mai wiyar fassara.

“Kaman motsi a ɗakin A'isha?." Ɗan daɗi ta ji da jin Bashir ya faɗa haka.

“Uhmm ina ruwanka da ita, Ni ka zo ka min wanka, ina jin sanyi.” cewan Zulee Baby, dama garin akwai sanyi sosai.

Aisha daga nan ta dena jin motsinsu gaba ɗaya, lumshe ido ta yi ta malale gefe ta baje, tana ji a yau zamanta da Bashir ya ƙare, a yau in ta samu lafiya za tasan duk yadda za ta yi sai ta miƙasa kotu.

Tana cikin tunani kawai ta ji wani irin azaba da ya tawo ta ƙasanta, ta zare ido tana jin damshin dake bin jikinta, tasan jini ne dan tun cikin dare yake bin ƙafafunta.

Lokaci guda ta saki wani ihu dai-dai da danno kan sabuwar bakuwar duniya, ji tayi kaman duk ciwon da take ji ya biyo halittar da ta faɗo duniya ne, sai dai abin mamaki, yarinyar bata kuka kaman sauran jarirai.

Nunfashi ta sauke a hankali tana kai hannunta da suka mata nauyi, abin da ta haifa ta ɗago, macece wacce ke ɓace da ƙazantar haihuwa, ga cibin yarinyar dake jikin mahaifatarta.

Haka A'isha ta kama cibin ta katsa ba tare da tunanin komai ba, ta rungume yarinyar wacce idanunta suke a buɗe amma taƙi yin kuka.

A'isha da har lokacin tana jin jinin jikinta na zuba da wani irin gudu ta ƙasanta, ta ɗamƙe jaririyar sosai a jikinta tana jin wani soyayya da tausayin yarinyar har cikin ranta.

A daidai lokacin Bashir ya buɗe ƙofar yana cewa.

“Ihun uban me.......” cak ya tsaya da magana ganin A'isha cikin wani irin hali, ga Jaririya a kafaɗarta, duk sun ɓaci da jini.

Duk yadda ya kai ga jin haushin Aisha sai ya ji tausayinta ya kamashi, ya durgushe gwiwowinsa yana duban halin da take ciki.

Aisha da tuni nunfashinta ya fara ƙoƙarin ɗauke wa ta riƙe hannunsa tana ɗaurawa kan Jaririyar, sannan cikin rauni da roƙo ta ce.

“Ga amana.........ga amana na baka amanar ƴa ta Sakeenat." Ta faɗa tana fara shaƙuwa, hakan yasa ya zabura ya fara kiran suna Zulee.

“Zulee!! Zulee.” sai ga ta, ta fito ɗaure da zani a ƙugu, sai wata ƙaramar riga mau dogon hannu.

“Meye kake faman ƙwalamin kira." Ta faɗa tana tsayuwa a bakin ƙofar.

Bashir ya fashe da kuka yana cewa.

“Ɗauko hijabi muje asibiti karta mutu, Zulee, A'isha za ta mutu." Ya faɗa cikin ruɗewa yana kallon yadda ta fara jijjiga.

Zulee ta kau da kanta daga kallon jikin A'isha.

“Kawai ka bari ta ƙarasa dan gab take, kaga babu mai cewa mu muka kasheta." Ta faɗa tana gyara tsayuwarta.

Bashir ya kalleta cikin wani irin yanayi.

“Banson ta mutu, A'isha kina jina?." Ya faɗa yana ɗagota.

“Ru...ru......ruwah." ya ji ta furta a hankali.

Da sauri ya a saketa ya nufa bocket ɗin ruwanta sai dai empty ne, hakan yasa ya nufa ɗakin Zulee yana shiga ya ɗauko roban fenti guda ɗaya ya fito da shi jikinsa yana rawa.

Yana zuwa Zulee ta sha gabansa.

“Bashir ɗan tsaya mana, kasan Allah A'isha ba za ta sha ruwan nan ba. Ka barta ta mutu mana, dama kowa dole ya mutu ai." Ta faɗa tana ɗan jijjiga.

Bashir ya dalla mata harara yana ƙoƙarin kaucewa ya shiga, Zulee ta sake tsare hanya.

“Zulee ki ban hanya karta mutu." Ya faɗa yana hawaye.

“Wallahi ba za ta sha ruwan nan ba." Tana faɗar haka ta shammace shi ta ture bocket ɗin ya faɗi ƙasa, ruwan ya malale gaba ɗaya.

Cikin wani irin zafin nama ya kai mata mari sai kuma ya tsaya cak, da sauri ya tureta ya shiga ɗakin A'isha jin tana salati.

Sai dai kafin ya ƙarsa ta zama gawa, murmushi na kwance kan fuskarta, sai a lokacin Jaririyar dake jikinta ta tsala wani irin kuka kamar wacce tasan cewa ta yi kuskuren zuwa duniya, kaman tasan ba ta faɗo hanya mai ƙyau ba, kaman tasan ita ƙaddararta daga ranar da ta zo duniya ta fara, kuma daga kowani rana ƙaddararta na buɗe sabon shafi ne, sannan kowani shafi da nashi ƙalubalen mai wiyar fassara..............

*MILINIUM CITY*

Tun kafin gari ya waye hayaniyar masu ɗaukan Sakeenat ya cika parlourn, wanan ya dauka waccan ta ɗauka, ita kuma Sakeenat aka yi sa'a sai binsu take da ido, ba ta yi rigima ba.

Alhaji Nura dake breakfast a dining table yana kallonsu yana ta danne zuciyarsa, dan Fatima ta ce karya ce komai ya yi kawaici ƴar fari ce.

Doya yake ci amma idanunsa nakan Musharraf dake riƙe da yarinyar yana ƙoƙarin cillata sama, besan lokacin da ya daka mai tsawa ba, take Musharraf mai shekara 8 ya ruɗe ya kusa sakin Sakeenat dake hannunsa.

Alhaji Nura ya miƙe cikin sauri, ya isa wajen ya amsheta.

“Haba dan Allah, haihuwar jiya shine Fatima ta sakar muku, saboda ita batasan zafin haihuwa ba, to Ni na sani, a cikin ku, Asma'u ke kaɗai na yadda ki riƙe ta, kaita wajen Mamanta.” ya faɗa yana ba Asma'u babbar ƴar yayarsa wacce shekarunta 14, ta amsa tana murmushi, sai ta faka idon Alhaji Nura, ta yi ma sauran ƙwalo tana fara tafiya, take ta falla da mugu, sakamakon Musharraf da Hanifa suka rufa mata dan sun shaƙa ƙwallon da ta yi musu.

Alhaji Nura ya dafe kai yana jin kaman ya ƙwala ma Asma'u kira, amma yadda ta kwasa da gudu yasan ba za ta ji saba sam, Gashi stairs ta haye, ta matse Sakeenat, tana ta cilla gudu, su kuma bilhaƙƙi suka rufa mata baya da gudu.

Alhaji Nura, Ganin idan ya zauna a gidan sai ya kusa hadiyar zuciya, hakan yasa ya shirya ya bar gidan gaba ɗaya.

★ Fatima a yau ta ga soyayyan dangi fiye da misali, ƴan uwa da abokan arziki sun cika gida, kowa sai farin ciki da wannan ƙaruwar da suka samu, wasu dama zuwa suka yi su tabbatar da haihuwar, sai gashi Sakeenat ta ƙwaso bafullatanin mahaifinta haka ta ɗauko idanun mahaifiyarta.

Kowa sai san barka, gida kaman ranar suna haka ya cika, Sakeenat kuwa tasha ɗauka, ga yarinyar akwai shiga rai, duk wanda ya ɗauke ta ba zai zo ya bayar da ita ba, haka suka dinga miƙa-miƙa.

Fatima dake zaune bakin gado ta kalla Yayarta wanda namiji ne a tsakiyarsu kuma shi ya rasu tun yana ƙaramin, a Abuja Aunty Sakeenat ke rayuwa da mijinta da yaranta, a yau ta biyo jirgin safe ta zo dan ganin takwararta.

“Ina ga a sake ɗaura abinci a huta, baƙi sai zuwa suke." Fatima ta yi murmushi.

“To a sanar ma Salma sai su sake ɗaura wani." Ta faɗa tana ɗaukan autan Aunty Sakeenat, yaro ne mai shekara biyu.

A shekarun baya ta so Aunty Sakeenat ta bata daya daga cikin yaranta shida, maza biyu mata huɗu, har sunyi magana za ta bata sumayya wacce ke da shekara 8 a lokacin, sai mahaifiyarsu ta ce babu mai bata ƴa, tunda ance ta bar aure ta aura wani taƙi, kar wanda ya bata ƴa.

Daga lokacin kuma maganar ta rushe saboda Fatima ta shaƙar al'amarin.

“Gata tana kuka." Aka kawo Sakeenat dake kuka.

“Ƴar ma akwai haƙuri, kusan 1h bata kusa da ke fa." Ta amsa Sakeenat tana fara bata ruwan nono.

“Na so Mama na da rai ta ga gudan jininta." Aunty Sakeenat ta yi murmushi.

“Rayuwa kenan, amma wani suna za ku kirata da shi?." Fatima ta kalla Yayarta da suke kama sosai.

“Ke za ki zaɓa ai, na baki wuƙa da nama.” Aunty Sakeenat ta riƙe hannun Fatima.

“Na gode ƙanwata, Allah ya raya takwararta, tabbas kin......” sai hawaye.

Fatima ta turo baki tana murmushi .

“Ai na faɗa miki indai na haihu sunanki zansa, saboda ina ji da ke." Aunty Sakeenat ta jinjina kai.

“Ina so a kirata da Adeelah.”

“Adeelah.” Fatima ta maimaita sunan.

“Adalci ko Aunty?.' Aunty Sakeenat ta ɗaga mata kai. Haka suka sha hirar yaushe gamo, suna yi suna tuna rayuwarsu ta baya, wani a yi shewa, wani a yi jimami.

★Gidan nan bai samu hutu ba sai da yamma ta yi, duk an watse sai wa'inda za su kwana, dan akwai masu zama har suna, daɗinta gidan babbane, a ranar Alhaji Nura ya dawo gida ɗauke da kayan wasa harda su Dolly, keken yara, da abubuwan da duk yaro mai yawo ke wasa da shi.

Ita kanta Fatima da ta ga kayan dariya ta kwashe dashi, dan babu wanda za'a ba Adeelah a yanzu da sunan kayan wasa.

Haka ya jibge mata a wani ɗaki da tun da aka samu cikin ya ce na abinda aka haifa ne, ciki ya kai kayan, sannan ya kalla Fatima da ta ta yashi jera kayan.

“Gobe zansa a kawo gado da babban wardrobe, launin mata....uhmmm pink ko purple, kinsan ya nake so ɗakin nan ya koma?.” ya faɗa yana bin kowani ƙusurwa na ɗakin da kallo.

Fatima ta matsa kusa dashi ta rungumesa ta baya, a tare suka sauke ajiyan zuciya.

“Ka bari ta girma ta zaɓa ra'ayinta, ba lalle launin take so kenan na. Karku samu Banbancin Ra'ayin." Murmushi ya yi.

“Shike nan amma Adeelah ba za ta ƙi duk ra'ayin da na zo mata da shi ba, ina so mu raine ta cike da kulawa da soyayya." Ta sake shi sai ya juyo yana kallonta.

“Allah ya bamu ikon rainon ta.....ameen." suka yi murmushi.

“Hmmmm Sakeenat Nura Saleh." Ta kuma faɗa tana jin kaman mafarki wai ita ce da ƴa.

“Haka za ta dinga amsawa a school *‘Yes Madam.’* " dariya suka sa saboda yadda ya kwaikwaya maganar yara, sun ɗau lokaci a haka suna fira kuma duk akan Adeelah, bayan sun gama suka fita kowa ya nufa part ɗinsa dan ƙwanciya.....................

*Hayin Ɗan Mani.*

“Ta mutu....... innalillahi wa'in.....” da sauri Zulee ta katse sa.

“Uhmm alhamdulillah dai, wai kamanta ko ba ta mutu ba kasheta zamu yi, to Allah yana son mu da Rahma shi yasa ta mutu tun kafin mu aikata zunubi." Ta faɗa babu ko ɗigon tausayin A'isha a ranta.

Lokaci guda suka kalla Jaririya da ta fashe da sabon kuka, suka kalla juna suka sake kallon jaririyar.

“Ya zamu yi da ita to?." Ya faɗa yana share hawaye tare da miƙewa tsaye.

“Yauwa Mijina, yanzu ka bari Ni zan tsafta ɗakin gaba ɗaya, na mata wanka, kai kuma kasanar ta rasu bayan ta haihu, da an zo a ɗauke a bar gidan nan da ita, ba shike nan ba."

“Kin iya wankan gawa ne?." Ta yi murmushi.

“Wasu ma haka ake kaisu ba wanka, to ko wanketa na yi da ruwa da sabulu ai ya yi.” kai ya ɗaga yana kallon yarinyar.

“Ya za mu yi da wannan!?.” Zulee ta kalla Jaririyar.

“Mu danna mata pillo ta bi mahaifiyarta shike nan.” hannun Zulee ya riƙe.

“Hmmm kice a zarge Ni da ƙyau, abinda zai faru ita yarinyar a barta na wani lokaci, kinsan mutane ba ƙaramin haushina suke ji ba akan ina cutar da A'isha, kawai mu barta tukun.”

“Shike nan to." Da haka shi da ita suka shiga aikin gyara ɗakin A'isha, suka kwashe jinin da ya zuba tas dan zuwa yanzu jinin ya tsaya daga zuba a jikinta.

hypo Zulee ta ɗauko suka yi mopping ɗakin, sanan a tare suka mata wanka soso da sabulu sai suka suya mata kaya suka kwatar da ita kan gadon zuwa lokacin jikinta duk ya sanƙare.

Bashir dai dauriya yake amma har cikin ransa yana jin be ƙyauta ba sam.

Haka suka yi shela Aisha ta rasu, wasu sun manta ma akwai wata A'isha dake rayuwa a gidan, wasu kuma sun zaci ta yi tafiya ne.

Mutane suka cika gidan ana ta matsar ƙwalla, ciki harda Zulee dake riƙe da jaririya wacce ta yi shiru abin tausayi.

Ko da mutane suka fara watsewa kowa yana ma Zulee fatan ta riƙe amanar marainiyar da aka bari, Jaririya da ta tun faɗowarta duniya ba ta sa komai a baki ba, ta fara neman abu hakan yasa ta fara kuka, Zulee ta goyata a baya tana ta jijjiga, har dai mutane suka watse.

Bashir ya shigo gidan, ya shiga ɗakin Zulee, daidai nan take sauke goyon tana cewa.

“Ke dalla kimin shiru.” ta faɗa harda harran jaririyar.

Bashir ya zauna cikin jimami, A'isha ta yi mutanen da ya sa jikinsa ya mutu, bayan an fita da ita mai Unguwa yasa aka kaita gidan me gari, aka sake mata wanka, da yake a nan ƙofar gidan sarki ake sallar juma'a, bayan an idar aka salla ce ta, kowa ya ji wajen haihuwa ta rasu, sai mata Barka ake dan ta yi shahada, bayan idar da sallar yara da manya suka rakata makwancinta, idan yace jikinsa be mutu ba ya yi ƙarya.

“Ɗauke ta na gaji da ba ta haƙuri, ina dalili yarinya sai kuka." Zulee ta faɗa tana ɗaura mai Jaririyar a jikinsa, sai ya kallata da ƙyau.

Yarinyar ja ce sosai, wacce ke nuni da baƙa za ta koma, ga shi tun tana Jaririya fuskar A'isha gareta sak, yarinyar sai neman nono take, tana ta motsi da bakinta, tare da tsotsa leɓe.

A hankali ya kalla Zulee da ke latsa waya.

“Baby tana jin yunwa sosai, ki taimaka ki shayar da ita ko na wani lokaci ne.” ya kai nan yana kallon Zulee.

Zulee ta zaro ido yana aje wayar dake hannunta.

“Me...me kace?."

“Ki taimaka ki shayar da......” hannu ta ɗaga mai sannan ta girgiza ƙirjinta, manyan dukiyar fulaninta suka fara rawa kamar mazari.

“Ga gansu nan, kallesu da ƙyau, wallahi bana shayar da yara bane, ko haifa ɗa na yi ba zan iya shayar da shi nono na ba, dan ina son kayana." Ta kai nan tana dena kaɗasu.

“Ai nasani wannan dukiyar ta wace, to ya za'ayi da yarinyar tana jin yunwa?."

“Hmmm zan maka taimaki ɗaya, ka siyo Dano milk zan kaɗa na bata.” murmushi ya yi.

“Yauwa Zulee shi yasa nake ƙara sonki, kina da tausayi sosai.” ya faɗa yana aje yarinyar kan kujera.

“Sakeenat jira na siyo madara ki sha, nasan kina jin yunwa” da haka ya yi hanyar fita ya fice, Zulee ta kalla Jaririyar, sai ta saki wani shu'umin murmushi, ta miƙe ta isa inda take kwance tana shan hannu cikin zalama.

“Sakeenat, suna mai daɗi, Bara na raba ki da duniyar nan kowa ya huta dan ban shirya raino ba wallahi.” ta faɗa tana janyo pillow dake kan kujera, sannan ta ɗaura kan fuskar Jaririya Sakeenat dake ƙananun kuka na yunwa, sai tsotsan hannu take kaman ta ci babu, pillown babbane hakan yasa ya rufe mata gaba ɗaya jiki. Zulee ba ɗigon tausayi ta kai hannunta, gefe da gefen pillown ta danna..........................✍️ END

> Hmmm guy's pretty Sk ta ɗibo da zafi, ku shirya kawai, SAKEENAT daban ne, salon, tafiyar da komai, ku dai kasance da Ni, dan jin labarin SAKEENAT su biyu, kowacce da ƙaddararta.....hmmmmm 🫠 🫠 🫠 🫠 na yi shiru dai 👋😅.

╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*