SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI

Chapter 2️⃣4

by @prettys01

> Leenah da Ayla kuwa, murmushi ya bayyana a fuskokinsu lokaci guda, Yayinda Sarki Rayyan da Hajiya suma fuskokinsu ya bayyana da farin ciki na musamman.................

“Da......Da gaske Hajiya.” Hajiya ta ɗaga ma Ayla kai, wacce dan daɗi ji ta yi kaman ta suma.

“Allah ya dawo da shi lafiya.” Sarki Rayyan ya faɗa a natse.

“Ameen ya Allah.” da haka kowa ya yi shiru.

Armashin kusan kowa ya rage a waje.

Haka dai aka wuni a wannan ɓangare.

Ana kiran magrib, kowa ya nufa bangarensa cikin tashin hankali.

Sarauniya Sarah na shiga part ɗinta, ta zauna daɓas, kai ta fara girgiza wa a hankali.

Ko da wasa bata son ganin Yarima Laith, bata ƙaunar ya dawo hutu, balle har ya hau karagar mulki ko kaɗan.

“Da shi ya hau, da kuma Zain ya hau karagar fa!?.” ta tambaya kanta. Da sauri ta miƙe tsaye.

Ta fara zagaye filin wajen, tasan dai tabbas ɗaya shine zai hau kujerar mulki watan-wata rana, kafin lokacin da ɗanta zai hau kujerar mulki shima.

Meerah dake bayanta ta yi murmushi sannan ta ce.

“Umma, ba dai akan zuwan Yarima Laith ne kika shiga wannan damuwar ba.” ta ɗaga kai tana cizan leɓe.

“Idan har Yarima Laith ya dawo, mai yiwa Mai martaba ya fara maganar murabus, idan har hakan ya faru, to ɗayan biyu, ko Zain ko Laith, dole ɗaya shine zai hau kujerar mulki.......” sai ta dafe kanta........

“Umma kenan, na baki shawara.” Kai ta ɗaga mata.

Meerah ta kusa da ita, ta riƙe hannunta sannan ta ce.

“Umma mai zai hana, kisan duk ƙofar da za ki yi amfani, ki toshe duk hanyar da Yarima Laith zai dawo kujerar mulki, Inya so Ya Zain shi ya.........” Lafiyayyen mari Sarauniya Sarah ta wanke fuskar Meerah.

“Ashe baki da hankali ban sani ba.....ko da wasa kar ki sake furta sunan ɗan iskan yaron a gabana ....” ta ja tsaki sannan ta haura sama, kamar za ta tashi sama.

Meerah dake dafe da kuncinta, ta bi mahaifiyarta da kallo, har ta ɓace mata.

Murmushin da ita kaɗai ba tasan ma'anarsa ta yi, sannan ta sake ranta, ta juya tana amsa kiran da Leenah ke mata.

“Yes Leenah.” Leenah da ke sanye da irin kayan dake jikinta, ta riƙe hannunta cikin farin ciki.

“Finally, Yarima Laith zai dawo.....wow wallahi I'm so Happy about it.” ta faɗa tana rungume Meerah, Meerah ta danne duk wani abu da take ci, ta kuma rasa murna mai Leenah ke yi haka akan dawowar makiyin ta dana Umma, harda na masoyinta..................

*Nuseey*

Yadda kasan itace Mom haka ta dinga jiji da kai a cikin ƙawayenta da suka zo, ba ƙyarya ta yi ƙyau, Swiss less ne jikinta launin maroon, an mata ɗinkin riga da skirt, ta zauna a parlour ta kashe kala, ta kashe ɗauri.

Ko da ƙawayen na ta suka zo, haka ta dinga kauɗi tana ta yauƙi.

Suka shana a cikin gidan sosai, gashi Mom bata nan, hakan yasa Nuseey ta saki jiki sosai, ta yi yadda take so.

Bayan sun huta, sun sha, hira, anci an sha, sai suka tattara komai na su za su wuce.

Nuseey ta jera da su dan musu rakiya, tana tafiya tana hamdala akan girmanta bai zube ba, ta kuma ƙara kankara ma kanta mutunci a cikin ƙawayenta.

“Ke Nusaiba an gama dafa abinci kuwa!?.” Mai aikin lambu ya tambaya yana zaune daga gefen wani fure mai ƙyau.

Nuseey gabanta ya faɗi, ta saki kallon ƙawayen nata da suke kallon shi cikin mamaki.

“Nuseey, isn’t this guy crazy? Who even is he?” a cikin ƙawayen ɗaya ta faɗa tana yamutsa fuska.

“Hmm… Zarah, forget about him…”

“What do you mean, Nuseey? Who is he anyway!?.....” ta faɗa cikin ƙyama.

“Uhmmmmm......… he’s a worker.”

“And he’s the one talking to you like that? Who the hell does he think he is?”

“No, don’t worry. I’ll teach him a lesson today.” ta faɗa tana dalla mai harara.

“He better be ready for it.”

Bayan ƙawayenta sun hau motar suka wuce, Nuseey ta nufi wajen Bala a zafafe. Fuskarta cike da ɓacin rai.

“Bala, wani irin iskanci ne wannan? Ina tare da ƙawayena za ka zo kana tambayata abinci? Dama ni ce ke dafa abincin?”

Ta faɗa cikin masifa, tana kallonsa.

Bala ya miƙe a hankali, ya ɗan kalleta kafin ya ce.

“Ɗan dakata, Nusaiba Na lura kin mai da ni kamar mahaukaci. Kin ɗauka wai ban fahimci Turanci ba ne ko me?”

Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ƙara da ɗan murmushi mai ban haushi.

“Hmmm… ƙarya da gidan wasu dai babu kyau.”

Nuseey ta ƙara harzuƙa.

“Bala, ka daina shiga abin da babu ruwanka!”

“Ke ma ki daina ƙaryan cewa gidan ku ne nan,” Bala ya mayar mata da magana kai tsaye.

“Ni ban ce gidanmu ba ne!”

“To me ya sa kike magana kamar ke ce uwargidan gidan gaba ɗaya ko Adeelah bata irin abun nan gaba ɗaya?”

“Kasan menene babbar matsalar ka!?.” ya girgiza kai

“Shegen sa ido, ka cika tsoma baki a cikin abin da bai shafe ka ba!”

“Ni kuma ina ganin ke ce kika fara tsoma kanki a cikin abin da ya fi ƙarfin ki.”

Nuseey ta zaro ido.

“Me kake nufi da haka?”

“Babu komai. Sai dai ki rage wannan masifar, ki je ki yi aikin ki.....”

“Uban aiki ne ba aiki ba.”

Bala ya yi shiru yana kallonta, ita kuma ta ja tsaki mai tsawo.

“Na gaji da ganinka a cikin gidan nan!”

“Kisa a Kore Ni dan Allah......Shashasha kawai.”

Ta juya a fusace, ta nufi ɓangaren da suke kwana ba tare da ta sake kallonsa ba.

Bala ya tsaya yana kallonta har ta ɓace daga ganinsa, sannan ya girgiza kai.

“Allah ya ganar da ke.”

Nuseey ba ta sake fitowa ba har sai bayan Magariba.

Da ta fito, kai tsaye ta nufi babban part ɗin gidan. Da farko Mom ta fara gani, suka gaisa, sannan ta nufi part ɗin Adeelah.

Da ta shiga, ta tarar da Adeelah zaune tana karatu. Littafi yana gabanta, tana karantawa tana kuma rubuta wasu abubuwa a littafinta.

Sai ta buɗe ƙofar ta shigo.

Kafin Adeelah ta ɗago kai, ta ji muryar Nuseey tana sallama.

“Assalamu alaikum.”

“Wa alaikumus salam,” na amsa ba tare da na kalleta ba.

“Kin kyauta sosai. Ace mun dawo gida, ba za ki iya zuwa ki ba ni labarin yadda walimar naku ta kasance ba.”

Na ɗago kai ina kallonta.

“Me ya faru ne?”

Ba ta amsa ba. Sai ta zauna kan kujera, sannan ta kalle ni.

“Maganar Doctor Ahmad na zo. Kin yi masa magana?”

Na girgiza kai.

“A’a.”

“Why? You know I love him.”

“Yes, I know,” na amsa cikin nutsuwa. “Amma bana son ki da shi.”

Ta ɗan daure fuska.

“Why?”

Na yi shiru na ɗan lokaci kafin na ce,

“Kawai Nuseey… akwai wani abokina Samir, Ustaz ne, kuma mutum ne mai nutsuwa da tarbiyya. Zan haɗa ki da shi. Bari ma na kira shi yanzu.”

Ina faɗin haka, na ɗauki wayata na shiga contacts, ina neman lambarsa.

Da Nuseey ta ga haka, sai ta miƙe tsaye da sauri.

“Bana so. Na gode.”

Ta juya ta fice daga ɗakin cikin sauri, ba tare da ta jira na sake cewa komai ba.

Kafin na yi wani yunkuri har ta fice.

“Wai meke damun yarinyar nan ne!?.” na girgiza kai kawai.

Hankalina ne ya koma kan wayar, jin ana sallama.

Ustaz ya yi sallama cikin muryarsa mai cike da kamala.

“Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh, ya Habeebaty.”

Na yi murmushi.

“Wa alaikumus salam warahmatullahi wabarakatuh, Ustaz. Kayfa haaluk?”

Ya amsa cikin fara’a,

“Alhamdulillah, ana bi khair. Anti kayfa haaluki?”

Na yi murmushi kaɗan, saboda yadda yake magana, shifa tsabar iya tajweed, hatta hausarsa yana tajweed.

“Alhamdulillah, ana bikhairin ma.”

“Ah, gaskiya maganar na ji daɗin ganin kiranki, Ustaza Sakeenat. Wallahi da na ga kiranki, sai na ji kamar an min busharah da gidan aljannah.”

Na yi shiru ina saurarensa.

“Wato Alhamdulillah kenan… addu’ata ta karɓu? Na ji daɗi sosai.”

Na lumshe idona, murmushi ya bayyana a fuskata.

“Ustaz, No, kira na yi ne kawai mu gaisa.”

“Mu gaisa kawai?” ya maimaita, cikin wata irin murya ta raha. “Alhamdulillah. Duk da hakan ai ba ƙaramin abu ba ne.”

Na ɗan yi murmushi.

“Ustaz, wallahi babu wani abu.”

“Hmm, to shikenan. Amma ni dai na fara ganin alamar abu. Idan yau kin kira, gobe ma kika kira, jibi kuma sai mu fara maganar aure. Kai Masha Allah, Alhamdulillah!”

Na ɗan buɗe idona, sannan na dafe kai.

“Ya Allah! Ustaz.”

Ya yi dariya a ɗayan ɓangaren.

“Me na yi? Ni fa addu’a nake yi kawai.”

“Addu’a irin taka dai ta fi kama da tsokana.”

“Tsokana?” ya ce cikin dariya. “To ki yafe min. Amma gaskiya na ji daɗin kiran naki.”

Na yi shiru na ɗan lokaci, sannan na ce cikin son rufe maganar,

“To, mu kwana lafiya.”

“Amma—”

“Bye, Ustaz.”

Ina faɗin haka na katse kiran kafin ya samu damar ƙarasa maganarsa.

Na ajiye wayar gefe, sannan na girgiza kai ina murmushi, ina mai sha'awar ganin Nuseey ta amince, dan tabbas zasu dace............

*Sakeenat* Na kalle shi cikin ƙyama, zuciyata cike da haushi. “Me kake ce?” Ya sake maimaita maganar, wannan karon yana matsowa kusa da ni sosai har ina jin saukan nunfashinsa a kan goshi na, dan ya fini tsayi. Ban jira ya ƙara furta komai ba. Nan take na ja baya, sannan na ɗaga hannu na wanka masa lafiyayyen mari. Nan take hankalin mutanen da ke wajen ya dawo kanmu. Bosho ya zaro ido, ya ɗaga hannu kamar zai kama ni, amma na ja da baya da sauri ina huci. “Karka kuskura ka sake irin wannan ƙazamin maganar a gabana! Ko wallahi, duk abin da na maka kai ka siya!” Na faɗa cikin fushi, murya ta cika da tsawa. Mutanen wajen suka fara taruwa a kusa da mu. “Me ya faru ne?” “Me yake faruwa tsakanin ku?” “Ku yi haƙuri mana, me ya sa kuke wannan hayaniyar?” Kowa yana tambayar ba’asi, amma ni ban damu da amsa kowa ba. Na ja tsaki, na juya na nufi cikin gida. “Ke Sakeenat!” Na ji Bosho ya kira sunana Ban tsaya ba. Na shiga gidan, zuciyata cike da ɓacin rai, jikina har yanzu yana rawa saboda nauyin da Zuciyata ya yi.. Bayan ɗan lokaci, sai na ji takun sawunsa yana biyo bayana. Bosho ya shigo cikin gidan a matuƙar zafafe, fuskarsa cike da fushi. “Ke! Sakeenat!” Na tsaya cak. A hankali na juyo na kalle shi. “Me kuma kake so?” Ya tsaya yana kallona, numfashinsa yana fita da ƙarfi. “Ni za ki mari ni a gaban mutane?” Na ɗaga gira. “Eh. Kuma idan ka sake maimaita irin maganar da ka yi, sai na sake marinka ko a gaban waye......” Ya yi shiru na ɗan lokaci. Yanayin fuskarsa ya nuna cewa har yanzu yana cikin fushi, ni kuma ban nuna alamun tsoro ba. A wannan lokacin ne na ji ƙofar ɗakin mu ya buɗe daga can gefe. Na kalla da sauri, Mama ce. Zuciyata ta buga da ƙarfi. Ta kalle ni, sannan ta kalli Bosho. “Me ke faruwa a nan?” Kafin na samu damar cewa komai, sai kawai na ji wani abu mai nauyi ya sauka a kaina. “Ahh!” na faɗa ina dafe kai. Duniya ta fara jujjuya min, Ban san abin da ya faru ba sai kawai komai ya yi duhu, idona ya lumshe, na faɗi ƙasa rigijib. Mama ta zaro ido cikin firgici. “Bosho! Meye haka?!” Ta nufi inda nake cikin tashin hankali, yayin da Bosho ya tsaya cike da fushi, riƙe da wani katako. “Sakeenat!” Ta kira sunana sau da yawa, amma ban amsa ba. Mutanen da ke kusa da mu suka fara taruwa, hankalin kowa ya tashi. Mama ta roƙi a kawo ruwa, aka yayyafa min a fuska. Bayan ɗan lokaci, na fara motsa idona a hankali. “Ta farka! Ta farka!” Na buɗe idona, amma komai yana min duhu-duhu. Kaina yana sarawa, jikina ya yi min nauyi. “Subhanallah… Sakeenat!” Na ji muryar Mama kusa da ni. Na yi ƙoƙarin tashi, amma ta hana ni. Na lumshe ido ina jin ɗumin mahaifiyata a jikina, ɗumin da rabon da na raɓe shi na manta, sai na ji kaman na dawwama a haka, ina mai jingine a jikinta.

Mama ta kalla Bosho cikin fushi. “Bosho, me ya sa ka yi haka? Idan ka cutar da ita fa?”

Take naji wani daɗi ya mamaye Zuciyata jin furucin Mama.

Bosho ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin ɓacin rai, “Wannan da kike gani munafuka ce, wallahi!” Mama ta kalle shi cikin mamaki. “Me kake cewa?” Ya ɗaga murya. “Kin san me na gani kuwa a cikin shagonki yau?” Mama ta kasa magana. “Kin san inda take biyawa daga shago? Hmm....…” Ya yi shiru, kamar yana son ƙara musu tashin hankali. Mama ta kalle ni. Ni kuma na kasa ɗago kai. Zuciyata ta cika da tsoro. Bosho ya ci gaba, “To ki fara tambayarta. Ki tambaye ta ina take zuwa, ina kuma take kai miki kuɗinki! Sannan daga ina take har wannan lokacin!?” Gabana ya faɗi, dum! Dum! Dum!! Mama ta kalleni cikin fushi. “Daga ina kike?! Ina kike zuwa daga shago? Ina kuɗina suke?” Na buɗe baki da ƙyar, sai dai babu kalma da ta fito. Hawaye suka fara zubo min. Mama ta ƙara tambayata tana komawa ainiyin siffanta. “Ki yi magana ke dalla!” Na rasa abin da zan ce. Sai kawai kuka ya kubce min. A hankali na fara ba ta labarin abin da ya faru, cikin murya na da ke rawa, ina yi ina tsayawa, saboda tsoro da rikicewar da nayi. Mutanen da suka kewaye mu suka yi shiru suna sauraron muryata, wanda kuka nake amma zan iya rantse yana ma wasu daɗin saurare, indai murya ne Allah ya bani. Da na kai ƙarshen labarin, sai aka fara jan salati. “Subhanallah!” “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” suke ta cewa kaman wa'inda suka san Allah.

Mama ta tsaya cak. A fuskarta na ga mamaki da ɓacin rai. Karo na farko kenan a rayuwata da ta ƙyaryata kalamaina. Nan take ta buge bakina cikin fushi. Na sunkuyar da kai, hawaye na ci gaba da gangarowa kaman an buɗe pampo. Bosho ya kalli mutanen da suka taru, sannan ya ce. “Ai nasan haka za ta ce. Bara na faɗa muku abin da ya faru.” Ya koma gefe ya zauna, cike da ɓacin rai kamar shi ne aka zalunta. Kallon sa na yi, da sauri ya ɗauke kansa daga gare ni, sannan ya fara magana cikin nutsuwa, yana ƙoƙarin nuna kamar abin da yake faɗa gaskiya ne. Ko ma ince dama shi idan ya faɗa abu, dole kowa ma ya yarda saboda yadda yake ganinsa a cikin gidan namu......ya haɗe fuska sosai, kike so serious ɗin nan, ya ce......................✍️ End ╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝

💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***

🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***

✍️ PRETTY SK ❤️

★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*