SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER 6

by @prettys01

> Kayan suna yi min nauyi sosai, amma haka nake ɗauka na nufa gida, wai nan duk cikin excesise. Nasha tafiya cikin wahala, ga nauyin jikina, gana kayan nan, har ta isa gidanmu, wanda muka sauya a washegarin dana fara tuyar awara...............

Gidan ba laifi, yana da ɗan faɗi idan aka kwatanta da tsohon gidan da muka baro.

Gidan ya sha fenti ciki da waje, har ya haska wasu gidajen ma dake layin namu, duk wanda ya ganni babu mai cewa daga gidan nake fitowa, kuma a haka wai gidan Mamana ne.

Cikin gidan akwai ɗakuna goma da suke a jera, yayin da a tsakiyarsa aka bar fili mai yalwa.

Kowani daki yana girma sosai, inda duk ƴan uwan Mama, ko ince, yaran kasuwancinta suke rayuwa a ɗakuna tara na gidan.

Zan iya cewa, Mama tana da jama'a sosai, dan gidan mu kullum a cike yake da mata da maza har da ƴan daudau, balle idan dare ya yi, yadda kasan ana sha'ani.

Da ƙyar na ƙarasa cikin gidan, numfashina na fita da ƙarfi saboda nauyin kayan da na kwaso.

Na sauke buhun a hankali, na dafe bayana ina lumshe idanuna masu kasama sexy eyes.

A natse na jera komai a kitchen ɗin tsakar gida, sannan na nufa babban flat ɗin dake ƙarshen gidan, wanda ya fi kowanne girma, da ƙyau, kuma shine ɗakin mu.

Kusan mutanen gidan basa nan, na shiga parlourn mu da sallama, babu komai sai motsin tv.

A ƙasa na zauna dan an hanani zaman kujera.

Daidai nan aka shiga sallar magrib.

Na tashi na yi alwala kamar yadda Baba ya koya min, ɗakin da nake kwana na shiga, inda mu biyu muke kwana da wata sa'ata.

Jakkar kuɗin na aje kan katifata, na shiga bayi daura alwala.

Ina shiga, Amrah ta shigo ɗakin kunnunta toshe da earphone, tana jin kiɗa.

★Amrah kusan sa'ar Sakeenat ce amma ta ɗan girmeta, sai dai ita tana haske ba laifi duk kuwa da ta ƙara dana mai, haka kuma ta fara zama ƴam mata masu buɗewar ido.

Yarinyar ƙanwar Mama ne, ta dawo hannunta da zama.

Kuma nasu ya zo ɗaya da Mama Zulee, haka take son yara masu wayau.

Idanunta ne suka zauna kan jakkar kuɗin awara, ta yi murmushi, ta isa bakin katifar, ta ɗau jakkar ta buɗe, dubu biyu ta zara a ciki, ta rufe jakkar, ta fice.

★Baba ya ɗan fara koyar da Ni karatun addini, inda a wajensa na iya karatun izu biyu, na iya Sallah, da karatun da ake yi, sannan ya koya min Hausa, shima ba sosai na iya ba, dan daga baya Mama ta hana shi koya min karatun.

Sai dai karatun ya riga ya shiga jikina, kuma ya ɗanɗanamin garɗin karatun addini, hakan yasa nake so, ko islamiyya ne na koma.

Ina fitowa daga bayi, na yi sauri ta ɗau jakkar kuɗin nan ya mai da jikina.

Na shimfiɗa darduma na fara jera salla, azahar, la'asar, magrib, sai na haɗa da isha'i gaba ɗaya.

Ina idarwa na ji ana kiran sunana, ko addu'a ban tsaya yi ba, na fita da sauri.

Amrah na iske zaune a parlour tana cin indomie, na haɗiye miyau, dan rabona da abinci tun daren jiya, haka tsarin yake, da safe Abu mai ruwa ake bani na sha, da rana bana cin komai sai ruwa, da daddare kuwa aka ban abinci karamin plate shima baya isana, haka dai nake ci.

Gari ya yi duhu, amma tsakar gidan mu kaman rana, dan globe ne masu haske, suka haska gidan.

Manyan taburma biyu ne a tsakar gidan.

Yayinda Mama ke zaune cikin leshi mai tsada, sai ƴam mata takwas kewaye da ita.

Zainab, bazawara ce ta dawo gidan Mama, tana kasuwanci, wanda har yau Ni bansan me suke siyarwa ba.

Hafsat, daga ƙauye ta zo, an mata auren dole shine ta gudu, itama a gidan nan take rayuwa, dan gidan Mama ya jima da ƴam mata a ciki.

Atika, itama daga ƙauye ta zo, amma yanzu ta kile sosai, saboda kasuwancin Mama.

Rumasa'u, ita budurwa ce, bansan dalilin da ya sa ta bar iyayenta ta zo kasuwanci wajen Mama ba.

Bilkisu, tana da yara maza uku, sukan kawo mata ziyara ma wani lokacin, itama ƴan tawagar kasuwancin Mama ne.

A'isha da Hauwa'u, su kuma marayu ne.

Sai Rukky, uwar Shagala, budurwa dake rikita zaratan maza, ita ce ta hannun daman Mama, wato Garkuwar mata, kuma a cikin matan nan kaf, na fi sonta, saboda tana sona, kuma tana tausaya min.

A harɗe na isa wajen, da ƙaton hijabi na, na zauna ina gaishe da su ɗaya bayan ɗaya.

Wasu suka amsa, wasu dai hankalinsu baya kaina.

Garkuwar mata ta kalleni ta ce.

“Oh Ni Zulee, yaushe za ki sanin inda yake miji ciwo ne!?........ai sai ki ba mutum tsoro, ga baƙin hijabi, ga baƙin fuska." Dariya suka dan yi.

“Ban cinikin, je ki daura taliya da miya, kowa yunwa yake ji."

“To Mama." Na miƙa mata jakkar, ina dai zaune ta fara ƙirgawa.

“Na nawa na sa miki!?.“

“Na Dubu takwas da dari biyar." Na faɗa ina jin babu daɗi, saboda dana ƙirga cinikin babu ɗari biyar, kuma bansan yadda aka yi ba.

“Ya naga dubu shida." Da sauri na kalla Mama jin abinda tace, bayan Ni dubu takwas na dawo da shi.

“Ma...Mama dubu takwas na......“ kuɗin ta watso min.

Da sauri na shiga tattarasu, ina ƙirgawa.

Nasan Mama ta fi ƙarfin wannan kuɗin, dan ba ƙaramin samun kuɗi take ba, kawai dan karna huta ne, nake wannan sana'ar.

Take idanuna suka cika da hawaye, ganin dubu shida, jikina ya yi sanyi, na kasa magana, sai kuka dana fashe da shi, dan wallahi, wallahi bansan yadda aka yi dubu biyu ta ɓace ba........a hankali ta kira sunan Allah.

“Ya Allah..............”

“Nawa kika gani!?.“ Mama ta faɗa tana kallona.

“Du....dubu....shida.....kuma......”

“Kuma uban me..........uhm, ina kika kai min sauran kuɗi!?." Hawaye suka gangaro daga cikin idanuna.

“Mama....wallahi, wallahi, dubu takwas na shigo da shi gidan nan.....ban....bansan ya aka yi ba.”

Mama ta yi ƙwafa.

“Wallahi sai na miki dukan kuɗi na, je ki fara girki, zamu haɗu.” jiki a mace na tashi, ta wuce kitchen.

Mama ta ja tsaki, na takaicin yadda kullum nake ƙara kiba, gashi rashin wayau ya min yawa.

“Garkuwar Mata, yau zan yi baƙo da wuri, bara na shiga ciki na watsa ruwa.” cewan Rukky tana miƙewa tsaye.

Sai kuma ta buɗe jakkar dake hannunta, dubu goma 10k ta ciro, ta miƙa ma Garkuwar mata.

“Ga wannan na asarar da ta miki, dan Allah sarki duke ta.”

Mama ta amsa kuɗin tana murmushi.

“Insha Allah.......Rukky mai zuciyar tausayi." Rukky ta wuce tana amsa kirar da ya shigo hannunta.

“Mama....taliya nawa zan ɗaura." Na faɗa ina daga nesa.

“Daura Biyar, nasan ba kowa zai ci ba." Na juya na wuce.

“Garkuwar Mata, yarinyar nan yaushe za'a fara ɗaura mata karatu ne!?, ga dai Amrah, yarinyar ta fara kilewa sosai.”

“Hafsat, wallahi na rasa yadda zanyi da ita, gaba ɗaya kanta a toshe yake, ta fi gane rayuwar wahala ai, sai dai bazan yi rainon banza ba, dan ubanta za ta ɗau karatun ko ta tsiya.” da haka suka sauya hira.

A kan gawayi na yi girkin, ban gama ba sai wajen 9pm, har kuma lokacin suna zaune a tsakar gida.

Na gaji sosai, tun safe ban huta ba, ga yunwar da nake ji.

Kular taliyar na ɗauka na fita da shi, lokacin kuwa gidan ya ƙara cika harda maza.

A cikin su dai huɗu kawai na sani, Aunty Duwais, wanda a yanzu nasan dalilin da yasa ake kiranta da wannan sunan, akwai mazauna manya-manaya, Allah ya bata.

Sai Shanawa, da wasu ƴan daudu biyu, Beasty, da Beauty, kuma duk maza ne, amma tantiran ƴan iska, suke binciko wa tawagar Mama, manya-manyan alhajawan da suke kasuwanci, sannan musamman ake hayansu wajen kiɗa, duk bikin da suka je kuwa, tabbas a wannan satin shine zai yi ta trending, dan sun iya rawa, ko mace albarka, hakan yasa suka siya nasu kayan kiɗin suke zuwa da kansu.

Na aje kular na koma kitchen, na tattare komai, na fito.

Mama ta kalleni tace.

“Ki sha ruwa ki kwanta, yarinya sai kace aljanna, ko ƙashin wiya baki da shi, cire hijabin nan." Da sauri na cire hijabin, jikin yana rawa.

Mama ta nuna Ni da yatsa.

“Ku kalla yadda wiyarta ya kusa haɗiyewa da kanta, ko mai cin abinci sau goma a rana sai haka.......daga yau zan ƙara miki aiki, na gaji da ƙibar nan gaskiya.”

“A hanye casss.......Garkuwar matas, kawai ki bata maganin mu na mata, za ta rame, ta dawo kamar Ni haka." Beauty ya faɗa yana jujjuyawa jikinsa, wanda da shi da one babu banbanci.

Dariya suka yi

“Ta zama kamar ka, ai an samu matsala....

“Atika bansan iskanci, ya kike mai da Ni jinsin maza."

Atika ta yi dariya.

“To da menene!?." Ta faɗa cike da tsokana.

“Atika zan miki hauka, dube Ni da daga sama har ƙasa, kema kisan babu abinda za ki nuna min." Atika ta zaro ido.

“Haba, ɗan kwance zanin mana.“ ta kai hannunta kan zanin dake kirjinsa.

Ihu ya fashe da shi, yana ture ta

“Za ta min tsirara, innalillahi jama'a." Take wasu suka yi dariya, cikinsu har da Ni, dan na yi murmushi.

Ganin Mama hankalinta yana kan Aunty Duwais da suke magana.

Sai na wuce ɗakin mu.

Ina jin yunwa sosai, haka na kwanta dafe da cikina, dama ga gajiya, take barci ya yi gaba da Ni mai daɗi....................

*Adeelah* “Bayan gaisuwa irin ta addinin Musulunci, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin Rahotanni, inda har wayau ni, Sakeenat Nura, ke kawo muku wannan shiri daga gidan talabijin na Duniyarmu.

Babban rahotonmu na yau shi ne... Saki.

A kwanakin nan ana yawan jin labarin rabuwar aure. Wasu sukan ce rashin haƙuri ne, wasu su ce matsin tattalin arziki ne, wasu kuma su ce rashin fahimtar juna ne.

Amma ni ina da tambaya guda ɗaya.

Me yara suke ji idan iyayensu suka rabu?“

Adeelah ta gyara tsayuwa tana rike da mic na roba, ta tsaya da daga jikin stool, ta kalla Nusaiba yarinyar Maman Daddy, wacce ke riƙe da I-pad tana mata video.

Murya ta gyara sannan ta ci gaba da cewa.

“Sau da yawa manya suna tattauna matsalolinsu, amma ba kasafai ake jin an tambayi yara yadda suke ji ba.

Ko suna kewar mahaifinsu? Ko suna kewar mahaifiyarsu? Ko kuwa suna jin tsoron abin da zai faru da rayuwarsu?

Ni yarinya ce, ban san komai game da rayuwar aure ba. Amma ina ganin duk yaro yana son ya ga iyayensa suna farin ciki, kuma yana son ya rayu cikin kwanciyar hankali.

Wataƙila idan muka fara sauraron muryar yara, za mu ƙara fahimtar irin tasirin da rabuwar aure take yi a kansu.

Wannan shi ne ƙarshen rahotonmu na yau.

Amma akwai tambaya guda da zan yi.“

Adeelah ta yi murmushi, sannan ta juya wajen Maman Daddy da ke ta yankan ganye.

“Maman Daddy, za ki iya amsa mana wannan tambayar?”

Maman Daddy dake yanka ganye ta ɗaga mata kai tana murmushi

“Eh, ina jinki.”

“Shin a ganinki, me yake kawo yawaitar saki a wannan zamanin?”

Maman Daddy ta ɗan yi shiru tana ci gaba da aikinta, sannan ta ce,

“To Adeelah, Ni uwace kuma matar aure, abin da nake gani shi ne, idan haƙuri ya ragu, sauraron juna ya ragu, sannan aka bar mutane suna shiga tsakanin ma'aurata fiye da kima, sai matsala ta yi girma. Wani lokaci kuma rashin neman mafita cikin natsuwa ne yake kai aure ga ƙarshe, ko zargi, rashin daraja abokin zama, cin amana da sauransu dai. Allah Ya kyauta.”

Adeelah ta gyada kai cikin gamsuwa.

“Mun gode sosai da wannan amsa, Maman Daddy.”

“Babu komai princess .”

Adeelah ta sake fuskantar iPad ɗin da Nusaiba ke riƙe da shi.

Sai dai kafin ta yi magana, idanunta suka sauka kan Mom, wacce ke tsaye a bakin ƙofar kitchen, hannayenta a haɗe, tana kallonta fuska a haɗe.

Adeelah ta yi ɗan murmushi, sannan ta ce,

“Masu sauraro, a nan za mu dakata da shirinmu na yau. Idan Allah Ya yarda, za mu sake haɗuwa a wani lokaci.

Ni ce ta ku Sakeenat Nura, tare da abokiyar aikita Nuseey...

Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.”

Da ta gama faɗin haka, ta yi alamar an gama ɗaukar bidiyon.

Nusaiba ta kashe iPad ɗin tana dariya.

“Wallahi Adeelah, kina iya gabatar da shiri sosai, sai aka ce da gaske.”

Adeelah ta yi murmushi kawai.

Daga nan ta nufi Mom, wacce ta miƙa mata plate ɗin abincin da ta aiko ta ci.

“Abin cin kenan.”

“Sorry Mom.....Thank you, Mom.”

Ta isa kusa da ita ta karɓar plate ɗin, sannan ta zauna cikin natsuwa.

“Nuseey come and join me.“ Nusaiba ta matsa kusa da ita, suka ci abinci, suna yi suna hira kaman yaya da ƙanwa.

Bayan sun gama cin abincin, Adeelah ta koma babban ɗakinta. Ta zauna a gefen gadonta, ta ɗauki iPad ɗinta, ta ci gaba da bincikenta cikin nutsuwa.

Ta yi ta karanta bayanai daban-daban, tana rubuta wasu muhimman abubuwa a littafinta. Wani lokaci takan tsaya tana tunani, sannan ta koma kan iPad ɗin.

Bayan ta gama binciken, ta ajiye iPad ɗin gefe.

Sai ta miƙe ta nufi closet ɗinta.

Ta buɗe ƙofar closet ɗin, ta fara duba rigunan da ke jere cikin tsari. Idanunta suka riƙa yawo daga wannan zuwa wancan, tana neman wadda za ta fi dacewa da abin da take shirin yi.

Daga ƙarshe, idanunta suka tsaya kan wata doguwar gown mai kyau.

Ta ɗan yi murmushi.

“Wannan ce.”

Ta miƙa hannu ta ɗauko gown ɗin a hankali, sannan ta ɗora shi a gabanta tana kallonsa.

Sai ta koma gaban madubi, ta ɗan ajiye gown ɗin a jikinta tana kallon yadda zai yi mata.

Murmushi ya sake bayyana a fuskarta.

“My best.”

Ta ninke shi cikin tsari, sannan ta ajiye shi a kan gadonta.

Bayan ɗan lokaci, Adeelah ta fito daga ɗakinta riƙe da rigar da ta zaɓa. A lokacin Mom tana zaune a babban parlour tana kallon wani shiri a talabijin, yayin da Maman Daddy ke kusa da ita.

Da suka ga Adeelah ta fito, Maman Daddy ta yi mata sallama.

“Assalamu alaikum, Adeelah.”

“Wa alaikumus salam, Maman Daddy.”

Adeelah ta amsa cikin murmushi, sannan ta nufi inda Nusaiba take. Ta miƙa mata rigar da ta riƙe.

“Nusaiba, ga wannan.”

Nusaiba ta karɓa tana kallon rigar da mamaki.

Maman Daddy kuwa ta zaro ido.

“Ke! Adeelah, wannan rigar fa?”

Ta kalli rigar sosai, sannan ta kalli Adeelah.

“Princess, me za ki yi da wannan? Gaskiya ta yi kyau sosai.”

Adeelah ta yi murmushi.

“Na baki ne, Maman Daddy. Na ba Nusaiba.”

Nan take Maman Daddy ta girgiza kai.

“A'a, a'a! Ba zan iya karɓar wannan ba. Wannan rigar ta yi tsada sosai. Ki mayar da ita.”

Adeelah ta ɗan yi dariya.

“Maman Daddy, don Allah ki karɓa.”

“A'a Princess, wallahi na gode. Amma wannan ya yi yawa.”

Adeelah ta sake miƙa mata rigar.

“Don Allah. Kyauta ce.”

Maman Daddy ta kalli Mom, sannan ta sake kallon Adeelah. Idanunta suka cika da farin ciki.

“Allah ya saka miki da alheri, Princess. Ban san me zan ce ba.”

“Ki gode ma Allah”

Maman Daddy ta yi murmushi sosai.

“Insha Allah. Allah Ya albarkace ki, Ya ƙara miki arziki da farin ciki.”

“Ameen.”

Bayan Maman Daddy da Nusaiba sun yi mata sallama suka wuce, Mom ta tashi daga kujerarta.

Ta nufi Adeelah, ta rungumeta cikin farin ciki.

“Ina son ki sosai. Halin ki na son mutane da kuma yadda kike tunanin wasu, shi ne abin da nake so a tare da ke.”

Adeelah ta yi murmushi tana cikin rungumar Mom.

“Na gode, Mom.”

Sai ta ɗan ja da baya tana kallon Mom.

“Na zata za ki min faɗa akan rigar. Saboda ko sawa ban taɓa yi ba, kuma akwai tsada sosai.”

Mom ta yi murmushi.

“A'a. Na san kina da dalilin da ya sa kika ba ta rigar, ko?”

Adeelah ta ɗaga kai.

“Eh.”

“Me ya sa?”

Adeelah ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce cikin nutsuwa:

“Ana so mu yi kyauta da abin da muka fi so. Shi ya sa na ba ta rigar, saboda ina son ta sosai.”

Mom ta kalleta cikin alfahari.

“Allah Ya miki albarka.”

“Ameen, Mom.”

Mom ta sake rungumeta, wannan karon cikin ƙauna da farin ciki ne..................✍️ End

╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*