CHAPTER 1️⃣3
by @prettys01
> Na yi murmushi ina mai kauda kaina daga kallonta gaba ɗaya................
*Adeelah*
Na ɗauki wayar Dad wanda ta ci gaba da ringing.
Idona ya sauka kan screen ɗin wayar, inda sunan “A-One” ya bayyana.
Na ɗan yi murmushi, sannan na miƙa masa wayar.
Ya karɓa ba tare da ya ce komai ba, sannan ya nufi stairs.
Na bi shi da kallo har ya ɓace daga ganina.
Ban san waye wannan A-One ɗin ba, amma duk lokacin da sunansa ya bayyana a wayar Dad, nakan lura da yadda yake ɗaukar kiran da muhimmanci.
Sau da yawa nakan ji Dad yana kiransa da “Abubakar.” Wani lokacin kuma sai ya kira shi da “My One.”
Gaskiya, har wani lokaci nakan ji wani irin kishi saboda irin amincewa da kusancin da ke tsakaninsu.
Ban san me ya haɗa su ba, amma a fili zan iya cewa A-One ba mutum ne kawai a rayuwar Dad ba, ɗa ne kuma aboki.
Na taɓe baki ina sauya channel zuwa tashar labarai........................
★★★★★★★★★★★★
*JORDAN 🇯🇴*
★ Jordan wata ƙasa ce da ke cikin Gabashin Tsakiya, a tsakiyar duniyar Larabawa. Ƙasa ce mai tarihi, al'adu, birane masu tasowa da kuma wuraren da suka haɗa tsohon tarihi da rayuwar zamani.
Tana da fadin kusan 89,213 square kilometres, kuma tana da iyaka da Saudi Arabia daga kudu, Syria daga arewa, Iraq daga gabas, da yankin Falasɗinu daga yamma.
A kudancin ƙasar kuma akwai bakin teku a Gulf of Aqaba, wanda yake ba Jordan damar samun mashigar ruwa zuwa Red Sea.
A ƙarshen shekarar 2025, yawan mutanen Jordan ya kai kusan miliyan 11.9. Mafi yawansu Larabawa ne, tare da wasu ƙananan al'ummomi kamar Circassians, Chechens da Armenians.
Yawancin jama'ar ƙasar suna zaune ne a yankunan arewa da tsakiyar ƙasar, musamman a Amman, Zarqa da Irbid.
Jordan ba ta da jihohi kamar yadda Najeriya take da su. A maimakon haka, an raba ƙasar zuwa governorates guda goma sha biyu.
Su ne:
Amman, Zarqa, Irbid, Mafraq, Ajloun, Jerash, Madaba, Balqa, Karak, Tafileh, Ma'an da Aqaba.
AMMAN
Amman ita ce babban birnin Jordan, kuma ita ce zuciyar ƙasar ta fuskar gwamnati, kasuwanci, ilimi da rayuwar zamani.
Birnin yana kan tuddai da dama, kuma gine-ginensa suna shimfiɗe a kan waɗannan tuddai. A ciki akwai manyan tituna, wuraren kasuwanci, otal-otal, makarantu, jami'o'i, asibitoci da cibiyoyin gwamnati.
Har ila yau, Amman na ɗauke da tsoffin wuraren tarihi waɗanda ke tunatar da mutane cewa wannan birni ba na zamani kawai ba ne.
YANAYIN ƘASAR
Jordan ƙasa ce mai busasshen yanayi a mafi yawancin yankunanta. Akwai wuraren da yanayin ya fi karkata ga na Bahar Rum, musamman a yankunan tuddai, yayin da gabas da wasu sassan kudancin ƙasar suka fi zama hamada.
Ƙasar tana da manyan yankunan ƙasa guda uku: Jordan Valley, Mountain Heights Plateau da Badia, wato yankin hamadar gabas.
Kusan kashi uku bisa huɗu na ƙasar hamada ne, shi ya sa yanayin ƙasar ya bambanta sosai daga wani yanki zuwa wani.
Akwai kuma Dead Sea, wanda yake cikin Jordan Valley, kuma yana daga cikin wuraren da suka fi shahara a ƙasar.
AQABA
A kudancin Jordan akwai Aqaba, birnin da yake da muhimmiyar rawa saboda shi ne ke da tashar jirgin ruwa ta Jordan, kuma yana kallon Red Sea.
Saboda wannan matsayi, Aqaba ta kasance muhimmiyar cibiyar kasuwanci da yawon buɗe ido.
PETRA
Idan akwai wani wuri da ya sa sunan Jordan ya shahara a duniya, to yana daga cikin wuraren da ake samu a Petra.
Petra tsohon birni ne mai tarihi, wanda aka sassaka wasu daga cikin gine-ginensa cikin duwatsu. Yana cikin Ma'an Governorate, wanda kuma shi ne governorate mafi girma a faɗin ƙasa, duk da cewa yawan mutanensa ba shi da yawa idan aka kwatanta da Amman.
Larabci shi ne harshen hukuma na ƙasar, kuma yawancin jama'ar Jordan Musulmai ne, Akwai kuma Kiristoci da sauran ƙananan al'ummomi.
Rayuwar mutane tana haɗa al'adun Larabawa da rayuwar zamani. A birane kamar Amman, ana samun manyan cibiyoyin kasuwanci, makarantu, jami'o'i da kamfanoni, yayin da a wasu yankunan ake ci gaba da kiyaye tsoffin al'adu da tsarin rayuwar gargajiya.
MULKIN ƘASA
Jordan ba jamhuriya ba ce.
Masarauta ce.
Tsarin mulkinta shi ne hereditary parliamentary monarchy, wato masarautar da sarauta take gadon ta, tare da tsarin majalisa da gwamnati.
Kuma a nan ne labarinmu zai fara canza salo...
Domin a bayan waɗannan birane, tituna, kasuwanni da manyan gine-ginen Jordan...
Akwai wani gida da ya bambanta da sauran gidaje.
*Gidan Sarauta.*
Wurin da ba kowa ne yake iya shiga ba.
Wurin da dokokinsa suka bambanta.
Wurin da mutane ke magana cikin ladabi.
Wurin da suna ɗaya yake isa ya sa mutane su yi shiru........Sarki
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
*AMMAN, JORDAN 🇯🇴*
*FADAR MASARAUTAR AL-JAWHARA — ROYAL PALACE*
Ba wai kawai wani katafaren gida ba ne da aka kira da sunan fada. A'a, ginin kansa ya kasance kamar wata ƙaramar duniya ce da aka ware daga sauran ƙasar.
Daga babban ƙofar fadar zuwa cikin harabar gidan, akwai wata doguwar hanya wadda aka yi mata shimfiɗa da duwatsu masu sheƙi. A gefen hanyar kuwa, dogayen bishiyoyi sun yi jere cikin tsari, wasu furanni masu launi daban-daban suka yi ta kawata wajen, yayin da ma'aikatan lambu ke ta kai-komo suna kula da kowanne sashe.
Da ka ɗago ido, babban ginin fadar ne zai fara ɗaukar hankalinka.
Ginin ya yi matuƙar girma, hawa uku ne, an gina shi da duwatsu masu haske, manyan tagogi kuma suna jere a bangon gaba. A saman babban ƙofar shiga akwai tambarin masarautar Al-Jawhara, wanda aka sassaka shi da abu mai daraja.
A cikin fadar kuwa, komai yana da nasa wuri.
Da ka taka cikin babban zauren shiga, wani katafaren chandelier ya rataye daga saman rufin, yana haskaka marmarar ƙasan da take sheƙi kamar madubi. A gefen bangon akwai manyan hotunan tsoffin sarakunan Al-Jawhara, kowannensu yana kallon gaba cikin yanayin da ke nuna girman matsayinsa.
Ma'aikata suna ta kai-komo ba tare da hayaniya ba.
Wata yarinya tana wucewa ɗauke da tray ɗin shayi, wani kuma yana goge doguwar hanyar marmara, yayin da wasu mata biyu suke gyara furannin da aka ajiye a kan wani babban teburi na ado.
Daga babban zauren ake shiga babban parlour.
Da ka shiga parlour ɗin, sai ka ji kamar ka shiga wani wuri ne daban.
Babban ɗakin ya yi faɗi ƙwarai. Manyan kujeru masu laushi ne aka jera cikin tsari, wasu suna kallon juna, wasu kuma suna kallon babban television ɗin da aka saka cikin bangon. A tsakiyar ɗakin akwai wani babban coffee table na gilashi, ƙarƙashinsa kuma an shimfiɗa carpet mai kyau wanda ya rufe kusan rabin falon.
Manyan tagogin da suka kai har ƙasa suka mamaye bangon ɗaya, dogayen labule suka rufe su. Idan aka buɗe labulen, lambun fadar ne zai bayyana a waje cikin kyawunsa.
A wani gefe kuma akwai ƙaramin wurin zama na musamman, inda ake ajiye tea, coffee da sauran abubuwan sha idan Sarki ko Sarauniya suna karɓar baƙi.
Ba a taɓa barin parlour ɗin cikin rashin tsari ba.
Da zarar wani ya tashi daga kujera, ma'aikaci zai gyara wurin. Idan an gama shan shayi, wani zai zo ya kwashe kayan. Idan furanni suka fara yin rauni, za a sauya su.
Wannan ba abin mamaki ba ne.
Domin ma'aikata sun kasance da yawa a cikin wannan fada.
Wasu suna aiki a kitchen tun kafin wayewar gari, suna shirya abincin iyalan gidan sarauta. Wasu suna kula da ɗakuna, wasu suna wanki da guga, wasu suna kula da kayan sawa, yayin da wasu ke kula da lambuna da wuraren shakatawa.
Akwai kuma waɗanda aikinsu bai wuce su yi hidima ga iyalan gidan sarauta ba—su kawo musu abinci, shayi ko coffee, su shirya musu kaya, su raka baƙi zuwa inda ya dace, ko kuma su tabbatar da cewa duk abin da ake buƙata ya kasance a shirye kafin a nemi shi.
Ko da cikin manyan corridors ɗin fadar, ma'aikata suna ta zirga-zirga.
Wasu suna magana cikin raɗaɗi, wasu kuma suna yin sallama da zarar sun haɗu da wani daga cikin iyalan sarauta.
Babu wanda yake ɗaga murya.
Komai yana tafiya ne cikin ladabi da tsari.
Amma duk wannan katafaren gidan yana da wani sashe da ya fi sauran wuraren ɗaukar hankali.
Sashen da iyalan sarauta suke rayuwa.
A nan ne ɗakunan Sarki suke.
A nan ne Sarauniya take da nata ɓangaren.
A nan ne Yarima da Gimbiya suke da ɗakunansu.
Kuma a nan ne rayuwar gidan sarauta take gudana a bayan ƙofofin da ba kowa ne yake da damar buɗewa ba.
A waje, duniya tana ganin hasken sarautar Al-Jawhara.
Amma cikin fadar…
Akwai rayuwar da ba kowa ya san yadda take ba.
Iyalan gidan sarautar su 10 ne gaba ɗaya.
Sarki Rayyan Al-jawhari, yana da mata biyu.
Uwargidarsa ita ce Sarauniya Rania, mace mai baƙin hali da mugunta.
Tana da yara mata uku Gimbiya Jana Al-jawhari Gimbiya Reem Al-jawhari Gimbiya Noor Al-jawhari
Amaryarsa kuma Sarauniya Sarah, itama ba baya ba, dan duk shu'uman kansu ne.
Yaranta biyu itama duk mata.
Gimbiya Mira Al-jawhari Gimbiya Lina Al-jawhari
Sai ƙannan Sarauniya Rania, da suke zaune tare da su.
Zain da kuma Ayla.
Sune suke a bangare ɗaya, sai kuma sashen matan tsohon Sarki Kareem Al-jawhari wato Sarauniya Malikha, yaron ta ɗaya namiji, gagara kowa a masarautar, mai magana ɗaya baya na biyu, mai bada umarni da kaifafan idanunsa, sadauki kuma jarumi wato YARIMA LAITH (Lais-Zaki).
Yarima Laith yana ƙasar Amurka, inda yake gudanar aiki a wani babban kamfani na fasahar Robotics. Boston Dynamics kamfanin yana ƙera robots masu amfani da fasahar zamani, musamman waɗanda ake amfani da su wajen ayyuka daban-daban. Duk da yawan aikinsa a Amurka, yakan dawo Jordan lokaci zuwa lokaci amma baya kwana biyu yake juyawa.
Duk da kasancewarsa ɗan gidan sarauta, ya kasance mutum mai son dogaro da kansa, kuma hakan yasa da jajirce wajen neman na kansa.
Yarima Laith Al-Jawhari (Lais-Zaki) ba ya cikin fadar a wannan lokacin. Yana wata ƙasa amma hakan bai hana sunansa yawo ba. Daga cikin manyan iyalan Larabawa zuwa jami'an gwamnati, masu kasuwanci da matasan ƙasashen waje, mutane da yawa sun san sunansa.
Wasu sun san shi saboda kasancewarsa ɗan gidan sarautar Al-Jawhara, wasu saboda jarumtarsa, wasu kuma saboda girman nasararsa da sunan da ya yi ta fannin aikinsa. Ko ina ka je, idan aka ambaci.
“Laith Al-Jawhari,” mutane sun san wanda ake magana a kai. Shi kuwa, duk wannan shaharar ba ta dame shi ba.
★ Rayuwar cikin gidan Sarauta cike yake da hassada cin amana, da kullace-kullacen, makirci irin dai na gidan sarauta.......................
*GARKUWAR MATA*
Kamar yadda Mama ta faɗa, washegari gidan GARKUWAR MATA ya sauya.
Tun daga ƙofar gidan har zuwa cikin harabar, mutane suka fara cika wajen. Mata da samari ne suka yi cincirindo, wasu sun zo da wuri domin su samu wuri mai kyau, wasu kuma suna ƙara shigowa a hankali yayin da hayaniyar kiɗa da ganguna ke ƙara tashi.
Tawagar Shanawa kuwa sune cikin fili.
Ganguna suna kaɗawa ba kakkautawa, ana tafa hannu, ana shewa, yayin da wasu daga cikin matan da samarin suka fara rawa a tsakiyar jama'a, rawar rashin ɗa'a, samari ƴan Allah ya shirya sun cika wajen, wasu na musu liƙi, wasu kuma sai bushe-bushe suke yi.............✍️ End
> Idan Banga comments ba, gobe da jibi babu update.
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍 SAKEENAT ABDULLAHI CE 🤪✍️ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
More likes, more comments = more motivation to keep typing and posting, Insha Allah. 🥲🫢❤️✍️