CHAPTER 1️⃣ 4
by @prettys01
> Ganguna suna kaɗawa ba kakkautawa, ana tafa hannu, ana shewa, yayin da wasu daga cikin matan da samarin suka fara rawa a tsakiyar jama'a, rawar rashin ɗa'a, samari ƴan Allah ya shirya sun cika wajen, wasu na musu liƙi, wasu kuma sai bushe-bushe suke yi..........
Wasu mata suna rawa cikin annashuwa, wasu suna ta dariya da shewa, yayin da wasu samari ke ta nuna bajintar rawarsu, suna ƙoƙarin ganin wanda zai fi ɗaukar hankalin jama'a.
A gefe guda kuma, wasu daga cikin samarin sun tsaya suna taɗi, wasu suna busar hayaƙin sigari, yayin da wasu suka shagaltu da abubuwan da suka zo domin su more wannan dare.
Sautin kiɗan ya ƙara tashi.
GANG! GANG! GANG!
Nan take aka ji saki babbar shewa daga cikin taron.
“Ku ƙara mana sauti!”
“Yau fa sai mun girgiza GARKUWAR MATA sunan mu ya ƙara sama.!”
Mata suka fashe da dariya, wasu suka shiga tsakiyar filin suna rawa, yayin da jama'ar da ke kewaye da su suka fara tafawa.
Daga nesa, gidan ya zama kamar wata babbar cibiyar nishaɗi. Fitilu suna haskakawa, mutane suna ta zirga-zirga, ƙofar gidan kuma ta kasa samun sarari saboda yawan waɗanda suka taru.
Wasu daga cikin matan suna sanye da kayan ado na musamman, yayin da samarin ma suka yi kwalliya yadda kasan biki ko sallah.
Amma abin da ya fi jan hankali shi ne rawar da wasu ke yi—rawa mai tsananin zafi wadda ta saba da tarbiyyar da yawancin mutanen unguwar suka saba gani.
Inda suke yin waƙan *Jazaba* mata da maza sai baɗala suke da sunan rawa.
Da yake an shirya ma taron, harda masu kuɗi sun zo, alhazawa duk sun hakince a kujeru, kowa na baza ido yana zaɓar wacce ta mai.
Hajiya Mama kuwa, sai ɓarin kuɗi take yi a cikin filin.
A gefe guda, wasu dattawa da suka wuce ta hanyar suka tsaya suna kallon abin da ke faruwa, wasu suna girgiza kai kawai.
Sai wani ya ce cikin ƙaramar murya,
“Sufa wa'inna ba ruwansu da Allah, gaba ɗaya sun lalata mana unguwa, duba yadda yaranmu suke ta zuwa kallon wannan iskancin..”
Ɗayan ya amsa,
“Hmmm yanzu muyi magana, sai mun kwana a kanta, hmmm Allah ya kyauta ” suka wuce suna masu ƙyamar rayuwar da suke yi.
A gefe kuwa, hayaniyar ta ƙara ƙarfi
Ganguna...
Shewa...
Dariya...
Rawa...
Komai ya gauraye wuri guda.
Kuma a wannan dare, GARKUWAR MATA ta ƙara suna.
kiɗan da aka fara tun karfe huɗu na yamma, shine ya kai goma na dare, a hakan ma sauti sai ƙara ci gaba yake yi.
★ Tun bayan da na dawo na shige ɗaki ban fito ba sai yanzu, so nake na leƙa waje ko zan hangi Mama na tambaye ta abinci dan yunwa nake ji.
Na sanya takalmi, na fara tafiya a hankali, hijabi ne jikina kamar kullum dai.
Na buɗe kofa na fita ina kallon yadda wajen ya sake cika kaman rana.
Shanawa yana cikin filin, sai girgiza yake yi, na zaro ido ina kallon yadda yake rawa.
Jinjina kai na yi, sannan na nufa inda Mama take, sai da na ratsa cikin filin, na isa kusa da ita.
A hankali na tsugunna sannan na raɗa mata.
“Mama yunwa..... yunwa nake ji dan Allah.” na yi raurau da ido.
Tsaki ja sannan ta buɗe jakkar dake hannunta.
Ina tunanin bata lura da ƙyau ba, dubu uku ta zaro ta bani, na amsa ina mamaki.
“Mama kuɗin.......”
“Dalla wuce ciki, karki dame ni.” ai da sauri na bar wajen ina sake kallon kudin a hannuna.
Farin ciki kamar na zuba ruwa a ƙasa na sha dan daɗi.
Ai ban zarce ko ina ba sai shago, wayyo yau banza ta faɗi, kafin na isa shagon har na gama lissafin abubuwan da na ke so na siya.
Na yi sallama na shiga, na ji daɗin ganin yaron shagon ne ba Shamsu ba, na fara mai lissafin abubuwan da nake so.
Indomie, ƙwai, biscuit, sweet, chocolate, madara, burodi da sauran abubuwan da na gani, har sai da kuɗi na ya ƙare tas.
Na amsa ledar na koma gida.
Na dafa indomie, na soya ƙwai biyu, gefe guda ga tea na, na gyara zama, na cinye kayana tas, na yi ƙyatsa.
Daga nan na kunna tv tunda yau Ni kadai ce a ɗakin, na fara kallo ina cin biscuit, bayan na cinye leda ɗaya, na sha sweet, sai na tashi na aje sauran a can ƙasan akwati.
Yau dai na more duniya, sai da na gaji da kallon naje na kwanta wajen 11pm, amma har lokacin ana ta buga gangan shedain, na girgiza kai tare da musu addu'a, na kwanta dan nasan gobe akwai Ni da aiki sosai ga kuma shago....................
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
*Adeelah*
Da kaina na kai Dad filin jirgi na Kaduna International Airport. Tun kafin mu isa wurin, na fara ganin yadda harabar filin jirgin take cike da zirga-zirgar mutane, motoci da matafiya da ke ta faman shiga da fita.
Babban ginin filin jirgin ya bayyana a gabana cikin tsari, yayin da wasu daga cikin fasinjoji ke jan akwatunansu zuwa cikin tashar jirgin. Wasu kuma suna tsaye suna jiran lokacin tashinsu, yayin da jami'an filin jirgin ke gudanar da ayyukansu.
Na raka Dad har inda ya kamata, ina kallonsa yana shirin tafiya.
A lokacin da muka tsaya domin yin bankwana, sai wani irin yanayi na kewar juna ya lullube mu.
“Ki kula da kanki sosai,” Dad ya ce cikin murya mai sanyi.
Na gyada kai.
“Kaima ka kula da kanka, Dad.”
Mun sake kallon juna na ƴan daƙiƙu kafin daga bisani mu rabu.
Da ya juya ya fara tafiya, na tsaya ina kallonsa har sai da ya ɓace daga ganina.
Na sauke numfashi a hankali, kaman wanda zai yi shekara baya nan, alhalin kwana biyar kwai zai yi.
Daga nan na koma motata, na zauna a kujerar direba. Na ɗaura seat belt, na kunna motar sannan na nufi makaranta.
Bayan na isa, na fito daga mota, kamar kullum yau ma sanye nake da dogon hijabi, har baya iya hango launin shaddar dake jikina.
Na kulle mota na fara tafiya, cak na tsaya ganin an shiga gaba na, na ɗan ja da baya kaɗan, a hankali kuma na kalla matashin dake gabana.
Take ya daburce, ya fara kame-kame, Ni kuma na sake haɗa fuska, sannan na kewaye shi na wuce ina murmushi.
★Da na shiga cikin ajinmu, sai na ci karo da Safraz, Ball Star, zaune a kujera.
“Wayyo” shi na furta a hankali ina yalwanta fuskata da fara'a.
Sai dai yau kam, kayan da ya sanya sun ba ni mamaki.
Na saba ganinsa da ƙananun kaya ko kuma simple outfits da suke da mugun tsaɗa kuma na gayu. Amma yau ya canza salo gaba ɗaya.
Sanye yake da wata babbar riga mai faɗi, an yi mata ɗinki mai kyau da tsari, wadda ta sauko masa har zuwa kusa da guiwa. Launin kayan ya kasance mai kyau, tare da ɗan ƙaramin zane a gefen hannayen rigar.
A ƙasa kuma ya sanya wata babbar wando mai faɗi, irin wadda ba ta matse jiki, ɗinkin ta kuma ya yi daidai da rigar. A ƙafafunsa kuwa akwai sneakers masu kyau, yayin da agogon hannunsa ya ƙara masa kyan gani.
Na tsaya na ɗan kallonshi.
“Hmm…” na faɗa lokacin da idanuna suka sauka a kanshi, be yi aski ba, amma ya sanya hula.
Na sauke idona da sauri, kamar ban gan shi ba, sannan na nufi kujerata.
Amma kafin in zauna, sai ya ɗago kansa ya kalle ni.
Idanunsa suka haɗu da nawa.
Sai ya yi murmushi kaɗan.
“Good morning.”
Na amsa masa cikin sanyin murya,
“Morning.”
“To yau na yi shigar da kike so ko?!” ya tambaya, yana kallona da murmushi.
Na ɗaga kai a hankali.
“Ba laifi.”
Sai ya yi murmushi, kamar amsar ta yi masa daɗi.
“Thanks God! Your number, please.”
Ya miƙo wayarsa zuwa gare ni.
Ba yadda zan yi, don haka na karɓi wayar na saka masa number ɗina.
“Here.”
“Thanks.”
Ya karɓi wayarsa, ya duba number ɗin, sannan ya saka wayar cikin aljihunsa.
“Okay, see you later My Love”
“Okay.” kawai na iya faɗa.
Ya tashi ya nufi ƙofar class ɗin, ya bar ni zaune ina kallonsa na ɗan lokaci kafin na mayar da hankalina kan littafina.
A cikin class kuwa hayaniya ta fara ƙaruwa. Wasu suna ta magana, wasu suna dariya, wasu kuma suna ta faman duba wayoyinsu kafin a fara darasi.
“Guys, please keep quiet!” wata yar ajinmu ta faɗa.
“Who made you the class prefect?” wani ya amsa, sai aka fashe da dariya.
Na girgiza kai ina murmushi.
“Wallahi wannan class ɗin ba zai taɓa yin normal ba ashe kaf school ɗin nan, Kamar Safraz ball star yana da budurwa a jikin mu, ai abun murna ne” wata ta faɗa tana kallona.
Bance komai ba sai kai kawai na girgiza.
Bayan gama dukkan darasi, na biya gidan marayu, muka gaisa, sannan na nufi kasuwa.
Na shiga cikin kasuwar, hayaniyar ƴan kasuwa da masu saye ta cika ko’ina. Na nufi wajen mai kayan miya, na sayi carbage da alaiyahu da nake buƙata.
Bayan na gama siya, na ɗauki ledar hannuna na juya, na nufi inda na yi parking.
Na shiga motata, na aje kayan a gefe, sannan na zauna a kujerar direba. Na kunna motar, na ɗan kalli hanya kafin na fice daga wajen kasuwar.
Bayan na koma gida, sai na ba mai aiki kayan da na siyo.
“Ki yi min sinasir da miyar ganye.”
“Okay, Princess.”
Na nufi sama, amma ban kai ga shiga part ɗina ba sai wayata ta fara ringing.
Na duba screen ɗin, Mom ce.
Na ɗauka.
“Hello, Mom.”
“Hello, my daughter. Kin dawo gida?”
“Eh Mom, yanzu na shigo.”
“Alhamdulillah. Yaya makarantar?”
“Alhamdulillah, komai lafiya.”
“Yau zan yi dare a asibiti. Ina so a aiko min da abinci, don ba zan iya cin abincin nan na asibiti ba.”
Na yi murmushi.
“Me kike so? Ni da kaina zan kawo miki.”
“Uhmm… tuwan shinkafa nake so.”
“Okay, an gama. Da kaina zan miki yanzu nan.”
“thank You my only daughter.”
“Mom Ki kula da kanki.”
“Ke ma ki kula da kanki. Sai kin zo”
“To Mom, I love you.”
Muka yi sallama.
Duk da gajiyar da nake ji, ina haurawa sama na watsa ruwa kawai, na sauya kaya, sannan na nufi kitchen.
Na shiga na tarar da masu aiki suna ta faman shirye-shiryen abincin. Na shiga cikinsu, na fara taimakawa wajen shirya abincin da zan kai wa Mom asibiti.
Gajiyar jikina tana nan, amma na yi haƙuri. Abu ɗaya kawai nake tunani—Mom za ta yi dare a asibiti, kuma ina so ta samu abincin da take so.
Na gama shirya abincin, na tattara komai cikin kwantena masu kyau, sannan na shirya kaina.
Na sanya riga da wando falazo, sannan na ɗora jalbab a jikina. Bayan na tabbatar komai yana tare da ni, na ɗauki jakata na nufi motata.
Na shiga, na kunna ta sannan na nufi asibitin da Mom ke aiki.
Asibitin mai suna Specialist Hospital ya kasance babban asibiti ne mai kyau, an gina shi cikin tsari na zamani.
Babban ƙofar shiga tana da faɗi, akwai reception a gaba, yayin da sashen Emergency, wards da sauran sassan asibitin suke a cikin babban ginin. Harabar asibitin tana da ƙyau sosai, kuma motoci suna ta shiga da fita.
Da na isa, na yi parking a cikin harabar asibitin.
Ina kashe engine ɗin, sai na sauke numfashi.
A zuciyata na yi addu'a.
“Ya Allah, kada ka haɗa ni da Doctor Ahmad.”
Ban san dalilin da ya sa bana son haɗuwa da shi ba, amma abin da kawai nake so shi ne in kai wa Mom abincinta ba tare da na ci karo da shi ba.
Na buɗe ƙofar motar na fito.
Sai dai…
Na yi rashin sa'a.
Da na ɗago idona, sai suka sauka kai tsaye a kansa.
Doctor Ahmad.
Yana tsaye a ɗan nesa, sanye da kayan aikin likitanci, yana magana da wani ma'aikacin asibitin, amma idanunsa na cikin nawa..
Na tsaya cak.
“Oh no…” ya nufo Ni a natse yana da sakar min murmushi..............✍️ End
> 🥰🥰🥰🥰🥰 ╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*