CHAPTER 1️⃣7
by @prettys01
> Take gabana ya faɗi, hawaye suka fara zubar daga cikin idanuna jin yadda hannun wani gardi ya fara shafar jikina a hankali..............
Ban tsinke da labarin ba sai da na ji hannu mutun a cikina an fara yawo da shi, take na yi wani kukan kura, na gatsa ma hannunsa cizo, ban ɗau lokaci ba, da taimakon Allah, na ƙwace matsan da ya min sannan na kurma uban ihu.
Ba wani haske sosai a bayin hakan yasa namijin ya juya zai gudu, na ko damƙo ƙafarsa ina ƙara fasa wani uban ihun.
Hamdala na yi jin mutane sun cika bakin ƙofar bayin, sai a lokacin na kalla matsahin dake tsaye jikin ya yi sanyi.
Take na zaro ido, ganin Saurayin Amrah, Bosho, yaron da Amrah ke masifar so kamar ta yi hauka, yaron da za ta iya bada rayuwarta akansa.
Bangama shan mamaki ba, na ji ya ɗauke Ni da wani lafiyayyen mari, ya yi ƙwafa sannan cikin raɗa ya ce.
“Zan shayar da ke giyan mamaki yau.” na kalla cikin idanunsa da sauri.
“Waye a ciki.....ku buɗe.......Su waye.......” muryoyin mata suka fara tashi.
Bansan mai ya taka ba, ya sanya hannu ya buɗe ƙofar, kafin mata su hau salati, ya tura Ni waje, na faɗi a ƙasa.
Belt ya zaro daga ƙugunsa cikin ɓacin rai, kafin na ankara ya fara zuba min bulalar yana cewa.
“Ni za ki yi ma sharri.......Ni za ki wulaƙanta.......Ni za ki zubar ma mutumci gaban ƴan gidan nan......Ni za ki tozarta gaban Budurwata.” sai mata suka fara tafa hannu suna salati tare da mamaki.
Ni kuwa babu wanda ya bani daman magana, haka ya dinga zuba min bulala cikin fushin da ɓacin ran rashin sa'ar da be yi a kai na ba, dan ya jima yana target ɗina, kuma shi ya sanya Amrah shiga bayi lokacin, da cewan yana so ta yi mai videon jikinta, shine ta shiga, shi kuma ya zauna a tsakar gida, yana dakona.
Amrah dake tsaye gefenmu, ta fashe da kukan baƙin ciki, take ta yo kaina, mutane suka ja ta baya, ta fara fizge-fizge tana son ta iso gabana ta duke Ni.
Shi kansa Bosho da ƙyar aka ja shi baya, sai wuci yake yi kaman mahaukacin zaki.
Ni kuwa kuka kawai nake yi, ina mai jin tsanar kowa na wajen, ai ya kamata su fara tambayar ba'asi amma babu wanda ya yi hakan.
Garkuwar mata ta fito daga ɗaki, dan ko tashi ba ta yi ba. Doguwar rigar barci ne a jikinta mai laushi, wanda ya sauka har kusan gwiwar sahu.
Ta iso wajen, tana hamma, sannan ta ce.
“Wani Shegen ne ya haddasa wannan hayaniyar.....barcin safen ma ba za'a bar mutum ya yi ba.......mtwssss.” ta yi tsaki, ganin nice a ƙasa ina kuka.
Da yake tana yin Bosho, kodan kuɗin da yake bata, sai ta ce.
“Bosho me ta yi maka da zafi ka duke ta haka!?.” Bosho ya ciza leɓensa na ƙasa.
“Garkuwar mu gaskiya eh ku bari na fara mata illa ehyyee, sai na faɗa muku.....”
“A'a ka barta haka dai, Ni zan ƙara hukuntata idan har babban laifi ta yi maka.” na rintse ido, jikina yana rawa.
Take Bosho ya fara koro wata zazzafar ƙarya wanda yasa jikina ya mace.
“Garkuwa.....Kinga wannan yarinyar ta ki, a ido take na Allah, amma sheɗaniyar kanta ce, tana yawan neman na amince mata amma..........” Amrah ta saki wani ihu tana cewa. “Ku sake Ni na kasheta, Ni za ki ci ma amana.....ku sake Ni.” Garkuwa mata ta matsa kusa da ita, ta ringumeta tana dukan bayanta kaɗan-kaɗan, cikin rarrashi.
Bosho ya ci gaba da magana.
“Ni idan ba jahili bane, mai zan yi da ita, me zan yi da yarinyar da ke kama ga saniya, bayan Amrah ta tafi kowa ƙyau a cikin gidan nan........... Garkuwa, wai na zo zan shiga bayi eheeeeey, sai ta buɗe kofar wanda take ciki, muka haɗa ido, na ja saki na shiga bayin tsakiya, ina fitowa sai na ji tana kuka ƙasa-ƙasa a cikin bayin, sai na matsa na fara tambayar meke faruwa.........ashe yarinyar nan da abinda ta taka, ina zuwa ta jani cikin bayi, ashe kibar ba banza ba akwai ta samin ƙarfi, ina shiga ta kulle ƙofa, ta matse Ni jikin bango, wai sai na biya mata buƙata.........”
“Innallahi wa'inna ilaiyi raji'un.” a ka hau salati.
“Ni kuma shine na ƙi, na fara kokawa da ita, na buga mata goshi a kai, take ta fashe da ihu, wai sai ta min sharri........wallahi Sakeenat sai na ci uban........” ya kuma yin kaina ya fara dukana, mutane suka ja shi baya.
Shanawa dake tsaye ya yi wani guɗa.
“To ai dole sha'awa ta dameta, ga yanayin gidan namu, da mu da maza duk a haɗe muke, sai ku mata uzuri sha'awa ce ta fi ƙarfin kowa.” dariya wasu suka yi.
Ni kuwa cikin kuka na buɗe baki na fara cewa.
“Na rantse da girman Allah ba haka bane.....shine ya.....” Mama ta daka min tsawa.
Na tashi jikina yana min ciwo, na ruga ɗakin mu da gudu.
Bosho da Amrah kuwa aka dinga basu haƙuri, ana ta rarrashin su.
Ina shiga ɗaki, na sanya wata atamfa, na zura baƙin hijabi, take fuskata da hijabin suka haɗe, banbi takan komai ba, na yi waje, har kuma lokacin hakuri ake ta basu, yadda kasan za'a goyasu a baya.
Kowa na wajen ya yarda da ƙyaryan Bosho, banda Mama, wacce tasan ƙarya ne, amma saboda karta ɓata mai rai, haka ta dinga lallaɓasu.
Sai dai Amrah duk abinda ake cewa shiga kawai yake yana fita, tana zaune ne kawai, amma hankalinta ya yi nisa, tana kitsa irin azabar da za ta gana min cikin dare idan na yi barci.
Bosho kuwa kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha dan daɗi, ganin Amrah ta yadda ta dashi, sai ya sake jiki suka shige ɗakin mu, suka fara faranta ma juna rai.......a'uzubillahi..........
Idanuna sun yi ja sosai, har kaina yana sarawa.
Haka na isa har shago, na fara aikin dake gabana, ina yi ina share hawaye.
Wani lokaci sai na saki aikin na fashe da wani irin kuka, babu mai rarrashi na, babu mai tambayata abinda ke damuna, a rayuwata bansan ƙawaba, bansan daɗin sharing problems ba, sai dai na ta shanye komai.
Haka aka fara shigowa siyan abinci, wasu su tambaye Ni lafiya, sai na ce kaina ke ciwo, dan har kan nawa yana ciwon.
Ban iya dafa shinkafa ba yau, saboda ban jin daɗin, doya da dankali kawai na yi.
Ina jin yunwa amma haka na kasa cin komai.
Na kwanta kan ta burma, fuskata duk ta kumbura.
Inuwar Baba na gani tsaye a kai na, hakan yasa na tashi na zauna.
A hargitse ya shigo, duk ya yi dauɗa sosai.
Ya zauna yana ta haki, da alamun gudu ya yi.
Kallonsa na yi na ɗan lokaci sannan na tashi da ƙyar. Doya na zuba mai guda bakwai, na bashi, ya amsa ya fara ci da hannunsa duk da toka.
Yana gama ci, ya kalleni.
Take raunina ya sake bayyana, sai na fashe da kuka, na fara labarta mai duk abinda ya faru, kaman wani mai hankali, shi kuma ya zuba min ido yana saurarata.
Na kai ƙarshen maganar, ina rintse idanuna.
Take na ji tafin hannunsa akan fuskata yana share min hawaye.
Sai na buɗe ido da ƙyau, na zuba ma ɗan dattijon mahaukacin ido, murmushi na ga ya sakar min, na mai da mai ina kallon tsantsan ƙyau dake ɓoye bayan wannan dattin, yana da ƙyau mai sunan ƙyau, akwai shi da dogon hanci, ga ƙaramin baki, haka da dogon gashi, wanda ranar da na fara ganinshi sai da na tsorata, bayan mun saba kuwa, sai da na duba gashin da ƙyau, ashe dai na shi ne, ko Ni da nake da gashi mai tsawo baki, na shi ya fi nawa ƙyau sosai.
“Ka....ku....ka.” ya faɗa yana miƙewa tsaye.
Kafin na ce wani abu, ya fice a wajen da gudu, kaman walƙiya, murmushi na yi, sannan na tashi dan tattara wake-wake zuwa wajen da zanyi.......................
*Adeelah*
Ban bar asibitin nan ba sai da na tabbatar Mom ta ci abinci ta ƙoshi.
Daga nan na koma gida. Ina shiga bedroom ɗina, na kwanta kan gado, ina ɗan hutawa.
A daidai lokacin ne Nuseey ta shigo cikin ɗakin.
Sanye take da wata shadda mai kyau, an yi mata fitted gown ɗin da ya bi jikinta sosai. Na kalleta da kyau, musamman yadda take tafiya, na kalleta sosai.
“Yaushe kika huda hanci?”
Na tambaya ina kallon fuskarta.
Ta yi dariya, sannan ta nuna min haƙoranta.
kyakkyawan tooth jewellery (brace) da aka yi mata a haƙori, wanda yake ƙara mata kyau sosai, suka bayyana.
“Jiya na je aka min,” ta amsa cikin farin ciki. “Shi ne kuma aka ƙara min na kunne, yanzu sun zama ɓuli takwas.”
Na ɗaga gira ina kallonta.
“Guda takwas?!”
Ta sake dariya.
“Eh mana.”
Na girgiza kai, ina kallonta cikin mamaki.
Nan na fara mata nasiha, ina faɗa mata kan yawan kashe kuɗi da irin waɗannan abubuwan kwalliya.
Ita kuwa sai ta haɗe fuska.
“Honestly Adeelah, ni ba shi ya kawo ni ba.”
Na girgiza kai.
“Me ya kawo ki to?”
Ta mike tsaye, ta fara ɗan takawa cikin ɗakin, sannan ta isa wajen closet ɗina. Ta buɗe ƙofar tana kallon abayoyina da aka jera cikin tsari, kala-kala.
“I need a pink Abaya. Gobe muna da party, kuma shine our anko. So I came to pick one from yours.”
Ta faɗa tana duba abayoyin ɗaya bayan ɗaya.
Sai ta ɗauki wata pink Abaya.
Ban ce mata komai ba. Ni ko kayan jikina take so, ba na iya ce mata komai. Abin da nake iya yi kawai shi ne in cire mata na bata.
“This one is perfect. Zan kai wa tailor yanzu ya rage min tsayin kaɗan.”
Na yi murmushi, domin kayana suna mata tsawo sosai. Shi ya sa duk Abayar da ta ɗauka sai an rage mata tsayi, a haka ma heal shoe take sawa.
Bayan ta rufe closet ɗin, ta juyo ta yi min sallama, sannan ta fice daga ɗakin.
Na bita da kallo har ta ɓace daga gani, ina yi mata addu'a a raina.
Cikin ƴan daƙiƙu kaɗan, sai wayata ta fara ringing.
Na juya na kalli wayar.
Da na ga sunan da ke haske a screen ɗin, sai na haɗe fuska.
Doctor Ahmad.
Na tura baki kaɗan, ina kallon wayar da wani irin yanayi. A wajen Mom ya amsa numberta, tun kwanaki da suka wuce.
Bayan ta yi ringing sau biyu, sai na miƙa hannu na ɗauka.
“Hello…” ya faɗa.
Sai na amsa masa da sallama irin ta addinin Musulunci.
“Assalamu alaikum.”
Ya yi murmushi kafin ya amsa cikin wata murya mai daɗin ji.
“Wa alaikumus salam, kyakkyawata.”
Na ɗan yi shiru, sannan na tambaye shi.
“Me yasa ka kira ni?”
Sai na ji ya ɗan yi dariya a ɗayan ɓangaren.
“Because ina cike da kewarki, abar sona.”
“Hmmm…”
Ya sake yin murmushi.
“Why? Ba gaskiya nake faɗa ba? I really miss you, Adeelah.”
Ji na yi kaman na shaƙe wiyarsa, sai na lunshe ido.
“Kin san abin da na lura akan yi kuwa?”
“Sai ka faɗa?” muryarsa ya ɗan rage.
“Kin fi matata wayewa. Kina da abin burgewa sosai, haka kuma ke ta daban ce sosai”
Na ɗan yi shiru.
“Doctor Ahmad, don Allah kar ka fara wannan maganar.” na katse shi da sauri, dan babban matsalata da shi, baya da sirri, kuma duk abinda ya zo bakinsa faɗa yake.
“Me na yi?”
“Ka daina kawai.”
“Amma gaskiya nake faɗa ai, Ko yadda kike tsara maganarki ma ya bambanta da na ta, gashi kina da sura mai jan hankali, ita kuwa hakuri kawai nake da ita.........”
“Wai kai me ya sa kullum kake kawo min maganar matarka ne, wannan ba daidai bane?”
Ya yi dariya.
“Sarauniyar zuciyata gaskiya nake faɗa miki, wallahi kin fita iya komai.”
“Ni ban tambaye ka ba ai....”
“Eh amma ina so ki sani ne.........wallahi Adeelah ina sonki, kuma aurenki zan yi, idan baki son kishiya zan sake ta, yaran suna idan baki ƙaunar zama da su, zan kai wa mahaifiyata ta riƙesu.....Ni fatana na mallakeki.”
“Doctor Ahmad!” na daka mai tsawa.
Ya yi shiru tsit
Na sauke numfashi, amma har yanzu maganar tasa tana bani haushi.
“Ka kiyaye furucinka.....”
“Okay, Adeelah.” take na katse kiran ina jin raina yana ɓaci.
Hannu na kai na janyo system ɗina kusa da ni.
Na fara binciken sabbin labaran da suka shafi duniya, ina duba ɗaya bayan ɗaya kamar yadda na saba. Take na manta abinda ya min na shiga yanar gizo.
Nan ne na ci karo da wani labari da ya ɗauke hankalina.
« Wani matashi ya aikata ma wata yarinya mai kimanin shekaru 10, fyaɗe.» Na buɗe labarin, sai na ga hoton saurayin da kuma yarinyar, ƴar shekara goma, wadda take kwance a asibiti tana samun kulawa.
Tausayinta ya kamani sosai.
Na ɗan tsaya ina kallon hotonta, zuciyata ta cika da baƙin ciki.
“Ya Allah…”
Na sauke numfashi, sannan na rufe shafin.
Na wuce gaba da binciken.
Sai ga wani labari ya sake bayyana a gabana.
« Miji ya yi wa matarsa mugun duka bayan ta saci kuɗinsa domin sayen abinci ita yaranta.»
Na buɗe labarin da sauri.
Na karanta shi sosai, daga farko har ƙarshe.
Sai na gano cewa abin ya faru ne a Kaduna, cikin unguwar Rigasa, kuma hukuma ba ta yi komai akan haka ba.
«An bayyana cewa bayan abin da ya faru, matar ta samu mugun rauni, yayin da mijin ya gudu aka rasa inda yake.»
Na lumshe idanu na na ɗan lokaci.
Gaskiya abin ya taɓa zuciyata.
“Gobe Insha Allah, daga makaranta zan je Rigasa na duba matar.”
Na yi shiru na ɗan lokaci, sannan na ƙara da murmushi kaɗan.
“Shi kuma mijin…” sai na yi murmushi.
Tun ban zama ƴar jarida ba, ina matuƙar son kare haƙƙin mutane da kuma ganin an taimaki wanda aka zalunta.
A gaskiya, akwai wata gidan TV da suka ɗauke ni aiki, amma ba na cika zuwa ba. Ina zuwa ne idan na samu lokaci, saboda burina shi ne na fara da kammala karatuna.
Yanzu ma saura kaɗan in gama makarantar sai na mai da hankali sosai wajen aikina.
Sai na koma kan screen ɗin, ina ci gaba da binciken wasu labaran duniya, zuciyata cike da wani irin rauni.
Domin na san abu ɗaya:
Wata rana zan zama cikakkiyar ƴar jarida.
Kuma ba zan zama ƴar jaridar da take kallon labari kawai ba.
Ina son zama wadda za ta nemo gaskiya, ta tsaya wajen wanda aka zalunta, kuma ta sa a ji muryar waɗanda ba su da damar yin magana....................
*FADAR MASARAUTAR AL-JAWHARA — SASHEN SARAUNIYA SARAH*
“Uwar ɗakina zinariya, Mai ɗaura daraja a wuya, Ƙaramar magana, babbar inuwa, Mai sanyaya zuciyar fada, Furen da ba a tsince shi, Mai tafiya da kamshin sarauta, Uwar rawani, Mai ɗauke da sirrin masarauta. Uwa ga Gimbiya Mira da Gimbiya Lina. Uwa ga Magajin dake tafe Allah ya ƙare gabanki da bayanki. Allah ya ƙara miki nisan kwana....Taka lafiya Sarauniyar Duniya..........” Amintacciyar Hadimar Sarauniya Sarah wato Hadima Asabe, cikakkiyar bahaushiya ƴar Nigeriya, wacce ta zo bauta gidan sarauta, tun shekara da shekaru, hakan yasa ta goge ta larabci kamar ta gada.
Ta kai ƙarshen kirarin, suna isa tsakiyar babban parlourn na alfarma.
Sarauniya Sarah wacce take sanye da kayan sarauta irin na larabawa, ta zauna kan kujera cikin izza, ta kalla Sarauniya Rania dake zaune sai cin magani take, jin an ambaci *Magaji*
Sarauniya Sarah ta yi ma kuyangun wajen ishara da hannu, duk suka tashi suka wuce, banda Hadima Asabe.
Sarauniya Rania ta buɗe baki cikin izza tace.
“Da ke kawai zan yi magana.” sarauniya Sarah ta kalla Hadima Asabe.
Da sauri Hadima Asabe ta jinjina hannu tana cewa.
“A fito lafiya Sarauniyar mata. Murmushinki yayyafin alheri......Uwar Magaji mai dunbin nasara.” da haka ta bar musu parlourn.
Sarauniya Sarah ta saki murmushi sannan ta kalla Sarauniya Rania ta ce.
“Ina sauraranki Rania.” Sarauniya Rania ta miƙe tsaye cikin izza, ta kalla Sarauniya Sarah daga sama har ƙasa ta buɗe baki tace cikin Izza, isa, ƙasaita, da shu'umanci......................✍️ End > An fara 🤪, naga likes ko na tafi hutu 😅. PRETTY SK nace ku shirya, SAKEENAT ɗin nan ba wasa, alƙalamin da kaifinsa, za ku shaida hakan idan kun kasance da Ni 😘🫠
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 8126151523
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*