CHAPTER 1️⃣ 5
by @prettys01
> “Oh no…” ya nufo Ni a natse yana da sakar min murmushi.............
“Assalamu alaikum, My Beautiful Baby Adeelah.” ya faɗa yana murmushi.
“Wa alaikumus salam,” na amsa a taƙaice, ina ƙoƙarin kau da fuskata daga kallonsa.
Ya tsaya gabana yana kallona kamar ya haɗiye Ni haka yake ji.
“Kin san na yi kewarki kuwa? Aiki ya riƙeni kwana biyu, da na zo ganinki........sai gashi kin zo da kanki, ashe kin damu da Ni haka.”
Na ɗan zaro ido jin sharrin da zai yi min.
“Doctor Ahmad, ya isa haka. Sauri nake yi.”
Fuskarsa ta ɗan sauya, kamar maganata ba ta masa daɗi ba.
“Ai da baki zo ba, da kaina zan zo gida na same ki har gida yau.”
Na ɗan kalle shi.
“Hmmm… to gani ai.”
Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin sanyin murya,
“I love you.”
Na sauke idona ƙasa, ban ce komai ba.
“Ngd,” na amsa a taƙaice, sannan na fara tafiya.
Amma kafin in yi nisa, sai ya karɓi basket ɗin da ke hannuna.
“Bari na ɗauka.”
“Ba sai ka ɗauka ba.”
“A'a Beauty.”
Na yi shiru. Da yake ya riga ya karɓa, sai na bar shi da basket ɗin, sannan na ci gaba da tafiya.
A zuciyata kuwa tambaya ɗaya ce kawai take yawo.
Me yasa duk lokacin da nake ƙoƙarin guje masa, sai cusa min kai, alhalin yana da mata.
“Kai wai baka shakkar a ganni tare da kai, a faɗa wa matarka....Ni bana son rigima, shi yasa nake ta kauce maka, amma ka kasa ganewa.”
“Ai ba haram bane, karki manta huɗu aka ce muyi idan muna da hali, sai dai Ni biyu kun isa, daga ke babu ƙari.” na girgiza kai kawai.
Surutu ya dinga zuba min har muka isa office din Mom, ya ban basket ɗin sannan ya ce.
“Dan Allah ko kallon soyayya ki min mana, kinji.......” bansan na yi murmushi ba, na mai kallo mai cike da kasheɗi, ashe a wajensa kallon soyayya ne, har da wani dafe zuciya.
Na girgiza kai, sannan na yi knocking ƙofar office ɗin Mom.
“Yes coming.” sai na tura ƙofa na shiga da sallama..............
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
*Abuja*
A cikin wani katafaren ɗakin meeting, Barrister Nura Sale yana zaune a saman babban teburin taro, gabansa cike da takardu da wasu files.
Ya ɗauki ɗaya daga cikin takardun, yana nazarinta cikin nutsuwa, yayin da wasu daga cikin abokan aikinsa ke zaune a gefen teburin, suna tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi aikin da zasu gabatar a washegari.
Ɗakin yana da girma sosai, dan zai iya cin mutane 30, Babban teburin an yi shi da itacen mahogany mai sheƙi, kujerun da ke kewaye da shi kuma masu kyau ne. A gefe guda akwai babban allo da ake amfani da shi wajen gabatar da bayanan aiki, yayin da hasken fitilun ɗakin ya haskaka komai cikin tsari.
Take...
Click!
Aka buɗe ƙofar tare da sallama cikin wani dakakkiyar murya.
Kafin Muryar ta isa kunnuwansu, daddaɗan ƙamshin turarensa ya isa ƙofofin hancin su.
Barrister Nura ya ɗago kansa.
Murmushi ya bayyana a fuskarsa.
Idanunsa suka sauka kan wani ƙyaƙƙyawan matashi da ya shigo cikin nutsuwa.
A-One.
Matashin mai kimanin shekara ashirin da bakwai.
Namiji ne mai cikakkiyar haiba da kwarjini. Tsayinsa ya yi daidai, kafadunsa suna da faɗi, fuskarsa cike da natsuwa, yayin da kallonsa yake ɗauke da wani irin nutsuwa da ke nuna mutum mai iya sarrafa kansa a kowane yanayi.
Sanye yake da riga da wando na yadin Menless, wadda aka yi da wani irin ɗinki na zamani mai kyau. Rigar ta sauko masa har ƙasa da guiwa, an yi mata ɗan ƙawanya a wajen wuya da hannayen riga, ba tare da an cika ta da ado ba.
Takalman da ke ƙafafunsa sun hau kayan jikin nasa sosai.
Duk da irin shigar da yake yi, akwai wani abu a tattare da shi da ya bambanta shi da sauran mutane.
Natsuwa.
Ita ce ta fi bayyana a tare da shi.
Barrister Nura ya ajiye takardar da ke hannunsa.
Nan take ya miƙe.
A-One ya ƙaraso kusa da shi, yana sakin murmushi wanda ya kafa bayyana ƙyawun fuskarsa.
Barrister Nura ya rungume shi cike da farin cikin.
“You’re welcome, A-One.”
A-One ya yi murmushi, ya amsa cikin girmamawa.
“Thank you, Sir.”
Barrister Nura ya ɗan ja da baya yana kallonsa.
“Ina fatan komai an kammala”
“Eh, Sir.”
“An gama aikin?”
A-One ya ɗan yi shiru, kafin ya gyada kai.
“An gama.”
Barrister Nura ya murmusa.
“Good.”
Daga nan ya nuna masa kujera.
“Zauna. Muna kan wani meeting ne.”
A-One ya ja kujera ya zauna cikin nutsuwa, sannan ya gaishe da mutanen da suke waje, duk suka amsa.
Ɗaya daga cikin mutanen da ke cikin meeting ɗin ya kalle shi.
“Long time, A-One.”
A-One ya ɗaga kai.
“Long time.”
Barrister Nura ya koma kan kujerarsa, ya ɗauki wani file dake gabansa.
“Yanzu da ka dawo, akwai wasu abubuwa da za mu tattauna. Amma kafin nan, ka huta.”
A-One ya girgiza kai a hankali.
“I'm fine, Sir.”
Barrister Nura ya kalle shi na ɗan lokaci.
“Na san ka. Ba ka taɓa cewa ka gaji ba.”
Ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskar A-One.
“Saboda ba na gajiya da aiki.”
Wasu daga cikin mutanen suka yi murmushi.
Barrister Nura kuwa ya girgiza kai yana murmushi.
“Shi ya sa ake kiranka A-One.”
A-One bai ce komai ba.
Ya ɗauki file ɗin da aka ajiye gabansa, ya buɗe shi cikin nutsuwa.
A cikin ɗan lokaci kaɗan, yanayin ɗakin ya sake komawa cikin natsuwa.
Meeting ɗin ya ci gaba.
Amma kasancewar A-One a cikin ɗakin ya canza yanayin gaba ɗaya.
Domin duk wanda ya san shi ya san abu ɗaya—
A-One ba irin mutanen da suke magana da yawa ba ne.
A hukumar 🛡️ NATIONAL INTELLIGENCE BUREAU — NIB yake aiki
NIB ita ce wata babbar hukumar leƙen asiri da tattara bayanan sirri a ƙasa.
Aikinsu ba wai kama mutane a titi ba ne kamar Police; aikinsu shi ne bincike, tattara bayanan sirri, gano barazana da kuma bibiyar wasu al'amura cikin ɓoye, wanda suke dan ƙama wa'inda suka basu aikin.
Shi A-one wato Abubakar, yana ma barristers aiki ne, wanda yake musu bincike na sirri, daya gaba yake basu, su kuma ana shiga kotu, suke bayyana gaba ɗaya asirin mutum, hakan ke sa suke yin nasara sosai.
Barrister Nura bashi da amintacce wajen aiki kamar A-one, ya yadda da shi fiye da misali, sannan ba kallo matashi kawai yake mai ba, yana mai kallon Ɗa ne gaba ɗaya.
Matsayin matsahin a hukuman Senior Field Agent — National Intelligence Bureau (NIB)................
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
*FADAR MASARAUTAR AL-JAWHARA — AMMAN, JORDAN 🇯🇴*
A cikin babban Majalisar Masarautar Al-Jawhara, aka taru domin gudanar da wata muhimmiyar tattaunawa.
Babban ɗakin majalisar ya kasance cike da mutanen da ke da matsayi a masarautar. An yi wa bangon ɗakin ado da manyan zane-zanen tsoffin sarakunan Al-Jawhara, yayin da fitilu masu sheƙi suka haskaka wajen cikin wani irin salo.
A tsakiyar ɗakin kuwa akwai kujerar mulki ta Sarki.
A can ne Sarki Rayyan Al-Jawhari yake zaune.
Sanye yake da wata babbar thobe na alfarma, wadda aka yi mata ɗinki na musamman, a kansa kuma akwai keffiyeh fari da ja, an daure ta da agal baƙi. A hannunsa akwai misbaha da yake juyawa a hankali yayin da yake sauraron mutanen da ke gabansa.
Fuskarsa ba ta nuna fara'a.
Kallo ɗaya kawai daga gare shi ya isa ya sa ɗakin ya yi shiru, tsabar kwarjini da haiba.
Gashi ɗan dattijo mai cikar ƙyau, Fari ne tas, kunsan sai dai larabawa, akwai ƙyau, balle duk alhalin Al-jawhari, suna da wani ƙyau ne na musamman.
A gabansa akwai manyan masu ruwa da tsaki a masarautar—manyan jami'an gwamnati, masu ba da shawara, shugabannin wasu sassa da kuma mutanen da ke da alhakin kula da harkokin masarautar.
Babu wanda yake magana sai wanda aka ba dama.
A hankali, wani dattijo daga cikin majalisar ya miƙe.
Ya gyara bisht ɗin da yake sanye da shi, sannan ya tsaya cikin girmamawa yana fuskantar Sarki Rayyan.
Ya sunkuyar da kansa kaɗan.
“Assalamu alaikum, Ya Jalaalatu-l-Malik.”
“Wa alaikumus salam.”
Dattijon ya ɗan ja numfashi. Take kuma ya fara jero mai kirari irin na sarauta cikin natsuwa da kalaman hikima.
“Allah ya ja zamani Lafiya Barɗen Al-Jawhari, Lafiya Ɗab Suda da Sara Salati, Lafiya Sha Sabo, Lafiya Mai Horon Abi Allah, Lafiya Kiƙanshe Kafiri da Maƙi Sallah, Lafiya Hadari Malhon Duniya, Lafiya Kibiya Saƙon Nesa..Ya Malik Rayyan Al-Jawhari, mai gadon sarautar da kakanni suka bari, mai kare martabar Al-Jawhara, garkuwar masarautar da ke tsaye kan adalci da tsari…....haske mai shaƙi, bawan Allah mai kyakkyawar zuciya........Sarki mai halin kwarai........”
Mutanen da ke zaune suka yi shiru suna sauraronsa
Ya ci gaba.
“Allah Ya ƙara maka lafiya, hikima da ƙarfin tafiyar wannan masarauta.”
Sarki Rayyan bai ce komai ba.
Sai dai idanunsa suka tsaya a kansa.
Dattijon ya buɗe wani babban file da ke hannunsa.
“Ya Mai Martaba, yau mun taru ne domin tattauna wasu muhimman al'amura da suka shafi masarautarmu.”
Ya ɗaga takardar farko.
“Na farko, tsaron masarautar da iyakokin ƙasar. Mun samu wasu rahotanni da ke buƙatar kulawa ta musamman.”
Ya juya zuwa takarda ta biyu.
“Na biyu, harkokin tattalin arziki da kasuwanci, musamman yadda za mu ƙara ƙarfafa hulɗar kasuwanci da sauran ƙasashen larabawa.”
Sai ya ɗaga kai ya kalli Sarki.
“Na uku, al'amuran jama'a da ci gaban birane, musamman shirye-shiryen da masarautar ke da su domin inganta rayuwar jama'a.”
Ya ɗan dakata, domin jin abinda Sarki Rayyan Al-jawhari zai ce.
Sai dai bai yi magana ba saboda izza, ya ɗai daga hannu da ƙyar, sannan ya ɗau dogon lokaci tukun ya yi maganar ƙasa-ƙasa.
Wanda ke kusa da sarki ya buɗe baki da ƙarfi yace.
“Sarki mai zuciyar zinari yace.......” mutane suka sake yin shiru.
“Kowa ya faɗa ra'ayinsa akan ci gaban ƙasar mu............” ba tare da ɓata lokaci ba, ɗaya bayan ɗaya aka fara bada shawarori akan inganta rayuwar mutane.
Sarki Rayyan yake yana jin, sai bayan da aka gama, sannan ya sake magana, wannan mai Muryar Sarki na biyu ya ce.
“Sarki mai zuciyar zinari ya tsaiɗa matsaya, dan haka ya ku shirya, ya sallame ku.” take aka shiga jera mai kirari, kuma ɗaya bayan ɗaya aka fara tafiya.
Fada ya rage Sarki Rayyan Al-jawhari da muƙarrabansa ne suka rage.................✍️ End
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍 SAKEENAT ABDULLAHI CE 🤪✍️ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*