CHAPTER 2️⃣ 5
by @prettys01
> Kallon sa na yi, da sauri ya ɗauke kansa daga gare ni, sannan ya fara magana cikin nutsuwa, yana ƙoƙarin nuna kamar abin da yake faɗa gaskiya ne. Ko ma ince dama shi idan ya faɗa abu, dole kowa ma ya yarda saboda yadda yake ganinsa a cikin gidan namu......ya haɗe fuska sosai, kike so serious ɗin nan, ya ce.....................
“Ni kaina na yi mamaki sosai, ace ta dinga nuna halin kwarai a gaban kowa, ashe a can tana yadda take so, tana shanawa a bayan idanun mu ne..........Garkuwar mata.....” Mama ta amsa.
“Na'am, Bosho ina jinka.” ya sauke ajiyar zuciya.
“Akwai wani abokina da yake yawan faɗa min, yana ganin Sakeenat a wani hotel........”
Nasan gaba ɗayansu ba sa sona, yadda suka yi shine ya ƙara tabbatar min da abinda nake zargi.
Idanuna yana ƙasa, amma ina jiyo yadda suke ta salati, wasu na ta raɗa-raɗa.
“Ni ban yadda da abinda yace ba, saboda nasan halin Sakeenat, tana da kamun kai, tana da natsuwa, dan haka na shirya tsab, yau muka nufa shagon da yamma......bayan da muka je, mun iske a dai-dai ta gama komai, tana kulle shago, daga haka sai ta fito, ta hau mashin.....na za ci gida za ta zo, sai kawai muka ga ta an miƙa hanya, mashin ɗin bai tsaya a ko ina ba, sai baƙin wani hotel, muna zuwa ta sauka a mashi ta biya shi, sai wani matsashi ya isa gabanta ya rungumeta, a take, a gaban idanun mu, ta bashi jakkar kuɗin ki, sannan ta bi bayan shi suka shige.........” ya girgiza kai, ina murmushin da yafi kuka ciwo.
“Da haka muka dawo, jikina gaba ɗaya a mace, muna zaune yanzu ta zo, ta kira Ni gefe, take tambayata aron kuɗi, na taimaka, Ni kuma nace ban da shi, wai sai ta min sharri idan har ban bata kuɗi ba, Ni kuma na dakatar da ita tare da mata warning, shine ta wanke Ni da mari, ta shigo ciki da sauri..............” sai ya zabura ya kuma yin kaina, da sauri aka samu aka ja shi baya. Mama ta fusata sosai, ta janye jikinta baya, ta ƙanƙance idanunta. “Shegiya!....... Babu yadda ban yi ba a kan ki shiga irin wannan harkar, amma kika ƙi saurareta! Ashe kina bin maza a waje ne kina ɓoye min!” Ta ci gaba da tsawata min cikin fushi, yayin da ni nake kuka ina ƙoƙarin kare kaina. “Mama, wallahi ƙarya yake yi…” “Ki yi shiru!” Na kasa cewa komai. Hawaye kawai suke zuba min, zuciyata cike da tsoro da ciwo. Nan take ta hau duka na, tana cewa.
“Sai kin biya Ni kuɗi na, ko na miki illa, kuma dan ubanki daga yau za ki fara harkan a cikin gidan nan, ko kin so ko baki so ba.” Bosho ya ji kaman yace yana son ya zama a layin farko, amma idanun Amrah dake kansa yasa ya kama kanshi. A dai-dai lokacin ne Shanawa ya shigo. Da ya ga abin da ke faruwa, nan take ya ƙaraso ya janye ni daga wurin, yana ƙoƙarin kare ni. “Meye haka, kasheta za ki yi.... haba dan Allah!” Mama tana huci ta ce, “Yau sai na ci ubanta! Yarinyar nan ta iya munafunci. Ka bani ita!” Shanawa ya riƙe ni sosai yana mai cewa, “A’a, Garkuwa, ki ƙyaleta haka. Ki bar ta.” Mama ta tsaya cak, tana kallon Shanawa cikin fushi, numfashinta yana fita da ƙarfi. Ni kuma na tsaya a bayansa ina kuka, jikina a sanyaye, ban iya cewa komai ba. Da ƙyar Shanawa ya samu ya kwantar da hankalin Mama har ta bar ni. “Kinci darajar shi yau, amma gobe sai mun zauna Ni da ke,” ta faɗa cikin fushi, tana nuna Ni da yatsa. Shanawa bai ce komai ba. Ni kuwa na kasa ɗaga kai na kalla inda take. Daga nan aka bar ni a tsakar gidan. Mama ta nufi kitchen ɗin da nake kwana, ta kulle ƙofar, ta bar ni a waje. Na zauna a tsakar gidan, kamar mara gata. Raina babu daɗi ko kaɗan. Jikina ya yi min nauyi, kaina kuma yana sarawa sosai. Bakina yana min ciwo, kuma duk abin da ya faru na wannan ranar yana ta dawowa min a zuciya. Na share hawayen da ke fuskata, amma suka sake gangarowa. Na kalli ƙofar kitchen ɗin da nake kwana. An rufe ta. Ashe gata ne ma kwana a ciki. A wannan daren, ban san inda zan kwanta ba, ban san yadda zan fuskanci gobe ba, kuma ban san yadda zan bayyana wa Mama cewa duk abin da Bosho ya faɗa ƙarya ne ba. Sai na haɗa gwiwoyina da hannuwana, na sunkuyar da kai na ƙasa. “Ya Allah…” Wannan ne kawai abin da na iya furtawa.
Ina tsugunne, ina rera kuka a hankali.
Mata da samari kuma sune gefe, wasu na wasannin banza, wasu na buga karta, ga kuma masu busa hayaƙi.
A cikin rai na nake roƙan Allah, akan yasa kafin washegari na mutu, ina so na mutu, na huta, na kuma haɗu da Babana, tunda haka aka ce, idan an mutu ana haɗuwa da matattu, ina so idan na haɗu da Baba na tambaye shi, wacece A'isha, ko dai sunan Mahaifiyarsa, ko kuma dai ina da ƴar uwa....
“Baby haba ki bari mana, sau ɗaya kawai zan taɓa.” Muryar wani a cikin samarin wajen ya faɗa. Bantantance wacce ke dariyar ba, sai ta ce.
“Ka bari an jima mana.”
“A'a dan Allah Baby.” sai suka fara wasan banza cikin mutane. Idanuna sunyi ja sosai, rai na ya fara bushewa, na ɗago daga kallon ƙasa, na kalla tsakar gidan na mu.
Ji nake kaman na tashi na tsawatar musu, amma ko miƙewa ban jin zan iya, gashi ko sallah ban yi ba.
Na mai da kaina ƙasa ina ci gaba da kiran sunan Allah...........................
*MASARAUTAR AL-JAWHARI*
Wani ƙaramin ɗaki ne, komai na ciki launin ja ne, hatta hasken ɗakin ja ne sosai, ga wani jan labule daya zagaye bangon ɗakin.
Wani farin mutum ne zaune, sanye yake da jajayen kaya irin na tsofaffi larabawa, ya naɗe kansa da ƙyalle ja, haka gemunsa gaba ɗaya ja ne.
Gabansa kuwa Sarauniya Sarah ce zaune, ta haɗe ƙafa tana kallon ƙaramin kwanon dake gabanta.
Take wannan mutumin ya saki wani shu'umin murmushin. Sai kuma ya buɗe tafin hannunsa, hayaƙi ya bayya a ciki, sannan ya bi iska.
Idanunsa ya buɗe jajaye dasu, amma baya gani, saboda Aljanu sun taɓa mai su.
Muryarsa cikin wani irin amo ya fara magana da larabci.
“Sarauniya Sarah, ki je gida ki kwanta ki huta, Laith ba zai dawo yanzu ba, ba ma zai taɓa dawowa ba har sai idan ƙaddararsa ta taka cikin masarautar nan........” a ɗan ruɗe ta ce.
“Ban fahimta ba Boka Zahran.”
Kai ya girgiza, sannan ya ce “Tabbas akwai ƙaddararsa wanda a duk lokacin da ta taka masarautar nan, dole ya dawo, in ya dawo kuma, ba kowani aiki ne zai ci shi ba.”
“Zahran ta ya zamu hana ƙaddararsa shigowa masarautar nan!?.” kai ya girgiza.
“Na duba hakan ma zai faru ba, kije ki kwanta, babu abinda zai faru, a can zai ƙare rayuwarsa, bashi ba mulkin masarautar Al-jawhari.......amma idan har ba shi ba, to Zain shine zai hau mulki tabbas......” da sauri ta girgiza kai.
“Ina bazan bar hakan ta faru ba, a ci gaba da cusa ƙiyayyarsa a cikin zuciyar Sarki Rayyan.”
“Hahahaha.....Sarauniya Rania tsaye take a kansa, kuma idan har tana numfashi, bata da burin da ya wuce ta ga ya hau karagar mulki.....”
“Ni bana son haka ya faru, ina so ka yi duk mai yiyuwa kawai.” sai ya murmushi. “An gama uwar ɗaki na..........a aiko da dabbar yanka.”
“Shike nan, na Barka lafiya.....” da haka ta juya ta fice.
Boka ya sake murmushi sannan yace
“Wannan hasken dake gab da masarautar nan ya kusa bayyana, Ni kuma ina son ganin wacece wannan, dan haka na ƙarya asirin, Inaso ƙaddarar nan ta bayyana domin shine cikan wani babban aikina......” take ya hura iskan bakinsa akan tafin hannunsa, sai wani haske ya bayyana, ya daidaita bakinsa ya hura wannan hasken......................
..,................A daidai wannan lokacin ruwan sanyi cike da bokiti ya sauka akan fuskar Sakeenat dake kwance a dunƙule..........
*Sakeenat*
Na yi sauri na buɗe ido na ina kallon Mama dake tsaye a kai na da farar safiyar nan.
Tsoro ya ƙara bayyana a tare da Ni.
Na haɗiye miyau da ƙyar, ina kallonta da idanuna da suka kumbura sosai, dan a ƙasa na kwanta, haka nasha sanyi, inda Allah ya so Ni, wasu maza uku sun kwana a tsakar gida, shine na samu ɗan natsuwa.
“Hmmm jira kike na zo na tashe ki ko!?” na girgiza kai da sauri.
“Ma....Mama ina kwana.” ta watsa min harara.
“Ki tashi ki fara aiki, kinsan Allah sai kin nemo min kuɗi na, daga yau zuwa gobe, dan haka ki tashi ki sauya kaya, zan miki hoto babu hijabi, zan sa a group ɗin Manyan mata, yadda kike da dirin nan, zuwa gobe za ki yi kasuwa.” ta kai maganar tana cillo min makullin kitchen.
“Mama dan Allah karki ce haka, wallahi zan yi aikin komai banda wannan, zan je shago, zan yi aiki fiye da na baya, zan kawo miki kuɗi, wallahi ba zan sake Miki wasa da kuɗi ba.....zan ma iya tafiya shagon yanzu.........ki taimaka, komai kike so zan yi, zanyi Mama.....” na fashe da kuka mai taɓa zuciya
“Mama kinji.” Mama ta zuba min ido.
“Tom ina zuwa.” ta faɗa haka ta juya ta koma ɗaki.
Wallahi na za ci ta yadda da abinda na ce..
Dan haka na lallaɓa na miƙe tsaye, na buɗe ɗakin na shiga.
Hijabin jikina na cire, jin tsayuwar Mutum yasa na juyo da sauri.
Mama ce tsaye, na kalla ƙasa ina rufe jikina duk kuwa da kaya a jikina, ta ja tsaki.
“Za ki zama wise ne kwanan nan ki fara yawo da kayan barci a gaban kowa, sanya wannan, minti uku na baki.” ta cillo min wata riga ta juya ta fita.
Ina tsaye sai da na tsugunna, na kasa buɗe rigar, amma daga gani, ba kayan arziƙi bane.
Na ɗaura hannu a kai.
“Na shiga uku.” na furta ina tunanin abin yi.
Take Mama ta shigo, na kalleta da sauri.
“Na rantse da Allah, idan na sake shigowa na ganki a haka, hmmmmm.” ta juya ta fita.
Na haɗiye duk abinda nake ji, na ɗauka rigar ina kallo.
Rigar kanti ne mai shegen ƙyau, launin pink, doguwar riga mai laushi, da alamun bin jiki zai yi, be da faɗi, kuma an mai design mai ƙyau.
“Ku cire mata kaya ku sanya mata wannan.”. Da sauri na kalla Mama wacce suke tsaye da su Beasty (Ƴan daudu)
Beauty ya fara shigowa, jallabiya ce jikinsa, sai zani dake kwankwasonsa.
“Garkuwa ba matsala, ki jira daga waje, ai kwanda da kika nema mu, tunda duk jinsi ɗaya ne, zamu sa mata yanzu.” Beasty shima ya dasa.
“To ki tare ƙofar kar wani namijin ya ganta, dan ba zamu so a kalla jikin ƴar uwar mu ba.”
“Ku yi sauri to, bana son ɓata lokaci.” da haka Mama ta fara ƙoƙarin fita.
Bansan lokacin da na ce.
“Na rantse da Allah yanzu zan sanya rigar, Mama zan sa, wallahi, su fita, dan Allah.” sai ga hawaye sun sake gangarowa daga cikin idanuna. Mama ta juyo ta ce.
“Sakeenat Ni ba yarinyar bace, dalla ku cire mata ko na kira maza bansan bata lokaci.” da haka ta fice.
Na kalla Beasty na haɗa hannuna biyu, ina kuka ina cewa.
“Dan Allah ku bari.....zan sa da kai na, wallahi zan sanya rigar da kai na......” na sake fashewa da sabon kuka.
“Karki damu Sakeenat, duk mu mata ne ai, ba matsala.” cewan Beauty yana murmushi
Mamaki da takaici duk sun isheni, har ta ya Mama za ta tura min ƴan daudu su sauya min kaya.
“Na sani, amma dan girman Allah, ku bari zan sa da kai na.”
“Shike nan ki yi sauri, Garkuwar mata na jira.” na ɗaga kai da sauri.
Fita suka yi, na yi sauri na kulle ƙofar, sannan na share hawayena, na miƙa tsaye jikina yana rawa.
Nasan idan banyi abinda Mama take so ba, to tabbas yau mai ceto na sai Allah.
Ina tsoran Allah, ina tsoron rayuwar da suke yi.
Miyau na haɗiye mai kauri, sannan na fara ƙoƙarin sanya rigar dake hannuna, ina yi ina kiran sunan Allah..................
*Adeelah*
Na rasa dalilin da ya sa yau nake cikin wani irin farin ciki. Haka nan kawai na tsinci kaina ina murmushi a kowane lokaci.
Bayan mun gama lecture a school na hau mota.
A kusa da hanyar fita, na iske Nuseey tsaye da wani saurayi suna magana. Na yi mata horn sau uku, amma bata juyo ba. Na girgiza kai kawai, sannan na bar school ɗin.
A hankali nake driving, har na isa gidan marayu.
Da na faka motata, sai na fito na rufe ƙofar. Na gyara zamowar hijabina, sannan na nufi cikin gidan.
Da yaran suka gan ni, sai suka fara ihu cikin murna.
“Aunty Sakeenat ! Aunty Sakeenat ta zo!”
Wasu suka zo suna yi min oyoyo, wasu kuma suna dariya cikin farin ciki. Na tsaya ina amsa musu, ina shafa kawunan wasu daga cikinsu, kafin daga bisani na nufi wajen mai kula da su.
“Assalamu alaikum, Baba.”
“Wa alaikumus salam,” ya amsa yana murmushi.
Muka gaisa sosai, sannan muka zauna na ɗan lokaci muna tattaunawa kan yadda yaran suke.
Sai ya ce, “Yau dai za ki haɗu da wannan mutumin da yake taimaka mana sosai. Ɗazu ya zo, ya kawo wa yaran abubuwan ci da sauran kayan buƙata masu yawa. Yanzu haka yana can ɓangaren Islamiyya. Ya shiga babban aji yana musu karatu.”
Na yi murmushi jin wannan labarin.
“Da gaske?”
“Eh. Mutumin nan yana yawan taimaka mana sosai. Allah ya saka masa da alheri.”
Na ji daɗin jin hakan. A zuciyata ma sai na ji wani irin farin ciki, domin na daɗe ina sha'awar sanin mutanen da yake taimaka wa gidan marayun na.
Nan take na miƙe.
“Zan je in ganshi, ina so na mai godiya na musamman.”
Mai kula da gidan ya yi murmushi.
“To, ki je. Yana can cikin babban ajin.”
Na ɗauki wayata, sannan na nufi hanyar da ta kai ɓangaren Islamiyya.
Burina kawai shi ne in ga wannan bawan Allah ɗin da yake taimaka wa yaran nan, in kuma yi masa godiya.
Ina cikin tafiya a natse har na kusa isa ɓangaren Islamiyyar, sai kawai na ji an riƙe min ƙafa ta baya.
Na tsaya cak, sannan na kalli ƙasa.
Wata yarinya ce ƙarama ta rungume ƙafata, fuskarta ɗauke da murmushi har kumatunta yana lotsawa.
“Uncle! Ga Auntynmu wacce take kula da mu tun muna yara.”
Na yi murmushi. A hankali na zagayo da ita, na rungume daidai tsayinta, sannan na ja dogon hancinta a wasa.
Ta fashe da dariya.
“Aunty, ga Uncle ɗin nan da yake zuwa kawo mana alawa,” ta faɗa cikin Yarinta.
Na yi murmushi.
“To, zan gaisa da shi. Ke kuma tafi aji, kin ji?”
Ta gyada min kai, sannan ta ruga da gudu.
Na tsaya na ɗan saki ajiyar zuciya, sannan na juya a hankali domin ganin waye wannan mutumin da yaran suke magana a kansa.
Idanuna suka fara sauka kan takalminsa.
A hankali na ɗaga kallona sama.
Daga takalminsa zuwa ƙafafunsa, hasken fatar ƙafar ya haska cikin baƙin takalmin da ya sanya. A hankali na ci gaba da kallon jikinsa. Yadin Menless ne jikinsa, launin army green, wanda aka mai ɗinki mara hayaniya. Idanunsa suka sauka kan faffaɗan kirjinsa, kafadunsa, sannan wuyansa.
A ƙarshe dai idanuna suka sauka kan fuskarsa.
Fararen idanunsa, masu ɗauke da kaifin kallo.
Na tsaya cak.
Wani irin yanayi ne ya ratsa ni, har na kasa motsawa na ɗan lokaci.
A daidai wannan lokacin, sai na ji zuciyata ta buga da ƙarfi.
Duk!
Na lumshe idanuna na ɗan daƙiƙa, kamar ina ƙoƙarin fahimtar abin da ke faruwa da ni.
Idan ba gizo idanuwana suke ba, wannan mutumin ne, mutumin da ya shigo rayuwata ta wani kalan siga, wato Taimako....
Na ɗan tsaya ina kallonsa, kafin na tattara sauran natsuwata, na ɗanyi taku uku.
Da na ƙaraso kusa da shi, sai na ɗan sunkuyar da kai daga kallonsa, san shima idanunsa a kaina suke.
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam,” ya amsa a hankali, shi ma yana kallona cikin mamaki.
Muka tsaya muna kallon juna na ɗan lokaci, kafin kowane ɗayanmu ya yi murmushi.
“Ya ya kake?” na tambaya.
“Lafiya lau, ke fa?” ya amsa, yana murmushi.
“Alhamdulillah, lafiya.”
“Masha Allah.”
Sai wani ɗan shiru ya sake shiga tsakaninmu. Kowa yana murmushi.
“Sau uku kenan ina ganinki a wurare daban-daban, amma ba mu taɓa magana ba sai yau,” ya faɗa.
Na jinjina kai.
A raina kuwa sai na ce,
“Kenan duk ya lura dani?”
Kafin in samu damar magana, Baba ya iso wajenmu, cikin kamala.
“Kinga ɗana mai zuciyar zinari? Shi ne yake taimaka mana sosai.”
Mutumin ya yi murmushi.
“Don Allah nake yi. Kuma na sha faɗa maka, bana so a sani. Hatta mai gidan nan ban so ya sani.”
Baba ya yi dariya.
“Yarona, sai haƙuri kam. An riga an makara. Ga ’yata Sakeenat ita ce mai kula da gidan marayun nan, kuma mallakinta ne.”
Kafin ya ƙarasa maganar, wayarsa ta fara ruri. Ya duba wayar, sannan ya ce,
“Ku kafarce Ni, ina zuwa..”
Ya ɗaga wayar ya ɗan ja gefe, ya ba mu waje.
Na kalleshi da kyau.
“Mun gode sosai. Allah ya saka da alheri,” na faɗa, ina ƙoƙarin juyawa, dan wani irin yanayi nake ji.
“Two minutes, please, Malama Sakeenat.”
Ya furta ta muryarsa mai daɗi, da na ji hakan, sai ƙirjina ya sake buga da ƙarfi.
Ban san na me yasa ba.
Na jiyo a hankali, na zuba masa idanu.
Shi kuma ya tako zuwa kusa da ni.
“Idan babu damuwa, ina so ki ba ni lokacinki ko mintuna biyar ne kawai.”
Na kalli agogon da ke hannuna.
“Ba damuwa.”
Na ɗago kaina na kalle shi.
Shi kuma ya yi murmushi.
A lokacin ban san cewa waɗannan mintuna biyar da zan bashi, shine mabuɗin shafin wani rubatattacen al'amari, ya daɗin hasashe da fatan faruwansa, amma kafin faruwar, abubuwane masu yawa ne suka kewaye shi..
“Malama Sakeenat…”
Ya furta a hankali, na ɗaga kai na kalle shi, bayan mun zamu waje mun zauna a gefe guda.
“Za ki aure ni?”
Na zaro ido jin kalmar da ya fara fitowa daga bakinsa.
“Aure?”
Ya jinjina kai.
“Eh.”
Na ɗan yi dariya saboda mamaki, sannan na girgiza kai.
“ban gane ba.” na sauke ajiyar zuciya.
“Me ya sa baki gane ba?”
“Ka ce min in ba ka mintuna biyar kawai, sai kuma ka fara tambayata shin zan aure ka?”
Ya yi murmushi, amma ni ban daina kallonsa cikin mamaki ba, duk kuwa da Zuciyata a shirye take da yin rayuwa da shi
Na sauke numfashi a hankali.
“Ni ban san ka ba. Ban san sunanka ba, ban san inda kake ba, ban san iyalinka ba, ban san komai game da kai ba. Yanzu kawai ka zauna a gabana ka ce min, ‘Za ki aure ni? Nima baka Sanni ba gaba ɗaya’”
Ya yi shiru.
Na kuma girgiza kai ina murmushi saboda yadda lamarin ya bani mamaki.
“Wai dama ana haka a zahiri?” murmushi na ga ya yi.
“Tabbas ana haka, kuma Ni ba wasa nake yi ba.” ya faɗa a dake da muryarsa mai cike da burgewa.
Murmushin da ke fuskata ya ɗan gushe.
Na kalle shi sosai.
“Da gaske kake?”
“Da gaske.”
Na yi shiru.
A zuciyata kuwa, tambayoyi suka fara ta yawaita.
Me ya sa ni?
Me ya sa yanzu?
Me ya gani a tare da ni har ya yanke irin wannan hukuncin?
Na ɗan sauke idanuwana ƙasa.
“Sunana Muhammad, a nan K.K nake zaune tare da kakannina..........” sai na kalla fuskarsa, a hankali kuma na sauke idanuna ƙasa.
“Ban iya ɓoye-ɓoye ba, ban iya barin abu a ciki na ba, shi yasa na faɗa miki yadda nake ji a kanki..........l Na jima ina neman Allah ya haɗa Ni da mace ta gari, mai ƙyawawan halayya, wacce za ta dace da Ni, sai gashi Allah ya amsa addu'ata, ya shigo dake cikin rayuwata babu zato babu tsammani.......... Mun haɗu dake waje daban-daban, kuma duk kin nufa wajen dan kai agaji.........kin zo gidan wannan matar, da kuma kika ganni, sai kika aje kayan dake hannunki kika wuce.......kin nuna kyautace ta kawo ki ba, badan a san ki ba........bayan nan, kika yi yunƙurin kai ba wannan mutumin agaji, a lokacin da yake buƙata, shima sai na taimaka miki........ki sani tun daga wannan ranar nake tunaninki, na gama mantawa da ke, kullum sai kin min gizo, gaba ɗaya tunaninki ya sa na zauce a ƴan kwanakin nan.....” ya ɗan yi murmushi, yayinda gaba ɗaya jikina yayi sanyi.
“Bantaɓa soyayya ba, ban taɓa faɗawa soyayya ba, sai a kanki, halinki da na gani ya isheni miji sheda ko a wajen Ubangiji...........sai dai ba zan takura miki ba, just think...... think na gode da lokacin ki.” da haka ya aje min wani card mai ɗauke da numbersa, sannan ya min sallama ya wuce.
Na lumshe ido sannan na buɗe, take na saki lafiyayyen murmushi, na ɗau number na jujjuya ina mai kallon tsaf.
Idan nace ban faɗa wa tarkonsa ba na yi ƙarya, Ni kaina exactly abinda ya faɗa a kai na, haka Zuciyata take fassara shi.
Sai gashi ashe ba Ni kaɗai ce ke jin haka ba, harda shi. “Ya allah.” na furta daga can ƙasan Zuciyata. Jin yara sun nufo inda nake, yasa na bar tunanin Bawan Allahn na mai da hankalina wajensu, ina sakar musu murmushi mai ƙyau, wanda yake da alaƙada da saƙon Zuciyata, dan gane da sabon masoyina..................✍️ End ╔══════════════════════════════╗ 🔐 PREMIUM PAID BOOK • ₦500 ╚══════════════════════════════╝
💳 BIYAN KUƊI: OPay — Sakina Abdullahi 📱 ***
🧾 SHAIDAR BIYA / TUNTUƁA: *** • ***
✍️ PRETTY SK ❤️
★SAKEENAT★ *BAMBANCIN RA'AYI* _Between joy and sadness......Between smiles and tears........✍️_ By PRETTY SK CE 😍
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
*LAST FREE PAGE'S 🫠🎉😀"