SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER 2️⃣ 2

by @prettys01

> “Waye shi? A ina zan sake ganinsa!?.......” na yi sauri kawar da tunanin, ina mamakin kaina. Na gaji babu laifi, take kuwa barci ya ɗauke Ni mai daɗi.................

Ban farka ba sai wajen ƙarfe biyu, na buɗe idanuna jin an kunna hasken ɗakin.

A hankali idanuna suka sauka kan Nuseey dake tsaye ta zuba min ido.

Na kalla agogo, ganin karfe biyu, sai na tashi na zauna ina ɗan salati.

“Madam kin tashi lafiya!?.” na ɗaga mata kai.

“Ai na shigo ya kai sau uku kina barci.” na yi murmushi.

“Ayya, ya kike!?.”

“Lafiya ba lau ba.” ai nasan zuwan na ta akwai dalili.

“Okay ina jinki.” na faɗa ina sauka daga kan gadon, na fara rage kayan jikina.

Nuseey ta nema waje ta zauna sannan ta ce.

“Alfarma nake so a wajenki dan Allah Adeelah.” na mata hararan wasa.

“Za ki yi magana ko na shiga wanka, banyi sallah ba.”

“Okay, ki fito ina jiran ki.” na girgiza kai sannan na shiga toilet.

Nuseey ta ɗau wayata ta fara latsawa, take kiran Doctor Ahmad ya shigo.

Ta yi saurin rejecting call ɗin, sannan ta ja ƙaramin tsaki.

Yana ɗaya daga cikin abinda ya kawo ta wajen Adeelah, dan tana so ta mata hanya, ko Doctor Ahmad zai so ta, har ta aure shi, dan tun ba yau ba, ta kamu da soyayyarsa.

Tasan ko Adeelah tana son shi, idan har ta furta ta bar mata shi, za ta mata haka, yarinyar akwai son kyautata ma mutane, balle tsakaninsu babu komai.

Murmushi ya ƙwace akan fuskarta, tana harsaso fuskar Doctor Ahmad a cikin idanunta, ta rasa daga yaushe ta yi zurfi cikin tafkin soyayyarsa ba, ta dai san idan dai Doctor Ahmad yana rayuwa da duniyar nan, to tabbas ba za ta iya kula ko wani ɗa namiji ba.....................

*MASARAUTAR AL-JAWHARI* _Sashen Sarauniya Sarah_ “Umma Ni ba yarinya ƙara ba ce, ina da ikon zuwa duk inda na so, a lokacin da na so......” Meerah ta faɗa a dake.

Sarauniya Rania ta jinjina kai.

“Nasan kin girma, amma so nake nasan inda za ki je.”

“Wajen Hajiya zani.” tana faɗin haka ta juya ta ci gaba ta tafiya.

“Meerah ba ta da kishi, yanzu wajen Malikha za ta je, matar da bama ga maciji da ita.” sai ta taɓe baki, suka ci gaba da cin abinci.

Bayan sun gama, Sarauniya ta koma ɗakinta ta shirya sosai, domin zuwan turakar mai martaba.

Meerah na shiga Sashen Hajiya, bayin da suke ƙofar wajen suka zube suna kwasan gaisuwa, ta ɗaga musu hannu kawai, ta shiga babban parlourn.

Hajiya tana kan darduma hannuta riƙe da carbi.

Ta gaishe da ita sama-sama.

Hajiya ta amsa cikin sakin fuska, duk kuwa da ta yi mamakin ganinta a wannan lokacin.

“Hajiya ina so na huta a nan, Umma sai min faɗa take yi, akan ƙaramin abu.” Hajiya ta yi murmushi.

“Kinyi ba daidai bane ko.” ta girgiza kai, ta zauna kan kujera cikin izza.

“Baba abu ba daidai ba, Hajiya, Bara na bi ta ƙofar gaba, na zagaye lambu ko na samu natsuwa.”

“To shike nan, amma a kula da hanya.”

“Insha Allah.” da haka fadawanta suka rufa mata baya, ta fita ta wannan kofar.

Wajen shuke-shuke ne ta ko ina, ya ƙwawatu sosai, fadawa da jami'an tsaro ta ko ina.

Wani kujera dake gefe kaɗan, ta hanga Zain zaune yana jiranta.

Ta yi murmushi, sannan ta yi alama da hannu, take fadawan wajen duk suka tsaya.

Ta ci gaba da takawa har zuwa kusa da Zain.

Ya miƙe da sauri ganin hasken ruhinsa.

Shi ya fara sumbatar hannunta, kafin ta sumbaci nashi, suka sakar ma juna murmushi mai cike da ma'anoni sannan suka zauna riƙe da hannun juna.

“Umma ba ta san wajena kika zo ba!?.” ta ɗaga mai kai.

“Kai ma ina fatan Ummee ba ta sani ba ko!?.” ya ɗaga kai yana murmushi.

“Ai ba za mu bari su san komai yanzu ba, sai nan gaba, a lokacin da zamu mallaka juna.......” a tare suka kwashe da dariya, tuna wannan lokacin, sun san ba ƙaramin yaƙi za'a yi ba idan aka gane suna soyayya.

“I Love You Meerah.”

“I Love You too Ya Zain.” suka kalla juna cikin tsantsan soyayya, soyayyar da suka kwashe shekaru uku suna yi a ɓoye, har kuma zuwa yanzu babu wanda ya ankara da su...................

*Sakeenat* Kwana biyar kenan, ina kwana a wannan ɗakin, inda Allah ya taimake ni, cizon sauro bai saukar min da ciwon komai ba.

Kamar kullum da safe na gama duk wani da ya dace na yi, na yi wanka a ɗarɗar a bayi, duk kuwa da ina kula sosai yanzu.

Bayan na gama, na shirya, na sanya hijabi, ina da suturun hijabi sosai, saboda sa'ar da nake yi. Doguwar riga na sa, sun fi min daɗi, haka na fi sakewa da shi, sai na ɗaura dogon hijabi launin toka.

Kunu kawai na sha, na yi ma Mama sallama sannan na wuce.

Bayan na isa shago, na fara aikina kamar yadda na saba.

Ina yi ina rera wata waƙa da a jiya da daddare na ji shi a cikin kai na, sai na tsara kuma nake ta rerawa.

Jama'a suka fara zuwa siyan abinci, a haka wani Alhaji ya shigo shagon.

Na gaida shi cikin fara'a.

Ya amsa, sannan ya ce.

“A kawo min doya.”

“To Alhaji.” na zuba masa na aje mai.

Bayan ya gama ya aje dubu biyar ya yi tafiyarsa.

Ina aikin sai na ji ƙarar motar ta wuce, na fito da sauri kar ace ya manta bai bani kuɗin ba.

Ina fitowa sai na ga kuɗi, na ji daɗi sosai, ai ban ɓata lokaci ba, na fita na tsallaka shago, biredi na siyo manya guda biyu, na dawo shago, na aje guda ɗaya, na buɗe ɗaya.

Allah yayi Ni da son biredi, gashi kuma ba'a siyan min, kuma kullum sai na ga ana ci a gidan mu.

Wasa-wasa sai da na cinye leda guda, na sha ruwa na yi hamdala.

Na ci gaba da aiki cikin nishaɗin cin biredi.

sai dai lokaci guda na ji jikina ya sauya min gaba ɗaya, na ji ƙirjina ya fara bugawa, bansan dalili ba, sai na fara ambaton sunan Allah.

yau Baba mahaukaci bai zo ba, kuma abinci bai ƙare da wuri ba.

Sai da aka fito sallar magrib tukun komai ya ƙare, na fito bayan na rufe shago.

Sai na ga mai mashin a gefen shagona yana kokarin tada mashin ɗin.

Na yi sauri na ce .

“Okada tafiya ne!?.” ya ɗaga min kai kawai, ban iya ganin fuskar sa ba, saboda ya sanya mask ga kuma glass.

Na ji daɗin samun abin hawa da wuri, na hau mashin ba tare da tunanin komai ba.

Har mun ɗan yi nisa, sai naga mai mashin ya koma gefen kwalta, yayi parking.

“Yayana mai ya samu mashin ɗin ne!?.” na tambaya ina kallon bayansa.

“Yauwa gashi nan.” ya faɗa yana ciro kwalban turare daga aljiwunsa.

“Ƙanwata turare na siya, sai na ji kaman baya jikina, ashe a aljiwun nan na sanya shi.” ya faɗa yana nuna min kwalbar turaren mai ƙyau.

Na jinjina kai, ina jin gabana Yana ci gaba da faɗi. “Na matata ne, na siya mata na ƙarin shekara. Amma ƙanwata kina ganin za ta yi farin ciki!?” Murmushi kawai na yi, na ɗago na kalleshi, sai kawai ya fesa min turaren a fuska.

Na yi atshawa sau ɗaya, sau biyu, shike nan.............idan nace shike nan, ina nufin shike nan, dan kuwa, take hankalina ya gushe, na kasa gane komai, na zama tamkar butum-butumi, a wajen..................

*Adeelah*

Bayan na fito wanka, na iske Nuseey zaune tana latsa wayata.

Tsakanina da ita babu wani shakka, don kallon ƙanwa nake mata.

Na shirya cikin riga da wando masu laushi, sannan na sanya hijabi.

Bayan na gama shirya wa, Daga nan sai na shimfiɗa sallaya, na tsaya gabanta, na fara gabatar da sallah.

Na samu nutsuwa sosai a lokacin da nake tsaye a kan sallayar, zuciyata ta yi shiru daga hayaniyar tunanin duniya. Na mai da hankalina gaba ɗaya ga ibadata, ina mai jin daɗin wannan nutsuwar da nake samu a duk lokacin da na tsaya ina sallah.

Da na idar, ban ja dogon azkar ba saboda jirana da ake yi, na tashi na zauna kusa da ita, ina kallonta da wani irin murmushi. Na lura tun kafin na zauna na lura ta ƙosa ta faɗa abinda ke ranta.

Na matsa kusa da ita, na gyara zamana, sannan na ce,

“To, ina jinki. Na san maganar mai muhimmanci ce ta zaunar da ke.”

Ta yi murmushi, amma murmushin nata bai daɗe ba. Sai ta ce,

“Sosai ma kuwa.”

Ta marairaice fuska, ta riƙe hannunta, kamar wacce take shirin faɗin wani abu mai nauyi. Take ta sauka daga gadon, ta durƙushe gwiwoyinta a ƙasa, sannan ta ɗago kai ta kalle ni cikin damuwa.

Na bi ta da kallo, zuciyata na ƙara tsinkewa da sha’awar jin abin da yake damunta. Yadda ta canza daga fara’a zuwa wannan yanayin ya sa na san lallai akwai wani abu a ranta da take son sanar da ni.

Na yi saurin ɗagota, ina cewa,

“Ba na son haka... wai menene?”

Ta yi shiru, ta kasa cewa komai.

“Ba za ki faɗa ba wai?”

A hankali ta ce,

“Adeelah, abubuwa biyu na zo nema a wajenki, don Allah.”

“Faɗa kanki tsaye. Ko menene, insha Allah zan yi miki.”

Nan take ta rungume Ni sosai.

Na yi ɗan dariya, ina raba jikina da nata a hankali.

“Ina jinki.”

“Uhmmm... dama na farko ba wani abu ba ne... sai... uhmmmmm, ranar Wednesday ’yan ajinmu za su zo nan gidan... matsalar na musu ƙarya cewa Ni ’yar gidan ce, ba yarinyar mai aiki ba...” Ta ƙare maganar tana sunkuyar da kai.

“Uhmm ina ji.”

“Shine suka ce za su, Ni kuma bansan ya zanyi da su ba......dan Allah ki min alfarmar nan, idan sun zo, su shigo babban parlourn gidan nan.” sai ga hawaye ya cika idanunta.

“Ina yawan faɗa Miki ƙarya babu ƙyau, bansan mai yasa komai da nake faɗa Miki a banza bane........wannan ba matsala bane, sai na biyun.”

Murmushi ya bayyana akan fuskarta.

“Na gode kuma insha Allah zan gyara.” sai ta saci kallon fuskata kaɗan.

“Na biyu, ba wani abu bane face.......ina so na faɗa Miki na faɗa soyayyar wani.” ido na buɗe ina murmushi.

“Masha Allah, waye wannan mai sa'ar da ya sake zuciyar ƙanwata.”

“Ni kadai ke haukata, bai ma san ina yi ba.”

“To a ina kika Sanshi ke!?.” sosa kai ta yi.

“Ina kai ma Mom abinci asibiti wani lokaci, a can ne na haɗu da shi..... Doctor Ahmad.”

“Doctor Ahmad da na sani dai!?.” ta ɗaga min kai.

“Dan Allah, ki taimaka min Adeelah, ki mai magana ko zai so Ni, ina so na aure shi.......” na rasa tsakanin haushi da mamaki wanne ya tsaya min rai.

Sarai tasan Doctor Ahmad yana sona sosai, sai dai bata iya kawaici ba, da ace ina son shi, da kishi ne zai dame Ni, amma ita Nuseey babu ruwanta.

“Yana da mata....”

“Na sani Adeelah, Ni dai dan girman Allah ki mai magana....” sai ta fashe da kuka.

Na ringumeta ina rarrashinta.

Da ƙyar ta yi shiru, sai kuma ta sake fashewa da sabon kuka.

Na rasa mai zance, har ga Allah, ba zan so, ta aura Ahmad ba, kawai saurayin bai min ba, amma zan duba lamarin.

“Shike nan zan mai magana kinji.” ta yi saurin raba jikinsu tace.

“Da gaske!?.” Kai na ɗaga mata.

“Insha Allah.”

“Na gode, na gode.” da haka ta fita da gudu, har da ɗan ihunta.

Na kwanta ina tunanin abinda tace.

Yunwa na ji, dan haka na ɗau wayata, na fita babban parlour.

Dinning table ta isa, na zauna.

“Madam bari na kawo miki abinci.” Wata mai aiki ta faɗa tana saurin nufa kitchen.

Ina latsa waya har ta gaba jera abincin, ta zuba min a plate sannan ta juya za ta wuce.

“Aunty Halima.” ta juyo da sauri.

“Na'am Madam, me kike so.......ko abincin bai yi miki bane!? ” na kalleta.

“Zauna a kujera.” ta ɗan zaro ido.

“A'a, aiki......” Kallon bansan gardama na yi mata.

Ta zauna a ɗan ɗarare.

“Haɗa min wani abincin irin wannan a wani plate ɗin.”

“To Madam.” ta fara zuba wani abincin.

Doya da ƙwai ne da miyan ƙwai, sai Irish a gefe.

“Na zuba.” ta faɗa tana ƙoƙarin tashi.

“Ban sallame ki ba, zauna nace.” ta zauna.

“To bismillah mu ci abinci.”

“Madam......”

“Bana san magana, ki ci kawai.” ta jinjina kai cikin jin daɗi, ta fara cin abincin a natse.

Na janyo nawa, na yi Bismillah na fara ciki.

Take na tuna da Sakeenat mai abinci, na yi ɗan dariya ina tuna ta, ta waƙar nan. A raina na raya, wata rana musamman zan je rigasa domin ganinta, yarinyar ta shiga raina sosai.

Ni na fara gama cin abincin, dan kaɗan na ci, na tashi na bar dining ɗin, Aunty Halima ta bini da addu'a a cikin ranta.

★★★★★★★★★★★

Yau take Laraba, na sa ma'aikata suka tsara abinci mai rai da lafiya a dining room, Mom tana asibiti, Ni kuma na shirya da misalin 2:30pm, dan zuwa 3pm ƙawayen Nuseey za su zo.

Maroon hijab na sanya, na shiga mota, tare da danna horn.

Kafin mai gadi ya buɗe get, Maman Daddy, da yaranta biyu suka fito, sai Aunty Halima, da wata mai aikin mu.

Suka shiga cikin mota kowa sai fara'a yake yi.

Na kunna motar, muka fita ina cewa.

Supermarket zamu je, kowa ya zaɓa abinda yake so, amma na dubu biyar-biyar, banda kuɗi sosai, gashi Dad bai turo min kuɗin kashewa ba” na faɗa ina miƙan layin mu.

Su kuwa ai a haka ma daɗi suke ji sosai.

Na fita da su ne, saboda Nuseey ta ji daɗin tarban ƙawayenta da ƙyau.

Tafiya muke yi, muna hira, har muka isa wajen bada hannu, aka tsaida motocin mu, ɗayan hannun suke tafiya.

Na kalla gefena, sai na ga wata akan machine gyalen jikinta ya sauka har wajen taya.

“Baiwar Allah ki gyara gyalenki.....” baki na na rufe, saboda Muryar wani ya riga nawa fita, da kuma daidai abinda ke Zuciyata.

Budurwar yarinyar ta juya ta yi ma wanda ya yi mata maganar godiya sannan ta kalleni.

“Na gode.” na mata murmushi, ashe dai na yi maganar, na dai ji sautin wancan yafi nawa tashi ne.

Muryar na ji kaman na san mai shi, hakan yasa na kalla motar dake gefana, wanda mashina ɗin ya raba mu.

Take Zuciyata ta tsaya cak da aiki, sakamakon haɗa ido biyu da wannan Bawan Allahn, yana sakar min tsadadden murmushinsa mai kashe zuciya................✍️ End

╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*