SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER 5

by @prettys01

> “Mama Allah ya tsare, a dawo lafiya." Na faɗa ina jin kaf duniyar nan ba Ni da sama da ita, duk wahalar nan da nake sha, ina mata wani irin mugun so, mai tsayawa a rai, domin kallon Uwa nake mata...................

*Millinium City*

Idan akwai kalmar da ya fi na gata, to tabbas shi za'a jingina a rayuwar Adeelah, Hajiya Fatima da Alhaji Nura, suna kula da ita fiye da misali, sun bata ko wani irin gata da ɗa yake samu wajen iyayeynsa, farin cikinta shine nasu.

Tun kafin ta nuna ta furta abinda take so, suke yi mata, haka ta suka raineta har fara zuwa girmanta.

Adeelah, farar yarinya ce mai natsuwa, karku manta Sakeenat ce, dama natsuwa shine siffar su.

Tana da fara'a sosai, amma wani lokacin bata da ƙyau, musamman idan aka kai ta bango, tana hakuri, haka kuma tana tausayi sosai.

Yadda kowani uba da uwa suke fatan ƴar su ta zama, haka Adeelah ta zama ma iyayenta, ta kowani fanni yadda suke burin ta zama, haka ta zama.

A lokacin da ta kai shekara 13, ta haddace Alqur'ani izu arba'in, tare da wasu manyan littafai.

Adeelah akwai son karatu, ga ƙwanya, hakan yasa, ta fanni karatu ba ta da matsala gaba ɗaya.

Ana yawan faɗan, ɗan adam tara yake, bai cika goma ba, tabas haka ne, domin kuwa duk yadda Adeelah take, tana wani abu guda, shine Gundura, badan komai ba, sai Surutu, ta iya tambayi ba'a tambaye ka ba, ta ƙware wajen surutu, tana zama da kai, za ka fara hawa maka kai, saboda rero zance.

Sai dai wasu basa kallon hakan a matsala, domin kuwa, ko wani tambaya da take yi, yana da matukar amfani, tambaya take akan abinda kai kanka za ka so kasan amsoshin sa.........

★Tsantsararren bedroom ne, mai faɗi da yalwa, wanda tun daga ƙofar shiga yake bayyana matsayin masu gidan. Bangayensa an yi mai fentin ivory mai kyau, tare da ƙananan zane-zanen launin zinariya da suka ƙara fito da ƙyawunsa. A saman rufin ɗakin kuwa, wani katafaren chandelier na crystal ne ke rataye, haskensa yana watsewa cikin ɗakin tamkar ana watsa taurari.

Tsakiyar ɗakin wani katafaren gado ne irin na sarauta (King Size), wanda aka ƙera da itacen mahogany mai tsada, aka yi masa sassaka irin na alfarma. An shimfiɗa farin bedsheet mai sheƙi a kansa, tare da duvet mai laushin gaske da matasan kai masu yawa, a ƙalla sun kai ashirin, duk cikin launukan fari da gold masu matuƙar ɗaukar ido.

A gefen gadon akwai bedside tables guda biyu, kowacce ɗauke da fitilar zamani mai haske mai laushi, yayin da aka ajiye turaren ɗaki masu ƙamshi da ƙananan vases ɗauke da furanni na roba masu kama da na gaske.

A ɗaya gefen ɗakin akwai katafaren wardrobe na zamani mai ƙofofin gilashi, wanda aka tsara cikin tsari irin na manyan otal-otal. Cikinsa cike yake da kaya masu tsada, takalma iri daban-daban, jakunkuna da kayan ado, kowanne yana da nasa mazauni.

A kusa da tagar ɗakin kuma an tanadi wani elegant sitting area, mai kujeru masu laushi guda biyu da ƙaramin teburi na marmara a tsakiya, inda aka ɗora wasu mujallu da littattafai masu kyau domin nishaɗi.

Labulen tagogin kuwa masu kauri ne, haɗin farin lace da gold velvet, suna sauka har ƙasa cikin tsari mai ɗaukar hankali. Idan aka buɗe su, hasken rana kan mamaye ɗakin cikin ƙawa, yayin da iska ke ratsawa a hankali.

Ƙasan ɗakin an shimfiɗa wani carpet mai kauri da taushi, wanda idan aka taka shi ƙafafu kan nutse cikinsa saboda laushinsa. A gefe kuma akwai madubin tsaye mai tsayin mutum, mai frame na zinariya, wanda ke ƙara wa ɗakin armashi.

Komai na cikin ɗakin an tsara shi cikin salo na classic da alfarma, babu abin da ya yi yawa, babu wanda ya yi kaɗan. Daga ƙamshin turare da ke yawo a sararin ɗakin, zuwa tsaftar da ke bayyana a ko'ina, za ka tabbatar cewa wannan ba ɗakin talakawa ba ne, ɗaki ne na gidan da kuɗi da jin daɗi suka zama ruwan dare.

Haka kuma kana kallon ɗakin kasan an tsara ma namusamman ne.

A hankali Hajiya Fatima ta murɗa handle ɗin ƙofar, ta tura ta ciki ba tare da ta yi wata hayaniya ba.

Da danna madannin haske, nan take ɗakin ya haska da wani haske mai burge idanun, ya kuma fito daga chandelier na crystal da ke rataye a tsakiyar rufin.

Murmushi ɗauke a fuskarta ta taka a hankali zuwa katafaren gadon da Adeelah take kwance a cikinsa, ta lulluɓe cikin wani pink ɗin bargo mai taushi, Barcin a natse, fuskarta cike da annuri.

Gefen gadon Hajiya Fatima ta zauna, ta shafa lallausan gashin kanta cikin kulawa, sannan ta sumbaci goshinta.

“Princess... tashi mana, lokacin breakfast ya yi.” Ta faɗa cikin muryan kulawa.

Adeelah ta ɗan motsa jikinta, ta buɗe idanunta a hankali, tana kallon Hajiya Fatima da murmushi.

“Good morning, Mom.”

“Morning, sweetheart. Kin tashi lafiya?”

“Very well, Mom.”

“Alhamdulillah. Mu je ki wanke baki?”

Ba musu ta miƙa mata hannu. Adeelah ta kama, Hajiya Fatima ta taimaka mata ta sauko daga gadon.

Hannunta riƙe da na Adeelah suka nufi toilet ɗin da ke cikin ɗakin.

Ya Salam, toilet ne aka yi shi yadda kasan wajen ɗaukan hoto, an tsara, an kashe kuɗi, an yi shi cikin tsari da kyau, idan na tsaya baku labarin toilet ɗin zan cinye lokaci, mu dai je kawai.

Da kanta Hajiya Fatima ta ɗauko brush da toothpaste ɗinta, ta shafa mata MacLean, tana yi mata wasa da hira har dariya ya ƙwace ma Adeelah.

“Mom, kin san na yi mafarki jiya?”

“Da gaske? To za ki ba ni labari yayin da muke karya kumallo, mu dena magana a restroom.”

Adeelah ta gyada kai tana murmushi, suka ci gaba da brush ɗin cikin annashuwa.

Bayan ta gama, Hajiya Fatima ta goge mata fuskarta da wani farin towel mai laushi, sannan suka fito daga ɗakin hannu cikin hannu.

Kai tsaye babban parlour suka nufa.

Da ka taka ƙafarka cikin babban parlour kuwa, za ka fahimci cewa gidan masu kuɗi ne na haƙiƙa. Falon yana da faɗi matuƙa, an shimfiɗa katafaren carpet mai taushi wanda ke mamaye kusan dukkan ƙasan falon. A tsakiyarsa akwai haɗaɗɗun kujerun leather na zamani cikin launin cream da gold, waɗanda aka tsara cikin salo mai kayatarwa.

Tsakiyar kujerun wani babban centre table ne na marmara mai sheƙi, a kansa akwai vase ɗauke da sabbin furanni masu ƙamshi da wasu mujallu na zamani da aka jera cikin tsari.

Bangon falon kuwa an kawata shi da manyan zane-zanen bango masu tsada, yayin da katafaren smart television mai girman gaske yake manne a bango, tare da sound system na zamani da aka ɓoye cikin tsarin ɗakin.

Tagogin falon sun kasance masu tsawo daga sama har ƙasa, an yi musu labulai masu haɗin farin lace da gold velvet, waɗanda hasken safiya ke ratsawa ta cikinsu yana ƙara wa falon annuri.

A kusurwar falon akwai wasu tsire-tsire na ado cikin manyan tukwane na crystal, yayin da ƙamshin air freshener mai daɗi ke yawo a ko'ina, yana sanya duk wanda ya shiga falon jin nutsuwa da walwala.

Falon gaba ɗaya ya haɗa alfarma, tsafta da tsari irin na gidajen manyan attajirai, ta yadda komai da idanu za su kalla zai nuna cewa an kashe kuɗi masu yawa wajen ƙawata shi.

A gefe guda wani babban hoto ne, wanda aka kafesa daga sama.

Hoton Adeelah ne, wanda take tsaye cikin wasu kaya masu tsaɗa, tasha kitso ya zuba har gadon bayanta, shigar sarauniya aka mata, kuma ba ƙaramin ƙyau ta yi ba. Tana tsaye riƙe da wani rufe, yayinda take kallon gefe cikin style mai burgewa.

★ Hannuta cikin hannu Mom suka ƙarasa dining hall.

Wurin ya kasance mai faɗi da ƙayatarwa, an kawata shi cikin salo na zamani. Tsakiyarsa wani dogon dining table ne, an kewaye shi da kujeru shida.

A saman teburin an jera nau'ikan abinci iri-iri cikin tsari; akwai bread, pancake, waffles, sausages, omelette, dankalin turawa da aka soya, fruits kala-kala, cereal, yogurt, tea, coffee, fresh orange juice da sauran abubuwan karin kumallo masu ɗaukar ido.

Bayan sun zauna, wata mata mai kimanin shekara arba'in da biyar, wadda duk ma'aikatan gidan ke kira Maman Daddy, ta matso cikin girmamawa. Ta ɗauko plate, ta fara zubawa Adeelah abincinta cikin kulawa.

Adeelah ta ɗaga kai ta kalleta.

“Maman Daddy, kin yi breakfast?”

Matar ta girgiza tana mata murmushi.

“Yanzu zan je na yi, Princess .”

Murmushi Adeelah ta yi, sannan ba tare da wata-wata ba ta ɗauki plate ɗin da aka zuba mata, ta miƙa mata.

“Ki je ki ci wannan.”

Maman Daddy ta girgiza kai da sauri.

“A'a Princess, nawa yana kitchen.”

Nan take fuskar Adeelah ta haɗe.

“Na sani... amma wannan nake so ki ci.” Ta faɗa cikin shagwaɓa, tana tura plate ɗin gafen ta.

Hajiya Fatima ta kalli Maman Daddy, ta yi mata alama da ido cewa ta karɓa.

Cikin jin daɗi ta karɓi plate ɗin.

“Na gode sosai, Princess. Allah ya miki albarka.”

Adeelah ta yi murmushi mai cike da natsuwa.

“Uhmm... Maman Daddy.”

“Na'am, Princess?”

“Don Allah a dinga ba ma'aikata breakfast da wuri. Jiya na ga anyi Lattin basu.”

Maganar ta sa Maman Daddy kallon Hajiya Fatima, sannan ta sake mayar da idanunta kan Adeelah, murmushi ya bayyana a fuskarta.

“To, Princess. Daga yau In shaa Allah za a tabbatar kowa ya ci cikin lokaci.”

Ta faɗa cike da farin ciki, tana jin daɗin irin zuciyar alherin da Allah Ya yi wa yarinyar.

Ta wuce bakinta har kunni.

A daidai lokacin da suka fara cin abincin cikin nutsuwa, suka ji sautin takun sawu daga saman bene.

Alhaji Nura ne ya sauko.

Sanye yake cikin wata shaddar sky blue mai matuƙar ƙyau, wadda aka yi mata ɗinkin zamani. Takalmansa na fata masu sheƙi sun yi matuƙar dacewa da agogon hannunsa da ɗan ƙaramar hularsa. Ƙamshin turaren da ya shafa ya mamaye wajen tun kafin ya iso dining ɗin.

Da murmushi ya ƙaraso.

"Good morning, my girls."

"Good morning, Dad." Adeelah ta amsa cikin fara'a.

"Morning, Honey." Hajiya Fatima ma ta amsa tana murmushi.

Ya zauna a kujerarsa, Maman Daddy ta ƙaraso cikin girmamawa, Adeelah ta ɗaga mata hannu.

“Ki je zan zuba mai.“ Maman daddy ta wuce tana girgiza kai.

Alhaji Nura ya yi murmushi, yayinda yake kallon Adeelah tana zuba mai abinci tare da haɗa masa tea.

"Thank you."

"You're welcome, Dad."

Shiru ya ɗan ratsa wajen, kowannensu yana cin abincinsa cikin nutsuwa. Sai can Alhaji Nura ya kalli Adeelah yana murmushi.

“Mom da gaske abinda na gani a TV jiya!?......wani babban jirgin ƙasa ya ɓace, wanda ke ɗauke da mutane dubu biyu da dari uku da sha biyar....“ Adeelah ta faɗa ba tare da kalla Mom ba.

“A wani unguwa!?.“

“Mumbai ake ƙasar india.........al'amarin sam babu daɗi, tsakanin shekaran jiyq zuwa yau, gaba ɗaya garin ya girgiza....shuban dake.......“

“Adeelah time for breakfast.“ Mom ta katseta, dan yanzu za ta fara zuba kamar kanya.

“Okay......Dad yau za ka tafi Abuja ko!?.“ kai ya ɗaga mata.

“Ok."

"Princess..."

"Yes, Dad?"

"You are really trying. Kina da ƙoƙari sosai, ga iya tambayoyi, ga son bincike... why not ki zama lawyer kamar ni?"

Ya ƙarasa maganar yana murmushi.

Hajiya Fatima ta girgiza kai tana ɗan dariya.

"No... tana da tausayi sosai. I think doctor zai fi dacewa da ke. Kina da soft heart sosai."

Ta juya ta kalli Adeelah.

"Ko ba haka ba?"

Adeelah ta yi musu murmushi, ta ajiye spoon ɗin hannunta.

"Dad, ka ji abin da Mom ta ce."

Suka yi dariya.

Sai ta ci gaba da cewa,

"Amma Dad... idan na tambaye ka wani abu, zaka bani honest answer?"

"Of course, Princess."

"Shin kana so na zama lawyer ne dole... ko zaɓi za ka bani?"

Alhaji Nura ya girgiza kai.

"It's your choice, Princess. Ni dai shawara na bayar."

Ta juya wajen Hajiya Fatima.

"And you, Mom?"

"It's also your choice, sweetheart. Na faɗi ra'ayina ne kawai."

Adeelah ta yi murmushi mai faɗi.

"To... ni ina son ko ɗaya.........ina so na zama journalist."

Lokaci guda Alhaji Nura da Hajiya Fatima suka ɗaga kai suka kalleta.

"Journalist?" Suka faɗa kusan a tare.

Adeelah ta gyada kai cikin tabbaci.

"Yes."

Alhaji Nura ya ɗan jingina da kujerarsa yana murmushi.

"Why?"

Adeelah ta ɗan gyara zamanta, ta ɗaga glass ɗin ruwan lemu ta ɗan kurɓa, sannan ta mayar da shi a hankali.

Ta kalli Dad, ta sake kallon Mom.

"Because... journalist ba kawai aikin ɗaukar microphone ba ne."

Ta ɗan yi shiru na daƙiƙu kaɗan, sannan ta ci gaba.

"Likita yana ceton rayuwar mutum ɗaya a lokacin da yake jinyarsa... Lawyer kuma yana kare haƙƙin wanda aka zalunta a kotu."

Ta ɗan yi murmushi.

"Amma journalist... yana iya ceton rayuwar dubban mutane da kalma ɗaya kawai."

Alhaji Nura ya ɗan ɗago gira.

Adeelah ta ci gaba.

"Idan akwai zalunci, journalist ne zai fallasa shi."

"Idan akwai cin hanci ko sata, journalist ne zai tona asirinsa."

"Idan akwai yara da ake cutarwa, ko marasa ƙarfi da ba su da mai magana a kansu, journalist zai iya zama muryarsu."

Ta ɗan sauke numfashi.

"Wani lokaci mutum ba ya buƙatar kuɗi ko magani... yana buƙatar kawai a ji kukansa. Ni ina so na zama wanda zai sa duniya ta ji kukan waɗanda ba su da murya."

Dining ɗin ya yi tsit.

Adeelah ta ci gaba cikin natsuwa.

"Kuma Dad... idan mutane suka san cewa akwai wanda zai fallasa gaskiya, da yawa za su ji tsoron aikata ba daidai ba."

Ta yi murmushi.

"Shi ya sa nake ganin journalist ba iya rubuta labarai kawai... yana canza rayuwa."

Shiru ya sake mamaye wajen.

Alhaji Nura da Hajiya Fatima suka zuba mata ido baki a buɗe, cike da mamakin irin tunanin da ke cikin kan yarinyar.

Hajiya Fatima ta kai hannu ta dafa kirjinta.

"Oh professor..."

Alhaji Nura kuwa ya yi murmushi irin na jin daɗi, ya girgiza kai a hankali.

"Wallahi Fatima... wannan ba maganar ƴar shekara goma sha uku ba ce, tana da hikima sosai."

Hajiya Fatima ta gyada kai, idanunta cike da alfahari.

"Hakika. Allah ya yi mana baiwa."

Alhaji Nura ya miƙa hannu ya shafa kan Adeelah cikin ƙauna.

"I'm proud of you, Princess."

Adeelah ta yi murmushi mai cike da kunya.

"Thank you, Dad."

Da haka ta ture plate ɗin gabanta wanda kaɗan ta ci abinci

“I'm okay Mom, please kar kice komai." Tana faɗin haka ta wuce zuwa cikin parlour.

“Yarinyar nan ba ta son cin abinci, bansan me ke damunta ba.“ Mom ta faɗa cikin damuwa.

“Ki dai mata a hankali, uhm bayan duk halin ku, ɗaya, ke kanki ba cin abinci kike sosai.“ Mom ta turo baki, tana ci gaba da cakulan abincin.

Bayan sun gama, Mom ta ɗauko mai da jakkarasa, ta ba masu aiki, suka kai compound.

Alhaji Nura ya tsaya da ƙyau yana kallon matarsa da ƴarsa.

“Ku kula da kanku, weekend zan dawo."

“To Barrister, Allah ya tsare hanya."

“Ameen, Daughter ba za ki ce komai ba." Ya faɗa yana kallon Adeelah da idanunta suke cikin na I-pad.

A natse ta ɗago ta kalla Dad, ta sakar mai murmushi sannan ta ce.

“Allah ya tsare hanya, ya baka abinda ka fita nema, ya taimaka akan aikin ka, ya kuma sa Malama Hajara su samu ƴan ci a shari'ar da za ku yi." Ido ya dan zaro.

“Ya kika san case ɗin da nake yi." Murmushi ta yi.

“Uhmmmm Dad, bincike, bincike dai.“

“Binciken ƙwaƙwaf dai." Suka yi dariya cikin jin daɗin.

Daga nan suka yi sallama, ya hau mota ya nufa airport dan zuwa Abuja, kwana biyar yake ake a Abuja, sai dai idan aiki ya mai yawa sosai, amma tsakanin Abuja da Kaduna, Dad ya ɗauke shi, kaman shiga parlour da bedroom.

Juyawa suka yi, suka shiga babban parlourn, Mom ta kalla Adeelah.

“Na kusa fasa wannan I-pad ɗin, kullum kina cikin neman labarai, ki kai Ni karshe ki gani." Ta yi maganar cikin ɓacin rai.

Sai dai Adeelah ta yi nisa, bata fahimtar komai, da sauri ta ɗago ta kalla Mom tana cewa.

“Mom, me yasa wasu matan suke kashe mazajensu, a ƙasar........“ Mom ta dalla mata harara.

Adeelah ta yi murmushi, ta aje I-pad ɗin, kusa da ita ta koma, ta kwanta jikinta.

“Mom idan baki yi fushi ba, kina da ƙyau sosai, idan kika haɗe fuska, kin fi ƙyau, ƙyau, idan kuma kika haɗa da harara, sai ki ƙarama ma kyau ado.“ Mom ta yi murmushi tana girgiza kai.

“Murmushin kuwa, tamkar farin......“

“Ya ishe Ni, kinsan bana son yawan magana, tashi ki je ki ci abinci.“ Adeelah ta turɓune fuska.

“To." Ba musu ta tashi, ta nufa dining ɗin, ta zauna, ta zuba ma abincin wajen ido, ita haka take, ba ta cin abinci sosai, yayinda wasu suke nema da ƙyar.............

★★★★★★★★★★

La'asar sakaliya, ranar ana ƙwalla rana sosai, dan rana ya yi zafi, hakan yasa wasu ke sa ran samun ruwan sama a ranar.

Duk wanda ya kalleni dole ya tausayin, ga zagin huta, ga zafin rana, haka kuma hayaƙi ya cika min idanuwa, sai hawaye nake ta yi.

Gumi ne ke zuba a jikina, gashi gefe titi nake, babu wani waje da mutum zai iya fakewa domin shan inuwa.

Gashi na gaji sosai, yanzu ko barci dare bana samu sosai, cewa Mama

“Hutu da yawa shike sa jikina ƙara ƙiba.“.

Sai dai duk da kusan sati biyu kenan dana fara sai da awara, aikin gidana ya ƙaru, sau guda nake cin abinci, babu wani abu da jikina ya yi, ina nan a cure, ƴar duma-duma, ƴar Lukuta.

Ƙibarta shi ke ɓata ma Mama rai, abu kaɗan ta hau dukana da zagi.

Idanuna na matsa, ina kau da kai, a haka na tattara sauran ledojin dake wajen, na tura cikin murhu, na shiga fifitawa, har Allah yasa ya kama.

Na sauke a jiyan zuciya ina kwashe awarar cikin kasko.

Mama ta hanani da cin ko gutsire, hakan yasa bana ci ko ɗanɗane.

“A ban awara." Cewan wani yaro da ke riƙe da kuɗi da abin wasa a hannu ɗaya.

“Na nawa!?.“

“Na duka." Na amsa kuɗin ina ganin dari biyu.

Na zuba mai na bashi, ya amsa ya wuce.

Na jima zaune har na gama tuya, ba'a sake siya ba, gashi idan na mai da shi, duka zan sha.

Inda na ji daɗi, yamma ta fara yi, babu rana.

Ina nan zaune aka zo aka sake siya har mutane huɗu, awarar ta rage saura kaɗan.

Ban jima sosai ba, aka zo aka siye wanda ya rage.

Dan haka na tattare kayan tuyar.

Na zuba a buhu, na riƙewa a hannu na riƙe, sannan na nufa gidan mu, bayan an taimaka an ɗaura min babban buhun dake ɗauke da, murhu, sauran ice, kasko, ludayi, da duk abubuwan tuya.

Kayan suna yi min nauyi sosai, amma haka nake ɗauka na nufa gida, wai nan duk cikin excesise. Nasha tafiya cikin wahala, ga nauyin jikina, gana kayan nan, har ta isa gidanmu, wanda muka sauya a washegarin dana fara tuyar awara................✍️ End ╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*