CHAPTER 1️⃣8
by @prettys01
> “Ina sauraranki Rania.” Sarauniya Rania ta miƙe tsaye cikin izza, ta kalla Sarauniya Sarah daga sama har ƙasa ta buɗe baki tace cikin Izza, isa, ƙasaita, da shu'umanci..................
Tace “Ban fahimta ba......ban gane ba..........zuwa na yi ki min ƙarin bayani!?.” Sarauniya Sarah ta miƙe itama cikin izza.
Ta juya ma sarauniya Rania baya, kowa ya kalla gefe guda.
“Ai zancen ya riga ya zaga ko ina a cikin Al-jawhari, cewan ina ɗauke da Magajin Izza a cikin cikina.” ta kai nan tana wani irin murmushi.
“Hmmm tabbas Sarah, kin ɗibo ma kanki masifa.....sanin kan ki ne, tunda Ni Raina ban haifa ɗa namiji ba, to babu mai haifarsa a cikin masarautar nan.......” ta nunfasa.
“Sai da kika san na gama haihuwa, banda ikon sake haihuwa shine za ki munafunce Ni ki ɗau ciki........” a tare suka jiyo suka fuskanci juna, kowa a dake rai a ɓace.
“Rania ɗan daka mana............daa da yanzu ba ɗaya bane, ciki kuma sai na haife shi.”
“Ki sani idan har ina nunfashi ba za ki haifa ɗa namiji a gaban ido na ba.”
“Hmmmmm Ni kuma na ce ki zuba ido ki sha kallo, ke kanki kinsan cewa, ba'a taɓa Ni a zauna lafiya, hakan yasa nake raye cikin aminci Allah.........babu irin mugunta da baki min ba, akan sai na rabu da Sarki Rayyan, sai dai nima ba ki san na shigo ne da nawa ikon ba..........hakan yasa daga ƙarshe kika yarda makaman yaƙi, muka zuba ma juna ido, sannan idan kin manta na tuna Miki........” Sarauniya Sarah ta ƙara taku biyu ta isa gab da sarauniya Rania sannan ta ce.
“Ni da ke muka hana kowacce mace samun gurbi a cikin gidan nan, Ni da ke muke halaka duk wacce sarki ya Shammace mu ya auro, Ni da ke muka cire masa sha'awar auren wata macen......dan haka ki bani waje........ki dena shiga harka ta, launina sauya wa yake tamkar hawainiya..........”
Sarauniya Rania ta yi murmushi.
“Komai da kika faɗa haka ne, amma kin manta abu guda......” sarauniya Sarah ta ɗaga mata gira alamun tana ji, sai ta ci gaba da magana.
“Kin manta ainiyin waye magajin kujerar sarauta......kin manta cewa ko kin haifa namiji kafin ya yi mulki kin bar duniya........kin manta cewa daga ranar da Laith ya dawo komai zai rushe.......hmmmmm sai dai Ni ina da babban shiri a ƙasa, wato ƙanina Zain, shi zai gaji Sarki Rayyan Al-jawhari.” dariyar manya sarauniya Sarah ta yi.
“Lallai Raina, kema Bara na tuna Miki.......kin manta cewa jinin Al-jawhari sune kaɗai suke mulkan kujerar mulki....kin manta ƙaninki ba ɗan alhakin Al-jawhari bane......hmmmmm ki sauya taku........ Na barki lafiya.” tana kaiwa nan ta juya ta fara tafiya.
Sarauniya Rania ta ciza leɓenta, sannan ta juya itama a fusace ta yi hanyar fita.
Sarauniya Sarah ta juyo ta kalla yadda Sarauniya Rania ta fice cikin ɓacin rai, sai ta yi murmushi sannan ta haura sama...............
Sarauniya Rania ta isa sashenta cikin ɓacin rai.
Tana shiga babban parlourn nata, ta fara kai da komo, zuciyarta cike da tunane-tunane.
Maganganun Sarauniya Sarah suka ci gaba da maimaituwa a cikin kanta, take ta tuna abinda da shi take kwana tana tashi.
“Daga ranar da Laith ya dawo komai zai rushe…”
cak ta tsaya
Ta ɗago kai ta kalli bayin da suke tsaye cikin ladabi a gefe.
“Ina buƙatar ganin dukkan yarana yanzu nan”
Ta ɗan yi shiru, sannan ta ƙara da cewa,
“A kira su gaba ɗaya. Har da Ayla da Zain. Duk su zo.” ta faɗa cikin ɓacin rai.
“An gama, Sarauniya mai adalci.”
Baiwar ta yi saurin rusunawa, sannan ta juya ta fice daga sashen Sarauniya Rania.
Ta nufi sashen da yaran Sarauniya Rania da ƙannanta suke.
Baiwar ta isa bangaren yaran Sarauniya Rania, wani sashe ne mai faɗi da aka kawata shi da kayan alfarma irin na gidan sarauta.
Da ta shiga babban parlourn, idanunta suka sauka kan ’yan mata huɗu da suke zaune cikin nishaɗi, kowacce ta shagaltu da abin da take yi.
Ƙyawawane sosai jikin larabawa, kana ganinsu kaga ƴan gata.
Babar ƴar Sarauniya wato Gimbiya Jana, mai kimanin shekara 21, tana zaune kan wata babbar kujera mai laushi, hannunta ɗauke da waya mai tsadar gaske, tana ta danna-danna a kai cikin natsuwa. Sanye take da wata doguwar rigar Larabawa mai ƙyalli, an yi mata ado da zaren zinariya, yayin da wasu ƙananan kayan adon zinariya suka ƙawata wuyanta da hannayenta.
A gefenta kuwa, ƙanwar Sarauniya Rania ce, Gimbiya Ayla itama shekarunta 21yrs, tana kallon wani shirin da ke gudana a babban talabijin ɗin da aka rataye a bangon parlourn.
Ta jingina cikin kujera, tana sanye da wata doguwar riga mai launin ruwan kasa mai duhu, wadda aka yi wa ƙawanya da duwatsu masu walƙiya.
Gimbiya Ayla, tafi gaba ɗaya yaran Sarki nuna izza da jiji da kai, ga wulaƙanta ɗan adam, halinta har yafi na Sarauniya Rania ma, dan shu'uma ce sosai.
Sai ƴar Sarki ta biyu Reem mai shekara 20yrs.
Tana kwance a kan wata kujera ta musamman, yayin da wata baiwa ke yi mata tausa a kafaɗunta. Sanye take da wata doguwar riga mai laushi wadda ta sauka har ƙasa, a kanta akwai ɗan rawani mai ƙyau, yayin da zoben zinari suka cika yatsunta, dan ita akwai son ado.
’Yar ta huɗun, Autar Sarauniya Rania mai suna Noor, shekarunta 18, tana zaune a gaban wata ƙaramar madubi, tana gyara gashin kanta da hannunta. Sanye take da wata doguwar riga mai kyau ta sarauta, wadda aka yi mata ado.
A cikin babu wacce ta fi wani ƙyau, dan Allah ya zuba musu ƙyau na musamman.
A hankali baiwar ta ƙaraso gabansu.
Ba tare da ta ɗago kai sosai ba, sai ta durƙusa har ƙasa cikin girmamawa.
“Ya ’ya’yan Sarauniya, ’yan mata masu daraja, taurarin Fadar Al-Jawhara, waɗanda aka haifa cikin daula, aka raina cikin alfarma…...”
Ta ɗan ɗaga kai, sai sunkuyar da kai.
“Allah ya ƙara muku.......”
“Me ya kawo ki!?.” Gimbiya Ayla ta faɗa cikin Izza.
“Uhmmmm.....Uwargidan mai martaba Sarauniya Rania ce ta aiko ni da saƙo........ Sarauniya Rania tana buƙatar ganin ku gaba ɗaya yanzu.”
Shiru ya ratsa parlourn.
Babu wacce ta amsa.
Wata ta ci gaba da kallon wayarta, wata ta maida hankalinta kan talabijin, yayin da wadda ake yi wa tausa ta lumshe idanunta kamar ba ta ji komai ba.
Baiwar ta jira na ɗan lokaci.
Amma saboda izza da ƙasaitarsu, babu wacce ta damu da amsa mata.
Daga ƙarshe baiwar ta sake sunkuyar da kai.
“An sanar da ku, Ya ’yan Sarauta.”
Da haka ta miƙe ta fice daga parlourn.
Tana fita sai ’yan matan suka kalli juna.
Ba tare da wata magana ba, ɗaya bayan ɗaya suka fara miƙewa.
Gimbiya Jana, Reem da Noor Suka fara tafiya, sai Gimbiya Ayla ta bi bayansu.
Takun sawunsu ya cika falon da ƙaramar ƙara, yayin da dogayen rigunansu masu ƙyalli suke motsawa a hankali, dan sai na da ƙasa suke yi.
Kowacce tana tafiya cikin izza, ƙasaita da girman kai irin na ’yar gidan sarauta.
Tafiya suke ba kamar waɗanda aka kira ba…
Sai kamar waɗanda aka yi wa gayyatar zuwa ga wani muhimmin taro.
Suna shiga babban parlourn Sarauniya Rania, suka iske ta, tsaye rai a ɓace.
Suna shiga Gimbiya Ayla ta daka ma bayin da suke wajen tsawa, da sauri suka watse, ta ja tsaki sannan ta isa gaban sarauniya Rania ta sumbaci hannuta irin dai al'adar Larabawa, saura suma sun suka sumbaceta sannan suka Zazzauna cikin ƙasaita.
A dai-dai lokacin Zain ya shigo cikin nasa izzar.
Ba ƙarya saurayin yana da ƙyau shima, dogo mai manyan idanuwa, sanye yake da kayan sarauta shima, sai dai fuskarsa a haɗe yake kamar hadari.
Ya nema waje ya zauna a fusace ba tare da ya ce komai ba.
Sarauniya Rania ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce.
“Kuna jin babban labarin dake yawo a cikin masarautar nan kuwa!?.”
“Sarauniya Sarah tana da juna biyu....haka ne!?” Ayla ta faɗa cikin ko in kula.
“Wannan ba wani abu bane a wajen ku.....na ga kamar baku damu ba.” sarauniya Rania ta sake faɗa tana zuba musu ido.
Gimbiya Jana ta lumshe ido ta buɗe.
“Hmmmm ni abinda ya fi ban haushi ma shine, sai cewa ake wai Magaji za ta haifa, ai mu zuba ido kawai musha kallo.” Reem ta yi murmushi
“Ummee kinsan dai idan har muna nunfashi ba za mu ga abinda zai ɗaga miki hankali mu bari ba, dole musan abin yi......”
“Yauwa Yarana abin alfahari na.....Zain baka ce komai ba.” Zain ya kalla Ummee.
“Ni banda ta ce wa, amma kinsan dai ina matuƙar son na hau karagar mulki......kuma ko ta halin ƙa-ƙa, ban damu da Ni ba jinin Al-jawhari bane, kawai na hau karagar mulki idan lokaci ya yi......” yana kai nan ya tashi ya fita fuuuu kaman zai tashi sama.
Ummee ta yi murmushi
“Shi fa wannan gani yake komai cikin ruwan sanyi ake samu.......Ayla ki bamu shawara mana.” Ayla ta kalla Sarauniya Rania.
Take ta miƙe tsaye, ta dan yi tuku uku sannan ta tsaya, ta buɗe baki ta ce.
“Mafita biyu gare mu..........kunsan Ni bana bari ya wuce...........na farko........” sai ta saki wani shu'umin murmushi, su kuma duk suka ƙosa da jin shawarar ta, dan akan komai ita ke kawo musu shawara kuma yana ɓullar da su...................
*Sakeenat*
Bayan na dawo gida daga shago, jikina ya yi laushi kamar ba ni da ƙarfi.
Zazzaɓin da nake fama da shi ya ƙara tsananta, har tafiyata ta koma jan ƙafa.
Na miƙa wa Mama cinikin kuɗin da na yi yau.
Mama ta ɗauki kuɗin, ta ƙidaya su a hankali.
Sai ta ɗago kai ta kalle ni.
Fuskarta ta sauya.
“Ina sauran kuɗin?”
Na sunkuyar da kai.
“Mama ban iya girkawa duka ba, bana jin daɗi.”
Mama ta ja dogon tsaki.
Kafin in samu damar sake magana, sai ta hau ni da faɗa kamar za ta doke ni. Muryarta ta cika gidan.
Ni kuwa ina tsaye ina sauraren ta, jikina na rawa saboda zazzaɓi. Ban san ko yunwa ce ta fi damuna ko zafin jikina.
Daga ƙarshe ta dungure min kai ta wuce.
Alhamdulillah ba ta duke Ni ba, amma ranta ya ɓaci sosai.
Na nufi cikin ɗaki da ƙyar, na kwanta a kan katifa. Raina ya yi nauyi sosai. Hawayen da suka taru a idanuna na ƙoƙarin hana su zubowa, amma zuciyata ta fi ƙarfin hakan.
Cikina ya fara ƙara ƙara.
Yunwa nake ji.
Sai a lokacin ne na tuna cewa akwai ragowar madara da wasu kayan ciye-ciye na jiya.
Na share fuskata, sannan na tashi a hankali.
Ƙafafuna kamar ba nawa ba. Na yi tafiya zuwa inda ake ajiye ruwa a flask, na samo ruwan zafi, sannan na koma ɗakina.
Ban lura cewa Mama tana zaune a parlour ba, tana kallona.
Na shiga ɗaki, na fito da kayan ciye-ciyen, sannan na haɗa tea. Hannuna na rawa saboda yunwa da rashin lafiya.
Na zauna, na ɗaga kofin zuwa bakina.
Sai kawai na ji muryar Mama daga bayana.
“Innalilahi......!”
Na yi saurin juyawa, har ruwan shayin yana ɗan zuba kaɗan a hannuna.
Mama tana tsaye, hannayenta a ƙirji, tana kallona da wani irin kallon da na kasa fassarawa.
“Sakeenat…”
Na ajiye kofin a hankali.
“Sata kika fara, ko bin maza?”
Kalamanta suka daki zuciyata.
Idanuna suka cika da sabon hawaye.
Na girgiza kai a hankali, ina kallon fuskarta.
“Zaki faɗa ne, ko sai na ci ubanki?”
Ta nufi inda nake cikin fushi.
“Mama….... a'a wallahi.....zan..... zan faɗa.”
Ta tsaya.
“Ina jinki.”
Na haɗe hannuwana, hawaye suka fara gangarowa.
“Mama, wallahi, wallahi ban yi sata ba. Ban kuma bin maza. Wannan ragowar siyayyar da na yi ne da kuɗin da kika bani…”
“Ragowar siyayya?”
Mama ta katse ni.
“Sharri za ki min? Yaushe na baki kuɗi?”
Na fashe da kuka.
“Mama, kuɗin da kika bani…”
“NI...?”
“Eh.....” na dakata da kukan na ci gaba da cewa.
“Kin bani kuɗi jiya, daga nan na je na yi siyayya. Ga sauran kayan nan…”
Na nuna mata kayan da ke gabana.
Mama ta kalle su, sannan ta sake kallona.
“Dubu nawa na baki da hannuna?”
Na ɗaga kai da sauri.
“Eh, Mama dubu uku.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci, kamar tana ƙoƙarin tuna abin da ya faru.
Sai ta jinjina kai.
“Saboda ke ba ki da hankali! Sai ki kashe duka. Ni a tunanina dubu ɗaya na baki, shima na zuba miki ido ko za ki dawo min da canji, tunda ba duka na baki ba.....hmmmmm Ashe har dubu uku na baki!”
Na sunkuyar da kai.
Hawayen suka ci gaba da zuba min.
A wannan lokacin ban san abin da ya fi min ciwo ba—zargin da Mama ta yi min, ko yunwar da nake ji, ko yadda zuciyata take min zafi.
Na kalli kofin tea ɗin da ke gabana.
Yunwar da nake ji ya dena damuna.
“Za ki sani....” da haka ta yi ƙwafa ta juya ta fita.
Na lumshe ido sannan a hankali na kai kofin bakina, na shanye lokaci guda, kamar wani magani, na cinye sauran kayan raina yana min zafi.
Ina gamawa na kwanta tare da jan wani hijabin nawa na rufe jikina da shi, ina sane da sallolin dake kaina, amma jikina ya yi zafi, na bari an jima sai na yi gaba ɗaya harda isha'i.......ido na lumshe nan da nan, barci mai nauyi ya yi gaba da Ni..................✍️ End.
> 🫢😢 ╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*