CHAPTER 8
by @prettys01
> Yanzu haka kuma ya dawo hutu, shine yake zuwa makaranta saboda abokansa, yana da masoya sosai, shi yasa kafin ya kasance a waje, sunansa ya zaga ko ina.................
Safraz ya ɗan ja kujera ya zauna a gefena, duk da cewa ban gayyace shi ba. Ya jingina da kujerar, yana kallona da wannan murmushin nasa da ya fara ɓata min rai, ƴan ajin mu kuwa, kowa sai kallonsa yake cike da burgewa, wasu har hoto suke mai, mata kuwa sai ƙus-ƙus suke yi.
“Hi, Adeelah.”
Na ɗaga kai a hankali.
“Hi.”
“That's all?”
Na ɗan ɗaga gira.
“Me kake so in ce?”
Ya yi dariya kaɗan.
“Nothing. I just came to say hi.”
“To, ka ce.....Hi, na amsa.”
Ya sake yin murmushi.
“You’re always like this.....?”
“Like what?” na faɗa ina ɗan kallonsa, kashe min ido ya yi, hakan yasa na mai da kan abinda na ke yi.
“Too serious.”
Na sauke idona kan system ɗina.
“I'm in class, Safraz. Ina so in yi karatu.”
“Class bai fara ba fa.”
“Amma zan iya yin bincike kafin lecturer ya shigo.”
Ya ɗan matso da kujera.
“Kin san na dade ban gan ki ba?” na ɗan zaro ido, dan kuwa sati biyu kenan da ya fara ganina, tun daga wannan ranar kuwa, sai ya zo makaranta ya dame Ni.
“Ni kuma........ashe...uhmmmm.”
Ya yi dariya.
“magana na miki wahala.”
“Ba wahala ba ce. I just don't like unnecessary conversations.”
“Okay, okay. But at least ki daina pretending kamar baki san ni ba.”
Na kalle shi.
“Na san ka...!.”
“Really?”
“Eh. Safraz Ball Star.”
Murmushinsa ya ƙara faɗi.
“Ah! Finally.”
“Kar ka yi farin ciki sosai. Sanin sunanka ba yana nufin ina sha'awar sanin komai game da kai ba.”
Ya yi dariya yana girgiza kai.
“Your attitude is something else.”
Na koma kan system ɗina.
“Thank you.”
“That's not a compliment.”
“I know.”
Ya yi shiru na ɗan lokaci, amma har yanzu yana zaune kusa da ni.
“By the way, how are you?”
“I'm fine.”
“Family?”
“Fine.”
“School?”
“Fine.”
“Your life?”
“Fine.”
Ya fashe da dariya.
“Wallahi answers ɗinki duk iri ɗaya ne.”
Na ɗan kalle shi.
“Saboda questions ɗinka ma duk ba su da amfani.”
“Okay, I surrender.”
Na yi murmushi kaɗan, kafin na sake mayar da hankalina kan system ɗina.
A haka muke zaune, shi yana ta neman wata hanya da zai sa na yi magana da shi mai tsawo, ni kuma ina ƙoƙarin kauce masa, take muka ji motsin ƙofar class ɗin.
Lecturer ɗinmu ya shigo ɗauke da wasu littattafai da papers a hannunsa.
“Good morning, everyone.”
“Good morning, sir,” muka amsa gaba ɗaya.
Nan take Safraz ya miƙe.
“Good morning, sir.”
Lecturer ɗin ya tsaya yana kallonsa, sai fuskarsa ta haskaka da murmushi.
“Oh! Safraz!”
Safraz ya yi murmushi.
“Yes, sir.”
“It's been a while! Welcome back.”
“Thank you, sir.”
Malamin ya matso kusa da shi yana kallonsa cikin farin ciki.
“I've been seeing you everywhere. Your fans are really proud of you.”
Safraz ya yi dariya.
“Thank you, sir. I appreciate it.”
Wasu daga cikin ɗaliban da suke cikin class ɗin suka fara murmushi da ɗaga waya.
Lecturer ɗin ya kalli ɗaliban.
“Since our star is here today, I think you guys should let me take a picture with him.”
Nan take aka fara dariya.
“Sir, please!”
“Safraz, one picture!”
“Ball Star!”
Safraz ya tsaya kusa da lecturer ɗin, ɗaya daga cikin ɗaliban ya ɗauki waya ya ɗauki hoton. Wasu kuma suka matso suka nemi su yi selfie da shi.
Ina zauna a wurina ina kallonsu kawai.
A ƙarshe lecturer ɗin ya ɗaga hannu.
“Alright, enough. We have a class to attend.”
Safraz ya yi musu sallama.
“See you guys.”
Sai ya juya ya fita daga class ɗin.
Yana fita sai na sauke ajiyar zuciya a hankali.
Na jingina da kujerata, na ɗan kalli ƙofar da ya fita, sannan na furta a hankali.
“Wannan shine ɗaya daga cikin samari ukun da suke caza min kai.”
Na girgiza kai.
“Bana son ko ɗaya... domin har yanzu ban haɗu da ƙwarzo na ba.”
Sai na ɗan yi murmushi ni kaɗai, kafin na dawo da hankalina kan malamin dake gabanmu......................
*Sakeenat*
“Assalamu alaikum warahmatullah, Assalamu alaikum warahmatullah.” Na idar da Azahar, sannan lokaci ya ja kaɗan, na tashi na yi La’asar, na yi Magariba, daga baya kuma na yi Isha’i. Ban ɓata lokaci ba, bayan na idar da Isha’i sai na fara jero addu’a da Hausa, ina farawa idanuna suka cika da hawaye, take suka fara zuba, tunawa da Baba, da kuma rayuwar da nake yi yanzu.
Nasan komai lokaci ne, amma Ni a yaushe wannan lokacin zai wuce, sai yaushe zan fara jin daɗin duniya, sai yaushe Mama za ta fara sona kamar yadda kowace uwa ke son ɗan da ta haifa, sai yaushe zan yi murmushi wanda zai fito daga zuciyata, sai yaushe.....sai yaushe.........kullum cikin tambayar kai na nake, amma babu mai bani amsa, na san dai, a duk lokacin da ƙaddara ta sake ƙwanƙwaso min ƙofa, zan buɗe dan ina fatan dace da farin ciki kamar kowa.
Tabbas daga tasowa na zuwa yanzu, na azabtu wajen Mama, na sha wahala, na aikatu sosai, gashi ba boko ba islamiyya, haka nake rayuwa tamkar baiwar da ba ta gata.
Ni ce, aikin gida, Ni ce soya awara da rana, da dare kunu da ƙosai, kullum a waje nake wuni saboda neman kuɗi, wanda ni na zaɓa ma kai na hakan.
Hawayen dake kan fuskata na share, ina mai tuna mummunan rana a gareni, ranar da bazan taɓa mantawa da shi ba..........
_Tunani_
Baba ya yi fama da ciwon hanta sosai, an yi magani, an yi magani amma babu ci gaba, haka ya zauna a gida, magana ma wani lokacin wahala yake mai.
A lokutan da nake gida nike kula da shi, shima yana nuna min kulawa sosai, yana sona, kuma yana yawan ce min.
“Sakeenat, ki yafe min.......” Ni kuma sai na fashe da kuka, na rungumesa ina girgiza kai.
“Ba....Baba baka min komai, Baba na yafe maka, amma babu abinda ka min.” haka nake faɗa, sai dai ya girgiza kai kawai.
A lokacin na fara kokarin zama yadda Mama take so, dan na bar zuwa suya, ina zaune a gida, ana fara koyar da Ni yadda idanuna zasu buɗe, har boko mai tsaɗa Mama ta sani, na fara zuwa, sai dai Baba baya so, hakan yasa ya shiga damuwa ba kaɗan ba.
Wata biyu ina zuwa boko, amma ta ƙi sani islamiyya, a wata ranar Litinin, bayan na dawo daga makaranta.
Uniform na cire, sannan na nufa kitchen, an tsara abubuwan da zan dinga ci, wanda zai sa jikin ya ragu, sai dai ko kadan baya raguwa, ina nan a ƴar duma-duma ta.
Bayan na ci abinci, na shiga ɗaki dan duba jikin Baba, take gaban ya faɗi, ganinsa zaune yana ta zufa shi kaɗai, dan Mama ta fita.
Na yi sauri na isa kusa da shi, na fara jera mai tambayoyi, sai dai babu wanda ya iya amsa wa.
Sai ma kokarin yi min magana yake yi, amma ya kasa, wani fallen takarda dake hannunsa, ya bani yana mai cewa.
“Ki......kimin....al....alƙwari....kan cewa duk abinda ke rubuce a nan, shi za ki yi......ina so ki min alƙawari.” cikin kuka na tabbatar mai da na yi alƙawari, sannan na tura fallen cikin ajiyun dake rigata.
Take Baba ya yi murmushi yana mai jingina da kansa kan kujera, shiru na yi ina kallon yadda ya yi shiru lokaci guda, gashi yana murmushi.
“Baba yanzu wani magani za ka sha, ko ciwon ya tafi ne!?.”
A hankali na kai hannuna dan taɓa shi, sai kawai na ga Baba ya tafi luuuu ya faɗi.
“Inna.... innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un BAAAAABAAAAA.” Baba ashe lokaci ya cika.
A ranar na suma ya kai sau bakwai, daga wannan ranar na fara rashin lafiya, sai da aka sanya min drib leda bakwai, a lokacin ne ma Kamatuna suka ɗan rage, amma jikina yana nan.
Kusan sati biyu na yi cikin wannan halin, na sha zagi sosai wajen Mama, saboda damuwar da na shiga, acewarta ya yi yawa.
Zan iya rantsewa da Allah, Ni ce kawai na zubar ma Baba da hawaye, Mama ko a jikinta, sai ma ci gaba da harkokinta kawai ta yi.
Cikin ikon Allah na ji dama-dama, har na ɗan saki ina iya cin abinci.
Ina zaune kan katifa na yi tagumi, sai Mama ta shigo ɗakin ta zauna kan gado ta zuba min ido.
“Mama ina wuni.” Mama ta amsa da ƙyar.
“Na rasa gane miki gaba ɗaya, Ni miji nane ya mutu, amma ban shiga damuwar nan ba, kina so ki ce kinfi damuwa da shine ko me.” na girgiza kai hawaye na cika min ido.
Mama ta dungure min kai.
“Komai kuka, Shegiya mai ƙaton kai, idan za ki dena wannan kukan ki dena, ki kuma shirya gobe za ki je makaranta......kina jina!?.”
Na ɗaga mata kai.
“Ba ki da baki ne!?.”
“Ina da shi Mama.” Mama ta ja tsaki sannan ta fice.
Na share hawaye ina kallon hanyar da ta fita.
Take na miƙe, fallen takarda da Baba ya bani, na ɗauko, na zauna da ƙyau, sannan a hankali na buɗe ƙaddarar dake zane a rayuwata, lamarin da ya sauka min tunanina da komai nawa...................
“Sakeenat.....Sakeenat!.” da sauri na amsa dan na yi nisa cikin tunani.
Na tashi daga kan darduman na yi waje da sauri dan jin muryan Mama.
A parlour na iske ƴam mata kusan su bakwai, duk suna kallo a tv, cikinsu harda Amrah wacce ta zama ƴam mata mai aji.
Yanzu Ni kai na bance nasan adadin mutanen da suke zaune a cikin gidan mu ba, ƴam mata ne kala-kala a cikin gidan mu, zaurawa, da samari hardu ƴan daudu.
Shi yasa Mama tasa aka ƙara wasu ɗakuna saboda yawan mu, ga gidan namu ya yi suna, kusan unguwar mu gaba ɗaya babu sunan da yake tashe kamar na gidan mu, kuma da sunan Mama ake kiran gidan *GARKUWAR MATA*
Mutanan gari babu yadda za su yi ne, amma babu mai ƙaunar rayuwar da ake yi a cikin gidan mu, amma babu mai magana, saboda ƴam matan gidan mu, daga masu hurɗa da, polisawa, manyan ƴan kasuwa, ƴan siyasa da masu kuɗi, hakan yasa faɗa da gidan GARKUWAR MATA sai an shirya.
“Mama gani” na faɗa ina tsugunnawa gaban Mama wacce ke zaune tana latsa waya.
Bata kalleni ba ta ce.
“Rufaida gata nan.” ina jin haka na mai da idanuna kan Rufaida, wacce Mama ke ji da ita.
Ta girmeni amma na fita jiki sosai, kallona ta yi cike da shaƙiyanci, ta tauna chewing gum sannan ta ce.
“Indomie za ki dafa min, ga kuɗi ki siyo guda uku, sai ƙwai biyar.” amsar dubu biyun na yi sannan na yi waje.
Hakan ya fiye min sau dubu akan rayuwar da suke yi.
Takalmin roba na sa, sannan na juya na fara tafiya.
Gefe guda mata uku da maza samari huɗu, suna zaune akan taburma suna buga wasan kati.
Ban kulasu ba, na nufa get, danni yakan yi wiya na yi magana da mutum sai da babban dalili.
Kafin hannuna ya kai ƙofa, aka buɗe ana shewa da dariya, da sauri na matsa gefe, ganin wani ƙato rungume da ɗaya daga cikin yaran Mama, kaman ma a buge take, hanya na bashi, ya wuce da ita ciki, na girgiza kai ina jin tsanar rayuwar da suke yi, hawaye na ji ya cika min ido, murmushi na yi, na share, dan haka nake, ko ya naji babu daɗi a cikin rai na, sai na dai na ji hawaye kawai, hakan nan wani lokacin nake kuka ba tare da nasan dalilin yin ba.
Hatta ƙofar gidan mu akwai mutane sosai, wasu na hira, wasu na taɗi.
Na miƙe layin mu zuwa shago, na shiga.
Mai shagon ya min murmushi.
“Sakeenat baiwar Allah ya kike!?.” ba yabo ba fallasa na ce.
“Lafiya lau, indomie uku nake so, da ƙwai guda biyar.” ya amsa kuɗin yana ta jana da hira amma ban bashi fuska ba gaba ɗaya.
Ya miƙo min na kai hannu zan amsa, take ya riƙe min hannu, da sauri na kalla fuskarsa, ganin yana min murmushin ƴan iska yasa raina ya ɓaci, take na kasa control ɗin kai na, na ɗaga hannu na sharara mai mari.
Na fizga ledan ina cewa.
“Wannan ya zama karo na ƙarshe da za ka sake gigin taɓa hannuna, an ce maka kowa ɗan iska ne.....ka ci sa'a bana faɗa, da wallahi ko.......” na ja tsaki ina share hawayen da ya zubo min.
Na juya na fara tafiya ina jin ya fara zagina yana cewa.
“Kinci bashi wallahi, ke in banda ma taimaka miki zanyi, waye zai kalleki ya ji sha'awa, dube ki yadda kika san buhun masara, ga baƙi kamar baƙin gawayi.......”
“Wannan tsohon zagi ne, ka faɗa baso, na gaji da wanna.” na faɗa ina wucewa, na manta ban amsa canji ba gaba ɗaya.
Sai da na shiga gida na tuna, na kira sunan Allah sannan na buɗe labule na shiga.
Kusa da Rufaida na tsaya, na miƙa mata a tsaye.
Mama ta dallamin harara, na tsugunna na bata.
“Ina canjin!?.” ta tambaya tana zuba min ido.
Na yi shiru bance komai ba.
“Oh..... Sakeenat kinsan Cherry nake ci, ki mai da bana son super park.” na faɗa cike da iyayi.
“Tom bara na mai da.” na amsa na fita jikina a mace.
Ban san ya zamu wanye da mai shago ba, nasan ko kallona ba zai yi ba, ga Rufaida ba ta mutumcin tsafta za ta sa Mama ta duke Ni, na yi shiru ina kallon shagon, miyau na hiɗeye sannan na nufa shagon a natse ina ta ambaton sunan Allah a cikin raina...........✍️ End 😱😱😱😱😱😱😱
More likes, more comments = more motivation to keep typing and posting, Insha Allah. 🥲🫢❤️✍️
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*