CHAPTER 9
by @prettys01
> Ban san ya zamu wanye da mai shago ba, nasan ko kallona ba zai yi ba, ga Rufaida ba ta mutumcin tsafta za ta sa Mama ta duke Ni, na yi shiru ina kallon shagon, miyau na hiɗeye sannan na nufa shagon a natse ina ta ambaton sunan Allah a cikin raina.............
Na taka zuwa bakin shagon, sannan na shiga ciki.
Mai shagon ya harare ni da wani irin kallon banza, kafin ya ce cikin ɓacin rai,
“Fita min a shago!”
Na kalle shi cikin mamaki, sannan na ce,
“Indomie mai ledar ruwan ɗorawa nake so, ba wannan ba. Kuma ba ka ba ni canjina ba.”
Ya miƙe yana wani muzurai.
“Ni za ki mara ki yi zaton zan ƙyaleki, kuma wallahi gobe zan zo wajen wannan uwar taki mara tarbiyya na faɗa mata abinda kika aikata min.” raina ya sake ɓaci.
“Karka sake zagin min mahafiya, Shamsu bana son rigima amma kana nema kasa na yi.” na faɗa da wani irin tsiwar da baya tashi sai idan an zaga Mama.
“An zageta ɗin, ke wannan har kina mata kallon uwa, matar da ba ta da aiki sai lalata yara mata, hatta ita kan........” wani marin na sake wanka mai, ina wuci, na aje mai indomie na miƙa mai hannu.
“Ban wanda nake so, idan Allah ya kai mu gobe ka ce mata mari biyu na yi maka.” Shamsu ya danne zuciyarsa saboda har ga Allah yana so.
Na jima ina tsaye a cikin shagon, har na kai lokacin da idanuna suka fara zubar da hawaye, bansan ko tausayina ya ji ba, ya watso min dubu biyu, na ɗauka da sauri na bar shagon
Sai da na yi tafiya mai nisa tukunna na samu wani shago. Na shiga ciki, na siya Cherry, sannan na koma gida.
Da na isa, na tarar da Rufaida tana zaune kan taburma tana hira a waya.
Ban ɓata lokaci ba, na shiga kitchen. Na dafa mata Indomie, sannan na soya mata ƙwai. Bayan na gama, na kai mata abincin.
Amma ko ɗanɗanawa ban yi ba.
Na tsaya ina kallonta kawai, yayin da ta fara cin abincin da na shirya mata, ba sannu bare na gode, a haka ma na gode ma Allah ba ta yi complain akan na daɗe bangama ba.
Ina kallo sauran indomie wasu suka kwashe.
Bayan na gama komai, na koma ɗakinmu na kwanta kan katifata.
Ina kwance, sai na fara tuno wasiƙar Baba da ya rubuta min.
Kalamansa suka fara dawo min ɗaya bayan ɗaya, kamar da kanshi yake karanta min abin da ya sauya min rayuwata gaba ɗaya..........
*Adeelah*
Bayan an gama lecture gaba ɗaya, ban sake ganin Safraz ba. A zuciyata ina fatan ya wuce, hakan yasa na saki na ci gaba da aikin gabana.
Sai dai ina fita daga department ɗinmu, wani abu ya ja hankalina.
Dandazon maza ne a filin ball.
Na tsaya na ɗan kalli wajen...
Safraz!
Safraz ball star, yana tsakiyar filin ana wasa da shi. Kallon yadda yake motsi cikin filin ya sa wajen ya ƙara cika da mutane, kowa yana son kallonsa.
Na ja numfashi a hankali.
“Yauwa Alhamdulillah.”
Na faɗa a raina, sannan na juya na nufi motata, ina addu'ar na samu in bar wajen kafin ya lura da ni.
Amma da na isa wajen motar...
Na tsaya cak.
Babu yadda zan fitar da ita.
Motoci biyu sun tare ni gefe da gefe, sai kuma wani baƙin Sport da aka sa a bayan motata, ya rufe min hanyar gaba ɗaya.
Na tsaya ina kallon motocin, sannan na ɗora hannu a goshina.
Na sake duban filin ball.
Safraz yana can...
Ni kuma ina nan...
Kuma motata ta makale a tsakiyar wurin!
Na sake kallon baƙin Sport ɗin da aka aje a bayan motata, zuciyata ta fara ɓaci.
Na san wannan motar.
Motar Safraz ce.
Na haɗe gira.
Da farko na yi tunanin wataƙila ya aje motarsa ne ba tare da ya sani ba. Amma da na tuna yadda ya saba yin abubuwansa, sai na fahimci komai.
Da gangan ya yi.
Ya san motata tana nan, kuma ya san ba zan iya fita ba tare da an cire tasa ba.
Na ja dogon numfashi, sannan na jingina da motata ina kallon filin ball.
Safraz yana can, yana wasa cikin nutsuwa kamar babu abin da ya faru.
Na cije leɓena cikin fushi.
Ban gama maganar ba sai ya juya kansa daga filin, idanunsa suka sauka kai tsaye a kaina.
Sai ya tsaya.
Kallo ɗaya kacal muka yi ma juna.
Na yi saurin kawar da kaina.
Amma daga gefen idona, na ga ya fara takowa a hankali zuwa inda nake.
Na dafe goshina.
“Oh Allah... wannan mutumin ba zai bar ni in huta ba.”
Ga dukkan alamu da shirin ƙwallo ya zo, dan yanzu kayan ball ne jikinsa.
Bayan ya tawo wasu sai da suka biyo shi a baya.
“Ina so na ɗau motata.” na faɗa ina duba agogon dake hannuna.
A hankali ya juya baya, bansan mai ya yi musu ba, sai na ga duk an watse an bar Ni da shi.
“Baby so nake na ganki kafin ki wuce, dan Allah your number please.” ya marairaice fuska, yana son na bashi numberta amma na ƙi, bana son takura, shi kuma ya iya shi, babu yadda be yi ba ya samu numberta amma bai samu ba, dan Ni kaf school ɗin mu Nuseey ce ke da numberta, kuma na gargaɗeta.
“Safraz.......” zuciyarsa na ga ya dafa yana lumshe ido, bansan lokacin da na yi murmushi ba.
“Dan Allah zan wuce, ka ji.” na faɗa ina sassauta murya.
“To ki ban number kinji.” ya faɗa kamar wani yaro.
“Zan baka amma ba yanzu ba.”
“Sai yaushe Baby!?” ya faɗa cikin ƙosawa.
“Sai ranar da shigar ka ya yi ɗari bisa ɗari.” ina faɗin haka na shiga motata.
Murmushi ya yi sannan ya cire matarsa a hanya, Ni kuma na yi hanyar fita, ba tare da Nuseey muke komawa ba, dan tana rigani zuwa gida.
Kan titin na hau, na ci gaba da tafiya a natse, ban nufa ko ina ba sai supermarket.
Na shiga na yi siyayya sosai, duk kuma kayan cine irin na raya, biscuit, sweet, chocolate, cake da sauransu.
Na biya kuɗi sannan na fita daga wajen.
Gefen supermarket ɗin na iske wata mata tana bara cikin rana, ga yaronta sai kuka yake yi.
Iska na furzar daga bakina, na isa inda matar ke zaune.
Na tsugunna na gaishe da ita.
Ina da wani hali Ni, a duk inda na ga mai buƙata, to sai inda ƙarfina ya ƙare, bana son ganin kowani irin ɗan Adam cikin yanayin wahala.
Bayan na saurara kukar matar, ashe mijinta ne ya rasu, shine take bara, sai na ji babu daɗi.
Hakan yasa bansan adadin kuɗin da na bata ba, dan ta dogara da kanta.
Matar ta yi kukan farin ciki sosai, ta tashi ta wuce tana jin daɗi, na sauke ajiyar zuciya na shiga mota, sannan na nufa gida, amma ba gidan iyayena ba, gidan da ya kasance sashi ne na rayuwata wato gidan marayu..
Na ci gaba da tafiya a hankali har na isa wajen gidan marayun *SAKEENAT’S HOPE FOUNDATION*
Da na ɗago kai na kalli babban gidan, sai murmushi ya bayyana a fuskata.
Gidan ba irin gidajen marayu da ake zato ba ne. Babban gida ne mai kyau, an kewaye shi da doguwar katanga masu kyau, ƙofar shiga kuma tana da babban gate na ƙarfe mai kyau. A cikin harabar gidan akwai bishiyoyi da furanni iri-iri, yayin da gefen hanya aka jera kujeru da wuraren da yaran ke zama su yi wasa.
Akwai wani babban ginin bene biyu a tsakiyar harabar, wanda yake ɗauke da ɗakunan yaran maza da mata. A gefe kuma akwai babban dining hall, kitchen, ɗakin karatu, da wani fili mai faɗi da aka tanada domin wasanni.
A can gefe kuma akwai ƙaramin clinic da ɗakin ma'aikata.
Wannan gidan ba wani gida ne da aka gina domin neman suna kawai ba.
Baba ne ya gina shi domin ni.
Tun ina ƙarama yake gaya min cewa yana son in samu abin da zan yi wa marasa ƙarfi. Shi ya sa ya gina wannan gida, ya samar da duk abin da yaran suke buƙata, sannan ya damƙa min kula da su.
Na sauka daga motata, ban ma samu na rufe ƙofar motar ba sai na ji ƙarar muryoyin yara.
“Aunty Sakeenat!”
Na ɗago kai.
Wasu yara ne suka fito a guje daga cikin ajujuwan su.
Murmushina ya ƙara bayyana a fuskata.
“Ku bi a hankali mana!”
Amma ina gama faɗin haka, sai suka iso wajena.
Wasu suka rungume ƙafafuna, wasu suka kama hannuna, wasu kuma suka rungume ni sosai suna dariya cikin farin ciki.
Na durƙusa na rungume su gaba ɗaya.
“Ya kuke ƙananan yara na?”
“Mun yi kewarki!”
“Kin daɗe ba ki zo ba!”
“Kin kawo mana wani abu?”
Na fashe da dariya.
“Ahhh! Ashe ba ni kuka yi kewar ba, kayan da na kawo muku kuka yin kewarsu!”
Suka yi dariya.
Na shafa kan ɗaya daga cikinsu.
“Ku je ku taimaka min da kayan da ke mota.”
Nan take suka fara zagaye motar cikin murna.
Na buɗe boot ɗin motar, na fitar da manyan ledojin da na cika da biscuit, chocolate, sweet, cake da sauran abubuwan ciye-ciye.
“Ga naku.”
Kafin na gama basu, sai murna ta barke.
Na fara raba musu kayan ɗaya bayan ɗaya, kowa ya samu nasa. Wasu suna godiya, wasu suna dariya, wasu kuma suna kallon kayan nasu kamar sun sami babbar kyauta.
“Na gode, Aunty Sakeenat.”
“Allah ya saka da alheri.”
“Thank you!”
Na yi murmushi ina kallonsu.
“Ku ci a hankali fa. Kada ku yi faɗa.”
“Ba za mu yi ba!”
Na sake dariya.
Bayan sun karɓi nasu, suka watse cikin murna, wasu suka koma ɗakinsu, wasu kuma suka nufi wajen wasa.
Na tsaya ina kallonsu na ɗan lokaci, zuciyata cike da wani irin farin ciki da ba zan iya bayyana shi da kalmomi ba.
Sai na juya na nufi babban office ɗin gidan.
Na shiga cikin office ɗin, inda Bana mai kula da gidan yake zaune a bayan teburinsa yana duba wasu takardu.
Da ya ɗago kai ya gan ni, sai murmushi ya bayyana a fuskarsa.
“Ƴata!”
Na zauna a kujerar dake gabansa.
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumussalam. Yau kin tuna da mu kenan?”
Na yi murmushi.
“Ba fa haka ba. Na yi busy ne da makaranta.”
Ya girgiza kai cikin murmushi.
“Na sani. Amma yaran nan kullum suna tambayar yaushe za ki zo.”
Na kalli ƙofar office ɗin, inda wasu daga cikin yaran suke ta leƙowa, a haka kwana biyu ne kawai ban zo ba.
Na yi murmushi.
“Ni ma ina kewarsu.”
Ya aje takardun da ke gabansa, sannan ya ɗora hannayensa kan tebur.
“To, ya makarantar? Kuma ya gida?”
Na ɗan yi shiru.
“Alhamdulillah... komai lafiya.”
Ya kalle ni na ɗan lokaci, kamar yana son ƙara tambayata wani abu.
Sai na ce,
“Baba ka faɗa min duk abubuwan da ake buƙata, zuwa gobe insha Allah zan sa a kawo komai.”
Baba ya ɗan gyara zaman shi, sannan ya buɗe wata takarda da ke gabansa.
“Alhamdulillah, Ƴata. Gaskiya ba mu da wani abin da muke buƙata a yanzu. Komai akwai, yara suna da abinci, kayan sawa, magunguna da sauran abubuwan da suke buƙata.”
Na yi murmushi.
“Alhamdulillah.”
Baba ya ɗaga kai yana kalleni.
“Har ma jiya an sake turo mana da saƙo daga wannan mutumin da ya saba taimaka mana da kuɗi.”
Na ɗan ɗaga gira.
“Wanne mutumin?”
“Wanda duk wata yake turo mana da ₦500,000.”
Na yi murmushi, na girgiza kai a hankali.
“Allah ya saka masa da alheri. Gaskiya ina son ganin waye wannan mutumin da yake son taimakon mutane haka.”
Baba ya ta yi murmushi mai ma'ana.
“Ai duk yadda yake da son taimako... a bayanki yake.”
Na kalle ta cikin mamaki.
“Bayana?”
Baba ya gyaɗa kai yana murmushi.
“Wallahi ke ta daban ce, kafin a samu yarinyar irin ki za'a daɗe sosai, kuma zai yi wiya........tun kina da shekaru sha biyar kika sauke Alqur'ani, mahaifinki ya gina miki gidan nan a matsayin kyauta, tun kuma daga lokacin kina mai da hankali akan mu, wasa-wasa yanzu muna da Yara dari uku da talatin da huɗu a gidan nan, bayan auren da muke haɗawa idan yara sun girma ..... Abun farin cikin ba ki taɓa neman suna da gidan nan ba, hasalima kinfi zuwa a ɓakuwa, Sakeenat Allah ya albarka ci rayuwarki........”
“Ameen Baba, dan Allah nake yi ba dan komai ba.” na faɗa ina alfahari da yadda yake kula da yaran.
“Batun shi mutumin, babu wani information akansa!?.“ na tambaya dan har ga Allah ina fatan ganinsa na mai godiya.
“Eh babu komai nasa, Tun da farko ma ya ce kada a taɓa faɗa wa mai gidauniyar waye shi, amma yakan zo ganin yaran bayan lokaci mai tsawo.”
Na yi murmushi, amma zuciyarta ta fara cika da tambayoyi.
“Me ya sa zai taimaka mana haka, amma kuma baya son a san shi?”
Baba ya ɗan yi shiru, sannan ya ce,
“Wataƙila yana son lada ne daga Allah kawai.”
“Allah ya biyasa da gidan alheri”
“Ameen.” ban na jima sosai muna tattauanawa, sannan ya taka min, muka zagaya sauran yaran da suke ajujuwan karatu, duk yawan tsarabar da na kawo wasu ba su samu ba.
Haka na sake sanya wa aka siyo musu abun taɓawa, a ƙalla na yi awa biyu a gidan, sannan na musu sallama, yara suka rakani har bakin mota, na shiga na musu sallama sannan na fara tafiya a cikin moton.
Ina shiga layin gidanmu, idanuna suka sauka kan saurayina na biyu, wato Samir.
A shekarun baya, ni da shi muka yi gasar Tahfeez, inda muka wakilci Jihar Kaduna. Alhamdulillah, mun yi nasara—ni na ci a ɓangaren mata, shi kuma ya ci a ɓangaren maza.
Tun daga wannan lokacin ne Samir ya fara bibiyata.
Sai dai ina da ƙwarjini sosai. ina yi wa mutane ƙwarjini fiye da misali, gaskiya hakan ne. Wani lokaci ma hakan kan ke sa mutane su ji nauyin zuwa su yi min magana.
Amma ban taɓa raina wani ɗan Adam ba.
Na fahimci cewa Samir wajena ya zo, sai na yi parking a gefen gidanmu.
Na kashe motar, sannan na fito ina zuba masa ido.
Yana tsaye a gefen hanya cikin nutsuwa.
Sanye yake da farar jallabiya mai kyau, wadda ta ƙara fito da tsabtar kamanninsa na cikakken bahaushe. A hannunsa riƙe da tally counter kamar kullum, yayin da fuskarsa ke ɗauke da wannan murmushin da na saba gani duk lokacin da ya ganni.
Da na isa kusa da shi, ya ɗago kansa.
Idanunsa suka sauka a nawa, sai ya daburce take, a haka ya buɗe baki a hankali ya ce.
“Assalamu alaiki, Hafiza Sakeenat.”
Na amsa sallamarsa a hankali.
“Wa alaikas salam, Samir.”
Ya yi murmushi.
“Na dade ina jiran ki.”
Na ɗan kalle shi, sannan na ce,
“Me ya kawo ka?”
Ya sauke numfashi a hankali, kamar wanda ya daɗe yana shirya abin da zai faɗa.
“Na zo ne saboda ina son mu yi magana.”
Na haɗe gira.
“Magana?”
Ya gyada kai.
“Eh. Kuma wannan karon... magana ce da nake son ki saurare ni har ƙarshe.”
Na ɗan yi shiru, ina kallonsa.
“Madalla, ina sauraronka.”
Samir ya yi murmushi kaɗan, sannan ya kalli gefen titi kafin ya dawo da kallonsa gare ni.
“Sakeenat, kin san tun ranar da muka haɗu a gasar Tahfeez, ban sake iya cire ki daga raina ba.”
Na sauke idona ƙasa na ɗan yi shiru.
Ya ci gaba da magana cikin nutsuwa.
“Na yi ƙoƙarin ganin ko lokaci zai sa abin ya wuce, amma maimakon ya wuce sai ya ƙara ƙarfi.”
Na ɗago ido na kalle shi.
“Samir…”
Ya ɗaga hannu a hankali.
“Ki bari na gama.”
Na yi shiru.
“Ba wai yau ne na fara tunanin wannan magana ba. Na daɗe ina son in zo wajenki, amma da na zo sai na kasa faɗar abinda ke zuciyata, sai dai ina ji na kasa.........amma nasan ke kin kasan abinda ke kawo Ni wajenki......”
Na yi ɗan murmushi.
“Ni ban taɓa hana ka magana ba, sannan taya zan san abinda ke cikin zuciyarsa!?.”
“Uhmmmm ƙwarjininkin ya yi yawa ne shi ke hanani magana.”
Na kasa daurewa sai da na yi murmushi.
“Ni kuma ban san haka nake ba.”
“Kin sani mana.”
Ya faɗi hakan yana murmushi.
“Duk lokacin da nake ganinki a makaranta, sai in ce yau zan yi magana da ke. Amma idan na ga yadda kike tafiya da nutsuwarki, sai in rasa ƙarfin halin.”
Na girgiza kai.
“Samir, me kake son faɗa min?”
Ya ɗan yi shiru.
Sai ya ce,
“Na zo ne in gaya miki cewa bana son abin da ke tsakaninmu ya kasance magana kawai. Ina son na zo ta hanyar da ta dace.”
“Bangane ba.”
“Uhmmmm dama ina so ne na nema izini wajen su Baba, akan na fara zuwa hira wajenki.” raina ya soma ɓaci, amma ina daraja mutum, hakan yasa na ciza leɓena sannan na taka kusa da shi.
“Samir.....”
“Na'am.”
“Na baka dama ka jarraba sa'arka, idan har na amsa soyayyar ka shike nan, amma ban san takura .......... Sai anjima.” ina faɗin haka na shiga mota, tare da danna horn.
Samir cikin farin ciki ya shiga nasa motar, bai wuce ba sai da na shiga babban gidan mu, wanda aka sake gyara mana shi.
Na yi parking gefan motocin wajen, sannan na fita daga motar, da sauri wata sabuwar ƴar aikinmu, ta zo ta taimaka min da jakkata, muka jera muna hira gwanin sha'awa.
Part ɗina na fara shiga, na rage kayan jikina sannan na shiga toilet dan yin wanka, ban ɓata lokaci ba na fito, na sanya doguwar rigar shan iska, sai dogon hijabi, shimfiɗa darduma na yi sannan na hau, bana sallah, sai na zauna, ido na lumshe, take na fara rero karatun Alkur'ani cikin daddaɗan Muryata mai sanyi, ina karatun ne cikin natsuwa, fitar da ko wani hukuncin Alqur'ani, tare da dabburin ayoyin, wanda suke sanya jikina ya yi sanyi...................✍️ End > 😍😍😍😍😍😍😍
More likes, more comments = more motivation to keep typing and posting, Insha Allah. 🥲🫢❤️✍️
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
More likes, more comments = more motivation to keep typing and posting, Insha Allah. 🥲🫢❤️✍️