CHAPTER 2️⃣0
by @prettys01
> Ban san ya Sakeenat ta samu ganin Maman Abasiyya ba ko a'a, dan hankalina ya koma kan Baba gaba ɗaya ne................
*Adeelah*
Murmushi ya kwanta a kan fuskata lokacin da na ga Maman Abasiyya ta fito daga cikin motar tare da ’ya’yanta guda biyu. Hannayensu ɗauke da kayan abinci da aka loda musu, wasu kuma ledojin mutumin ya sauke daga cikin motar.
Na tsaya ina kallonsu cikin farin ciki, har suka ratsa ta kusa da ni suka shiga cikin gidan.
Na koma nawa motar, sannan na fito da ledojin da na siya dan Maman Abasiyya, na rufa musu baya.
Sallama nayi a tsakar gidan nasu, inda na iske Maman Abasiyya ta tsugunna tana ma wani matashi addu'a, kamar ta ara baki, har da hawaye.
Ban motsa daga inda nake ba, har sai da idanuna suka sauka kan wani matashi.
Tabbas kyakkyawa ne ajin farko.
murmushi ɗauke a fuskarsa. Daga yanayin shigarsa da tsayuwarsa kawai, za ka fahimci cewa ba ƙaramin mutum ba ne.
Sanye yake manyan kaya, babbar riga da wando masu kyau, cikin launi sararin samaniya, wacce ta yi masa kyau sosai. Babu hula akansa, sai baƙin gashin kansa kadan da yake kwance. Daga sama har ƙasa matsahin saurayi ya haɗu sosai, a karo na farko da wani ya burgeni kenan.
Na lura hankalinsu gaba ɗaya baya kai na, sai na raɓa na aje ledojin sannan na juya na fita, alhamdulillah abinda nake fatan ganin ta samu, an yi mata , to babu bukatar na yi magana da ita.
Mota na shiga sannan na kunna tare da fara tafiya.
Karatu na kunna, ina driving ina sauraron karatun, a daidai inda zan fita daga rigasa na hau babbar titi, na yi parking ganin wani mutum tsaye ya dafa poleware da hannu ɗaya, haka kuma ya dage zuciyarsa.
Ba shiri na fito daga mota, ga wajen babu mutane sosai.
Ina isa kusa da shi, kafin na furta abinda ke bakina, naga an kama Mutumin, sai bawan Allahn ya yi baya ya faɗa jikin wani.
Na yi sauri na kalla wanda ke tsaye gefena.
Mamaki ya bayyana akan fuskata, saboda wannan matashin ne tsaye gabana Yana taimaka ma wannan mutumin.
Murmushi ya ƙwace min, na ja baya kaɗan, lokacin da shi kuma ya nufa motarsa da mutumin, ya sa shi a ciki.
Ya bar wajen da gudu.
Sai na tsinci kai na da rufa masa baya.
A asibitin dake kusa da wajen, ya shiga da motarsa.
Ni kuma na sauya hanya, ina mai jin nishaɗi a cikin rai na, bansan waye wannan ba, amma tabbas ya tafi da tunanina kashi 40, ba dan komai ba sai dan ganin kirkinsa ya bayyana............
> Abinda ba ta sa ni ba shine, yanzu sabuwar ƙofar rayuwarta za ta buɗe, yanzu ƙaddarar soyayyar ta za ta fara, soyayya mai zarfi, ƙaddara mai raɗadi, wanda yake daure da BANBANCIN RA'AYI, Ƙaddarar da zai rushe komai, kafin abubuwa su daidaita...................
MASARAUTAR AL-JAWHARA — SASHEN SARAUNIYA RANIA
“Na farko, mu fara tabbatar da cewa akwai cikin da ake maganarsa.....idan har hakan ya tabbatar, sai mu san yadda zamu yi a lalata shi gaba ɗaya........ko na biyu.” Ayla ta lumshe ido sannan ta ce.
“Ko mu bari ta haihu, idan har ɗa namiji ne, sai mu shafe rayuwarsa, idan mace ce sai mu ba ta waje......” Sarauniya Rania ta jinjina kai.
“Hakane, amma ba zan ɗauka cin fuska daga wajen mai martaba akan wannan al'amarin, sanin kanku ne, rabon da mu haihu shekara 18 kenan, sai a yanzu ciki zai bayya a jikin Sarah.....hmmmmm wallahi da sake.” tana kai nan ta haye sama cikin izza.
“Oh Ummee tana damun kanta da yawa akan maganar mulki, bayan ainiyin karagar ta mijina ne na gobe.” Ayla ta faɗa tana murmushi.
Jana ta itama murmushi ta yi, amma na ta na kallon haukan Ayla take yi, wacce ta makance akan soyayyar Yarima Laith, mutum da ko magana bai cika yi ba, ita har ga Allah bata son shi, a ganinta jiji da kansa yayi yawa, ga shegen miskilanci.
Ayla ta shafa dogon baƙin Gashinta mai yawa, wanda ya zuba har baya, ta juya ta fara takawa a hankali ta nufa kofa.
“Ayla ina zuwa!?.” Cewan Noor dake latsa waya.
Ayla bata juyo ba tace.
“Wajen sirikata zan je, ko da matsala ne.....” kai ta girgiza itama tana murmushi.
“A dawo lafiya.”
Ayla ta fita, fadawa suka fara taka mata har zuwa sashen Sarauniya Malikha.
Ayla ta shiga sashen Sarauniya Malikha, inda fadawa suka buɗe mata hanya cikin girmamawa.
Tsarin bangaren ya kasance na musamman, mai cike da alfarma da nutsuwar gidan sarauta.
Dogayen ginshiƙai ne suka jere a gefen hallway ɗin, an kawata su da zane-zanen Larabawa masu ƙayatarwa. Bangon yana ɗauke da manyan fitilu masu haske, yayin da ƙasan yake shimfiɗe da wani katon carpet mai laushi, wanda aka zana shi da kyawawan ƙirar Gabas ta Tsakiya. A gefen bango kuma akwai manyan tukwane ɗauke da furanni masu ƙamshi.
Ayla ta taka a hankali har ta isa ƙofar babban parlourn Sarauniya Malikha.
Da ta shiga, wani irin yanayi na nutsuwa da alfarma ya mamaye wajen. Babban ɗakin ne mai faɗi, kujerun zama masu laushi suka kewaye tsakiyar ɗakin, yayin da wata babbar chandelier mai ƙyalli take rataye a saman rufin. Labulen da suka rufe manyan tagogin sun kasance masu nauyi da kyau, suna ƙara wa ɗakin kwarjini.
A gefe guda akwai babban talabijin ɗin bango, inda ake kallon labaran duniya a tashar Al Arabiya, ɗaya daga cikin shahararrun tashoshin labarai na Larabawa.
Sarauniya Malikha tana zaune cikin nutsuwa a kan kujera hankalinta yana kan talabijin. Tana sanye da wata doguwar riga mai kyau wacce ta dace da matsayin sarauniya, yayin da wani siririn mayafi ya lullube kanta cikin mutunci.
Da Ayla ta shigo, wata daga cikin fadawan ta sanar da ita.
“Ya Sarauniya, Gimbiya Ayla ta zo”
Sarauniya Malikha ta ɗago idanunta daga talabijin, sannan murmushi mai sanyaya rai ya bayyana a fuskarta.
“Ahlan wa sahlan, Ayla.”
Ayla ta yi murmushi, ta nufi wajen sarauniyar cikin ladabi.
“Assalamu alaikum, Hajiya.”
“Wa alaikumus salam, ya habibati.”
Ayla ta durƙusa kaɗan cikin girmamawa, sannan ta sumbaci hannun Sarauniya Malikha.
Hajiya ta shafa kanta cikin ƙauna.
“To yaya kike? Lafiya?”
“Alhamdulillah, ina lafiya. Ke fa, Hajiya?”
“Ni ma lafiya, Alhamdulillah. Zauna.”
Take aka cika gaban Ayla da abubuwan taɓawa a baki. Ayla ta zauna kusa da ita, tana kallon talabijin na ɗan lokaci kafin ta mayar da hankalinta kan Hajiya.
Sarauniya Malikha ta kalle ta da murmushi.
“Kin zo ne domin mu yi hira ne, ko akwai wani abu da kike so?”
Ayla ta yi ƙaramar dariya, sannan ta gyara zamanta.
“A'a Hajiya, kawai na zo ne in gaida ki.”
Sarauniya Malikha ta ɗan kalleta da murmushi a fuskarta.
“To, na gode sosai, a cikin ƴam matan gidan nan, kin fi kowa son zumunci, Allah ya miki albarka.”
“Ameen, Hajiya”
Ayla ta amsa, tana mai saƙa abubuwa da yawa a cikin zuciyarsa.
Bayan sun jima suna hira, Ayla ta mata sallama sannan ta wuce.
Hajiya ta bi ta da ido har ta ɓace, tana son Ayla sosai, yarinyar akwai hankali, hakan yasa a cikin ranta take fatan wani abu ya faru a nan gaba, yadda za ta ƙara samun kusanci da Ayla, a ganinta a wannan zamanin samun irin Ayla abu ne mai matuƙar wahala.
“Halinku ya banbanta sosai da Yayarki Sarauniya Rania, hmmm Allah ya Miki albarka.” da haka ta mai da idnaunta kan tv.................
*SASHEN SARAUNIYA SARAH*
Sarauniya Sarah tana zaune a tsakiyar teburin cin abinci, tare da ’ya’yanta mata guda biyu, Meerah da Leenah.
Su biyun kyawawan ’yan matan Al-Jawhara ne, masu kamanceceniya da juna dan tagwaye, Meerah, wacce ita ce babba, ta fi Leenah ɗan cika jiki, yayin da Leenah ta kasance siririya kuma doguwa, amma a fuska suna kama sosai. Ƴam mata masu shekaru 18, tun daga su Sarauniya Sarah ba ta sake haihuwa ba, ko ta samu ciki sai ya zube, bayan an yi haka kaman sau uku, sai ta dena samun cikin, ta za ci ba za ta sake haihuwa ba, sai a yanzu kuma Allah ya sa ta samu juna biyu.
Teburin cin abincin kuwa ya kasance cike da kayan marmari da abincin Larabawa iri-iri. Akwai farfesun nama, shinkafa mai ƙamshi wacce aka yi wa ado da gyada da zabibi, hummus mai laushi, salatin kayan lambu masu launuka daban-daban, gurasa mai laushi, da kwanon miya mai ɗumi a gefe.
Kowacce tana cin abincinta cikin nutsuwa, ba hayaniya, sai sautin cokula da faranti kawai ke ratsa ɗakin.
Sarauniya Sarah tana ɗan ɗaga kai lokaci-lokaci tana kallon ’ya’yanta, tana murmushi cikin jin daɗin kasancewarsu tare. Meerah kuwa tana cin abincinta a hankalinta rabi na kan wayarta, yayin da Leenah ke ɗan ɗaukar abinci kaɗan-kaɗan, tana sauraron hirar da mahaifiyarta ke yi.
Sai kawai—
TRRRR… TRRRR…
Sautin wayar Meerah ya katse shirun da ke ɗakin.
Meerah ta ɗago kai.
Ta kalli wayar da ke gefenta.
Ta bar shi ya yi ringing har ya katse.
Sai kuma aka sake kira.
TRRRR… TRRRR…
Sarauniya Sarah ta ɗago idanunta tana kallon ɗiyarta.
Kafin Meerah ta ɗauki wayar, kiran ya sake katsewa.
Sai aka sake kira a karo na uku.
Meerah ta ɗan daure fuska, ta kalli wayar, sannan ta kalli Umma.
Kiran ya sake dawowa a karo na huɗu.
Wannan karon Meerah ta ɗauki wayar, ta katse kiran kai tsaye.
Sai ta ajiye wayar a hankali a kan tebur, sannan ta ɗaga idanunta zuwa ga mahaifiyarta.
Sarauniya Sarah ta kalleta cikin nutsuwa.
“Meerah…”
Meerah ta haɗiye abincin da ke bakinta, sannan ta ce.
“Umma?”
Sarauniyar ta ɗan yi shiru tana kallon wayar, kafin ta tambaya cikin sanyin murya,
“Waye yake ta kiranki haka?”
Meerah ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta sauke idanunta kan farantin abincin gabanta.
“Umma… ba kowa.”
“Ba kowa ?” Sarauniya Sarah ta maimaita, tana ɗan murmushi.
“Classmate ɗinta ce.” ta faɗa tana tura baki gaba.
“To, me ya sa take kiranki a wannan lokacin.?”
Meerah ta fara kame-kame.
“Ni… uhmmmmm.....dai… wataƙila tana son ta tambaye ni wani abu ne.”
“Wane irin abu?”
“Umma, ban sani ba. Ai… ba wani abu ba ne dan ta kira ni.”
Sarauniya Sarah ta zuba mata ido, tana ƙoƙarin fahimtar abin da take ɓoyewa.
Kafin ta sake tambayarta, wayar Meerah ta sake ƙara.
TRRRR… TRRRR…
Meerah ta firgita kaɗan.
Da sauri ta miƙe tsaye, ta ɗauki wayarta.
“Umma, zan shiga ɗaki.”
“Meerah, zo ki—”
Kafin Sarauniya Sarah ta ƙarasa maganar, Meerah ta riga ta fara tafiya.
“Meerah!”
Ta kira ta, amma Meerah ba ta juyo ba.
Sarauniya Sarah ta bita da kallo har ta ɓace daga ƙofar, sannan ta girgiza kai a hankali.
“Lallai Meerah… kin girma.”
Ta yi murmushi kaɗan.
“Yanzu soyayya kika fara ko mene?”
Ta jingina da kujerarta, sannan ta ɗan yi dariya.
“Ki zo ki min bayani, ke yarinya.”
Leenah ta kalla Umma ta ce.
“Umma ina so ki yi ma Noor magana, ta dena shiga harkata a makaranta, bana so......kowa kawai ya kama kansa.” Umma ta yi murmushi.
“Zan mata magana, ci abinci dai.”..........
Meerah kuwa tana shiga babban ɗakinsu, ta rufe ƙofar.
Ɗakin ya kasance mai faɗi da kyau, an kawata shi da kayan alfarma masu ƙawa irin na gidan sarauta. Babban gadon yana tsakiyar ɗakin, an shimfiɗa shi da fararen zanen gado, yayin da fitilun bango masu haske a hankali suka ba ɗakin wani irin yanayi na nutsuwa.
Meerah ta zauna a gefen gadon, ta kalli wayarta.
Kiran da ta katse yana nan a saman screen ɗin.
Ta ja dogon numfashi, sannan ta yi gyarar murya.
Take wani kiran ya sake shigowa, sai ta ɗaga..
“Hello?”
Sai muryar wani saurayi ta fito daga ɗayan ɓangaren.
Meerah ta ɗan lumshe ido.
“Ya Zain… ina tare da Umma ne fa…” daga cikin wayar ta ji ya sauke ajiyar zuciya.
“Meerah ina son ganin ki, yanzu, ki fito.” Meerah ta marairaice fuska.
“Ta ya zan zo sashen Ummee, kai kasan hakan ganganci ne.”
“Ai na sani, ina ta bayan sashen Hajiya, ki zo nan kawai.”
“Okay Ya Zain.” da haka ta katse wayar.
Gaban mirrow ta nufa, ta ɗan gyara rigarta, bata son ta sauya kaya Umma ta gane, hakan yasa ta bar na jikinta.
Ta ɗan fesa turare kaɗan sannan ta nufa kofa, ta buɗe ta fita.
Kauda kai ta yi, ta nufa babban kofa kai tsaye, tana tafiya cikin izzar dake jinin mutanen Al-jawhari gaba ɗaya.
“Ke ina za ki je!?.” Muryan Umma ya daki kunnuwarta.
Meerah ta tsaya tana ɗan ya mutsa fuska, sannan ta juyi ta kalla Umma, a hankali ta buɗe baki ta ce.......................
*Sakeenat*
Mai mashin ya faka a dai-dai bakin gidan mu. Na sauka a mashina biya shi kuɗinsa.
Akwai matasa dake zaune a wajen, ko kallonsu banyi ba, na shiga gidan mu.
Yau ma rigima ake yi, na girgiza kawai na wuce ciki, kar na tsaya ta kwaɓe da Ni.
Ina shiga parlour na iske Amrah zaune ta haɗa kafa ɗaya kan ɗaya tana latsa waya.
Ban kulata ba, na nufa ɗakin mu, sai dai mai, ina zuwa na ga a kulle, an sanya key.
Na juyo na kalla Amrah. “Waya kulle ɗakin nan!?.” Ta yi banza da Ni.
“Amrah magana nake, waya kulle ɗakin nan.” sai ta ɗago kai, ta min kallon banza.
“Ɗaki na dai, dan yanzu kayana ne kawai a ciki.....” mamaki ya bayya a fuskata.
“Ban gane ba.” ta ɗaga gira.
“Ƙwarai, sakamakon laifin da kika yi ma Garkuwar mata kenan, an kwashe kayanki, an mai da tsohon kitchen.”
“Zance kike yi Amrah, kawai dan na yi laifi sai a mai da Ni tsohon kitchen, ta ya mutum zai kwana a ciki.........”
“Ni za ki tambaya ba ita ba.” na juya da sauri jin Muryar Mama.
“Mama da....gaske can zan koma da kwana..... kai ta daga tana tsaye daga bakin ƙofa.
“A can za ki dinga kwana har sai na ga kamanninki sun sauya tukun.” na durgushe a ƙasa ina girgiza mata kai
“Mama a'a dan Allah, ki min ko wani hukunci amma banda wanna, ki duke Ni.....ki mare Ni......ki min komai, amma dan Allah kar ki sa na kwana a wannan ɗakin.” na fashe da kuka abunku da mai saurin kuka.
Mama ta matso kusa da Ni, jakkar kuɗinta ta amsa, ta koma gefe ta hau ƙirgawa.
Take fuskantar ta washe da farin ciki, ganin na yi cikini sosai, Allah ya taimake Ni duk abinda na dafa ya ƙare, ga kuma dubu goman da Hajiya Sakeenat ta bani, na dai san na ɗau dubu ɗaya a cikin kuɗin na sa a hula na.
“Ah Masha Allah, an yi kasuwa yau sosai.” cikin kuka nace.
“Na ninka yadda nake sawa ne, sai kuma wata ta bani kyautar dubu goma, bayan ta siya abinci.” Mama ta kalleni da ƙyau.
“Hmmm ina sauran kuɗin da kika ɓoye, nasan ba shi ke nan ba ko.....” ta faɗa dan dakar ruwan ciki na, tasan ko mai zance gaskiya ne.
Hannu nasa cikin hula na ciro dubu ɗayan.
“Wannan kawai na ɗauka, shima saboda ina so na siya biredi gobe ne.” Mama ta amsa dubu dayan.
“Hmmm sai dai uban biredi, kuma a wajen za ki kwana, da na wata biyu za ki yi, amma saboda kin faranta min, kwana goma kawai za ki yi a can.” da haka ta tashi ta shige ɗakinta.
Na share hawayena, na miƙe na fita, ina jin duk babu daɗi.
Kitchen ɗin ba'a komai a ciki, sai dai akwai tarkacen kayan kitchen tsofaffi daga gefe.
Na ɗan ji daɗi ganin kofar shiga yana da kyau, akwai sakata, amma babu window, ya ɓalle.
Na shiga ina kallon yarda aka watsa min kayana a ciki, hakan ya tabbata a nan dai zan kwana.
Na kwashe su gefe, na hau gyaran ɗakin.
Yayi datti, yayi ƙura sosai, na fara shara bayan na tsoshe hanci na saboda ƙura.
Bayan na kwashe sharan na fita, na zuba a kwandon shara.
Hankalina gaba ɗaya yana kan yadda zan kwana cikin wannan ɗakin.
ban lura da wanke ke zaune a tsakar gida ba, cikin jerin ƴam mata da samari suna wasan caca ba, na shige ɗakinta.
Bosho ya yi murmushin mugunta, yana kai sigari bakinsa ya zuƙa, ya busar da hayaƙin cike da bariki, idanunsa biyu yana kan Sakeenat dake hange ta cikin window................✍️ End
> Daga yau na buɗe payment group, ku yi ku shiga kafin mu kai ƙarshen free pages, kunsan sai na kai inda za ka tsumu, sai na katse muku labari, waɗanda sukai payment da wuri kuwa, update Babu tsayawa.
Shiga group 300 ne Only 8126151523
Idan kuma na gama complete is 500, sauki daga Allah sai littafin Pretty SK, ba cika kuɗi ga ma'ana ga daɗi.
Har yanzu bamu fara komai ba, labarin bai hau layin da na gina labarin ba, ban fara komai ba, ku shirya kawai ladies 😀, SAKEENAT ɗin Ayyyyy 🫠.
╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*