CHAPTER 1️⃣1
by @prettys01
> “Alhamdullah, gata nan ta dawo.” gabana ne ne ya buga, na dage ƙirjina ina marairaice fuska, dan rabon da na yi magana da ita ma tun shekaran jiya, balle ace na mata laifi, hannuna ta riƙe da ƙarfi tana wani huci kamar zakanya, yayinda Garkuwar mata ta zuba min ido da sauran jama'ar wajen....................
Zeezee ta kalleni ta ce. “Faɗa mana, jiya da Rufaida ta aikeki siyan indomie, da za ki fita, wacece aka shigo da ita ta tashawu a cikin matan gidan nan?.” a hankali na sauke ajiyar zuciya, dan na samu ɗan natsuwa.
Na kalla yawan matan gidan ina kokarin tuna fuskar wacce na gani.
Take na tuna wacece, hakan yasa na sata kallon Ayusha da sauri.
Tabbas Ayusha ce, dan kayan jiya ne ma a jikinta.
Ayusha da muka haɗa ido, ta dallamin harara tare da min kashedi mai zafi da ido.
Nasan wacece Ayusha, idan ana neman ƴar bala'i number one a gidan mu, to ita ce, babu mai shiga harkanta, hatta Garkuwar mata ba ta shiga duk wani abu da ya shafeta ba, ba ta da imani, ita ta ƙona kishiyarta da ruwan zafi, mijin ya sake ta, ba ta bar gidan ba, sai da ta sanya aka karya mai ƙafafu, shine ta dawo gidan mu tana rayuwa.
Idan babban matsala ta faru a gidan, ita ake nema saboda tana harka da polisawa sosai.
Wani kakkaurar miyau na sake haɗiyewa sannan na kalla Zeezee ƴar daba, itama ba baya ba, yawancin masu zuwa wajen ta duk ƴan daba ne, nasu yawo da wuƙa a ƙugu.
Nan take jikina ya yi sanyi.
“Ke dalla kina ɓata mana lokaci, ki faɗa wacece a cikin matan gidan nan, ta ci amanar Zeezee, ki faɗa ko uban waye na ci uwarsa.” Zeezee ta faɗa tana tafa hannu cikin masifa.
Sallah ake yi a masallaci, amma gidan mu tashin hankali ake yi.
“Uhmmm jiya wai.....”
“Eh mana Sakeenat, ki faɗa Ni da kai na zansa polisawa su kama kowace ƴar iska ce.” Ayusha ta faɗa cike da bariki, yadda kasan ba itace ta shigo jiyan ba.
Nan take hayani ta kaure a wajen, na fahimci wanda ya shigo da Ayusha jiya saurayin Zeezee ƴar daba ce.
Garkuwar mata ce ta daka tsawa, wanda yasa kowa na wajen ya yi shiru.
Ta kalleni da ƙyau.
“Sakeenat faɗa wacece a cikin su.......yanzu nan.” na ɗaga kai a hankali ina tausayin kaina.
Wani kallo da Mama ta min yasa na buɗe baki da ƙyar na ce.
“Jiya da zan fita, ina zuwa daidai bakin ƙofa, sai aka buɗe, hakan yasa na matsa gefe guda, a daidai wannan lokacin wani matashi ya shigo ɗauke da Ayusha a hannu, kuma a buge take, suka wuce, Nima na fi..........” wani gigitaccen mari na ji akan kuncina, kafin na tantance raɗaɗi, naji an rufe Ni da duka, dukana ake kamar an samu jaka.
“Dan ubanki Ni za ki ƙala ma sharri, Ni Ayusha, kan bura ubancan....yau sai na ga wanda ya tsaya miki......” Ayusha ta faɗa cikin ɓacin rai.
“Buga ƴar iska, har sai ta faɗa gaskiya, ko dai kuɗi yarinyar ta bata.” cewan Zeezee ƴar daba.
Babu wanda ya hana Ayusha dukana, sai da ta tabbatar ta min shegen duka sannan ta matsa gefe tana wuci.
“Idan kika sake ambatan sunana, wallahi sai na karya Miki wuya.” ta harareni tana wani cika tare da batsewa.
Kuka na fashe da shi jin abin da Mama ta ce.
“Yanzu jikin ki yayi tsami, sai ki faɗa wacece, idan kuma bata nan ki faɗa sunanta, yanzu sai a kirata.” na haɗiye kukan sannan na buɗe baki a hankali na ce.
“Narantse da girman Allah Ayusha ce wacce na......” Ayusha ta yo kaina, Mama ta dakatar mata, take na ji sanyi a cikin raina.
“Amrah amso min jakkar kuɗin can, kar wani abu ya same su wajen dukanta, na lura ba za ta faɗa gaskiya ba.” Amrah ta zo ta amsa ta miƙa ma Mama.
Ayusha ta sake jibgata, har sai da bakina ya fashe, sannan aka sake tambaya ta wacece.
“Wacece!?.”
“A....Ayusha.” a lokacin na fara ba kowa haushi, hakan yasa Zeezee ƴar daba da Ayusha suka haɗu suka sake dukana, tun ina kuka har na yi shiru.
Na rantse da Allah Mama tasan ba zan yi ƙarya ba, bana ƙarya, tana yawan faɗa min ta tsana wannan halin nawa, amma Ni da na yi ƙarya na ƙwammace a kashe Ni.
Ganin ba zan sauya sunan ba, hakan yasa suka rabu da Ni bayan sun naɗamin na jaki.
Da ƙyar na iya shiga ɗaki, na kwanta kan katifa, jikina yayi zafi, idanuna suka yi ja.
Mama ce ta shigo hannunta riƙe da ruwan maganin da tun ina ƙarama nake sha, ta bani na amsa na sha.
“Na.... gode.” na faɗa ina share hawaye
Ta zauna tana kallona da kyau. “Na faɗa Miki sau da yawa, akan faɗin gaskiya, idan baki dena wannan halin ba, to wallahi wata rana zai ya ja miki babban masifa.....idan kin yi ƙarya wani abu ne zai same ki!?.” na girgiza kai da sauri.
“To ki gyara ko duniya ta gyara miki zama, kina jina!?.” na sake ɗaga mata kai, amma bai kai zuciya ba.
“Ma...Mama.” ta amsa da ƙyar. “Meye.” “Dan girman Allah ki taimaka min, yunwa nake ji sosai, rabona da abinci tun kunun safe, dan Allah ki taimaka min......” sai na fashe da kuka mai tsuma zuciya.
Mama ta girgiza kai cikin tausaya.
“Sakeenat, Ni mahaifiyar ki ce, ina so na ga rayuwarki ta sauya, ina so naga kema kin samu farin ciki, amma ina, ke kika zaɓa ma kanki wannan rayuwar........da yanzu kinfi kowa samun kasuwa a gidan nan, saboda kina da ƙyau, ke ƙyaƙyƙyawa ce, ga ki da sura mai kyau, duk kuwa da kina da ƙiba.” sai ta miƙe ta iso kusa da Ni.
“Har yanzu akwai sauran lokaci, Sakeenat cikin sati guda za ki murje, ki zazzage da ƙibar nan, kema ki zama mai capacity.” ido na rintse.
“Mama a haka ina jin daɗin rayuwata, dan Allah mu bar wannan maganar.”
“Ke kika sani, kullum ana nuna Miki hanya amma kinfi son wahala, ai shike nan.” tana kaiwa nan ta tashi ta bar ɗakin.
Na dungule waje guda, ina jin babu daɗi, ace mahaifiyar da ta haife Ni bata sona, bata ƙaunar farin cikina.
Da sauri na kau da tunanin komai, sannan na kwanta, banyi sallolin uku ba, gashi an kusa kiran isha'i, ga halin da nake ciki ba zan iya sallah ba, sai kawai na kwanta da cewan da asuba insha Allah duk zan rama su....................
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
*Adeelah*
Ina zaune kan kujera, na ɗaura kaina akan cinyar Dad. Hannunsa ɗaya yana zagaye da ni cikin kulawa, yayin da idanuna ke kan talabijin da ke gabanmu.
Daddy sanye yake da wata fararen kayan barci, wanda ya zauna masa da ƙyau a jikinsa, sai ƙamshin turare yake, yadda kasan zai fita, bayan kuma dare ne, da yake ma'abocin son ƙamshi ne, kamanninsa cike suke da natsuwa da kwarjini.
Mom kuwa tana zaune a gefenmu a kan doguwar kujera mai laushi. Sanye take da doguwar rigar atamfa mai kyau, mai launuka masu laushi da ɗan ƙyalli a jikinta, ta ɗaura ɗan mayafi da ya dace da kayan. A hannunta kuwa akwai cup ɗin kayan marmari tana sha a hankali.
Na lura Mom tana kallona, tana ta murmushi.
“Mom, me yasa kike kallona kina murmushi?”
Mom ta girgiza kai a hankali, amma murmushin bai gushe ba.
“Wani abu nake tunani ne a kanki.”
Da sauri na ɗago kai daga kan Dad na kalleta.
“To faɗa min mana.”
“A’a…” Ta yi murmushi, sannan ta girgiza kai. “Ba yanzu ba. Sai lokacin ya yi.”
Na ɗan tura baki, kafin daga bisani na yi murmushi.
“Why Mom, haka kike yawan faɗa idan na tambaye ki.”
“Uhm lokaci bai yi ba, idan yayi zan faɗa Miki ai.”
“Shi ke nan, Mom.”
Ta lumshe idanunta cikin wani irin farin ciki.
A cikin zuciyar Mom kuwa, wani buri take saƙawa a kan rayuwata—buri da ta yi imanin cewa wata rana zai zama gaskiya.
Dad ya shafa kaina yana tuna hirar mu a shekarun baya........
“Dad, yanzu wai a faɗin duniyar nan akwai waɗanda suke rayuwa cikin ƙunci da tashin hankali?”
Na tambaya cikin mamaki, ina ɗago kai na kalleshi.
“Eh Princess, akwai su sosai.”
Na yi shiru na ɗan lokaci, zuciyata ta yi nauyi.
“Ina jin babu daɗi ace akwai masu kuɗi a duniya, amma ba sa taimaka wa waɗanda ba su da shi,” na faɗa cikin rauni.
Dad ya kalle ni, murmushi mai taushi ya bayyana a fuskarsa.
“Princess, ai na Allah ba su da yawa.”
Na ɗan yi shiru, kalamansa suka ci gaba da yawo a cikin zuciyata.
“Amma Dad…” na ɗago kai na sake kallonsa, “me ya sa Allah yake barin wasu su rayu cikin irin wannan wahalar, wasu kuma suna da abin da ya fi bukatarsu?”
Dad ya yi murmushi a hankali, sannan ya shafa kaina.
“Saboda rayuwa jarabawa ce, Princess. Wani Allah zai jarabce shi da dukiya, wani kuma da rashin ta. Wanda aka ba shi dukiya, ana kallon yadda zai yi amfani da ita. Wanda aka hana shi, kuma ana kallon yadda zai yi haƙuri.”
Na gyada kai a hankali.
“To idan mutum yana da abin da ya wuce bukatarsa fa?”
“Idan ya taimaki wanda yake bukata, ya yi amfani da ni’imar da Allah ya ba shi yadda ya kamata.”
Na yi shiru, ina kallon hannuna.
“Dad…”
“Na'am Princess?”
“Ni ma idan na girma, zan taimaka mutane.”
Dad ya ɗan yi dariya.
“Hmmm yanzu ba ki girma ba, amma kin riga kin fara tsara abin da za ki yi idan kin girma.”
Na yi murmushi.
“Eh mana. Bana son wani ya kwanta da yunwa alhali ni ina da abinci mai yawa.”
Dad ya kalle ni na ɗan lokaci, murmushin fuskarsa ya ƙara faɗaɗa.
“Allah ya sa ki zama abin alfahari gare mu har abadah, Princess.”
“Ameen.”........
★ a hankali ta dafa Dad. “Tunanin me kake yi!?.” murmushi Dad ya yi.
“Tunanin irin yarinyar da Allah ya bani nake yi, mai zuciyar zinari.”
“Uhmmm Dad stop playing, da zuciyar zinari gare Ni, da na sa an ciro na siyar da shi.”
“Sai ki yi me da shi!?.” cewan Mom.
“Kuɗi zan mai da shi, sai na kyautar ga masu buƙata.” a tare suka yi dariya saboda sun san haka zan ce.
Na turo baki cikin shaƙwaɓa.
“Dad, insha Allah zan zama mai share wa mutane hawaye da yardan Allah, insha Allah da kuɗin da nake da shi, zan yi amfani wajen gyara mutane.......zan zama ƴar jarida domin jin koken mutane na zama mai share musu hawaye insha Allah.” na faɗa hakan cike da buri.
Mom da Dad suka zuba min ido cikin alfahari.
“Zan hau sama, mu kwana lafiya.” na sumbaci Dad a goshi, Mom kuma a kumatu, sannan na haure sama.
Iyayena suka kalla juna suka yi murmushi.
“Sakeenat kyauta ce daga Allah, Allah ya albarci rayuwarta.” Mom ta amsa da Ameen, tana isa kusa shi, ta rungume.
Tsakanin su babu wanda ya fi wani son Adeelah, haka kuma kowanne su yana da babban muradi akanta, lokaci kawai suke ji dan bayyanar ra'ayoyin kowa, ra'ayoyin da zai janyo musu babban matsala domin za'a samu BABBANCIN RA'AYI mai ruɗarwa.........✍️ End. > Har yanzu wasan muke yi jama'a
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
More likes, more comments = more motivation to keep typing and posting, Insha Allah. 🥲🫢❤️✍️