SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER

by @prettys01

> Part ɗina na fara shiga, na rage kayan jikina sannan na shiga toilet dan yin wanka, ban ɓata lokaci ba na fito, na sanya doguwar rigar shan iska, sai dogon hijabi, shimfiɗa darduma na yi sannan na hau, bana sallah, sai na zauna, ido na lumshe, take na fara rero karatun Alkur'ani cikin daddaɗan Muryata mai sanyi, ina karatun ne cikin natsuwa, fitar da ko wani hukuncin Alqur'ani, tare da dabburin ayoyin, wanda suke sanya jikina ya yi sanyi..............

*Sakeenat* ★A hankali na buɗe idanuna jin ana sallar asuba, na tashi da ƙyar, na zauna ina miƙa tare da mitsitsika idanuna, ai da sauri na zabura gajin namiji ya fita daga ɗakin mu da sauri, da sauri na miƙa hannu na kunna hasken ɗakin.

Amrah ce kwance kan gado, tana ɗaure da zani a jikinta, ga kuɗi masu yawa a hannunta, ganin na kunna haske yasa ta kalleni, ta ja ɗan tsaki tana mai da hankalinta akan kuɗin.

Raina ya ɓaci ainun, amma ba zan iya faɗar komai ba, saboda zan ja ma kaina masifa ne, kwanaki sau uku ina kamata da namiji a cikin ɗakin mu, Allah ya so Ni idan na kwanta sai asuba, kuma ban cika jin motsi ba idan ina barci.

Bayan al'amarin ya ishe Ni, na kai ƙara wajen Mama, hmmmmm ranar nasha duka sosai, Mama take sanar da Ni, babu ruwana akan duk wani abu da ake yi a gidan nan, tunda rayuwar da na zaɓa ma kaina kenan.

Kuma daga wannan lokacin bansake magana ba, sai kuma Amrah ta dena gayyato mana shi, amma yau sai ga wani ƙato ya fita daga ɗakin mu.

Da sauri na kalla jikina, hamdala na yi dan ganina da hijabi.

“Ke dalla kashe hasken nan, barci zan yi.” hannu na kai na kashe hasken, sannan na tashi na shiga bayi, na yi alwala, bayan na fito, na dungura sallah kamar yadda na iya, na yi addu'a sosai, sannan na fita tsakar gida.

Nasan babu masu yin Sallah akan lokaci, wasu ba basayi gaba ɗaya, Allah dai ya kyauta.

Aikin gida na fara yi, na yi shara, na yi wanki, sannan na yi abincin kari, babu abinda ke mugun ɓata min rai, sai halin wasu matan, gaba ɗaya sun mai da Ni ƴar aiki, zan gama girki, amma daga mai cewa “Soya min wanna, dafa min wannan, yi min kaza yi wannan.” ban kuma isa na ƙi ba, saboda ni ce zaɓa hakan.

Da misalin 9am na safe, na shirya tsaf, cikin material launin Kore, na sanya maroon hijab dogo har ƙasa, sannan na yi ma Mama sallama, bayan ta sanar min an kai cefane shago.

Mama tana da kuɗi masu yawa, amma duk hanyar da tasan zan sha wiya sai ta sa na bi.

Wani shago ta kama wanda nake siyar da abinci, kuma alhamdulillah duk abinda na girka, duk yawan shi, zuwa yamma yake ƙarewa, Allah ya samin nasibi akan sana'ar, sai dai ko sisi bana samu, a haka ma idan wata rana kuɗin ta bai yi riba ba, sai ta duke Ni, Ni kuma akan komai ina yi ne tsakani da Allah, bana cin komai, sai dai na yi ɗanɗano akan karshe, shima bana haɗiyewa, na ƙwammaci na tofar ko na goge kan harshen.

Na ƙarasa shagon da Mama ta kama min, na tsaya a bakin ƙofar ina kallon wajen na ɗan yi murmushi. Shagon ba babba ba ne, amma yana da kyau kuma yana kan hanyar da mutane ke yawan wucewa. An yi masa fenti mai kyau, ga wata doguwar rumfa a gabansa wadda ke kare masu cin abinci daga rana.

A gefe guda na shagon akwai kujeru da tebura ƙanana da aka jera cikin tsari, inda masu zuwa cin abinci suke zama su ci. Wasu daga cikin kujerun kuwa an yi su ne da ƙarfe, wasu kuma na roba.

Na shiga ciki, sai na iske cefanen da aka kai min a jere. Albasa, tumatir, kayan miya, doya, ƙwai, ganye, wake, shinkafa da sauran kayan da zan yi amfani da su duk an kawo su.

“Alhamdulillah,” na furta a hankali.

Na aje jakata gefe, na ɗaura hijabina da kyau sannan na fara shirya wajen.

Da farko na wanke doya na yanka ta daidai, na ɗora mai a kan wuta. Bayan ya yi zafi, sai na fara saka doyar a hankali, ɗaya bayan ɗaya, ina kula kada ta yi yawa a lokaci guda.

Ƙamshin soyayyen doya ya fara tashi, har ya cika wajen daɗin ƙamshi.

Sai na ɗaura dafaffe fita a wani tukunyar, murhu uku nake amfani da shi, tabbas ina shan wahala, dan aiki nake kaman ingi, tun daga tara nake fara girke-girke har karfe biyu, Ni ce mai dafawa, mai rabawa, mai wanke kwanuka, mai komai, dai-dai da minti ɗaya bana samu na huta.

Bayan na gama soyayyar doya, sai na fara haɗa doya da ƙwai. Na soya albasa da tumatir da kayan ƙamshi, sannan na karya ƙwai a kai ina juyawa a hankali har komai ya haɗu.

Daga nan kuma na shiga yin faten wanke, na shirya shi cikin tsari, na tabbatar komai ya yi kyau kafin na ɗora shi, ya ji ganye ga bushashshen kifi.

shinkafa da wake ne ƙarshen ɗaurawa, na ɗaura shi bayan na ga wa'incan, na dafa garaugaru da mai da yaji, idan manja ko man ƙuli mutum ke so duk akwai.

Ban gama girkin ma mutane kuwa suka fara shigowa siyan abinci.

“Yarinyar nan, ki bani doya da ƙwai.”

“Ni kuma faten wanke nake so.”

“Faten wanke ma ki haɗa min.”

Ina ta aiki ba tare da tsayawa ba, hannuna ɗaya yana aiki, ɗayan kuma yana karɓar kuɗi ko shirya abincin masu siya.

A hankali wajen ya fara cika da mutane, wasu suna zaune a kujerun gefe suna cin abincinsu, wasu kuma suna tsaye suna jiran nasu.

Na ɗan kalli wajen, sai na yi murmushi.

“Alhamdulillah.”

Ko da yake ba na samun komai daga cikin kuɗin, ina jin daɗin ganin sana'ar tana tafiya.

Abin da nake fata kawai shi ne Allah Ya sa wannan sana'ar ta zama sanadin samun rabona a rayuwa.

A daidai lokacin da nake tsaye ina kwashe shinkafar cikin kula, wasu mutane suka zo suka sayi abinci. Na zuba musu a cikin takeaway, na miƙa musu, suka biya kuɗinsu suka wuce.

Ina komawa bakin wutar ne na hangi shi.

Na san shi.

Ba yau ne karon farko da zai zo shagon ba. Sau da yawa yana yawo a wannan layin, kuma idan ya zo, ba ya magana da kowa, ba ya neman komai. Kawai shigowa yake yi ya nemi wuri ya kwanta a cikin shagona.

Kamar kullum ya shigo cikin shagon a hankali.

Dattijon ne mai kimanin shekara hamsin da biyar. Duk da halin da yake ciki, har yanzu ana iya ganin cewa kyakkyawan mutum ne.

Fuskarsa doguwa ce, hancinsa madaidaici mai tsawo, idanunsa manya ne, amma suna da wani irin yanayi na rashin nutsuwa. Gashinsa ya yi tsawo ya har gadon bayansa kuma a yamutse, gemunsa kuma ya cika harda furfura mai yawa.

Sanye yake da wata tsohuwar riga mai launin toka, wadda ta yi datti da yage-yage a wasu wurare. Wandon da ke jikinsa ma tsoho ne, ya yi masa faɗi, ya kuma dusashe, Ƙafafunsa babu takalmi, ƙura ta rufe su, ga jiki ba wani jiki ga re shi ba, haka kuma bakinsan yana zubar da miyau kamar yaron dake fara haƙori

Kamar yadda ya saba, ya nufi wani gefen shagon, ya kwanta a ƙasa, ya juya gefe, ya matse kansa da hannunsa.

Ban ce komai ba.

Na dai kalle shi na ɗan lokaci, sannan na mayar da hankalina kan tattara wake-waken da nake tarawa.

Na saba da shi.

Kullum idan ya zo, haka yake yi.

Shigowa kawai yake yi

Ya kwanta.

Ya yi shiru.

Yana ban tausayi sosai, wani lokacin har kuka nake yi idan ina kallon yadda yake.

Bayan na gama, sai na zuba shinkafa da doyar a cikin plate. Na ɗauki plate ɗin na nufi inda yake kwance, na ajiye masa a gabansa.

Da sauri ya tashi ya zauna.

Ya ɗago kansa ya kalle ni, sannan ya sakar min murmushi mai ban tausayi, kafin ya sunkuya kan abincin ya fara ci.

Yana ci da sauri, kamar wanda ya daɗe bai samu abinci ba.

Na tsaya ina kallonsa na ɗan lokaci, zuciyata ta taɓu, hawaye ya cika min ido.

Da ganin yadda yake haɗiye abincin cikin gaggawa, sai na yi saurin komawa wajen teburin, na ɗauko roba mai ruwa na kawo masa.

“Ga ruwa.”

Ya amsa ba tare da ya ce komai ba.

Ya kai ledan purewater bakinsa, ya kai cafke da haƙorinsa, nan take ya zuƙe ledan ruwan, sannan ya sake komawa kan abincinsa.

Bayan ya gama, ya tashi ya tafi, na bishi da ido kawai.

Yana tafiya, shagona ya sake cika, ba Ni ce na samu natsuwa ba sai wajen karfe shida, komai na shagon ya ƙare tas, na haɗa kuɗi kuwa mai yawan gaske.

Yunwa nake ji sosai, ga shi na gaji, haka na share shagon bayan na yi wake-wake, sannan na fito na kulle shagon.

Mama tana tsoron wata rana kar na tawo a ƙafa a tare Ni a amshe gaba ɗaya kuɗin, hakan yasa kullum idan na tashi, nake hawan mashin daga nan har ƙofar gida.

Mashin na hau, ya ko kaini har gida, lokacin har an shiga Masallaci, na sauka na bashi kuɗinsa sannan na shiga gidan mu wanda na fara jiyo hayaniya, nasan rigima ake yi, dama wannan ba sabon abu bane a gidan mu.

Na tura ƙofa na shiga, ƴam mata ne da samari cike a tsakar gidan, kowa yana tsaye, harda Garkuwar mata wato Mama, zaune tana sauraren bayanin Zeezee ƴar daba.

Ina shigowa naga mutane sun kalleni, da sauri Zeezee ta ce.

“Alhamdullah, gata nan ta dawo.” gabana ne ne ya buga, na dage ƙirjina ina marairaice fuska, dan rabon da na yi magana da ita ma tun shekaran jiya, balle ace na mata laifi, hannuna ta riƙe da ƙarfi tana wani huci kamar zakanya, yayinda Garkuwar mata ta zuba min ido da sauran jama'ar wajen.....................✍️ End.

> Tashin hankali 😱😱😱🫢 Taƙwarata Allah ya fitar da ke lafiya. Ameen ╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

More likes, more comments = more motivation to keep typing and posting, Insha Allah. 🥲🫢❤️✍️