SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER 3

by @prettys01

> “Sakeenat, suna mai daɗi, Bara na raba ki da duniyar nan kowa ya huta dan ban shirya raino ba wallahi.” ta faɗa tana janyo pillow dake kan kujera, sannan ta ɗaura kan fuskar Jaririya Sakeenat dake ƙananun kuka na yunwa, sai tsotsan hannu take kaman ta ci babu, pillown babbane hakan yasa ya rufe mata gaba ɗaya jiki. Zulee ba ɗigon tausayi ta kai hannunta, gefe da gefen pillown ta danna........................

“Assalamu alaikum." Ta ji an raɗa sallama daga ƙofar ɗakinta, hakan yasa ta yi saurin cire pillow tana ɗaukan Sakeenat wacce ta ke kuka mara sauti.

“Wa.... wassalamu Alaikum shigo." Ta faɗa bayan ta sanya hijab.

Mata biyu suna sake sallama sannan suka shigo, ta musu Barka da zuwa tana jijjiga Sakeenat.

Gaisawa suka yi cikin mutumci.

“Dama sarki ne ya aiko mu, ga wannan na Jaririya, sannan duk sati za mu dinga zuwa dubata tare da kawo mata sadaƙar da ake tara mata fisabilillah domin maraicinta." Cewan ɗaya tana aje mata dubu ɗari da hamsi.

Zulee ta ɗan zaro ido, tana sake kallon kuɗin.

“Yanzu wannan na Ƴa ta ce?.” suka ɗaga mata kai.

Ta tsugunna ta kwasa kuɗin tana jera musu godiya.

“Karki damu, Sarki da kansa ma ya ce a gaishe ki,......... Allah ya ba ki ikon riƙe amana.”

“Ameen! Ameen!!." Da haka suka fita, suna fita ta a je Sakeenat, ta riƙe kuɗin da ƙyau, sai ta kalla Sakeenat take zuciyarta ta raya mata. ‘Macece, ana arziƙi da mace, za ki iya barinta ta rayu ko dan nan gaba ta zama miki babbar hannun jari, tunda tana da ƙashin arziƙi...'

murmushi ta yi tana ɗaukan Sakeenat, wacce jikinta ya yi zafi sosai, idanunta suka fara yin yellow, ta dena kuka zuwa lokacin, sai ƙirjinta dake bugawa sosai da sosai.

Bashir ya shigo da sallama, ta yi saurin miƙa mai Sakeenat, ta amsa ledar hannunsa, da sauri-sauri ta dama madara biyu a kofi da ruwan ɗumi, ta amsa ƴar, shi dai sai mamaki yake, ga kuma kuɗin da ya gani a kan kujera.

Da cokali ta shiga ba ta, Sakeenat ta fara amsa a hankali.

Zulee ta tuna ana ma yara ɗure, dan haka ta matse bakin jaririyar ta fara ɗura mata ganin za ta ɓata mata lokaci.

“Zulee Bara na ɗauko fida." Da haka ya fita cikin sauri, ya dawo riƙe da fida, Zuwa lokacin jikin Sakeenat duk ya jiƙe da madarar.

Zulee ta ɗura a fidar sannan ga shiga ba ta a hankali, Sakeenat dake mugun jin yunwa ta sha sosai har sai da ya ƙare, sai ta shiga tsotsan leɓe.

Zulee ta sauke ajiyan zuciya tana lumshe ido.

“Baby na ga duk kin fita hayyacin ki lafiya?.” ta buɗe ido tana kallon Sakeenat da barci ya kwashe ta.

“Zamu raina yarinyar nan har girmanta, dan yarinyar tana da ƙashin arziƙi, dubi kuɗin da aka kawo da sunan a kula da ita." Ya ɗan zaro ido.

“Haba da gaske?."

“Sosai ma kuwa, dan haka zamu raineta, nan gaba ta zama mana dukiya, kasan dai mace.” ya zauna yana murmushi.

“To da madara kawai za ta rayu, ai ana son ba jarirai ruwan nono domin yana......."

“Bashir...... Bashir, wallahi nonuwana bana Shayarwa bane, ka dinga siyo mata nonon shanu, sai mu dinga haɗa mata da madara, amma Nonona haramiyarta." Ta kai nan tana ɗauke kai daga kallonsa.

“Shike nan, Zulee.....Zulee Baby, ai wannan kadaratace Ni kaɗai, muje ciki abani na sha, ina bukatarsa." Ya faɗa cike da bariki, ta yi murmushi tana mai fari da ido, da haka suka kwantar da Sakeenat a kan kujera suka yi cikin uwar ɗaki.........

★ Sun jima a ciki suna sheƙe ayarsu, kafin suka fara jiyo sautin kukan Sakeenat, wanda ke fita a hankali.

Zulee ta ja ƙaramin tsaki tana ture Bashir gefe.

“Oh Babyna, badai kukan........”

“Ta dameni, gaskiya ka yi wani abu.” ta faɗa tana juya mai baya.

Bashir cikin sauri ya ja zani tare da suturta jikinsa ya yi parlour, yana fita da minti 2, Sakeenat ta yi tsit, kaman an yi ruwa an ɗauke.

Ya dawo cikin uwar ɗakin yana mata murmushi.

“Ya na ta yi shiru lokaci guda!?.” ta tambaya tana gyara kwanciyar nata.

"Karki damu Baby, na sa mata ƙyalle a baki. Ba za ta ƙara damunmu ba."Murmushi suka yi a tare, sannan suka ci gaba daga inda suka tsaya.

Baiwar Allah Sakeenat, tana kwance tana fitar da numfashi da ƙyar, dan kuwa ƙaramin ƙyalle ya naɗe ya tura mata cikin baki, Sakeenat tana kuka tana wutsil-wutsil da ƙafafunta cikin azaba.............

*Millinium City*

_Yau take suna_

Tun kafin hasken safiya ya mamaye sararin samaniya, gidan Alhaji Nura ya riga ya sauya kamanni. Idan ba wanda ya san gidan ba, da zai rantse sabon katafaren event center ne aka buɗe.

Daga bakin gate ɗin har zuwa cikin harabar gidan, an shimfiɗa jan carpet mai tsananin kyau, gefensa kuma aka jera manyan flower vase cike da fresh flowers masu ƙamshi.

Balloon masu launuka iri-iri suna lilo da iska, yayin da fitilu masu walƙiya suka kawata bishiyoyin da ke cikin harabar gidan, duk da cewa rana ce, walƙiyarsu na ƙara fito da kyan wajen.

Can gefe kuma aka kafa wata babbar rumfa mai ɗaukar ɗaruruwan baƙi. An lulluɓe ta da farin yadi, sannan aka ɗaure golden da champagne ribbons waɗanda suke ƙyalli idan hasken rana ya bugi jikinsu. Tebura da kujeru kuwa an shirya su cikin tsari irin na manyan bukukuwa, kowanne tebur ɗauke da flower centerpiece da kyandirori masu ƙamshi.

A bayan gidan kuwa, hayaniyar masu girki ce kawai ake ji. Manyan tukwane cike da nama, wasu na juyawa da dogayen cokula, wasu na haɗa kayan miya, wasu kuma na gyara plates cikin sauri. Ƙamshin tuwon shinkafa, miyar taushe, pepper soup, soyayyen nama, grilled chicken da kayan ƙamshi ya gauraye iska, har duk wanda ya zo bakin ƙofar gidan sai ya ji cikinsa ya kaɗa.

Masu decoration kuwa ba su bar ko wani lungu ba. Kowanne kusurwa na gidan an kawata shi da flowers, ribbons da fitilu masu laushi. An tanadi photo booth mai matuƙar kyau domin baƙi su ɗauki hotuna, yayin da aka kafa wata babbar kujerar sarauta da za a zaunar da Hajiya Fatima da jaririya idan lokaci ya yi.

Tun ƙarfe goma na safe, manyan motoci suka fara shigowa jere bayan jere. Prado, Lexus, Mercedes, Range Rover da sauran motocin alfarma suka cika harabar gidan. Baƙi kuwa sai shigowa suke yi cikin shiga ta alfarma, kowa na tafe da kyaututtuka masu tsoka.

A wani gefen rumfar, fitaccen mai kiɗi ya zauna tare da tawagarsa. Da zarar ya ɗaga microphone ya fara rerawa, wajen ya ɗauki amo. Mata suka fara tafa hannu, wasu na kaɗa kai, wasu kuma na ɗan taka rawa cikin mutunci. Sautin ganga da kalangu suna gaurayawa da muryarsa, suna ƙara wa bikin armashi.

Hajiya Fatima kuwa... ranar tamkar an saukar da sarauniya ce daga fada. Wani leshi na alfarma mai launin emerald green ta sanya, wanda aka yi masa aiki da Swarovski stones masu walƙiya. Gele ɗinta ya zauna tamkar an zana shi, yayin da diamond set da ke wuyanta, kunnuwanta da hannayenta ke kyalli da kowace motsi da za ta yi. Fuskarta cike take da annuri, murmushinta kuma ya ƙara bayyana farin cikinta.

Sai kuma tauraruwar ranar... Adeelah.

An kwantar da ita cikin wata stroller mai tsananin kyau, wadda aka kawata da farin tulle da flowers. Kayan da ke jikinta na musamman ne, farin lace mai laushi haɗe da golden embroidery, ƙaramin rawani ya zauna a kanta tamkar gimbiya. Ƙananun safar hannunta da takalmanta duk sun yi matching da kayan jikinta. Duk lokacin da ta buɗe idanunta ko ta yi ɗan murmushi, sai a ji ana cewa,

"WOW... Allah ya raya mana ita."

Mata suna ta yin layi domin ɗaukarta, wasu suna manna mata kuɗi, wasu kuma suna yi mata addu'o'in fatan alheri.

Kamarar masu ɗaukar hoto kuwa ba ta daina walƙiya ba, domin kowane ɗan lokaci ana son a adana wani kyakkyawan yanayi na wannan rana mai cike da tarihi a gidan Alhaji Nura.

Sai wajen ƙarfe goma sha ɗaya na safe ne gidan ya fara ɗaukar ainihin armashinsa. Baƙi na ci gaba da shigowa babu ƙaƙƙautawa. Kowace mota da ta tsaya a bakin gate, masu tarba kan yi saurin ƙarasa suna buɗe ƙofa cikin girmamawa. Ana karɓar baƙi da murmushi, ana musu jagora zuwa inda aka tanadar musu domin zama.

A gefe guda kuma, matasa sanye da uniform fari da golden waistcoat suna kai da komowa, wasu na rabon drinks, wasu na miƙa bottled water, wasu kuma na karɓar kyaututtukan da baƙi suka zo da su.

Wani sashe na falon kuwa ya kusa cika da manyan hampers, kayan jarirai, atamfofi, lesuna, da kuma manyan envelopes da aka kawo cike da kuɗaɗe.

"Wallahi Alhaji Nura ya kashe kuɗi."

Wata dattijuwa ta faɗa tana kallon yadda komai yake cikin tsari.

"Ba kashe kuɗi kaɗai ba, kin ga yadda komai yake tafiya ba tare da hayaniya ba? Wannan shiri ne na mutanen da suka san abin da suke yi."

Abokiyar zamanta ta amsa tana gyara zaman gyalenta.

A can gaban rumfa kuwa, mai kiɗi ya canja salo. Ya fara yabon Alhaji Nura da iyalansa, yana ambaton karamci da mutuncinsu. Lokaci-lokaci sai a ji ana tafa hannu, wasu kuma su miƙe su liƙa masa kuɗi cikin farin ciki.

Daga cikin gidan ne aka ga Hajiya Fatima ta fito riƙe da Adeelah a hannunta.

Nan take idanuwa suka koma kansu.

"Allahu Akbar..."

"Wow kwanin burgewa ?"

"Innalillahi...ga kyawu d Iya kyawu!"

Maganganu suka fara tashi daga bakin mata.

Hajiya Fatima tana taku a hankali cikin nutsuwa, yayin da wasu 'yan mata biyu ke biye da ita suna gyara doguwar mayafinta kada ya taɓa ƙasa. Duk inda ta gifta sai a buɗe mata hanya cikin girmamawa.

Adeelah kuwa tana kwance cikin nutsuwa a ƙirjinta, tana ɗan motsa ƙananun hannayenta lokaci-lokaci. Fuskarta cike take da annuri, kamar yadda hasken rana yake sauka a kanta yana ƙara fito da kyawunta.

Da suka isa kujerar da aka tanada musu, aka taimaka wa Hajiya Fatima ta zauna. Nan take masu ɗaukar hoto suka yi musu ƙawanya.

"Madam, look here..."

"One more picture please..."

"Smile..."

Walƙiyar camera ta cika wajen, ana ɗaukar hoto ta kowane salo.

Ba da daɗewa ba, aka kawo manyan trays cike da kayan ciye-ciye da drinks aka fara zagayawa da su tsakanin baƙi. Yara kuwa farin cikinsu ya ninka, domin an tanadar musu da popcorn, ice cream, cupcakes da chocolates iri-iri.

A daidai lokacin ne Alhaji Nura ya fito cikin shiga ta alfarma. Farar babban riga ce ta alfarma da aka yi wa ɗinkin zare na zinariya, hularsa kuwa ta yi matuƙar dacewa da shigar. Agogon hannunsa da takalmansa kaɗai sun isa su nuna irin matsayin da Allah Ya ɗora shi a kai.

Da fitowarsa, baki ɗaya mutanen wajen suka miƙe tsaye suna gaishe shi.

Ya dinga amsa gaisuwa cikin fara'a, yana musabaha da manyan baƙinsa, lokaci-lokaci yana cewa,

"Barkan zuwa. Allah Ya saka da alheri da kuka samu lokaci kuka zo."

Duk da tarin jama'ar da suka cika gidan, fuskar Alhaji Nura ba ta nuna gajiya ba. Farin cikin da yake ciki ya fi ƙarfin komai, domin yau rana ce da zai sanya wa Adeelah suna tare da iyalai, abokai da masoyansa.

A taƙaice dai, gidan ya cika da shagali da annashuwa. Alhaji Nura bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen kashe kuɗi domin ganin komai ya gudana cikin tsari da armashi. Haka kuma, manyan abokansa sun iso tun daga Abuja musamman domin su taya shi murnar wannan babban al'amari da Allah Ya hore masa.

Abokan nasa huɗu ne kacal, amma kallonsu kaɗai ya isa ya tabbatar wa mutum cewa ba ƙananan mutane ba ne. Dukkansu sanye suke cikin tsadaddun suit masu ƙayatarwa, takalmansu na sheƙi, agogon hannunsu da sauran kayan adonsu kuwa sun ƙara fito da kamala da ƙimarsu. Kowa a cikinsu mutum ne mai yalwar arziki, daraja da kuma kwarjini.

Ba wai kuɗi kaɗai Allah Ya hore musu ba, har ilimi da ƙwarewa ma sun yi zarra. Dukkansu fitattun lauyoyi ne masu kare manyan shari'o'i a Kotun Ƙolin Najeriya (Supreme Court of Nigeria) da ke Abuja. Sun shahara wajen gudanar da manyan shari'o'i masu sarkakiya, lamarin da ya sa sunayensu suka yi fice a faɗin ƙasar nan. Matsayinsu da ƙwarewarsu ne suka sa ake girmama su a duk inda suka bayyana.

Ya Allah, anci ana sha an yi ma wasu guzuri a wajen, duk da ma harkan girma da girma ne, dan gaba familynsu kowa a jiƙe yake da kuɗi.

Jinin da kuwa aka yanka sai dai kawai ace Allah ya raya SAKEENAT (Adeelah).

Bayan an gama Shagali, zuwa dare an ragu sosai, wasu nan suka kwana, wasu kuma sun koma gidajensu, kowa cike da farin ciki da fatan tsayin rai ga Adeelah........................✍️ End.

╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*