SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER 1⃣ 2

by @prettys01

> Tsakanin su babu wanda ya fi wani son Adeelah, haka kuma kowanne su yana da babban muradi akanta, lokaci kawai suke ji dan bayyanar ra'ayoyin kowa, ra'ayoyin da zai janyo musu babban matsala domin za'a samu BABBANCIN RA'AYI mai ruɗarwa...............

Da misalin ƙarfe 6:30 na safe, ni da Dad muka nufi wajen motsa jiki dake ta gefan lambu.

Wurin kuwa an tsara shi cikin tsari mai kyau, an shimfiɗa ɗan lawn mai laushi wanda ke kewaye da bishiyoyi da furanni iri-iri. A gefe guda kuma akwai kayan motsa jiki daban-daban—treadmill, exercise bike, wasu na'urorin ɗaga ƙarfi, da kuma wani fili da aka ware domin stretching da sauran motsa jiki.

Iskar safiya tana kaɗawa a hankali, ƙamshin ciyawa da furannin wajen ya cika sararin, yayin da hasken rana ke fara bayyana a bayan bishiyoyi.

Ni sanye nake da wasu sport wears riga da wando mai launin baƙi, wanda ya ƙara bayyana hasken fatata.

Na ɗaura gashina sama domin kada ya dame ni yayin motsa jikin, sai wani ɗan ƙwalli irin na ƴan da, na ɗaure kana nawa da shi.

Shima haka Dad, sai dai na shi kayan launin Ja ne.

“Princess, ki fara da stretching.” Dad ya faɗa yana ɗaga ƙarfe.

Na miƙe tsaye, na fara shimfiɗa hannaye da ƙafafu a hankali, na fara sai dai ban cika yin masu wahala ba, shima saboda Dad ne nake yi.

Bayan nan muka yi walking da saurin tafiya a cikin filin, daga baya muka yi wasu sauƙaƙan motsa jiki kamar squats da ɗaga gwiwa a hankali.

“Kar ki yi sauri, Princess. Ki yi a hankali.”

Na yi murmushi.

“To Dad.”

Muka ci gaba da motsa jikin cikin raha, muna hira lokaci-lokaci, har wajen ya fara cika da hasken safiyar ranar.

Mun ɗauki lokaci muna ci gaba da motsa jiki, har gumin ya fara jiƙa mana goshinmu. A lokacin ne muka hango Mom tana tafe zuwa gare mu, riƙe da mug guda biyu na coffee mai zafi.

Ta iso wajenmu ta miƙa mana.

“Come on, take a break.”

Na karɓa cikin murmushi.

“Okay, Mom. Thank you.”

“You’re welcome.”

Ta miƙa ɗayan mug ɗin ga Dad, shi ma ya karɓa yana murmushi.

Muka nufi kujerun da ke ƙarƙashin wata babbar bishiya, muka zauna a hankali. Iskar safiya tana kaɗawa, yayinda muke shan coffee ɗin a hankali bayan dogon motsa jikin.

Bayan mun ɗan yi shiru, Mom ta kalli Dad, sannan muka fara wata sabuwar hira................

╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️ *Sakeenat*

Sai da na yi kwana biyu a kwance saboda wannan dukan, a rana ta uku Mama ta tilasta min sai na fita zuwa shago, dan ba ƙaramin samun kuɗi take da shagon nan ba.

Ban wani gama samun sauƙin ba, haka na lallaɓa na shirya, na tafi shagon.

Ina zuwa na ɗaure na aje duk ciwon da nake ji, na fara aiki cikin sauri-sauri, duk wanda ya ga irin aikin da nake yi zai iya rantsewa ba zan iya ba, saboda yanayin jikina, amma tsaf nake yin komai.

Kamar kullum, customers suka fara shiga da fice, ana ta siyan abinci.

Yau dai yunwa nake ji sosai, dan haka na ɗau plate, na zuba doya da ƙwan dake mugun burgeni, na sanya guda shida na ci, sannan na zuba shinkafa shima na ci na ƙoshi, na bi da purewater, take jikina ya warware dama harda yunwa ke damuna.

Nan na ji ƙarfi ya zo min sosai, hakan yasa cikin ɗan lokaci na kammala komai, abincin ya ƙare saura plate guda wanda na aje ma wanann mahaukacin, amma bai zo ba.

Yau na tashi da wuri, dan lokacin ƙarfe 5:23pm, sai na kulle shagon, na fita ɗauke da plate ɗin nan mai abinci.

Nasan inda mahaukacin nan yake, yana ɗan nesa da shagona ne, gefan wani bola, a nan yake rayuwa, idan kwana biyu bai zo ba, Ni da kai na, nakan biya na kai mai.

Ina zuwa kusa bolan na toshe hancina saboda warin wajen, na fara shige wajen inda aka katange dan zubda bola.

Ina shiga na fara dubduba shi, can na hangesa tsakiyar bola, yana kallon sama, yayinda ƙafarsa ɗaya ke kan ɗaya.

Tausayi ya bani sosai, a raina ina yawan tambayar "Ina ƴan uwansa suke!? Da haukan aka haifeshi ko kuwa wani mugun abun aka mai!?.” irin tambayoyin da suke min yawo kenan, amma banda mai bani amsa, dan haka na buɗe baki da ƙyar na ce.

“Baba...... Baba.” haka nake kiransa, sai dai bai amsa ba.

Sai na fara ambaton sunan Allah ina hau kan bolan.

“Allah ka tsare Ni, Allah mai rahma, Allah ka kiyaye ni.” rintse ido na yi ganin a inda yake kwance.

Kwata, pampas ɗin yara, ga kayan miya duk ya ruɓe.

Na kama hannunsa ina fashewa da kukan tausayin halin da yake ciki.

Jin an riƙe mai hannu yasa ya buɗe ido ya sauke a kai na.

Take ya kau da kai.

Murmushi na yi, nasan yana fushi da Ni, saboda kwana biyu ban zo shago ba.

Ba tare da ƙyama ba, na kwantar da kaina kan jikinsa sannan na yi magana duk kuwa da nasan bai cika fahimta ba.

“Kwana biyu banda lafiya ne Baba, shi yasa ka ga ban fito ba, amma yanzu Alhamdulillah na samu sauƙi, kuma na kawo maka abinci, ina fatan za ka ci ko.” da mamaki sai na ga ya maƙe kafaɗa.

“Nace ka yakuri, ba zan sake ba kaji.” sai ya fara kokarin tashi, na riƙe karatunsa da sauri ina fara kuka. Second ɗaya.....biyu....uku

A hankali ya tsugunna, ya kai tafin hannunsa masu taushi amma da matuƙar dauɗa kan fuskata ya share min hawayen.

Take ya amsa abincin, ya fara ci, duk yawan abincin nan, bai ɓata lokaci ba, ya cinye tas.

Sai ya kalleni, na miƙe da sauri.

“Na manta ruwa, ina zuwa.” na juya da ɗan gudu-gudu jikina har rawa yake yi, na fita daga wajen.

Shagon dake kusa, na shiga, purewater biyu na siya, har zan wuce idanunsa sauka kan wata riga da aka daura kan fridge.

“Mai shago nawa ne wannan rigar!?.” mai shago ya kalla rigar.

“Na goge-goge ne.” ya faɗa yana latsa waya.

Kamar zan wuce, sai kuma nace

“Dan Allah ka siyar min kaji, ina so dan Allah.” na marairaice fuska, ina fatan ya amince.

Mai shagon ya kalleni da ƙyau na ɗan sekonni.

“Ɗauka na baki.” baki na washe kamar gonar audiga, na mai godiya kaman na ara baki, sannan na wuce.

Bayan na koma wajen, can na hangesa yana zaune gefen bolan, na ƙarasa da sauri.

Na bashi purewater biyu lokaci guda, ya amsa, dukka ya shanye.

A hankali yake sauke ajiyar zuciya.

Na jingina da bangon dake wajen na bashi jallabiyar nan mai launin shuɗi.

“Baba ka sanya wannan, yafi na jikinka ƙyau.” ba musu na cire mai rigar jikinsa, sannan na sanya mai wannan.

Na zauna ina kallonsa da ƙyau, shi kuwa tuni barci ya ɗauke, kansa na kan cinyata.

Sai da na fara jin an fara kiran sallan magrib, sannan na lallaɓa na gyara mai kwanciya, ya tashi na wuce.

Mashin na hau har ƙofar gida, ina sauka, napep na tsayawa a ƙofar gidan mu, Tawagar Shanawa suka fito da ganguna da kayan kiɗi.

Beasty ne a gaba, ya ɗaura wani zani a ƙugu sai rausaya yake yi.

Sai da na bari suka fara shiga gidan, sannan na bi bayansu.

Ina shiga na ji matan sun saki shewa na jin daɗi

“Ashe gobe akwai ƙara'i a unguwar nan.” cewan Aunty Duwais tana daga zaune.

Na matsa gefe ina jin Beauty (shima ɗan daudu ne) ya tafa hannu sannan ya ce.

“Aunties ku bari kawai, gobe har shaiɗan sai ya sara mana saboda ƙaraƙi da ƴaƴanta za mu yi.......”

Ihu suka ɗauka wasu harda rangaji.

“Fatan ku gayyato mana masu ƴan canji, ta yadda Malam Umaru sai tantance ba'a taɓo gidan GARKUWAR MATA a zauna lafiya.” Mama ta faɗa cike da alwashi, ta yi ƙwafa.

Malam Umaru a masallacin layin mu yake limancin, a jiya ya zo yana ma su Mama wa'azi akan abinda take yi bai dace ba, ya dinga kawo mata ayoyi yana fassarawa, shine bayan ya wuce, Mama ta ce gobe za'a tada shaidanu a layin nan, a kuma gayyato duk ɗan Allah ya shiryan da ake ji da shi a faɗin rigasa, al'amarin ya faranta ma kowa rai, kuma sunci burin za su yi rawar da zai girgiza malaman unguwar, haka kuma su Tawagar Shanawa wannan babban damace da za su ƙara yaɗa sana'arsu dan samun kasuwanci.

Kai na girgiza kawai, na yi ma Mama Barka da gida, sannan na shiga cikin ɗakinmu.

Hijabi na cire sai na ji Mama na kwaɗamin kira, na amsa ina ma da hijabi na.

A parlour na iske ta, na duegushe kusa ina miƙa mata kuɗin da suka kai dubu ashirin da takwas.

Bayan ta ƙirga ta ce.

“Gobe za'a ƙaro cefe, sai ki girka wanda ya fi na yau, ina son kuɗin ya dinga kai wa dubu hamsin.”

“To insha Allah.” sai ta miƙe ta fara tafiya.

Nasan idan bance mata na ci abinci ba, ba za ta gane ba, amma idan ban faɗa ba bazan iya barci ba, zan hana kaina sukuni gaba ɗaya.

“Mama.” na furta a hankali.

“Meye.” Mama ta faɗa tana haɗe fuska.

Na marairaice fuska.

“Mama dan Allah ki ya ƙuri kinji.” sai ta dawo ta zauna, ta zuba min ido.

“Me kika yi munafukai Allah ta'ala?.” hawaye suka cika min ido.

“Yunwa ya dame Ni a shago, shine na ci doya shida, da shinkafa ludayi biyu.” na faɗa cikin rauni.

“Sai kuma me!?.”

“Uhmmm sai na....siya ruwa na hamsin......”

“Ba akwai ruwa a shago ba.” ta tambaya.

“Akwai, sai da bar shagon na siyan ma wani.” Mama ta jinjina kai

“Wa kika ba!?.”

“Wani mahaukaci.” Mama ta ja tsaki

“Oh saboda bakinsan darajar kuɗi ba ko.......hmmmmm zan yi maganinki wallahi, kuma abinci tunda sata kika fara, kinci na dare, haka kuma idan kika sake cin ko da ɓallin doya ne, sai na miki dukan mutuwa, tashi ki bani waje, Shegiya, mai kama da Mayu, ga baƙi kamar kwaltar, jiki kamar saniya.....mtwwwssssss” da sauri na tashi ta nufa ɗaki da gudu.

Ina shiga na silale jikin ƙofa, na dafe kaina.

Bansan me yasa Mama take yawan zagi na ba, har ga Allah bana so, Nima mutum ce, ina son naga tana nuna min soyayya da ƙyauna kamar yadda take yi ma kowa, sai Ni gaba ɗaya haushina take ji, kaman ba ita ce ta haife Ni ba.

A hankali na taka har jikin jakkan kayana, na zuge zip, na ciro wannan fallen takarda na shiga maimaita kalaman Babana, wanda a duk lokacin da zan karanta sai na ji kaman da muryarsa yake karanta min.

Na ɗau dogon lokacin kafin na iya haɗa kalaman, duk kuwa ba yau ne na fara karantawa ba, amma suna min wahalar karantawa.

“*(Sakeenat Ƴata, na rubuta miki wannan saƙon nan dan gyara rayuwarki.......ina ji a jikinsa mutuwa zanyi, sai dai ina tsoron rayuwar da za ki faɗa, hakan yasa nake so kimin alƙawarin cewa........ko bana raye, ba za ki taɓa zaɓan rayuwar da mahaifiyar ki take fatan ki zama ba, ki kwarara zuciyar ki, ki yi kowani irin aikin wahala amma banda wannan rayuwar, ki tabbar kin cika min wannan alƙawarin.....Allah ya albarkaci rayuwarki, Nima zan je na iske mahaifiyar ki......A'isha........”*)

Na fahimci komai amma banda kalmar A'isha, kuma babu mai bani wannan amsar, dan haka na yi tunanin ko sunan Mamana guda biyu ne, A'isha da Zulaikha.

Ba zan manta lokacin da na fara karanta rubutun ba, shine na sauya, na kuma yi alkawarin ba zan yadda da abinda Mama take so ba, wannane farin komai

Nasha duka, na wahalu, na kwana babu ci babu sha, duk dan na yi watsi da maganar Baba, amma naƙi, haka na yi kunnin uwar shegu da komai.

Na azabtu sosai, har sai da na kusa mutuwa, sai Mama ta yafe min, amma sa sharaɗin kowani aiki mai kawo kuɗi zanyi duk wahalarsa, na amince da hakan, dan yafe min sau dubu.

Amrah ce ta shigo tana waya da saurayi, tana magana tana dariya.

Hakan yasa ya mai da fallen takarda sannan na juya na zuba mata ido.

Idan mutum yana neman sitira na alfarma, ɗinki na zamani, to ya zo gidan mu, style ne na tashin hankali ake yi a kaya.

Kamar dai rigar dake jikin Amrah, leshi ne mai tsadan gaske, amma an yi mata wani irin ɗinki, riga da skirt ne amma sai dai ace subuhanallah kawai, dan gaba ɗaya a matse yake a jikinta, ko ina ya fito tamkar a jikinta aka ɗinka.

“Li'ilafi ƙuraish.” Amrah ta faɗa tana tofar da miyau gefe..

Na yi murmushi ina mai kauda kaina daga kallonta gaba ɗaya................✍️ End

> Ku zabga min comment

╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

More likes, more comments = more motivation to keep typing and posting, Insha Allah. 🥲🫢❤️✍️