CHAPTER 7
by @prettys01
> Mom ta sake rungumeta, wannan karon cikin ƙauna da farin ciki ne................
Kamar yadda ta saba, bayan ta yi shirin barci, sai da ta yi maraja'an izu biyu, sannan ta kwanta.
Bayan ta yi barci, mom ta sake zuwa ta gyara mata kwanciya, ta mata addu'a sannan ta wuce part ɗinta.
Haka rayuwa ta ci gaba ta tafiya musu cikin annashuwa da farin ciki, ba su da wata matsala su ta bangarensu............
*Sakeenat* Ba za to ba tsammani, na ji saukan bulalan inji a gadon bayana, na saki ihu ina buɗe idanuna da ƙyar.
Mama na gaji tsaye a kai na, ta riƙe bulala tana kallona.
Na fashe da kuka ina mai jan jikina baya tare da girgiza mata kai.
Sai dai mai, Mama dukana ta ci gaba da yi, ba tare da nasan ƙwaƙwƙwaran abin da na yi mata ba, Ni kuma saboda dare ne, bakina na toshe ina kuka a haka.
Sai bayan da ta gama duka na ta zauna a gefen Amrah dake barci kamar gawa, ta dalla min harara.
Ƙasa na kalla da sauri ina mai soma magana cikin dauriya.
“Ma....Mama ki ya haƙuri.......na sake ɓata miki rai kamar kullum, ki hakuri da na hanaki barci.......kwanda da kika duke Ni, idan har hakan zai sa ki samu sauƙi a zuciyar ki..........idan dukan bai sa kin huce ba, Mama ki ci gaba da dukana, har sai kin gamsu.......amma dan Allah ki faɗa min abin da na yi!.“ na kai maganar ina matsawa kusa da ita.
Tsaki ta ja sannan ta ce.
“So nake ki waye kamar Amrah, ki Dena wannan gidadancin, ki zama ƴar gari, amma kin kasa fahimta ta.....” sai ta ja tsaki.
“Wallahi Mama ina son ganin na faranta miki rai, amma ki min uzuri, Baba ne ya hanani aikata komai.” da sauri ta miƙa tsaye.
“Bashir wai!?.” na ɗaga mata kai, duk kuwa da Baba ya gargaɗe Ni akan kar na faɗa mata shi ke zigani akan duk wani abu da ta na yi.
“Lallai Bashir ya taro ma kansa masifa, Ni zai ƙwadama iskanci.....ƴar ba tawa ba ce!?..... ya ma isa.......ke biyo NI.” babu musu na bi bayanta duk kuwa da dare ta yi.
A parlour na zauna ina mai ci gaba da raira kuka a hankali.
Mama da Baba suka fito bayan ɗan lokaci da shigan Mama, ga dukkan alamu har ya fara barci ta tashe shi.
Baba ya zauna kan kujera yana hamma, Mama ta zauna a kusa da shi sai faman huci take yi.
“Bashir” haka Mama ke kiran Baba a ko ina.
Baba ya kalleta ya kuma kalleni.
“Ke Shegiya maimaita abinda kika ce min.”
“Baba ya ne yace, karna yarda na aikata duk wani abu da za ki sani dan neman kuɗi, ya amince dai na yi suyan awara ko wani abu, amma bai yadda na yi wani abu da sunan wayewa ba.” na faɗa ina wasa da gefan hijabin jikina.
Mama ta tsare Baba da ido.
“Sakeenat bata ƙarya.....meye naka da cewa kar ta min biyayya........sanin kanka ne, yarinya ta ce ba taka ba." Baba ya lumshe ido saboda ciwon da yake fama da shi a tsaitsaye.
“Haka ne, bana so ta zama yadda kike fata, saboda Nima ƴata ce, kuma ina da iko akan ta.”
“Au da gaske....” ta yi dariyar rainin wayau.
“Bashir, bana so muna rigima akan ƙaramin abu, amma wallahi, wallahi babu uban da ya isa yasa Sakeenat ta yi wani abu, wanda bana so.”
“Ni kuma na ce bana so.” ya faɗa cikin sanyi.
“To ka sani masifa da bala'i za ka siyar ma kanka......ke Sakeenat, tsakanin Ni da Ubanki wa za ki tsaɓa!?.”
Ƙirjina ne ya buga da ƙarfi, idanuna suka cika da hawaye.
“Mama ke zan zaɓa.” na faɗa rintse ido.
“Idan Ni da Babanki muka raba gida, kowa kuma yana so ya zauna da ke, gidan wa za ki zaɓa!?......”
“Mama gidan ki.” Mama ta yi murmushi.
“Idan Babanki ya ɗauke ki da kansa, ya kai ki gidansa, ya za ki yi!?.” ba tare da tunani ba na ce.
“Guduwa zan yi Mama.......ba zan iya rayuwa a inda baki yadda ba.”
“Je ki kwanta, gobe kina da aiki da yawa.”
“To Mama na gode, Babana sai da safe.” Baba ya min murmushi wanda bai kai zuciya ba, na wuce jikina duk a mace.
Ina shiga ɗaki, na kwanta, sai na saki wani marayan kuka, har ga Allah Baba ya fi sona, amma Zuciyata da ruhina Mama nake so.
Na jima ina kuka kafin barci ya yi gaba da Ni, cike da burin zama duk yadda Mama ta umarce Ni na zama.....
A parlour kuwa, Mama ta kalla Baba sannan ta ce.
“Bashir wannan ya zama karo na ƙarshe da hakan zai sake faruwa, ko na sauya maka gaba ɗaya.......”
“Sauyawa na nawa kuma!?, ke kanki kinsan abinda kike yi ba daidai bane, amma san kuɗi ya rufe miki ido, ki tuba, wallahi ki tuba, bayan abinda kike aikatawa, kina neman lalata rayuwar marainiyar Allah............Zulee hakan ba daidai bane, duk kuwa da nima na taka muhimmiyar rawa wajen rushe mata rayuwa, sai dai na tuba, na tuba ga allah.” sai ga hawaye sun gangaro daga cikin idanunsa.
“Ni yanzu tsakani na da Allah nake gyarawa, bana son sake shiga wani masifar.”
“Bashir kenan, tun a yanzu mun fara samun Banbancin Ra'ayin akan rayuwar Sakeenat............to ka sani, duk yadda na tsara mata haka za ta yi rayuwa, ka zuba mu gani.” ta miƙe a fusace.
“Yadda Allah ya tsara mata dai, kuma za ki sha mamakin yadda tsarinki dana Allah zai zo da tazara mai tsawo, tamkar tazarar zama da ƙasa, kuma insha Allah Sakeenat rayuwar jin daɗi za ta yi.”
“Wannan tatsuniya kake yi Bashir, Ni na yi nan banda lokacin shirmenka.” tana kai wa nan ta shige ciki.
Baba ya rintse ido yana jin tausayin Zulee, akan rayuwar da takeyi, gaba ɗaya babu Allah a cikin lamarin ta, addu'a ya yi kafin da ƙyar ya koma ciki ya kwanta gefan Zulee wacce barci ya ɗauketa......
*Washegari*
Da wuri na tashi kamar kullum, na yi gyaran gidan mu tas, Ni na yi abin kari, na dama kunu mai yawa, na zauna zaman suyan dankalin hausa.
Ina aiki fuskanta a sake, ina yi ina rera wata waƙa wacce da kaina na tsarata a cikin kai na, abu guda da nake da baiwarsa kenan, shine waƙa, ina tsara waƙa a cikin kai na, kuma na rerata ta yi daɗi sosai, sai dai bana rubutawa saboda Hausar ma ba wani iyawa na yi ba.
Haka na gama suyan dankalin ko ɗaya ban kai bakina ba saboda biyayya.
Kunu kawai na sha shima sai bayan da Mama ta tashi, shine na zuba min ko rabin kofi be yi ba, haka na sha ko ƴan hanjina basu cika ba.
Na yi wanki mai yawa, na kuma yi abincin raina, shinkafa jollof na manja da kifi, haka aka hanani ci, ba yadda na iya, bayan na gama na tafi suyan awara, ban dawo gida ba, sai yamma.
Wallahi na gaji sosai, har jiri nake gani saboda yunwa, amma haka na sake ɗaura abincin dare, Allah ya taimake Ni, bayan na gama, Mama ta bani daman na ɗiba na ci.
Farin ciki kamar ya kashe Ni, haka na cika wani plate, ba zauna a kitchen na cinye taliyar nan tas, na ji ban ƙoshi ba, na sake ɗiba na ci, sai da na ji cikina ya yi nauyi, sannan na yi hamdala na tashi na koma ɗakin mu........
Allah sarki rayuwa kenan
*Bayan wasu shekaru*
*Adeelah*
Murmushi ne kwance akan fuskata, a hankali na buɗe fararen idanuna, ina kallon Mom ɗin da ke tsaye a gefen gadona ta kunna globe.
“Good morning, Mom,” na faɗa cikin murya mai ɗan nauyin barci.
“Good morning, sweetheart. Come on, wake up. You’re going to be late for school.”
Na yi hamma, sannan na ja bargo na rufe fuskata ina turo baki cikin shaƙwaɓa.
“Mom, please… just five more minutes.”
Mom ta yi murmushi, ta girgiza kai.
“No, Adeelah. You said that yesterday too, and you almost missed school. Get up now.”
“Please, Mom. I’m still sleepy.”
“I know you are, but school won’t wait for you. You need to take your bath, get dressed, and have your breakfast.”
Na buɗe ido ina kallonta.
“What time is it?”
“It’s already past six-thirty.”
Na miƙe zaune da sauri.
“Six-thirty?! Oh my God! Me yasa baki tashe Ni da wuri ba ”
Mom ta yi dariya.
“I did. Twice. You told me you were awake, then you went straight back to sleep.”
Na rufe fuskata da hannuna.
“Oh… I don’t remember that.”
“Of course you don’t,” Mom ta ce tana murmushi. “Now hurry up, my dear.”
“To, Mom. I’m getting up.”
“That’s my girl. And don’t forget to say your morning prayers before you leave.”
“I won’t forget, Mom.”
Ta sumbaci goshina a hankali.
“Good. Now go and get ready.”
“Okay, Mom.”
Na sauka daga kan gadon cikin sauri, yayin da Mom ta fita daga ɗakin tana murmushi.
“Remember, Adeelah—no wasting time!”
“Yes, Mom!” na amsa ina dariya.
Da sauri na shiga toilet ɗina, wanda yake cikin part ɗina. Toilet ɗin kuwa ya tsaru sosai, an tsara shi cikin tsari na zamani, tiles masu sheƙi suka kewaye bango da ƙasa, ga babban madubi mai kyau a gaban sink, sannan shower ɗin da komai na cikinsa cikin mai tsari ne.
Na yi wanka cikin sauri, bayan na gama sai na fito ina mai ɗaure da towel a jikina.
A gaban mirrow na tsaya ina mai kallon kaina daga sama har ƙasa.
Nasan Ni fara ce sosai, irin hasken da kashe ido, dan ma zirga-zirgan makaranta yasa duk na yi duhu.
Doguwa ce Ni Masha Allah, ga jiki, dan a dire nake ta ko ina, Allah ya min zubin halitta mai ƙyau, dan babu abinda za'a kalla a jikina ace bai dace da Ni ba.
Na kwaso gaba ɗaya ƙyawun iyayena, hakan yasa na zama ƙyaƙyƙyawa ta gaban ƙwatance.
Fuskata kaɗai abin kallo ne, dan ina da idanunsa farare masu kyau, ga dogon hancina, sai ƙaramin bakina mai kyau, a takaice dai alhamdulillah, alhamdulillah.
Na ɗauki man shafawa mai tsada, mai ƙamshi mai daɗi, na shafa a jikina cikin natsuwa, sannan na koma gaban madubi.
Daga nan na buɗe wardrobe ɗina, na ɗauko wata atamfa mai matuƙar kyau. an yi masa ɗinki na musamman, mai sauƙi amma cike da kyau da class, doguwar riga ne, amma ya ji stone. Ɗinkin ya zauna a jikinsa sosai.
Na sanya kayan, sannan na ɗauki hijabi Mercedes launin ja, na sanya dan ya hau zanen kayan. Na duba kaina a madubi na ɗan zaman hijabin, dan yakan yi wiya na fita da gyale
flat shoe ɗina wanda shima ya yi daidai da launin kayan hijabina, na sanya.
Na ɗauki handbag ɗina mai kyau na buɗe shi, na saka wayata Samsung Galaxy S Ultra mai tsada, wadda take da launin black mai sheƙi da kyakkyawan design.
Na ɗauki system ɗina na laptop, sannan na ɗauki makullin motata.
Da sauri na aje kayan hannuna, na isa gaban mudubi, na sanya kwalli tun kafin Mom ta yi min magana.
Na sake kallon ɗakin na ɗan lokaci, kafin na fice daga part ɗina a hankali, cikin natsuwa kamar yadda na saba.
Da na fito daga part ɗina, sai na nufi dining area. Wurin ya yi kyau sosai, an tsara shi cikin tsari mai matuƙar burgewa. Teburin dining ɗin babban ne, an yi shi da ƙyalli mai kyau, kujerun kuma masu laushi ne, an yi musu cover mai kyau da ya yi daidai da launin bangon ɗakin. Manyan curtains masu launin cream suka rufe tagogin, yayin da chandelier ɗin da ke tsakiyar wajen ke haskaka dining ɗin da wani irin haske mai daɗi.
A saman dining table ɗin kuwa akwai abinci iri-iri cikin manyan plates masu kyau. Akwai golden-brown fried eggs, soyayyen sausages masu ɗan ja-ja, bread mai launin golden, pancakes masu laushi, da bowl ɗin fresh fruits masu launuka daban-daban. A gefe kuma akwai glass jug cike da fresh orange juice, wanda launinsa ya ƙara wa dining ɗin kyau.
Mom tana zaune a ɗaya daga cikin kujerun, tana jiran zuwana.
“Good morning, Mom.”
“Good morning, sweetheart. Come and sit down. You need to eat before you leave.”
Na zauna kusa da ita.
Mom ta jawo plate ɗin abincin kusa da ni, ta ɗauki abinci ta fara bani a baki.
“Open your mouth, Princess Adeelah.”
Na buɗe baki ina murmushi.
“Mom, I can feed myself.”
“I know you can, but let me spoil my little girl this morning.”
Na yi murmushi, na karɓi abincin.
“You’re too sweet, Mom.”
“Just eat, sweetheart. You have a long day at school.”
“Okay, Mom.”
Bayan na gama cin abincin, Mom ta raka ni har cikin compound.
Da muka fito, sai na ga wasu daga cikin ma’aikatan gidan suna can suna gudanar da aikinsu. Da suka gan ni, sai suka zo har inda nake, suka fara gaishe da ni cikin fara’a.
“Good morning, Adeelah!”
“Good morning, everyone!” na amsa ina murmushi.
Ɗaya daga cikinsu ta yi wata magana da ta sa muka fashe da dariya.
“Hmmn kun ƙyauta, ina My Nuseey, munyi latti.”
Nusaiba ta fito daga ɗakin bangaren da suke rayuwa, tun bayan rasuwar mahaifinsu, na sa Dad ya sa suka dawo gidan mu, kuma duk inda na kasance Nuseey tana tare da Ni, kawai dare ne muke rabuwa da ita.
“Alright, alright. I’m going!”
Na yi musu sallama, har muka ɗan yi wasa da dariya kafin na nufi motata.
Motar ƙirar Mercedes-Benz GLC 300 ce, mai launin pearl white, wadda take kyallin sabunta
Na buɗe ƙofar na shiga, na ajiye system ɗina da jakata, sannan na kunna motar.
A lokacin Nuseey ta shigo, ta sha doguwar riga mai kyau, ta faya gyale wanda ya hau kayan sosai.
Ba fara bace, amma tana ɗan haske, sai na bleaching ɗin da take yi.
Na ɗan kalli Mom dake tsaye tana kallona.
“Bye, Mom. I’ll be back later.”
“Bye, sweetheart. Drive safely.”
“I will.”
Na ɗaga mata hannu, sannan na fara jan motar a hankali zuwa hanyar fita daga compound ɗin.
Da na fita, sai na kunna karatun Alƙur’ani a cikin motar. Muryar Muhammad Al-Afifi ta cika motar cikin nutsuwa, yayin da nake tafiya a hankali ina sauraron karatun.
Nuseey kuma ta buɗe jakkarta, ta ciro kayan ƙwalliya, ta fara shafawa a fuska yadda kasan za ta ne biki ko wani party, Ni dai tun ina mata magana har na zuba mata ido, dan Nuseey akwai taurin kai sosai.
Bayan ɗan lokaci, sai muka iso University (KASU), babbar jami’ar da muke karatu.
Daga nesa ma kaɗai mutum zai iya gane cewa ba ƙaramin makaranta ba ne. Babbar gate ɗin jami’ar tana da girma sosai, an rubuta sunan jami’ar a saman ta cikin manyan haruffa, yayin da jami’an tsaro suke tsaye a bakin ƙofar suna kula da masu shiga da fita.
Da na shiga cikin campus ɗin, na fara sauke Nuseey, ta min sallama tana murmushi, na mai da mata, ta nufa bangaren Fashion and Design, dan a nan take karatu.
Manyan gine-ginen lecture halls da faculty buildings sun yi jere cikin tsari, wasu daga cikinsu dogaye ne masu hawa da yawa. Titunan cikin makarantar suna da faɗi kuma an yi su da kyau, ga dogayen bishiyoyi da ciyawa kore da suka kawata sassan campus ɗin.
Dalibai kuwa sun cika ko'ina. Wasu suna tafiya zuwa lecture, wasu suna zaune ƙarƙashin bishiyoyi suna karatu, yayin da wasu ke tsaye suna tattaunawa da abokansu. Motoci iri-iri sun cika parking areas, ga masu sayar da abinci da ƙananan shops a wasu sassan jami’ar.
Na ci gaba da tuƙi har zuwa wajen Faculty of Communication and Media Studies, inda nake karatun Journalism.
Tun ina ƙarama nake sha'awar aikin jarida. Ina son bincike, rubuce-rubuce da isar da sahihin bayani ga mutane, shi ya sa na zaɓi Journalism a matsayin fannin karatuna.
Na yi parking ɗin Mercedes-Benz GLC 300 ɗina a wajen da aka tanadar wa ɗalibai, na kashe motar sannan na ɗauki handbag da system ɗina.
Na sauka daga motar, na rufe ƙofar.
Na kalli agogo na yi murmushi.
“Thank God, I’m not late.”
Daga nan na nufi cikin Faculty ɗinmu cikin natsuwa, yayin da ɗalibai ke ta zirga-zirga a harabar jami’ar.
Ina shiga department ɗin mu, na yi sallama, na isa inda nake zama na zauna, bayan mun sake gaisawa da ƴan ajin.
Bani da ƙawa, sai abokan karatu, dan Ni Allah ya yi Ni da mai da hankali a school.
System na kunna na ɗan fara binciken labaran da na saba. Jin kunnuwana suka jiyo min sautin mutane da yawa suna ta kiran sunan matashin saurayin nan
“SAFRAZ BALL STAR.” Tsaki na ja a raina, domin nasan zuwa ya yi ne don ya takura min. Gashi ni bana wulaƙanta mutum; Allah Ubanmu da kansa Ya karrama halittar mutum, shi ya sa nake daraja duk ɗan Adam, ko waye shi kuwa.
Jin tsayuwar mutum a gabana ya sa na ɗaga kai a hankali. Idona suka sauka kai tsaye kan Safraz, wanda yake tsaye gabana yana kallona yana murmushi.
Murmushin na mai da mai kafin idona su fara yawo a hankali a kan shigarsa.
A shigarsa kaɗai ta isa ta bayyana irin rayuwar da ya fito.
Sanye yake da dark-blue crazy jeans mai kyau da ya zauna masa daidai. A jikinsa kuwa akwai wata farar shirt mai dogon hannu, Hannun rigar an naɗe su kaɗan zuwa gwiwar hannu, abin da ya ƙara fito da shigar nasa kenan.
A ƙafarsa kuwa akwai fararen sneakers masu kyau, tsaf kuma masu tsada, waɗanda suka yi daidai da farar rigar da ke jikinsa. A wuyansa ya saka ƙaramin silver chain, yayin da agogon hannu mai kyau.
Sai gashinsa...
Gashin kansa mai yawa, baƙi mai sheƙi. Gefe guda an kitsa cikin wani salon zamani, ɗayan side ɗin kuma ya bar shi amma an gyara kwanciyar gashin.
Na sake kallonsa daga sama zuwa ƙasa, kafin na dawo da idona kan fuskarsa.
Safraz kuwa har yanzu murmushi yake yi.
Safraz matashi ne ɗan shekara ashirin da shida, ɗan asalin Kaduna. Tun yana ƙarami yake da matuƙar son wasan ƙwallo. Duk lokacin da ya samu dama, filin wasa shi ne inda za ka same shi. Bayan ya girma, ya shiga jami'a domin ci gaba da karatunsa. Sai dai ƙwallo ta fara buɗe masa wata babbar ƙofa. Hazakarsa da kuɗinsa suka sa aka fara lura da shi, har ya samu damar shiga ƙungiyar da ke ba shi damar buga ƙwallo a matakin ƙwararru.
Yayin da yake ƙara samun suna, sai wata dama ta kai shi England. Tafiyar ba ƙarama ba ce a gare shi, domin ta nufin barin ƙasarsa da kuma fara sabuwar rayuwa a wajen gida.
A ƙarshe, ƙwallo ta zama aikinsa. Saboda yawan horo da ƙwazonsa, Safraz ya fara samun karɓuwa a cikin ƙungiyarsa. Duk da haka, bai manta da karatunsa ba, sai dai bai samu damar kammala jami'a ba saboda yadda harkar ƙwallo ta ƙara ɗaukar masa lokaci. Yanzu yana da shekaru 26, yana zaune a England, yana buga ƙwallo a matsayin Winger/Attacking Midfielder, kuma lambar rigarsa ita ce 11. Saboda irin yadda yake taka rawar gani a filin wasa, abokansa da masoyansa suka fara kiransa da suna “SAFRAZ BALL STAR.” ⚽🔥
Yanzu haka kuma ya dawo hutu, shine yake zuwa makaranta saboda abokansa, yana da masoya sosai, shi yasa kafin ya kasance a waje, sunansa ya zaga ko ina....................✍️ End
Har yanzu shimfiɗa muke yi.
Adeelah ★ Roll Star 🌟 Sakeenat ★ Heart of the story ❤️
More likes, more comments = more motivation to keep typing and posting, Insha Allah. 🥲🫢❤️✍️
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*