SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

CHAPTER 2️⃣ 3

by @prettys01

> Take Zuciyata ta tsaya cak da aiki, sakamakon haɗa ido biyu da wannan Bawan Allahn, yana sakar min tsadadden murmushinsa mai kashe zuciya..........

Da ƙyar na mai yaƙe ina zuba mai ido nima.

Ya ɗaga min hannu.

Na mai da masa shi nima, sannan muka ci gaba da kallon juna na ɗan lokaci.

Take aka ba ɓangarenmu hannu, motarsa ya yi gaba, nima na fara tafiya kaɗan-kaɗan.

Shi dama ya yi, Ni kuma na miƙe titin, ina ci gaba da tuƙi, amma hankalina gaba ɗaya yana kan shi, ina mamakin a inda ya gane Ni, dan a tunani na, bai taɓa lura da Ni ba.

Na ɗan yi murmushi ni kaɗai, sannan na girgiza kai.

“Me ya same Ni kuma?” na tambaya kai na a cikin zuciya.

Na mai da hankalina kan tuƙin, na ci gaba da tafiya, yayin sauran mutanen da suke tare da Ni suke ta hira a cikin mota ba tare da sun lura murmushi na ya faɗaɗa ba................

*SAKEENAT*

Mai mashin ya kunna ya fara tafiya akan titi, bayan ɗan lokaci ya kauce daga babban titi, ya shiga wani layi, inda babu yalwan gidaje. Babu cunkoson jama’a, babu hayaniyar komai.

Ya ɗan rage gudun mashin ɗin, sannan ya yi parking a gefen wani tsohon gida.

Ina zauna a bayansa kamar an daskarar da ni. Idanuna a buɗe suke, amma hankalina ya yi nisa. Ban san inda nake ba, ban san abin da ke faruwa da ni ba, ban ma iya motsa yatsa na ba.

Ya juya ya kalle ni.

Na ga fuskarsa a gabana, amma kamar ba ni da ikon yin magana ko tambayarsa komai.

Ya sauka daga mashin ɗin, ya tsaya na ɗan lokaci yana kallona, sannan ya miƙa hannu ya amshe jakar kuɗin Mama da ke tare da ni.

“Sauka.” na ko sauka kamar yadda ya umarce Ni.

Sai ya kalla gefe da gefe, ganin babu kowa, sai ya tsinke Ni da lafiyayyen mari.

Take na zube a wajen, cikin rashin sanin inda kaina yake.

Ban san lokacin da na ɗauke huta ba, daga wannan faɗin.

Na yi kusan awa biyu ina kwance a wajen, kafin na farka.

Da na buɗe idona, sai na yi saurin zabura, ina kallon wajen cikin ruɗani. Na yi ƙoƙarin tuna inda nake, sannan na duba jikina.

Nan take na ji babu jakar kuɗin Mama.

A take abin da ya faru ya dawo min a cikin kai na ɗaya bayan ɗaya.

Na daura hannuna a kaina, sai ga hawaye ya gangaro daga cikin idona.

“Na... na shiga uku.”

Shi kaɗai leɓena suka iya furtawa, saboda nauyin da bakina ya min.

Ban iya tunanin komai ba a lokacin, sai Mama.

Ita ce kawai ta faɗo min a rai.

Na share hawayen da suka sauka akan kunci na, sai dai ina gogewa wasu suka sake zubowa.

“Ya zan yi da Mama?” na faɗa ina bin unguwar dake ciki da ido.

Ko ina yayi duhu, sai nesa kaɗan da nake hangi titi da hasken fitilu.

Na miƙe daƙyar, na fara kalle-kalle, babu komai a wajen, na kakkaɓe hijabin jikina, na fara takawa har zuwa bakin titin.

Take gabana ya faɗi, dan bansan inda nake ba, wajen bai yi kama da inda idanunsa suka taɓa zuwa ba, ko da yake ina nake zuwa in banda shago.

Na haɗiye miyau da ƙyar, duk wanda ya kalleni yasan ina cikin tashin hankali.

Duba da yadda na koma, fuskarta sai maiƙo take yi, chocolate skin ɗin da yana ta shaning, ga idanuna da suka sauya launi kaɗan, kuma hawaye yana kwance a ciki, yayinda gashin idanuna suka nannɗe saboda danshin hawaye, leɓena kuwa motsi suke a hankali, inda Ni kaina ban san me nake furtawa.

Kallon dama da hagu na yi, na rasa wanne zan bi dan ya kaini gida.

Kacincin na yi. “Kacincin kacincin- a ina gidan ya faɗa- a gidan audu maƙeris....” hannuna ya tsaya kan dama.

Nasan Allah yana tare da ni, na ko miƙa hanya, Zuciyata cike da tsoron abinda zai faru idan na koma gida.

Na sha wahala sosai kafin na iya kai babban titin da na sani. Kafafuna sun yi min nauyi.

Na ɗauki hanyar gida, ina tafiya a hankali, ina yi ina share hawaye.

Tunani iri-iri suka cika min kai. Ban san yadda zan fuskanci Mama ba, ban san abin da zan ce mata ba. Abin da ya fi komai damuna shi ne jakar kuɗin da aka amshe, dan ba'a cutar da Ni ba.

Sai wajen ƙarfe goma sha ɗaya na dare na isa kusa da gidanmu.

Duk a galabaice nake.

Na kasa shiga gidan. Na tsaya daga nesa ina kallon gidan, zuciyata na bugawa da sauri saboda tsoron haɗuwa da Mama.

Na share hawayen da suka sake taruwa a idanuna, amma kafin na iya ɗaukar wani mataki, sai na ji an taɓa kafaɗata.

Na yi saurin juyawa.

Idanuwana sauka kan Bosho dake tsaye a gabana.

Na ja baya kaɗan, ina sake share hawayen idanuna.

“Baby, me aka miki?”

Ya faɗa cikin bariki yana kallona da damuwan da ya yafa ma kansa.

Na rasa abin da zan ce masa. Bakina ya kasa furta komai.

Na kasa riƙe kaina, na fashe da kuka, ina share fuskata da tafin hannuna, sannan cikin kuka na fara ba shi labarin abin da ya faru da ni.

Na faɗa masa yadda na hau mashin ɗin, yadda mutumin ya tsaya a hanya, sannan abin da ya faru bayan ya fesa min turaren. Na kuma faɗa masa yadda na farka bayan kusan awa biyu, na tarar da jakar kuɗin Mama ba ta nan.

Bosho ya yi shiru yana saurarena.

A fuskarsa na ga damuwa ta gaske. Karo na farko kenan da wani ya tsaya ya saurare ni cikin tausayi, ba tare da ya zarge ni ko ya yi min magana mai zafi ba.

Na ci gaba da share hawaye, jikina har yanzu yana rawa.

A hankali ya miƙa hannu ya riƙe nawa.

Ban hana shi ba, saboda a lokacin ina cikin wani irin yanayi da ban san yadda zan taimaki kaina ba.

“Zan taimaka miki, Baby,” ya faɗa cikin sanyin murya. “Nawa ne kuɗin?”

Na ɗago kai da sauri na kalle shi. Kauda idanunsa yayi daga kallon nawa, saboda yadda suka koma, so sexy.

Da rawar murya na ce,

“Dubu arba'in da uku da ɗari biyar ne.”

Ya jinjina kai, yana ƙoƙarin kwantar min da hankali.

“Ai ba yawa ma, zan taimaka miki. Ki daina kuka, kin ji?”

Na kasa cewa komai.

Sai dai na ɗago masa kai a hankali, zuciyata cike da mamaki. Ban san dalilin da ya sa yake son ya taimaka min ba, musamman bayan abin da ya faru da tsakanin mu.

Ya ɗan yi murmushi, sannan ya ce,

“Idan kin yarda, zan baki kuɗin yanzu... amma da sharaɗi abu ɗaya.......”

Na share hawayen fuskata, sannan na kalle shi.

“Ina ji.”

Murmushin da ke fuskarsa ya ɗan ɓace, ya maye gurbinsa da wani irin yanayi mai wuyar fahimta.

Sai ya yi shiru na ɗan lokaci, kamar yana tunanin yadda zai faɗi abin da yake son faɗa.

Ni kuma na tsaya ina jiran amsarsa, ban san irin sharaɗin da zai zo da shi ba, amma ina ji a jikina zan amince.

Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya kalla fuskarta, ya ɗan lasa leɓansa yace.

“Sharaɗin ba wani abu mai girma ba ne.” ya faɗa a hankali.

“Ina ji.” na sake faɗa ba tare da na kawo komai cikin kai na ba.

Take ya saki murmushi, ya ɗan matsa hannuna kaɗan sannan ya rage murya yace.

“Dare ɗaya kacal, dare ɗaya nake son kasancewa da ke...........idan kin amince yanzu muje na ciro kuɗin na baki....” ya kai maganar hankalinsa kwance yana mai ci gaba da kallona cikin sha'awa, ya kashe min ido ɗaya yana jiran amsar da zan bashi, yayinda yake ɗan shafar hannuna dake cikin nasa..................

*MASARAUTAR AL-JAWHARI*

“A ganinka yaushe ya kamata mu bayyana soyayyar mu wajen Mai martaba!?.” Meerah ta faɗa a sanyaye.

Zain ya yi murmushi.

“Karki damu, mu ɗan ƙara jinkiri kaɗan, kinsan burin mu ai.” ta jinjina kai

“Ni kuwa nasan sirrin mu, kuma tabbas gab yake da cika.” wannan karan a tare suka yi murmushi.

“Allah ya bani ikon mallakar Gimbiya Meerah har abada.”

“Ameen Ya Zain.”

Bayan sun sha hira sosai, suka yi sallama, Zain ya bi ƙofar da zai sada shi da sashen Sarauniya Rania.

Itama kuma Meerah ta bi inda ta biyo.

*Washegari*

A al'adar Fadar Al-Jawhari, duk ranar Juma'a, ana zama ne a babban sashe na gidan sarauta, inda 'yan gidan sarauta da bayi da kuyangu suke taruwa a waje guda. Kusan dai sun mayar da ranar kamar ranar taro ta musamman.

Babban harabar fadar ta yi kyau matuƙa a wannan safiyar.

Daga tsakiyar babban fili, an shimfiɗa manyan kafet masu kyau, wasu masu launin ruwan ƙasa da zinari, yayin da gefen wajen yake cike da kujeru da aka tsara cikin tsari. A tsakiyar harabar kuwa akwai wani babban marmaro mai kyau, ruwan da yake gudana a hankali yana ƙara wa wajen armashi.

A gefen dama akwai dogayen bishiyoyi da furanni iri-iri, waɗanda aka kula da su sosai. Ƙamshin furannin yana gauraye da iska mai sanyi ta safiyar Juma'a.

A hankali 'yan gidan sarauta suka fara fitowa.

Duk yawanci suna sanye da manyan kaya masu kyau da suka dace da matsayin su.

Gaba ɗaya yaran Sarki da Matansa, sun sanya kayan alfarma masu daraja.

Wasu cikin riga da zani, wasu kuma cikin riguna masu faɗi. Launukan kayansu sun bambanta, saboda kowannensu da nata aikin.

Bayi da kuyangu kuwa suna tsaye a gefen harabar cikin tsari.

Babu wanda yake hayaniya. Komai ana yin shine cikin tsari sosai.

Akwai Sarauniya Rania, Sarauniya Sarah, da sauran iyalan masarautar.

Zain ma yana daga cikin waɗanda suka zo, amma idanunsa sun yi ta yawo a cikin taron mutanen, sai can ya hangi, abar begensa.

Meerah kuwa tana zaune daga can gefe, tana magana da ɗaya daga cikin matan gidan sarautar.

Itama a lokacin idanunta suna sanye cikin nasa.

A duk lokacin da idanunsu suka haɗu, sai ɗaya ya kawar da nasa cikin sauri, bayan sunyi ma juna murmushi.

Ba wanda ya lura da abin da ke faruwa tsakaninsu.

A hankali aka fara jin motsin mutane a bakin ƙofar babban sashe.

Wani daga cikin masu kula da fadar ya fito, ya tsaya cak, sannan ya sunkuyar da kansa.

“Gaaaaa fara dai jama'a.......Mai martaba Sarki Rayyan yana gab da isowa.....”

Nan take kowa ya yi shiru.

Bayan ɗan lokaci kaɗan, Sarki Rayyan ya bayyana cikin kamala

Ya shigo cikin nutsuwa, tare da wasu daga cikin masu gadinsa a bayansa. Sanye yake da doguwar farar riga mai kyau wadda aka yi wa ado da ɗan zanen zinari a gefen wuya da hannaye. A saman rigar kuwa ya sa wani babban mayafi mai launin duhu wanda ya sauka a bayansa cikin tsari.

A kansa akwai rawani mai kyau, wanda aka yi masa ado da ƙaramin tambarin masarautar Al-Jawhari a gabansa.

Fuskarsa cike take da kwarjini da nutsuwa.

Ya ɗaga kansa sama kaɗan, yana kallon wajen cikin yanayin wanda ya saba da ganin kowa yana jiran umarninsa.

Ya ɗaga ƙafarsa a hankali, ya sauke ta cikin nutsuwa, yana tafiya da madaidaicin jikinsa. Kowanne mataki nasa yana da ma'auni, ba tare da gaggawa ko karkarwa ba.

Da yake matsowa kusa, masu gadin da ke bayansa suna tafiya cikin tsari, suna kiyaye tazara tsakaninsu da shi.

Kowa ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa yayin da yake wucewa.

Sarki Rayyan bai yi magana ba.

Sai dai ya ɗan karkata kansa a matsayin amsan gaisuwa, sannan ya ci gaba da tafiya har zuwa wurin da aka tanadar masa.

Ya tsaya na ɗan lokaci.

Ya duba mutanen da ke zaune a gabansa, sannan ya zauna a kujerar da aka tanada masa.

Da ya zauna, masu gadin suka tsaya a wuraren da aka tsara musu.

Harabar ta sake yin shiru.

Sarki Rayyan ya ɗaga idanunsa ya kalli kowa.

“Assalamu alaikum.”

Cikin girmamawa kowa ya amsa masa a lokaci guda.

“Wa alaikumus salam, Mai martaba.”

Sai Sarki Rayyan ya yi ɗan murmushi.

“Yaya kuka wayi gari?”

Kowa ya amsa cikin ladabi, yayin da wasu daga cikin kuyangu suka fara shirya abubuwan da za a kawo gaban taron.

Ranar gaba ɗaya Sarki Rayyan yana zama ne tare da iyalansa.

Bayan an gama tsara abubuwan ci, kowa ya zauna gefan Mai martaba, aka fara cin abinci.

Suna cikin ci, Sai ga Sarauniya Malikha itama ta zo tare da mabiyanta.

A kallo ɗaya za ka fahimci tana cikin tsantsan farin ciki, ta nema waje ta zauna tana amsa gaisuwar mutane cikin walwala

“Mai Martaba barka da wannan Lokacin.”

“Barka dai Hajiya, fatan kina lafiya.”

“Alhamdulillah.”

Ta zauna, cikin wa'inda suke zaune, da sauri Ayla ta matsa kusa da ita, ta sumbaci hannunta.

“Ina kwana Hajiya.”

Ta amsa da fara'a.

Sauran ma duk suka gaisheta cikin izza.

Sarauniya Rania ta kai abinci bakinta a hankali.

Sarki ya ce.

“Hajiya.”

“Na'am mai martaba.”

“Kinyi waya da Yarona kuwa!?.” kai ta ɗaga sannan tace

“Eh Mai martaba, Insha Allah rana ita yau zai zo hutu.” ta faɗa cikin fara'a.

Sai dai a take zuciyioyun Zain, Sarauniya Rania, Sarauniya Sarah, da Meerah duk suka buga da matsanancin ƙarfi.

Gimbiya Jana ta zaro ido cikin mamakin, har tana ɗan ƙwarewa.

Leenah da Ayla kuwa, murmushi ya bayyana a fuskokinsu lokaci guda, Yayinda Sarki Rayyan da Hajiya suma fuskokinsu ya bayyana da farin ciki na musamman...............✍️ End

╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*