CHAPTER 1️⃣ 6
by @prettys01
> Fada ya rage Sarki Rayyan Al-jawhari da muƙarrabansa ne suka rage..........
*FADAR MASARAUTAR AL-JAWHARA — SASHEN SARAUNIYA RANIA*
A wani katafaren ɗaki dake cikin sashen Sarauniya Rania, komai ya kasance cikin alfarma mai daraja.
Sarauniyar tana kwance a kan wata babbar kujera mai laushi, an shimfiɗa mata kayan ado masu tsada a gefenta. Sanye take da wata doguwar rigar thobe ta alfarma wadda aka yi mata ɗinki na musamman da kayan ado masu sheƙi. A wuyanta akwai sarƙa mai daraja, yayin da manyan zobba suka ƙawata yatsun hannunta.
Fara ce ƙal, kuma tana ɗan jiki, sai dai fuskantar a haɗe yake, kamar kullum, ba ta cika dariya ba, sai na mugunta, tana murmushi to tabbar ansan wani abun take shirin aikatawa.
Biyu daga cikin bayinta suna zaune a kusa da ita, ɗaya tana yi mata tausa a kafaɗa, ɗayar kuma tana koran mata ƙuda, da wani mafici.
Sarauniya Rania ta lumshe idanunta, tana jin daɗin massaging ɗin da ake mata akan fararen ƙafafunta.
A hankali wata mata ta shigo, cikin uniform ɗin bayin gidan.
Ita ce amintacciyar jakadiyar Sarauniya Rania, wadda take daga cikin mutanen da suka fi kusa da ita, sunanta Jakadiya Shatu.
Da ta iso gabanta, nan take ta durƙusa har ƙasa cikin girmamawa.
“Ya Sarauniya Rania…Lafiya Uwar Masarauta, Lafiya Furen Fada, Lafiya Mai Rawanin Daraja, Lafiya Garkuwar Gida, Lafiya Tauraruwar Masarauta, Lafiya Mai Zoben Zinariya, Lafiya Uwar Sarakuna, Lafiya Madubin Fada. Uwargida mai ɗaukaka, mai girman matsayi, ”
Sarauniya Rania ta buɗe idanunta a hankali.
Ba tare da ta motsa daga kujerarta ba, ta ɗaga hannu.
Jakadiyar ta sunkuyar da kanta.
“Na gode, Ya Sarauniya.”
Ta ɗan ja numfashi, sannan ta ce cikin girmamawa:
“Sarauniya Rania, uwar sarauta, mai girman hali da ɗaukakar matsayi, wadda ake......…” hannu Sarauniya Rania ta ɗaga mata.
Cikin isa, izza da ƙasaita tace.
“Je ki kai tsaye ga maganarki.” Jakadiya Shatu ta jinjina kai.
“Na zo ne da wani babban labari.”
Nan take Sarauniya Rania ta gyara zamanta.
“Ina jinki Jakadiya.”
Jakadiyar Shatu ta matsa kusa kaɗan, amma ta sunkuya cikin girmamawa.
“Ya Sarauniya… yanzu na samu labarin da zafi-zafinsa, daga bakin Amintacciyar Hadimar Sarauniya Sarah...........cewa Sarauniya Sarah tana da juna biyu.”
Wani ɗan zabura Sarauniya Rania ta yi.
“Juna biyu?”
“Eh, Ya Sarauniya. An kai ta asibiti, an yi mata gwaje-gwaje, kuma likitoci sun tabbatar da hakan.”
Jakadiya Shatu ta ci gaba cikin ƙaramar murya cikin raɗa-raɗa
“Amma abin da nake tsoro shi ne…”
Ta haɗiye yawu.
“Sarainiya tsorona Allah, tsoro na kar ya zama ɗa Namiji..........gashi......”
Nan take Sarauniya Rania ta ɗaga hannu da sauri.
“Ya isa!”
Jakadiya Shatu ta yi shiru.
Dukan ɗakin ya yi tsit.
Sarauniya Rania ta kalli bayin biyun da jinkinsu ya fara tsawa saboda yanayin ta.
“Ku fita.”
Nan take bayin suka sunkuyar da kai suka bar ɗakin da sauri
Sarauniya Rania ta koma kan kujerarta.
Fuskarta ta sauya.
Ta kalla jakadiya Shatu
“Ki sake maimaita abinda kika ce.....…”
Jakadiya Shatu ta ɗago kai a hankali.
“Ya Sarauniya?”
Rania ta karkatar da kanta kaɗan.
“Kin ce Sarah tana da ciki?”
“Eh, Ya Sarauniya.”
Rania ta yi shiru na wasu daƙiƙu.
Daga nan ta yi murmushi mai cike da ma'ana
“Idan ɗan namiji ne…”
Ta dakata.
Idanunta suka yi lumshe ta buɗe su.
“...to, wannan ba ƙaramin labari ba ne......Rikicin duniya, da mai rai ake yi.” ta numfasa.
“Sabon salo, gemu a kafaɗa, sarauniya Sarah da ciki............ina bazan taɓa yarda hakan ya faru ba!”
Muryar Sarauniya Rania ta fito da ƙarfi, cike da fushi.
Ta kalli Jakadiya Shatu da ke durƙushe a gabanta.
“Tashi ki tafi.”
Jakadiya Shatu ta sunkuyar da kanta har ƙasa.
“Godiya nake, Ya Sarauniya. Allah Ya ƙara miki girma da daraja.”
Da haka ta miƙe a hankali, ta juya ta fita daga ɗakin.
Sarauniya Rania ta zauna shiru na ƴan daƙiƙu.
Sai ta miƙe da sauri.
Fuskarta cike da ɓacin rai, ta fara taka zuwa ƙofar ɗakinta.
Amma kafin ta isa, sai wani murmushi ya bayyana a fuskarta.
Murmushi mai ɗauke da wani abu da ba a iya karantawa.
Ta gyara mayafinta, ta ɗago kai cikin izza, sannan ta buɗe ƙofar.
Tana fito, bayin da ke tsaye a corridor suka yi saurin bin bayanta.
Wasu daga cikin masu gadin sashen suka tsaya suka sunkuyar da kai yayin da ta wuce.
Sarauniya Rania ba ta ce komai ba.
Ta ci gaba da tafiya cikin natsuwa, dogayen kayan jikinta suna motsawa a hankali yayin da bayin suka bi ta a baya.
Ba ta tsaya ko ina ba.
Sai ta nufa sashen Sarauniya Sarah.
Da ta isa babban ƙofar sashen, masu gadin suka buɗe mata ƙofa nan take.
Sarauniya Rania ta tsaya na ɗan lokaci.
Ta gyara fuskarta, ta maye gurbin murmushin da wani yanayi na nutsuwa.
Sai ta shiga.
Rabon da su haɗu da Sarauniya Sarah tun ranar juma'a, babu mai shiga sashen kowa, sai da babban dalili, amma haka yau ta aje duk wani izzatarta ta nufeta domin ta tabbar da abinda ta ji, duk kuwa da tana da tabbacin haka ne....................
*Sakeenat*
Ina aikin gida ina tsintar labarin sheƙe ayar da aka yi jiya da daddare, ashe basu suka tashi ba sai karfe biyu na dare, ta fashe musu jiyan nan sosai, an zubda galan-galan, kuɗi sun yi kuka.
Zauna nake kan dutse dake gefen Pampo, ina wanke kayan Mama da nawa, da yake kayan da yawa, hijabin jikina kusan rabi ta gaba ya jiƙe, amma haka na nannɗe na zauna sosai, ina aikin ina jin hirar wasu ƴam mata da suke zaune daga can gefe, ɗaya a cikinsu ce bata nan a daren jiyan, shine suke bata labari.
Har na gama wankin na shanya, suna hirar abu ɗaya, ina gamawa na koma ɗaki dan na yi wanka.
Sai dai Amrah ta shiga bayin, kuma tana sane lokacin fitana ya yi, haka na zauna gefen katifata ina jiran ta fito, sai dai banji alamun ta fara wankan da ta shiga yi ba, dan babu ƙarar ruwa.
Na matsa kusa da ƙofar.
“Amrah dan Allah ki fito, kar na yi latti zuwa shago, zan yi dare sosai.” idan bango Ya motsa to an motsa a ciki, sai ka sautin motsinta da nake ɗan ji kaɗan. Na koma na zauna, na zuba ma ƙofar bayin ido.
Sau huɗu ina buka mata ƙofa akan ta buɗe, sai ana karshen ne ma ta yi magana.
“Ke dalla karki dame ni.” ta faɗa cike da ƙuɓula.
Tsaki na ja, na ɗau sosan wanka na, na nufa bayin tsakar gida, sai dai gabana faɗi yake, saboda bayikan tsoro suke bani, tun wani lokaci dana taɓa shiga, wani ƙato ya biyo ni, tun daga lokacin ban sake shiga ba, wankewa da ya zama min aikin yi kullum shike kaini wajen.
Yanzu safiya ce ba kowa ne ya tashi ba, dan haka na isa lungu bayin, na shiga na can ƙarshe.
Sai da na tabbar na kulle da sakata, na cire hijabin jikina, na sagale sannan na kunna Pampo ruwa ya fara taruwa cikin bucket ɗin mai sanyi.
Da ruwan sanyi nake wanka, tun ina ƙarama, duk sanyi ko zafi, haka nake yi, sai gashi Allah yana tsare Ni, ko mura bancika yi ba.
Bayan na gama wankan, na ɗaura zanina da ƙyau a ƙirji, na zubula hijabi.
Ban kawo komai a cikin rai na ba, na buɗe ƙofar, sannan na juya da nufin ɗaukar sosan da na maƙala jikin ƙusa, sai dai mai...... Da sauri na zaro ido, sai dai kafin na yi wani motsi na ji an toshe min baki tare da matse min hannaye, aka tura Ni jikin bango har sai da kaina ya bugu, na fara kokarin kwatar kai na amma ina an sa min ƙarfi, dan an matseni ne ƙam.
Take gabana ya faɗi, hawaye suka fara zubar daga cikin idanuna jin yadda hannun wani gardi ya fara shafar jikina a hankali...........✍️ End
> 😢😢😢😢😢
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 8126151523
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*