SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER 1️⃣9

by @prettys01

> Ina gamawa na kwanta tare da jan wani hijabin nawa na rufe jikina da shi, ina sane da sallolin dake kaina, amma jikina ya yi zafi, na bari an jima sai na yi gaba ɗaya harda isha'i.......ido na lumshe nan da nan, barci mai nauyi ya yi gaba da Ni.....................

Barci nake sosai, ina yi ina sauke nannauyan ajiyar zuciya, ga zufa da ya fara jiƙani, alamun zazzaɓin jikina ya sauka.

A hankali na buɗe lumshashshun idanuna, na ja jikinsa a hankali, sannan na tashi na zauna, ai da sauri idanunsa suka washe, na miƙe da sauri ina zuba ma Amrah wacce na samu ta yo kaina da riƙe da bulala, a cikin ɗan duhun dake sauran ɗakin.

Allah ya so Ni, da ina barci sai dai na ji wannan bulalan a jikina.

Murmushi na yi, ina kallon yadda ta iso gabana a fusace, da sauri na fizge bulalen ina kallon ta da ƙyau.

Tabbas idan aka bar Ni da ita, sai ina karyata pieces, amma saboda ƙarfin hali, ta caci meni da faɗa.

Na kauce dukan da ta min, na koma gefe.

“Sai na kashe ki yau......sai na miki illa.” tafaɗa tana komawa baya, wani ƙarfe ta ɗauko ta yi kaina.

Ba zan iya gujeguje ba saboda yanayi na, na tsaya har ta iso kusa da ni, sannan na ɗaga hannuna na lafta mata duka a kai.

Ba shiri ta saki ihu a cikin daren nan, kamar wacce na coka ma wuƙa.

Na taɓe baki na wuce bayi, sai dai me, tun ina cikin bayi, na ji tana ta fasa abubuwa cikin fushi.

Na ɗan ja tsaki kaɗan.

Alwala na yi bayan na yi duk uzurin dake gabana.

Ina buɗe ƙofa muka haɗa idanu da ita.

Amrah na tsaye cikin wani rigar barci dogo har zuwa gwiwa, ba laifi kayan yana da faɗi kuma yana da ƙyawun gani.

Tana tsaye duk ta hargitsa gashin kanta, tana kallona ko ƙyafta ido ba ta yi. Ta buɗe baki tace.

“Za ki tantance, wallahi sai na ja miki masifa...........” ihu ta kurma tana zubewa a ƙasa kamar mai aljanun ƙyarya.

“Amrah Allah ya baki lafiya.” na faɗa na nufa wajen da zan yi sallah.

Daidai nan ya Mama ta shigo da wasu ƴam mata uku.

“Me ke faruwa!?.” Mama ta faɗa tana isa kusa da Amrah.

Amrah da zafin kishi bai gama sakin ta ba, ta sake fashewa da kuka tana cewa.

“Garkuwar mata........ Sakeenat ce!?.” Mama ta kalleni da sauri.

Sai na girgiza mata kai da sauri.

“Mama babu abinda na......”

“Shiru!!!.” ta daka min tsawa.

“Amrah me ta Miki!?.” Amrah ta fara magana cikin kuka.

“Ina cikin barci..... Sakeenat ta tashe Ni......ban nuna mata komai ba akan abinda ya faru jiya ba, na zauna ina kallonta, sai kawai ta shaƙo ni tana cewa.......Na rabu da Bosho ko ta min illa.....Ni kuma na ce sai dai ta kashe Ni, shine ta fara du....du....dukana.....” sai kuka.

Ina mamakin yadda mutane ke tsara ƙarya su faɗa, kuma a yadda.

“Sakeenat ashe baki da hankali ban sani ba......”

“Mama ba haka bane wallahi, bara na faɗa miki yadda.....” ta ɗaga min hannu.

“Ki kuka da kanki, tashi Amrah mu wuce ɗakina, ke kuma ki yi addu'ar na mutu kafin safiya, in ba haka ba, sai na sauya miki kamanni.”

Suka tashi suka fita gana ɗaya.

Na ji babu daɗi a rai na, a ce uwata bata damuwa da Ni gaba ɗaya.

Na girgiza kai ina ƙarfafa kai na.

Na shimfiɗa darduma na fara sallah, bayan na yi duk wanda ake bi na, na zauna ina maimaita kalaman Mama.

Wasa-wasa barci ya min ƙaura, na kasa komawa, na zauna jugum ina jiran abinda Mama za ta min washegari, tabbas nasan zan sha jiki.

Idona biyu aka shiga sallar asuba, na tashi na gabatar, sannan na fara abinda nasan zan yi.

Har ga Allah ina tsoron haɗuwa da Mama.

Ko abincin kari ban musu ba, na yi wanka na bar gidan tun ƙarfe 8am na safe.

Yau ina so na faranta wa Mama rai, ina zuwa shago, na fara girki, kuma yau na zuba da yawa sosai.

Alhamdulillah an fara ciniki tun a safen, Ni da nake amfani da doya goma, amma yau guda ashirin na fere, shinkafa ma na sanya ninkin wanda nake zubawa.

Lokaci guda na ji duk damuwata ya bi iska, na dinga aiki cikin nishaɗi, ina yi ina rera wata sabuwar waƙar da na ƙirƙira.

Wajen azahar, na ɗan ji hayaniya ta gefan shagona, na leƙa ta window ganin abinda ke faruwa.

Wata baƙar mota na gani babban, sai ƙyalli take yi, a bakin gidan dake gefan shagona, wani ƙaramin gida.

Ba'a ɗau lokaci ba, naga Maman Abasiyya ta shiga motar, sannan motar ta bar wajen da ita.

Na ji daɗin a rai na, nasan taimaka mata za'a yi, kuma tana da buƙatar taimakon sosai.

Ita ce wacce mijinta ya mata shegen duka ya sake ta, ya kuma gudu.

Na girgiza kai ina mai da hankali kan wanda ya zo siyan abinci..........

*Adeelah*

Da sassafe na farka daga barci, hasken safiya yana ratsawa ta cikin labulen ɗakina. Na buɗe idanuna a hankali, na ɗan jima kafin na miƙe daga kan gadon.

Na shiga banɗaki na yi wanka, na fito na shirya.

Na zaɓi wata doguwar riga mai kyau mara nauyi, na saka ta sannan na ɗaura hijabi akai. Bayan na gama, na tsaya a gaban madubi na ɗan gyara hijab ɗin, na ɗauki jakata da littattafan da nake buƙata.

Da na fito daga ɗakina, sai na tarar da Mom zaune a wajen cin abinci.

“Zo ki ci breakfast ɗin nan kafin ki tafi,” ta faɗa tana kallona da murmushi.

Na ƙarasa na zauna kusa da ita. Mom ta ɗebo abinci da cokali, ta kawo min bakina.

“Mom, zan ci da kaina mana,” na faɗa ina dariya.

“Uhmmm Ni dai buɗe baki”

Ta sake ɗebo wani cokali ta kai bakina, tana kallona cike da ƙauna.

“Na girma fa, amma har yanzu kina son bani abinci a baki,” na faɗa, sai ta yi dariya.

“Har yau Ni kallon yarinya nake miki”

“Ina sonki Mom.”

Ta girgiza kai cikin jin daɗi, ta sake bani abincin.

“Ki ci sosai, kin ji? Kar ki tafi jami’a da yunwa.”

“an gama Mom.”

Bayan na gama, ta ɗauki tissue ta goge min gefen baki a hankali, kamar yadda take yi tun ina ƙarama.

“Allah ya kiyaye ki, ya ba ki sa’a a karatinki.”

“Amin, Mom.”

Na ɗaga jakata na rataya a kafadata, sannan na rungume ta.

“Zan tafi.”

“Allah ya dawo da ke lafiya, ɗiyata.”

“Ameen Mom, kefa kafin ki fita ki ci abinci!?.”

“Insha Allan Babyna.” da haka na fita daga ɗakin.

★ Mun isa Jami’ar kamar kullum, Nuseey ta fara sauka, na isa wajen parking na yu.

Bayan na shiga harabar jami’ar, na ga wasu daga cikin abokan karatuna. Muka gaisa cikin fara’a.

A yau muna da darasin Mass Communication. Na shiga ajinmu na zauna tare da sauran ɗalibai, jim kaɗan sai lecturer ɗinmu ya shigo.

“Good morning, everyone.”

“Good morning, sir,” muka amsa baki ɗaya.

Ya fara darasin, yana mana bayani kan Mass Communication, ma’anarta, hanyoyin isar da saƙo ga ɗimbin jama’a da kuma rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa a cikin al’umma.

Na buɗe littafina ina rubuta muhimman bayanan da yake bayarwa. Wani lokaci lecturer ɗin yana tambayar mu, mu kuma muna ba da amsa.

Darasin ya ɗauki lokaci, amma saboda ina sha’awar abin da nake karantawa, ban na gaji ba.

Bayan ya fita, sai lokacin Introduction to Journalism ya yi. Lecturer ɗinmu ya shigo ajin da wasu takardu a hannunsa. Ya ajiye su a kan tebur, ya kalli ajin gaba ɗaya kafin ya zauna.

“Good morning, everyone.”

“Good morning, sir,” muka amsa baki ɗaya.

Ya ɗauki takardun da ke gabansa ya duba su, sannan ya fara bayyana mana abin da zamu tattauna akai.

“Today, we are going to have a short individual presentation. I will call you one after another. Each student will come forward, pick a topic from the questions I have prepared, and explain it briefly. Your presentation will be assessed, and you will be given marks based on your understanding, confidence and delivery.”

Nan take ajin ya yi shiru. Kowa ya fara kallon takardun da ke hannunsa, wasu suna sake karanta abin da suka rubuta, wasu kuma suna ta raɗa-raɗin addu’a.

Sai ya fara kiran ɗalibai ɗaya bayan ɗaya.

“Number one.”

Ɗalibi ya miƙe ya fita gaba. Ya tsaya ya gabatar da nasa, lecturer ɗin ya saurare shi har ya gama, sannan ya yi masa wasu ƴan tambayoyi. Bayan ya amsa, lecturer ɗin ya rubuta masa mark.

“Next.”

Wata ta fita. Ita ma ta yi nata bayanin, aka bata maki.

Haka aka ci gaba.

Ɗaya bayan ɗaya ake kira, ɗaya bayan ɗaya ake fitowa. Wasu suna yin bayaninsu cikin ƙarfin hali, wasu kuma tsoro ya bayyana a muryarsu. Amma lecturer ɗin yana sauraron kowa cikin nutsuwa, yana gyara inda ya dace sannan ya rubuta musu maki.

Ina zaune ina kallon yadda kowa yake fitowa.

Har aka zo kaina.

“Next… Sakeenat Nura”

Na ɗago kai.

“Yes, sir.”

Na miƙe daga kan kujerata, na ɗauki fallen takarda sannan na nufi gaban students.

Da na isa, sai na gyara tsayuwata, na ja numfashi a hankali sannan na kalli takardar da ke hannun lecturer ɗin.

Na karanta taken da aka ba ni a zuciyata, sannan na ɗaga kai na kalli ɗaliban da ke gabana.

Na fara magana cikin nutsuwa.

“Good morning, sir. Good morning, everyone. Today, I will be talking about Journalism. Journalism is the process of gathering, verifying and presenting information to the public through different media platforms. A good journalist must be truthful, accurate and fair when reporting a story. Journalism plays an important role in society because it helps people know what is happening around them and gives attention to important issues. In conclusion, journalism is not just about reporting news; it is about seeking the truth and serving society responsibly. Thank you.”

Na yi shiru.

Ajin ya yi shiru na ƴan dakiku, kafin lecturer ɗin ya ɗaga kai daga kan takardarsa.

“Well presented, Sakeenat.”

Na yi murmushi.

“Thank you, sir.”

Ya yi wasu ƴan rubuce-rubuce a takardar, sannan ya kalli ni.

“You have a good understanding of the topic. Your confidence and delivery were impressive. Keep it up.”

Na sake murmushi cikin jin daɗi.

“Thank you, sir.”

Na koma wurin zama na, zuciyata cike da farin ciki. Ba wai don maki kawai ba, amma saboda duk lokacin da nake magana game da aikin jarida, nakan ji kamar ina kusantar burina na zama ƙwararriyar ’yar jarida.

Bayan an tashi, Na tattara littattafaina na saka su cikin jaka. Da na fito daga jami’ar, sai na biya gidan marayu kamar yadda na saba.

Ban ɗauki lokaci mai tsawo ba a gidan marayun. Bayan na gama abin da ya kai ni, sai na nufi Hayin Rigasa.

Ban taɓa zuwa unguwar ba, da goggle map na yi amfani, ya dinga nuna min location ɗin.

Na ɗau lokaci sosai, kafin na shiga Rigasa, tun ina kan kwalta, har na fara shiga layuka, ina ƙare ma gidajen da suke wajen kallo.

Inda alamar danja na ya nuna, a daidai nan na yi parking, na fito a sanyaye.

Idanuna ne suka kan wani waje da ake siyar da abinci, ga ƙamshin doya da ƙwai duk ya cika wajen.

Na taka zuwa wajen, domin tambayar gidan Maman Abasiyya.

“Assalamu alaikum.” na faɗa bayan na tsallaka kwalbatin dake gabana.

Lokaci guda yarinyar dake aiki a cikin shagon ta ɗago ta zuba min ido, tana amsa sallamata cikin murmushi.

“Wassalamu alaikum....Bismillah Hajiya, shigo mana.” Yarinyar da za mu yi Sa'a ta faɗa, duk kuwa da ita ƙatuwa ce sosai, ga launin fatarta bakinta mai ƙyalli.

Murmushi dake kan fuskar yarinyar ne, yasa na shiga ciki, na zauna ina cewa.

“Sannu da aiki, tambaya na zo yi dan Allah.” Matashiyar ta aje min purewater tana zama daga gefe.

“To ina ji Hajiya, Allah yasa na sani.”

Sai da na sha ruwan saboda na irin karamcin da ta min sannan na ce.

“Gidan Maman Abasiyya nake nema, a nan kusa aka ce gidanta yake.”

“Hajiya ai ba'a daɗe ba, wani mai ƙaton mota ya ɗauke ta, ita da yaranta, na ji dai mutane suna cewa asibiti ya kai ta, ba za su jima ba za su dawo.”

“Ok, sun kusa awa nawa da tafiya!?.”

“Kaman minti 40 haka.”

Na jinjina kai.

“In babu damuwa ki zauna a nan har su dawo, ba wani matsala.” murmushi na yi mata.

“To shike nan, a kawo min abinci.” da sauri na ga ta nufa wajen zuba abincin.

Murmushi kawai nake ina kallon ta, yarinyar ta burgeni sosai.

Ta kawo min doya harda cokali.

Na yi murmushi ganin wanda ta zuba min da yawa.

“Na gode sosai, na ce ya sunan Madam ɗin ce.” dariya na ga ta yi.

“Madam a ina....”

“Eh mana, kina da babban restaurant kamar wanan ai da Hajiya za'a dinga kiranki......”

“Hajiya ki bar wasa, shagon Mamana ne, ba nawa ba, sunana Sakeenat.” ta faɗa tana wasa da ƙasan hijabinta.

Kallonta na yi da sauri.

“Da gaske!?.” ta ɗaga kai

“Sunan babu daɗi ko!?.” na zaro mata ido, har ina ɗan ƙwarewa.

Da sauri ta zo kusa da Ni tana jera min sannu, na ɗaga kai ina cewa.

“Ke kika sa na ƙware ai.”

“Wayyo ya ƙuri Hajiya, kinsa wata mai sunan ne!?.” na ɗaga mata kai.

“Sunana Sakeenat nima.” a tare muka yi ɗan dariya

“Hajiya da gaske kike wai.”

“Eh amma a gida da Adeelah nake amfani, na daɗe banga mai irin sunana ba.”

“Adeelah” ta furta a kan leɓanta masu launin pink kamar ta shafa abu akan su.

“Ban taɓa tunanin akwai masu kuɗi da irin sunana ba.” dariya na ɗan yi.

“Hmmm Sakeenat ai yana da ma'ana sosai, kinsan ma'anar ai!.” kai ta girgiza tana ɗan lumshe idanunta masu kama da sexy eyes.

Ni fa gaba ɗaya yarinyar ta burgeni sosai, komai nata special ne.

“Bansani ba gaskiya Hajiya.”

“Sakeenat na nufin natsuwa… kwanciyar hankali da salama a zuciya.”

“Da gaske?” na ɗaga mata kai.

“Da gaske mana. Sunan ma yana da kyau sosai.”

Ta ɗan yi shiru, sannan na ɗaga gira ina kallonsu.

“To daga yau sai ki riƙe, ma’anar Sakeenat Natsuwa......amma ni ya nake!?”

Murmushi na yi ganin ta ja baya kaɗan sannan ta buɗe baki ta fara rero waƙa tana siffanta kamannina.

“Doguwa ceee… faraaa… Mai fararen idanuwaaa… Tamkar hasken wataaa… Gira siririyyaa… kamar an zanaaa… Hanci kyakkyawaaa… tamkar zanen fensir Lebɓe masu kyauuu… suna fuzgan hankali. Fuska mai annuriii…

Gashin kanta baƙiii… ya zubo a kafadaaa… Murmushinta kuwaaa… sai ya sa zuciya ta tsaya! Tafiyarta sannu-sannuuu… kai cike da natsuwa Kallo ɗaya ya ishe kaaa…

Doguwa ceee… faraaa… Mai kyau daga kai har ƙafaaa… Idanuwa masu maganaaa… Murmushi mai ɗaukar hankaliiiiiii… Amma idan ta yi fushiii… Kai! Ka ɗauki hanya ka gudaaa!

Sakeenat ceee… mai natsuwaaa… Amma kyawunta babu natsuwarsaaa… Domin duk inda ta bayyanaaa… Sai idanu su bitaaa… Sai zuciya ta ce, ‘Wacece wannan kyakkyawaaaaaaaaaaaaaaaaarrrrrrr?’”

Ta ƙare da dariya, ta rufe bakinta da tafin hannunta, ni kuma na yi mata kallon mamaki kafin murmushi ya kubce min.

“Wow....wow.....wow, waƙar nan ya yi daɗi sosai, waya yi waƙar!?.” kai ta jinjina min.

“Ni na tsara kuma na rera.”

“Imagine......da mawaƙiya nake tare dama!?.” dariya ta yi sosai.

“A'a, ina dai tsayawa a cikin kai kawai.” yadda kasan mun daɗe da sanin juna, haka muka shiga hira.

Dama Ni bana ƙyamar mutum, haka muka sha hira da takwarata.

Muna cikin hirar ne, sai muka ji ƙarar mota ta tsaya a bakin shagon.

Sai ta ɗan leƙa waje, sai ta ga waccan baƙar motar da na gani ɗazu ta dawo.

“Yauwa ga motar nan Hajiya” Sai na kalli Sakeenat, na mata murmushi.

“tom zan tafi yanzu, sai mun sake haɗuwa, zan zo musamman na ɗauje ki dan a buga waƙar nan,” na faɗa ina murmushi.

Na miƙe, sannan na ciro kuɗi daga cikin jakata na miƙa mata dubu goma.

“Ga wannan.”

Ta zaro ido.

“Wayyo Hajiya, a’a mana! Ni kyauta na baki abincin wallahi!”

“Ki karɓa kawai.”

Ta karɓa da ƙyar, tana ta yi min godiya.

“Allah ya saka da alheri, Hajiya. Wallahi ban san me zan ce ba.”

“Ba komai.”

Na yi mata sallama sannan na fito daga shagon.

Ina fita kenan, sai na ga wani mutum ya nufo shagon, hakan ya ɗauke min hankali............

*Sakeenat*

Baba Mahaukaci ne.

Na kalleshi, sai na saki murmushi.

“Baba akwai labari yau.?”

Bai ce komai ba, sai ya zauna a kaman yadda ya saba. Ni kuma na koma cikin shagon, na kawo mana abincin da Hajiya takwarata ta bari.

Na zauna kusa da shi muka fara ci.

Tsabar nishaɗin da nake ciki, sai na fara ba shi labarin hirar da muka yi da Sakeenat, yadda muka gano cewa sunanmu ɗaya, har ma na kwaikwayi wasu daga cikin maganganunta.

Baba ya fashe da dariya kamar yana fahimtar abinda nake cewa

Ni ma na kama dariya.

Haka muka ci gaba da hira da dariya, kaman taɓaɓɓu..

Hankalina ya tsaya kacokan a kan hirarmu da dariyar da muke yi, ban ma san abin da ke faruwa a wajen shagon ba.

Ban san ya Sakeenat ta samu ganin Maman Abasiyya ba ko a'a, dan hankalina ya koma kan Baba gaba ɗaya ne..............✍️ End

> 🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥

╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*