SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER4

by @prettys01

> Bayan an gama Shagali, zuwa dare an ragu sosai, wasu nan suka kwana, wasu kuma sun koma gidajensu, kowa cike da farin ciki da fatan tsayin rai ga Adeelah................

*Hayin Ɗan Mani.*

★ A al'adance kowani jariri, duk bayan dan kwanani, za'a ga sauya a tare da su, ko su cika, ko su ƙara haske, ko dai wani abu, amma banda baiwar Allah nan, cikin kwanaki shida da suka zo suka wuce kaman walƙiya, rayuwar Sakeenat abin ba'a cewa komai, baiwar Allah, sau uku ake dama mata madara, shima sai Zulee ta yi da gaske take bata.

Pampas kuwa tun safe idan ta sa mata sai dare ake cire mata, duk fisarin da za ta yi ko bayan gida, bata wanke mata, sai idan Bashir ya dawo daga kasuwa.

Yarinya duk ta tsure, ba kayan arziki, ba abincin arziƙi, balle a zo akan magunguna da ya dace ta sha.

Zulee dai kan mata kokarin ɗaya, idan ta ji jikin Sakeenat ya yi zafi kamar wuta, takan jiƙa paracetamol a ludayi ta ɗura mata.

Baiwar Allah tun tana kuka idan yunwa na damunta har ta dena, sai dai ta yi ta ƙyafta ido, ko kuma idanunta su sauya launi.

Tsoran kar su rasata, shi yasa suke bata magani da kula da ita, wasu lokacin.

Wasa-wasa haka rayuwar Sakeenat ya fara miƙewa, kullum jiya iya yau.

Idan Bashir ya fita aiki, babu mai kula da ita, dan Zulee harkokinta sun ishe ta.

★ Kamar kullum, kwance take a kan kujera, cikin wani kaya wanda kasan tsumma, hannunta da shine abokin tsotsanta, yana cikin baƙi tana tsotsa, yayinda idanunta suke kan fanka dake ta juyawa.

Yau watan Sakeenat uku, amma babu wani ci gaba a jikinta, a tsamure take, ta koma baƙa wuluk, sai dai gashin kanta wanda yake a nannaɗe, ya taru ya cika sosai, yadda kasan kan babban mace.

Idan ka kalla Sakeenat, za ka iya cewa wayau kawai ta ƙara, amma jikinta kamar yadda ta zo duniya ne.

A hankali ta fara kuka mara sauti, tana yi tana cille ƙafafaunta sama, dan yunwa take ji sosai.

Zulee take kwance a uwar ɗaki ta fito tana tuna tun safe ba ta sake bata komai ba.

Kallon Sakeenat ta yi, ta taɓe baki tana cewa.

“Ke dai taurin rai gareki, hakan ke nuna min za ki jura ko wani irin wahala......Allah ya kawo mana ke ne dan mu more ki, tun a yanzu na gama tsara duk abubuwan da za ki yi idan kin girma, wanda zai kawo mana kuɗi mai yawa.......“ ta ɗauketa ta ɗaurata a jikinta.

Madarar da ta kaɗa ta kai nata bakin, ta ɗan tsotsa kaɗan, sannan ta fara ba Sakeenat.

Take yarinyar ta fara zuƙa cikin haɗama saboda yunwar da ya cita sosai.

Zulee ta ƙura mata ido.

“Idan kika girma tabbas za'a yi kyakkyawar mace, sai da baƙa kamar uwar ki, bleaching zan fara miki, ki fes dan ki nemo mana kuɗi masu yawa..........da fari ki mana bauta har ki girma, lokacin da kika zama babbar mace, zan daura ki kan tsohuwar sana'a ta.....wayyo kai ƴa mace duniya ne wallahi.“ ta kai nan tana murmushi.

Sakeenat na gama sha, ta kwantar da ita, ta koma uwar ɗaki.

Itama kuma barci ya ɗauketa mai daɗi.

Bashir kuwa sai bayan magrib ya shiga gidan, hannunsa ɗauke da leda amma fuskarsa kana kallo za kaga damuwa sosai.

Yana shiga parlour ya iske Sakeenat kwance Kamar kullum, sanyi ya ɗanji a ransa wanda bai san na menene ba.

Ledar ya fara ajewa, ya ɗauketa, ganin pampas dinta a cike, yasa ya yi waje da ita, a bakin pampo ya wanke mata da ruwa mai sanyi.

Sanyin ruwan ya sa ta buɗe baki ta fara kuka, Bashir ya yi murmushi yana cewa.

“Kin samu waje harda kukan jin daɗi ma kika fara ko.“

Bayan ya gama wanke mata, ya rungume ta ya koma ɗaki.

Ya kwantar da ita yana kiran sunan Zulee.

“Baby! Baby!! Baby!!!"

Zulee ta fito ba tare da ta amsa ba.

Sanye take da wasu fitinannun kaya, wa'inda suka matseta sosai, ta iso gabansa tana ta ranƙwada, murmushi ya sakar mata yana mata muhalli da cinyoyinsa.

Ta zauna tana karantar fuskarsa.

“Meke damunka Baby!?.“ ya sauke ajiyar zuciya mai karfi.

Lokaci guda damuwa ta sake mamaye shi.

“Zulee, komai ya ƙare, na rasa ya zanyi, kowani sana'a na fara sai dai na yi asara, yanzu gaba ɗaya kudin da muke da shi, babu, daga wannan gidan, sai ɗayan wanda yake wancan unguwar, Gashi harkokin basa gaba basa baya............komai ya tsaya cak.“

“Na baka shawara!?." Kai ya ɗaga mata.

“A ganina ka sai da wannan gidan, ka bude provision, tunda ka guje tsohuwar Sa'anarka, wacce ta fi kawo maka kuɗi.“

“Bana so na koma harkan bariki, buɗe dai shagon zai fi.“

“Yauwa, to sai mu bar unguwar nan, in ya so duk ƙarshen wata ka dinga zuwa wajen Sarki, kana amsa kudin marainiyar nan.............“

“Eh hakan zai fi, Nima ina tsoron kar wata rana su Shammace zuwa duba yarinyar nan, za mu ji kunya, kuma kinsan Sarkin Dan Mani, akwai horo, ba bincike, kwanda mu tattara mu koma cikin rigasa.

Da haka suka tsaida matsaya.

A kuma wannan satin suka koma cikin rigasa, wani gida madaidaici.

Yayinda Bashir ya bude shago daga wajen gidan.

Abinda bai sani na shine, kusan rabin dukiyar Sakeenat yana wajen Zulee, ta kwasa kudaɗe masu yawa daga banking Bashir, ta kwasa wasu takardun filaye da gidaje, ta kuma ɓoye su.

A nan rigasa rayuwarsu ta ci gaba da tafiya.

Sakeenat har ta shiga wata takwas, a lokacin ta fara murjewa, dan tunda ta fara cin abinci, ta yi sallama da tsotsewar jiki.

Yarinya ta fara narka ƙiba, ta yi naman wuya, ta cure waje guda, dama tana da jikin ƙiba, wahala ce kawai.

Sai gashi cikin ikon Allah ta murje, dan tana samun abinci sosai, kuma komai ta samu ci take, tun a lokacin tasan ta zauna ta ci abinci da kanta.

Haka bakinta ya fara buɗewa da kalmar Baby, dan haka Bashir ke kiran Zulee, itama ta kirasa, sai kalmar ya shiga bakin Sakeenat.

Ranar da ta furta kuwa, ta sha duka wajen Zulee, yadda kasan ta samu babbar mace, haka ta mata shegen duka, wai ta kira ta sunan Baby, ita ba uwar banza bace.

Daga wannan lokacin sai suka fara koya mata cewa, Baba da Mama.

Cikin ikon Allah Sakeenat ta kama, ta fara kiran iyayenta da sunayen.

★Akwana a tashi babu wiya wajen Allah, Sakeenat an girma an kai shekara 11, ba boko ba islamiyya, sai aikin gida wanda ta take yi babu dare babu rana.

Wanki, wake-wake, shara, guga, girki, da komai na cikin gidan nan ita ce, gaba ɗaya ba ta da lokacin hutu, dan ma ƙibar ta ta, na gado ne, da tuni ya zube, sai dai duk da wahalar nan a cike take tam, yadda kasan ana hurata.

Duk wanda zai ganta zai rantse da Allah ta kai sha biyar, saboda irin jikinta, sai dai baƙace sosai, baƙin da mai shaning.

Ga manyan idanuwa farare, dogon hanci, haka tana da dogon gashi mai tsawo baƙi.

Har yanzu suna rayuwa a wannan gidan nan, inda Bashir ya koma sai da kayan miya saboda kowacce irin sana'a ya kama babu ci gaba.

★Sanye nake da wata tsohuwar rigar atamfa, rigar ma duk ya matse Ni saboda ƙiba, haka ina tafiya jikina ko ina yana rawa, dan irin riƙaba har tsoro yake bani.

Tukunyar dake gabana na buɗe, na zuba albasar dana yanka kam jollof ɗin shinkafa, na kulle.

Hutar na gyara, sannan na miƙe na fita a kitchen din.

Kayan Baba da Mama nake wanke wa, su na ci gaba da yi, ina yi ina ɗan rera waƙan da nake yawan jin Mama ta kunna, har ya shiga kai na ya zauna, duk kuwa da waƙar gaba ɗaya bana arziki bane.

Haka har na gama wankin, na sauri abinci, na juye a cikin kula, bayan na zuba nawa na ci na ƙoshi, dan tabbas idan Mama ta dawo za ta iya hanani abinci.

Bayan na ƙoshi, na sake share tsakar gidan mu tas, na zauna daga gefe ina jiran dawowar iyayena.

Duk wanda ya kalla fuska ta yasan ina da damuwa, ba kuma komai bane sai ina so na dinga zuwa makaranta kaman sauran yara, ko da islamiyya ce, amma Mama ta rantse bani da makaranta, wai kar idanuna su buɗe na dena mata biyayya.

Matar da ko inuwarta na gani, jikina ɓari yake saboda tsoro, ta riga ta dasa min wanan tsoron tun ina ƙara.

“A hanye.......cas." na ji babbar ƙawar Mamarmu ta furta daidai lokacin da suke shigowa gidan mu.

Miyau na haɗiye da sauri, na nufesu, na tsugunna ina yaushe da su.

Babu wacce ta amasa, suka wuce ciki suna hira, kan ta burma suka zauna.

“Ke munafuka zo nan." Gabana ya buga, dan a iya sanina ban yi ma Mama ko mai ba.

Jikina yana min nauyi wani lokaci, amma haka ta ɗan yi gudu zuwa inda suke na tsugunna.

“Kawo mana abinci, ga wannan naman ki dafa ki soya, a ƙirge yake, Allah yasa na ga babu guda, wallahi sai na ci ubanki, shegiya kawai."

“To Mama yanzu zan ɗaura.“ na ɗau Naman na wuce, ba tare da na damu da zagin da ta min ba, dan na sa da shi.

Kular guda na fito da shi tare da plate, na duegushe na zuba musu.

Mama na fara aje mawa, sai Aunty Duwais, daga nan na miƙa ma na karshe, wanda take bani dariya sosai.

Na rasa gane mace ce ko namiji, kullum dai cikin jallabiya yake, sai zani a kirji, yayinda hannunsa suka sha lalle, sai dai kan shi babu gashi gaba ɗaya, sai ɗan ƙwali da yake ɗaurawa, sannan tafiyarsa da maganarsa irin ta mata ce, muryarsa kuma ya kan matse sosai idan zai yi magana, ma'ana dai Ɗan daudu, kuma na gaban gashin Mama.

“Aunty Shanawa ga abinci." Baki ya washe.

“Yauwa Ƴar Lukuta." Ya faɗa cike da karya murya, ko wata macen albarka.

Da haka na tashi na koma kitchen, ina aiki, ina ji suna ta hira, wanda gaba ɗaya akan wani gidan da suke kasuwanci ne, Mama tana son mu koma rayuwa a can, amma Baba ya hana.

“Ku dai bari kawai, yau din nan sai mun tsaida matsaya idan ya dawo, Bara dai ya shigo." Mama ta faɗa tana ɗan wuci.

“Karki damu Garkuwar mata, zai amince......yanzu dai na ga Ƴar Lukuta ta fara girma, a hankali ki fara nusar da ita, ki fara nuna mata hanyar.......sai dai wannan ƙibar ta ta, akwai matsala, ya yi yawa, kisan abin yi gaskiya......." Aunty Duwais ta faɗa tana kai abinci bakinta.

Aunty Shanawa ya ce.

“Haka ne gaskiya, tana da ƙyau sosai, amma ƙibar nan akwai matsala, sannan ki sanya makaranta, bariki yanzu idan kana da ilimi ya fi kawo kuɗi.....“

“Shanawa bana so ta samu ilimi mai yawa, wanda zai sa ta guje aikin da za ta dinga yi."

“A'a, ai tana jin tsoron ki sosai, ke kinsan yadda za ki yi da ita." Da haka suka dinga ba juna shawarori.

Bayan sun gama cin abincin, suka ci namar da na soya, ko guda ban kai baki na ba.

Mama ta raba musu, suka ci, suka wuce.

“Abinci ya ƙare, gobe ƙyaci.......dole ma daga yanzu ki koma cin abinci sau ɗaya, sannan zan kara miki wasu aikin, dan ki dinga motsa jikin ki, kina ji....."

“Eh Mama." Na faɗa idanuna na kallon ƙasa, dan a maganganunsu, maganar makaranta ce kawai a rai na.

“Za ki fara tuyar a wara a bakin titi daga gobe."

“To Mama." Sai ta yi shiru tana kallona.

“Tashi ki wuce."

“To Mama." Na tashi na ɗau kular da Babu komai na mai da kitchen, buɗewa na yi, na iske babu komai dai a ciki. Kai na girgiza, yanzu Mama babu ruwanta da Baba, ya ci abinci ko kar ya ci, bai da me ta ba, harkokinta sun fiye mata komai.

Na girgiza kai ina zama a ƙasan, shiru na yi ina tunanin gobe zan fara tuyar awara, ta wani fannin na ji dadin, ko Yayane zan dinga hulɗa da mutane, ba kamar zaman gidan nan ba, kullum ina ci babu walwala.

“Sakeenat..." Muryar Baba ya daki kunnuwana.

Cikin farin ciki na amsa na fito da sauri.

“Kawo min abinci, tun safe ban ci komai ba." Ya faɗa yana zama kan taburman da Mama suka tashi.

Shiru na yi dan bansan me zan ce mai ba.

Ji na yi an sakar min wani dundu a gadon baya, hakan yasa na gantsare na tsugunna ina rintse ido.

“Shegiya, kin tasa shi da ido, za ki yi gulmar da kika saba ko..........Bashir babu, baka kawo komai ba, ba mu yi girki ba." Mama ta faɗa tana ɗan jinjiga.

Baba ya ɗago Ni daga ƙasa.

Yasan ina jin tsoron Mama, amma bana ƙarya, komai zai faru da Ni, sai na faɗa gaskiya.

“Kunyi girki!?." Ya tambaye Ni.

A hankali na ɗaga kai, ina cewa.

“Eh, amma ya ƙare, Mama da ƙawayenta sun cinye."

“Kinci ke!?."

“Eh kafin ta dawo na ɗiba na ci.”

Mama ta zaro ido.

“Sakeenat sata kika fara..... innalillahi...." ta kai min duka, Baba ya janye Ni yana kallon Mama.

“Ki dena dukanta, ba ta miki komai ba, kuma abinci ki barshi bana ci." Yana kai nan yana jana muka shige ɗaki.

Mama ta bi mu da ido har muka shige ciki.

“Ah Bashir, da sake, na ga ka fara tausaya ma wannan ƴar iskan ne, ka fara jin cewa ƴar kace, to wallahi da sake, a yau din nan ma zan dawo da kai kan hanya." Tana kai nan, ta figa gyalen da ke kan igiya ko bushewa be yi ba.

“Karna dawo na iske kayan nan a igiya......”

Yadda kasan an wurgoni haka na fito, na fara taɓa wa'inda suka bushe.

Mama ta dallamin harara.

“Shegiya kinyi da fuska kamar baƙin zunubi." Ta faɗa tana ficewa daga gidan.

“Mama Allah ya tsare, a dawo lafiya." Na faɗa ina jin kaf duniyar nan ba Ni da sama da ita, duk wahalar nan da nake sha, ina mata wani irin mugun so, mai tsayawa a rai, domin kallon Uwa nake mata...................✍️ End

╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*