SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER 2️⃣1

by @prettys01

> Bosho ya yi murmushin mugunta, yana kai sigari bakinsa ya zuƙa, ya busar da hayaƙin cike da bariki, idanunsa biyu yana kan Sakeenat dake hange ta cikin window...............

Bayan na gama gyara ɗakin, na shimfiɗa katifa ta a ƙasa, na fito na ɗau buta, ruwa na zuba a na tsugunna daga gefe na fara alwala, yanzu tsakar gidan a cike yake da mata sosai, mazan duk sun fita, hira suke yi, ana yi ana tafa hannu.

“Ahanye luwai, Alhaji Naira sati mai zuwa zai shigo Kaduna, ya kuma sanar ma Garkuwar mata cewan, gaba ɗaya matan gidan nan, mu yi ado, mu yi kwalliya, idan ya zo zai zaɓa wacce ya ƙasa.” Hawanzee ta faɗa cikin jin daɗi.

Take matan da suke wajen suka hau ihu da shewa

“Ku ce za ta fashe, Allah yasa Ni zai zaɓa.”

“Dalla Ashanty, mai zai yi mai bleaching.....dube Ni daga sama har ƙasa, babu ma kusa wallahi.” Rufaida ta faɗa tana jujjuya mazaune.

Amrah ta iso wajen tana cewa.

“Hmmm magana ake ta sabon jini, haka kuma farar mace alkyabbar mata.” sai aka sanya wani ihu.

Rukky ta miƙe tsaye, tana cewa.

“Hmmmm yara kenan, an faɗa muku, sura da ƙyau shi ke sanya namijin bariki ya ƙyasa.......” sai ta girgiza kai.

“Suna can da ƙyawawan mata, masu aji da class, suka zo nan dan neman wacce ta waye, ta kuma goge akan harkan bariki.......dan haka ku zuba ido kusha kallo...........da jan hankali zan siye zuciyarsa.”

“Allah ya ba mai rabo sa'a, ko ma wa ya zaɓa, duk dai zamu dan kwala arziƙi, dan Alhaji Naira, yana da kuɗin da bai san adadin shi ba.” cewan wata a cikinsu.

Ni dai har na idar da sallah, maganar Alhaji Naira suke yi, tun ana yi har ya kusa zama rigima, sai da Mama ta fito ta ce musu.

“Bansan shirme, ku ci gaba da haukar na ku, wallahi sai na hana shi zuwa.......ku da zaku haɗe kanku, idan ya zo, ya rasa wacce zai ɗauka, har ta kai ya kwasa biyar zuƙaƙa a cikin ku, ai duk ƙaruwar kanmu ne, kowa dai ya yi nasa kissan, Allah ya ba ku nasara.” suka yi ihun jin daɗin.

“Sai da ke Garkuwar mu, Allah ya ƙara lafiya.” suka amsa gaba ɗayansu da Ameen.

Rufaida ta ce.

“In dai Ni ya tsaɓa, to Garkuwar mata sai na siya mana babban gida, na siyan miki mota, Nima na siya ta kai na.” Garkuwar mata ta yi murmushi sannan ta koma ɗaki.

Ina daga kwance nake sauransu, har barci ya fara ɗaukana.

Ina da nauyin barci, dan har sace Ni za'a iya yi muddin ina barci.

A hankali nake sauke ajiyan zuciya, ina barci ina sake duƙunƙune jikina, saboda akwai sanyi wajen sosai.

Can ɗakin mu kuwa, Amrah da Bosho suna ta sha'aninsu, a'uzubillahi yadda kasan ma'aurata, ko ince kusan ko wani ɗaki abinda ke faruwa kenan.

Bayan sun gama alfashan, Bosho bai fito daga ɗakin ba, sai da ya tabbar Amrah ta yi barci.

Ya raɓa a hankali ya bar ɗakin, bai tsaya a ko ina ba, sai wajen windwon ɗakina.

Ya hau ya dirko cikin ɗakin. Murmushi ya wanke mai fuska, yayinda ya zauna gefena ya zuba min ido kamar maye.

A hankali kuma ya kai hannunsa kan ƙafafuna ya fara shafa yana lumshe ido, shi har ga Allah yana son kasancewa da Ni ko da sau ɗaya ne a rayuwarsa.

Ban san tsawon lokacin da ya ɗauka yana shafa jikina ba, har ya gama ya fita, da cewan sai ya fara shawo kaina sai mai afkuwa ya faru............

*Adeelah*

Bayan kwana biyu da haɗuwa da mutumin da ko sunansa ban sani ba, na yi iya ƙoƙarina wajen daina tunaninsa amma gaskiya abin ya gagare ni.

Kullum sai na tsinci kaina ina tunanin murmushinsa, yanayin kallonsa da kuma yadda yake da zuciya mai ƙyau.

A rana ta uku, ina zaune a wajen hutawa da ke gefen department ɗinmu. Na buɗe system ɗina, ina karatu cikin nutsuwa.

Kawai sai na ji an zauna kusa da ni.

Da sauri na ɗago idanuna da suke cikin farin glass.

Sai kawai na iske Doctor Ahmad yana kallona, yana sakar min murmushi.

Ina masa ƙyau sosai, a haka ma kullum da hijabi yake ganina, amma ina tafiya da imaninsa.

Na ɗan haɗe fuska ina kallonsa da kyau.

“Babyna ya kike!?.” na sauke ajiyar zuciya.

“Assalamu alaikum.” sai ya yi murmushi.

“Wassalamu alaikum, Adeelah.............Babyna wallahi kina burgeni sosai.”

“Hmmm na gode, me ka zo yi a nan?” na tambaya cikin rashin fahimta.

Ya yi murmushi.

“Kin san tun ranar nan nake neman damar yin magana da ke, amma kin ƙu ɗaukan kira na, kuma Ni ba zan sake ba, na damu sosai da rashin jin muryarki?”

“Maganar nan ta wuce”

Na koma kallon system ɗina.

“Doctor, ina karatu yanzu.”

“Na gani ai”

“To ka bar ni in yi.”

“Zan tafi, amma ki amsa min tambaya ɗaya tak.” ya faɗa da sigan roƙo.

Na ɗago kai.

“Wace tambaya?”

“Idan na kira ki za ki ɗauka?”

“uhmm.”

“Na gode sosai.”

Ya ɗan yi shiru, sannan ya ce, “Saura abu guda kuma.” ban kalleshi ba na ce.

“ina ji?”

Ya kalle ni na ɗan lokaci kafin ya ce:

“Ina son ki ba ni dama.”

Ya yi shiru.

“Damar me?”

“Damar in nuna miki cewa abin da nake ji a kanki ba wasa ba ne”

Na kalleshi na ɗan daƙiƙu. Kafin na yi saurin mayar da hankalina kan system.

“Doctor Ahmad, kar ka fara wannan maganar.....”

“Me na fara?”

“Wannan maganar.”

“Amma gaskiya nake faɗa.”

“Ni kuma bana so.”

Ya yi murmushi, yana zama kusa da Ni.

“Kin san abu ɗaya?”

“A'a?”

“I love you........ Me yasa baki son maganar soyayyar mu ne.....wallahi ina sonki har cikin zuciyata..”

“Hmmm na ji to.”

Na kalle shi da gefen ido ganin yana murmushi.

“Menene abin da kake shiryawa ne, wannan murmushi yana da ma'ana.” ya ɗaga kai

“Abin da nake shiryawa abu ɗaya ne.”

“Menene?”

“Zan ci gaba da neman amsarki har sai kin amince da soyayya ta”

Na girgiza kai kaɗan

“Allah ya taimake ka.”

Ya kalle ni yana murmushi.

“Amin.”

Kafin na yi magana, sai ga Safraz Ball Star, ya nufo mu rai a ɓace. Tun daga yadda yake tafiya, za ka gane ransa baya masa daɗi.

Yau gajeren wando ne jikinsa, sai T-shirt ɗin da ke ɗauke da sunansa a jiki. Da alama daga wajen parking ya hango ni tare da wani.

Da ya iso gabanmu, ya tsaya yana kallon Doctor Ahmad cikin ɓacin rai.

“Waye kai? Kuma a kan wani dalili za ka zauna kusa da budurwata haka?”

Doctor Ahmad ya ɗan ɗaga kafaɗa, yana kallonsa cikin nutsuwa.

“Budurwarka?”

Safraz ya ƙara haɗe fuska.

“Eh, budurwata. Ko kana da matsala ne?”

Doctor Ahmad ya yi ɗan murmushi.

“Ba na da matsala. Amma kai ma baka waye Ni ba.”

“Hmmm bana buƙatar sani, Abin da ya kamata ka sani shi ne, ka tashi daga nan ba muhallinka bane.”

Doctor Ahmad ya kalli inda nake, sannan ya dawo da kallonsa gare shi.

“Me ya sa?”

“Saboda na ce.”

“Wannan ba amsa ba ne, amma ita wacce kake magana akanta, wacce zan aure ce”

Safraz ya ɗan matsa gaba.

“Shut up.”

Doctor Ahmad ya gyara zamansa cikin ko in kula.

Ganin irin shariyar da ya yi mai ne, yasa ya kama kwalar rigarsa.

“Safraz!”

Sai na faɗi sunansa a karon farko cikin ɗan hassala.

“Ki bar ni, Adeelah. Wannan tsakanina da shi ne.”

Doctor Ahmad ya ɗan yi murmushi.

“Baby karki damu, babu abinda ya isa ya min..”

Safraz ya juyo ya kalle shi.

“Kar ka sake kiranta da wannan sunan.”

“An ce Babyn....Me za ka yi?”

Safraz ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, sannan ya ce cikin ɓacin rai:

“Zan maka illa idan ka sake furta hakan.”

Suka sake yin shiru, kowannensu yana kallon ɗayan cikin fushi.

Ni kuwa ban ce komai ba.

Na zuba musu ido kawai, ina mamakin yadda suke abu kaman yara, Ni dai ban ce ga wanda nake so, balle suce amma sai rigima suke yi.

Da na ga hayaniyar tasu ta fara damuna, sai kawai na rufe system ɗina na miƙe tsaye.

“Ku ci gaba da hayaniyar ku.”

Safraz ya juyo ya kalle ni.

“Adeelah, tsaya mana.”

Ban tsaya ba.

Doctor Ahmad ma ya kira sunana, amma ban waiwaya ba.

Na ɗauki jakata na bar musu wajen gaba ɗaya, ina jin haushin yadda suka mayar da wurin hutawa kamar filin gardama.

A raina kuwa abu ɗaya nake cewa.

“Soyayya ai ba hauka bane..”

Ban san wanne ya fi bani haushi ba—Safraz da ya zo da rigima, ko Doctor Ahmad da ya ƙi haƙura ya bar shi.

Amma abu ɗaya na sani: ba zan zauna ina kallon su suna gardama a kaina ba.

Ban san yadda suka ƙare ba, domin na bar su a wajen hutawar. Ni dai na shiga class na zauna, ina ƙoƙarin mayar da hankalina kan system.

Bayan ɗan lokaci, sai wani saurayi ya biyo ni baya na ya shigo ajin. Ya tsaya kusa da desk ɗina sannan ya yi min sallama.

“Assalamu alaikum.” na ɗago na kalleshi ina amsawa.

“Wa alaikumussalam.”

“Uhmmm sunana Bashir, I’m studying Computer Science..”

Na ɗan gyada kai.

“Okay, fatan lafiya, Malam Bashir.”

Ya yi murmushi.

“Lafiya lau. Dama akwai wani abu ne nake son magana da ke ne.”

Na rufe littafin da ke gabana.

“Tom ina ji?”

Ya ɗan yi shiru kafin ya ce:

“Dama number ki nake so, please. If you don’t mind.”

Na kalle shi na ƴan daƙiƙu.

Umm“uhm but why?”

Ya sauke numfashi a natse, Ni kuma ina ƙarantar yanayinsa.

“Saboda ina sonki… kuma wallahi da—”

Ban san me zai ƙara cewa ba, domin kafin ya ƙarasa maganar, sai na ji sautin mari!

Na firgita kaɗan.

Kafin in fahimci abin da ke faruwa, sai na ga Safraz a gabansa.

Hankalin kowa da ke cikin class ɗin ya dawo kansu.

“Safraz!”

Amma bai saurare ni ba.

Ya sake kai hannu yana ƙoƙarin dukansa, Bashir kuwa ya fara kare kansa.

“Please! Ka daina!”

Safraz ya yi masa tsawa.

“Uban wa ya baka izinin magana da ita.........”

“Babu kowa, Kuma Ni sonta nake yi da gaske.” ya faɗa cikin ƙarfin hali.

A zafafe Safraz ya sake kama wiyar rigarsa. “Karka kuskura ka sake cewa kana son ta!”

Bashir ya ja da baya kaɗan saboda yadda yayi magana.

Na bugi desk ɗina da ƙarfi na miƙe tsaye.

“Safraz.....What the hell is wrong with you?!”

Nan take ya tsaya ya kallo na.

Fuskarsa cike da fushi.

“Akan me yasa kowa zai so abin da nake so?”

Na ɗan zuba masa ido.

“Kenan babu mai ƙyancin ya so ni?”

“Eh.”

“Why?”

Ya matso kusa da desk ɗina, idonsa a kaina.

“Because you're mine”

Na yi murmushin takaici.

“Safraz…”

Ya yi shiru.

Na juya wurin Bashir.

“Amma kai Malam Bashir, If you really want my number......…”

Safraz ya sake kallona.

Ni kuwa na ci gaba cikin nutsuwa.

“Zan faɗa maka sau biyu. Ka haddace ko ka rubuta”

Na faɗi number ɗina a hankali sau ɗaya, sannan na sake maimaita shi.

Bashir ya ɗauko wayarsa yana rubutawa.

Na gama, sannan na kalli Safraz sai ya yi murmushi jin dadi.

“Learn to respect people. Hakan shi ne mutuntaka. You don't have the right to decide who can talk to me..... kai kanka ban gama tantance alaƙar dake tsakanina da kai ba, ba dan na baka number shi ke nuna na amince maka ba, na baka ne saboda cancanta..”

Safraz ya yi shiru.

Na tattara takarduna da littattafaina na saka su cikin jakka.

Ban ƙara cewa komai ba.

Na wuce ta gabansa na fita daga ajin.

Na nufi motata, na shiga, sannan na kunna ta, ban ɓata lokaci ba na bar makarantar gaba ɗaya.

Ban waiwaya ba

Amma a zuciyata, maganar Safraz ce kawai take ta maimaituwa:

“Because you're mine.” na furta a fili, leɓena na ɗan taune kaɗan, na kuma shafa gefena fuskanta a hankali.

“Wai me yake damun wannan mutumin ne?” na faɗa ni kaɗai, ganin babu mai bani amsa, yasa na aje maganarsa gaba ɗaya, na mai da hankali kan hanya.

Na isa gida bayan wani lokaci. Da na shiga, na tarar da Mom a falo.

Bayan na mata sallama ta amsa cikin sakin fuska.

“Kin dawo da wuri yau.... fatan lafiya?”

Na ajiye jakarta kan kujera a natse.

“Eh Mom. Na gaji ne kawai.”

Ta kalle ni da kyau.

“Lafiya kuwa? Fuskarki kamar kina cikin damuwa.”

Na yi murmushi.

“Nothing serious, Mom. Ina lafiya.”

Ta gyada kai, amma daga kallonta na gane ba ta yarda da amsar da na ba ta ba.

Na nufi ɗakina.

Ina shiga, sai wayata ta fara ringing.

Na duba screen ɗin.

Safraz.

Na yi shiru ina kallon wayar tana ringing.

“Yanzu kuma menene yake so?”

Na bar wayar ta yi ringing har ta katse.

Bayan wasu seconds sai message ya shigo.

Safraz: “We need to talk.”

Na karanta, na yi rolling eyes.

Na ajiye wayar.

Kafin minti ɗaya , wani message ɗin ya sake shigowa.

Safraz: “Please, Adeelah. Just give me five minutes.”

Na ɗan yi shiru.

A ƙarshe na rubuta masa:

“I have nothing to say to you.”

Nan take ya amsa.

“But I have a lot to say to you.”

Na kalli message ɗin na ɗan yi murmushi.

Sai na kashe screen ɗin wayar, na kwanta kan gado.

Amma duk da haushin da nake ji, ban san dalilin da ya sa zuciyata ta kasa daina tunanin maganarsa ba.

“Because you're mine…”

Na girgiza kai da sauri.

“Allah kamin zaɓi da miji na gari.” take fuskar Bawan Allahn nan ta bayyana a cikin idanuna kaman hasken walƙiya, sai na rintse ido ina cewa.

“Waye shi? A ina zan sake ganinsa!?.......” na yi sauri kawar da tunanin, ina mamakin kaina. Na gaji babu laifi, take kuwa barci ya ɗauke Ni mai daɗi...............✍️ End

╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*