CHAPTER 2️⃣ 6
by @prettys01
> Jin yara sun nufo inda nake, yasa na bar tunanin Bawan Allahn na mai da hankalina wajensu, ina sakar musu murmushi mai ƙyau, wanda yake da alaƙada da saƙon Zuciyata, dan gane da sabon masoyina...........
*Nuseey*
“Kin tabbatar idan na yi amfani da maganin nan zan sake zuciyar Doctor Ahmad!?.” ta faɗa tana kallon ƙullin baƙin ledan dake cikin white Ziploc.
Babbar ƙawarta Zahra ta ɗan ja tsaki kaɗan.
“Kina sa shakku a rai, to maganin nan ba zai yi aiki ba sam, ke da kina kallo yarinyar ƙanwar Babanki za ta miki ƙwaton saurayi, sai ki zuba mata ido......” ta kuma jan tsaki tana mai da hankali kan titi dan driving take yi.
“Ko ƴar motan nan kin kasa mallaka, Babanki na da kuɗi amma common G.L.K da muke ya yi ba'a siya miki ba.” Nuseey ta ɗan tauna gefen bakinta, cikin takaicin ta faɗo duniya a hannun da bai dace ba, ta so a ce itace Adeelah, wayyo Allah, da ba ƙaramin abu za ta yi ba.
“Karki damu Zahra, yanzu Ni ta soyayyar Abin so nake, Insha Allah a yau zan yi na gama komai, nasan Mom tana asibiti, zan kai mata abinci, kuma zan neme shi.”
“Yauwa Baby girl, that why I love you so much.” suka yi dariya.
Suna tafiya suna tsara yadda Nuseey za ta mallaka zuciyar Doctor Ahmad da sittin da boka ya basu.
Sai dai abinda basu sani ba shine, wannan shine babban ganganci da Nuseey ta yi a rayuwarta, shine tudun da zai mata wahalar sauka, za ta ciza yatsa, za ta yi kuka, za ta yi nadama amma duk cikin DANASANIII...............
★★★★★★★★★★★
“Bangane ba Mother.” Safraz ya faɗa yana zuba ma mahaifiyarsa idanunsa.
Mother ta gyara glass ɗin dake maƙale a idanunta.
“Tabbas Son, mahaifiyarta da bakinta take sanar min ta yi ma Sakeenat miji, muyi haƙuri.” Safraz ya zaro ido da sauri. A hankali kuma ya tashi, ya yi taku uku zuwa kusa Mother, ya tsugunna daidai fuskarta.
“Mother kiyi duk yadda za ki yi, na samu auren Sakeenat, ko Ni da aure har abada, haka kuma yau zan bar muku ƙasar, ba zan dawo ba, sai da tabbacin Sakeenat mallaki ta ce.” yana kai nan, ta ture plate ɗin dake gefen Mother, ya miƙe a fusace ya haura sama.
Mother ta sha wasa yake, kawai zai ta ga ya fito da trolly yana ja, ga kuma jakkar bayansa ya goya, already ya shirya saboda suna da match jibi.
“Safraz ka tsaya, idan ka tafi Ni taya zan siya zuciyarta, bayan kai ya kamata ka jajirce akan ta......” Mother tana tafe tana magana, amma safraz ko jiyowa bai yi ba.
Haka ya shiga motar ya mata key sannan ya bar gidan da gudu.
Mother ta sanya driver ya bi bayansa, driver shima ya fita da gudu a wata mota.
Mother ta ja dogon numfashi, ta dafe kai.
“Sakeenat......dole Safraz ya aure ki, dole ne hakan ya faru, ko mai zai faru, shine mijinki da yardan Allah.” tana faɗin haka ta juya a fusace ta koma babban parlourn gidan. Ta zauna kan kujera, sai ga mai aiki ta fito ɗauke da glass cup, ta haɗa mata coffee mai zafi.
“Madam your coffee.” a fusace ta miƙe tsaye.
Ta wanka matar mari a fuska.
“Zuba min a kai, zuba min na ce....nonsense.......Na Kore ki, oya get OUT....” ta yi sama fuuuu.
Ƴar aikin ta ɗaura hannu a kai, ta hau salati.
“Na shiga uku, Ni kuma me na yi!?.” jiki a mace ta nufa kitchen tana tunanin abinyi.
Mother na shiga part ɗinta, ta ɗau wayarta ta latsa wani number, bugu ɗaya.....biyu......uku aka ɗauka.
“Bar gaisuwa nan, akwai matsala Asiya, akwai babban matsala..................” ta faɗa mata komai akan abinda Safraz ya ce, da yadda suka yi da Mom.
Daga cikin wayar aka ɗan yi murmushin manya sannan wata murya mai sanyi tace
“Shine za ki tada hankalinki akan ɗan wannan abun, haba A'isha, ganin zuwa yanzu nan”
“Shike nan Asiya, sai na ganki.” da haka ta katse kiran tana jin sanyi na ratsa mata zuciya, ta zauna tana kallon screen ɗin wayarta wanda hoton Safraz ne a kai, inda yake riƙe ƙwallo a filin ball, ta summabaci fuskarsa tana cewa.
“Insha Allah za ka aura Sakeenat, idan har kuɗi yana maganin abu, to tabbas zan yi dan na wanke maka zuciya.......”
Abinda basu sani ba shine, wani abun farashi babban matsala ne, hakuri wasu lokacutan ya fi zama alheri, amma saboda ƙaddara na ƙwankwasa kofa, sai a manta da komai, a yi abinda zuciya take rayawa..... wato buɗe wa.........
*Mom*
Wayar dake hannunta ta aje kan Center table, ta saki murmushi tana kallon hoton tilon ƴarta Adeelah, a hankali ta buɗe ba ki ta ce.
“Lokacin cikar burina yayi, lokacin da zan bayyana Miki kudira ke da mahaifinki yayi, lokacin da za kisan cewa na miki miji, kuma nasan ba za ki ban kunya ba Adeelah.” sai ta lumshe ido tana fatan abinda ke cikin ranta ya zama gaske.
Abinda ba ta sani ba shine, Banbancin Ra'ayin ya isa bakin ƙofarsu, banbancin ra'ayin da zai rushe farin ciki mai yawa, banbancin ra'ayin da za'a zo daga baya a ciza yatsa, dan kuwa a dai-dai wannan lokacin.........
Dad zaune yake a office yana shan tea, lokaci zuwa lokaci yake sakar murmushi, ba dan komai ba, sai dan hirar da ta gudana tsakaninsu da Abubakar A-one a jiya.
★ Bayan sun gama komai, A-one ya mai sallama zai wuce.
Dad ya dakatar da shi, hakan yasa A-one ya dawo ya zauna yana ɗan sakin fuskarsa.
Dad ya dafa kafaɗarsa.
“Abubakar.” A-one ya amsa yana mai zuba ma Dad idanunsa masu matukar kaifin gaske.
“Yaushe za ka yi aure!?.” Dad ya tsinci kansa da mai wannan tambayar.
A-one yayi murmushi yana shafa kansa.
“Lokaci kawai nake jira.” Dad ya yi saurin cewa.
“Ka samu matar aure ne!?.” kai ya girgiza.
“A'a, amma soon Insha Allah, so nake na samu mace mai nagarta sosai.” Dad sai kawai ya rungume shi.
“Insha Allah, za ka aura mace ta musamman.”
“Allah ya amsa.” da haka ya bashi damar tafiya, A-one ya wuce.
Dad ya bi bayansa da ido, yana raya tabbas shi zai zaɓa a matsayin siriki, ya yanke wannan shawarar tun ba yau ba, kuma yana fatan komai ya tabbata........
“Ba ƙaramin dacewa za su yi ba.” Dad ya hasasho haɗuwar Abubakar da Adeelah.
“Allah ka tabbar mana da alƙhairi......Ameen ya Allah.”
> Hmmmmm shi kansa Dad, bai san yanzu wasan zai soma ba, bai san hargitsin dake tafe, ya shallaci tunanin kowa ba, bai san wani ƙaddarar soyayya ya riga ya mamaye zuciyar Adeelah ba, soyayyar da za ta sauya musu gaba ɗaya, soyayyar da za su ce ADEELAH Haka dama kike..................................
*Sakeenat*
Ina kuka, ina sanya wannan rigar har na gama. Na share hawayena, sannan na kalli kaina cikin madubi.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,” na furta a hankali.
Tun da nake ban taɓa sanya irin wannan suturar ba. Rigar ta kai min har ƙasa, ta kwanta a gaba ɗaya jikina, duk wani tudu da kwari sai da rigar nan ya bi ya lafe kaman danni aka yi shi.
Ga launin da ya haska baƙar fatata sosai. Dan dark pink ne, sai ƙananan taurari launin ja, yayinda fuskanta ta kasance baƙi mai ƙyalli. Rigar ta matse ni sosai, kuma hakan ya sa na ji wani irin rashin jin daɗi, ga kunya ɗaya rufe ni.
Na haɗiye miyau mai ƙyauri a maƙoshi na, sai na ji bugun ƙofar Mama daga waje.
“Buɗe ƙofar, Sakeenat!”
Na lumshe ido sannan na buɗe, ƙofar na ɓuɗe, ina ƙoƙarin rufe jikina da rigar da na cire.
Mama ta shigo tana sake haɗa fuska kamar taga kashi, amma acikin ranta kuwa, ba ƙaramin yaba halitta take yi ba.
“Tsaya da ƙyau. Na miki hoto a nan, ko wallahi a tsakar gida zan miki!”
Ai ba shiri na aje wannan rigar, na tsaya da ƙyau, cikin kuka na ce.
“Na.....na tsaya”
Haka na tsaya kamar daliba a gaban malami.
Mama ba ta saurare ni ba. Ta ɗaga wayarta ta ɗauke ni hoto guda biyu.
“Ke, ban san iskancinki ! Ki tsaya da ƙyau mana. Ki yi style!”
Na sunkuyar da kai, ina jin hawaye na sake cika min ido.
Mama ta ja tsaki, sannan ta sake ɗaukar hoton jinjina a daidai inda na ɗan daga idanuna, na kalla bayan wayarta da idanuna da suke cike da hawaye. Ashe style na yi mai ƙyau, har sai da Mama ta ce. “Masha allah.” dan kuwa na mata masifar ƙyau a yadda na tsaya.
Sai kuma ta haɗe fuska, ta juya ta fita ba tare da ta sake kallona ba.
Tana fita, sai na silale a hankali na durƙushe a ƙasa.
Na share hawayen da suka samu damar zubowa, na share amma kuka ya gagari tsayawa,
“Ya Allah… me ya sa ni?” na faɗa, sai kuma na miƙe dan yin abinda ya dace.
★ Mama ta zauna a kan kujera, ta shiga Whatsapp, jikinta har rawa yake, ta shiga group ɗin *Manyan Mata*, ta yi posting hoton Sakeenat, a ƙasan hoton ta rubuta.
‘Budurwa ce ɗanya shaƙaf, mace mai ƙyau da sura, farashin ta dubu dari da hamsin, duk awa ɗaya......mai daraja ce, matan manyan ce, ko da kuɗin ka sai da rabonka.....’ ta yi posting, tun kafin ta sauka a online har maza uku sun bita privet suna tagging hoton Sakeenat.
Mama ta yi shu'umin murmushi.
“Ashe Ni ke cutan kaina akan harkan nan.....” sai ta kuma dariya, ta sauka a online.
★Haka na wuni na zama a bar tausayi, babu wanda ya kula Ni, babu wanda yabi ta tawa, sai wajen yamma Mama ta shigo ɗakin da nake, ta aje min ledoji biyu a gabana.
Banyi tunanin komai ba, na duba na farko, ganin indomie biyu da kwai uku, sai nace.
“Yanzu zan dafa miki, ƙwan dafaffe ko soyayye!?.” na faɗa a sanyaye. Mama ba ta ce komai ba na tsawon lokaci.
Na ɗaga kai a hankali na kalleta, ganin Ni take kallo, sai na sunkuyar da kai.
“Ki dafa ki kuma cinye tas, sannan ki shanye duk maganin da suke cikin ledan nan shima.......na rantse da Allah, idan kika min asarar kuɗi, sai naci ubanki da A'isha, Shegiya baƙa kawai.....gobe zan siyo miki whiting up, ki ɗan yi haske, fatar nan taki kullum duhu take ƙara yi......da yake gadonsa kika yi wajen Aisha, amma ke na ki zai washe da mai ko ƙwayar haske.”
Na jinjina kai, jikina har rawa yake, na ɗau ɗayan ledan.
“Mama na gode, na gode, Allah ya saka da alheri, Allah ya ƙara ɗaukaka.” sai ga guntun hawayen jin daɗi ya zubomin.
Bansa komai a ciki na ba, kuma Ni na yi girkin safe, rana da dare.
Mama ta juya ta fita, na sanya hijabi, na fita Nima.
Daɗi kaman ya kashe Ni, indomie biyu da ƙwai uku, ai yau ranar tawace.
Dana shiga kitchen, sai na kama ƙugu na riƙe, na tsaya ina tunanin wani kalar dahuwa zan yi.
“Dambun indomie.” Zuciyata ta furta min, na ko yi na'am da hakan. Allah yaso akwai sauran rushi, na gyara huta, na ɗaura ruwa. Bayan ruwan yayi zafi, na zuba duka indomien, na kulle. Ban ɗau lokaci ba, na sauke shi, na tace a ƙwando. Muna komai na girki a gida, dan akwai babban store mai cike da kayan abinci.
Man ƙyaɗa naje na tambaya Mama, tace na yi amfani da duk abinda nake so.
Na ko soya indomien nan da ƙwai. Ya Allah, tuni ƙamshin ya fara sanya ƴan hanjina kukan azaba.
Bayan na gama, na zauna daga gefe, bayan na shimfiɗa tsumman riga a ƙasa. Ci na fara yi, hannu baka hannu ƙwarya. Na lumshe ido jin abincin ya kai min.
“Allah kai ne abin godiya.” na furta ina kai wani lomar cikin baki. na cinye tas, na sha ruwa na yi hamdala.
Ba tare da tunanin komai ba, koma inda nake kwana, na janyo ledan maganin nan, kala huɗu na gani, ƙananun gora biyu, sai ƙwaya biyu.
Na shanye gaba ɗaya, dan na ga an rubuta haka.
Take na ji Hajijiya na kamani.
Na ɗan fara lumshe ido, sai na jingina da bango, ai kuwa na yi barci nan take.
Bani na farka ba, sai da aka kira sallar asuba, na buɗe ido da ƙyar dan har lokacin akwai sauran barci a idanuna.
Na tashi na cire hijabin jikina na fita. Ban jima ba na dawo da alwala, na yi sallah tun kafin masallaci su shiga, dan wata rana har rige-rige nake yi da liman.
Na zauna ina azkar, tare da tunanin abinda na sha ya sani barci jiya.
Yau ɗina ta kasance rana ta musamman da bazan taɓa mantawa da shi ba.
Da safe Mama ta bani bread da kayan shayi, na sha, na ci biredi mai yanka-yanka. Da rana na yi girki tace na ɗiba na ci, wallahi harda kifi taliyar nan. Hmmmmm na ko ci da yawa. haka da yamma ina zauna Mama ta aiko min da awara, daɗi kaman ya kashe Ni, na ci ina mai farin ciki.
Yau gidan namu kaman za'a yi taron makaranta, an yi decorating compound ɗin sosai, ga kujeru da aka zuba.
Ni dai ina ɗaki ina kwance, yayinda matan gida, daga masu shiga wanka, sai masu fitowa, sai masu sanya zafaffun kaya, sai wa'inda ake ma make-up.
Sai da Mama ta kira Ni ɗazu nake jin wai, wani baƙo ne zai zo, Ni na haɗa mai abinci, fried rice, na zuba a wani sabon kula na aje, na ci ragowar.
★Bayan sallar magrib kuwa, tsakar gidan ya cika sosai, ƴam mata sun haɗu sun gaji da haɗuwa, kowacce ta kame a kujera, tana fatan Alhaji Naira ya zaɓe ta.
Mama da wani babban mutum suka shigo cikin haraban gidan.
kallon ɗaya za ka yi wa mutum zaka san ba talaka ba ne. Daga yadda yake tafiya har zuwa irin kayan da ya sanya, komai a jikinsa yana ɗauke da alamun kuɗi.
Sanye yake da original Menless white, mai kyau kuma an dinka shi da tsari na musamman. Farar rigar ta zauna masa daidai, babu hayaniya a jikinta, amma tsadarta na bayyana tun daga kallon farko.
A ƙafarsa kuwa, takalmi ne na wani shahararren brand, sabo mai sheƙi.
A hannunsa akwai Agogo mai tsada, wanda ko daga nesa za ka gane ba irin agogon da kowa zai iya saya ba. Ya ɗaga hannunsa kaɗan yana duba lokaci, sai hasken agogon ya ɗauki ido.
Hular da yake sanye da ita ma ba a bar ta a baya ba. Ta yi daidai da shigarsa, tana ƙara masa kamala, kamar mutumin kirki .
Sai wayar dake hannunsa...
iPhone ce, sabuwar ƙirar da idan ka gan ta a hannun mutum za ka san ba ƙaramin kuɗi aka kashe wajen mallakarta ba. Yana riƙe da ita cikin sakaci, kamar ya riƙe leda.
Shigarsu kawai zai gaya maka, gashi ɗan dattijo, mai ƙyau.
Mama ta kalla Alhaji Naira sannan ta mai da hankalinta wajen nuna mai wajen zama.
Suka taka har zuwa wajen da aka tanadar masa.
Ya zauna a hankali, yana mai sakin murmushi wanda ya bayyana fararen haƙoransa.
Da ganinsa, ƴam matan wajen suka fara washe baki, kowacce cikin irin kallon kissan.
Wasu suka kalli juna suna murmushi, wasu kuma suka kasa ɓoye farin cikin da ya bayyana a fuskarsu.............................
*🇺🇸 BOSTON — AMERICA*
A can nesa da ƙasar Al-Jawhara, a cikin birnin Boston, Massachusetts, wata irin rayuwa ce Prince Laith yake gudanarwa.
Rayuwar da ba ta da hayaniyar fada, ba ta da tarin bayi da masu gadin fada a kowane lungu, kuma ba kowa ne ya san ainihin matsayin da yake da shi ba.
Laith yana zaune ne a wani katafaren gida mai hawa uku, wanda yake cikin wani yanki mai matuƙar tsaro. Gidan yana da kyakkyawan tsarin gine-gine, an haɗa salon zamani da tsohon tsarin gine-ginen Boston.
A gaban gidan akwai wata ƙaramar lambu mai kyau, cike da furanni iri-iri, sannan akwai hanyar da ta kai kai tsaye zuwa babban ƙofar gidan. A gefe kuma akwai babban gareji da motarsa take ajiye.
Da zarar ka shiga cikin gidan, babban foyer ne zai fara tarbar ka. Ƙasan gidan an yi shi da marble mai sheƙi, yayin da wani babban chandelier yake rataye daga saman rufin yana haskaka wajen.
Babban parlour yana gefe ɗaya, an kawata shi da kujeru masu kyau da manyan tagogi da ke kallon titin Boston.
Akwai dining room, kitchen na zamani, da wani ɗan ƙaramin library mai cike da littattafai.
Amma ɗakin da ya fi ɗaukar hankali shi ne privet office ɗin Laith.
A can ne yake gudanar da yawancin abubuwan da suka shafi aikinsa. Manyan tebura ne, computers, takardu da wasu ƙananan kayan fasahar robotics da yake aiki da su.
Komai yana cikin tsari.
Babu abin da yake a wurin ba tare da dalili ba.
Hawa na biyu kuwa shi ne inda bedroom ɗinsa yake. Babban ɗaki ne mai faɗi, mai sauƙin ado amma komai na cikinsa yana nuna cewa mai gidan ba ƙaramin mutum ba ne.
Babban wardrobe yana gefe ɗaya, bathroom mai kyau yana ɗaya daga cikin ɓangarorin ɗakin, sannan akwai balcony da ke kallon wani ɓangare na birnin.
Duk da wannan katafaren gida da dukiyar da yake da ita, Laith ba mutum ne mai son nuna kansa ba.
Ya fi son natsuwa.
Ya fi son sirri.
Kuma a nan Boston, mutane da yawa suna kallonsa ne kawai a matsayin wani matashin ƙwararren ma'aikacin robotics...
Ba tare da sanin cewa mutumin da suke gani kullum ba shi ne Prince Laith Al-Jawhari, ɗan tsohon sarki kuma ɗan gidan sarautar Al-Jawhara ba.
A wannan ranar ma, Laith yana cikin office ɗinsa, zaune a gaban computer, hankalinsa gaba ɗaya yana kan wani aiki da yake gabansa. Daga baya idan ka kallesa, tabbas za ka iya ce mace ce, duba da tsawon gashin kansa, wanda ya zubo har kafaɗa, baƙi, dogo, mai santshi, gashi sai ƙyalli yake yi, wanda hakan ke nuni da ana kashe ma wannan gashin maƙudan kuɗaɗe, wajen gyarasa.
Matashin mai kimanin Shekaru 27yrs, yana da wani irin baiwar ƙyau ne na musamman, Fatar jikinsa fari ne sosai mai sheƙi, wanda yake kashe ido, yadda kasan kullum a ƙasan A.C yake baya fita Fuskarsa kaɗai abin zama ne a ƙalla, dan kuwa ba ƙaramin tarin abubuwa bane a cikinta.
Dogon gashinsa, ya ƙara ma fuskar wani irin yanayi, dogon siririn hancinsa wanda yake fuskarsa, kaman an zana, ga idanunsa masu matukar kaifi, kuma launin ƙwayar ciki, ba ɓaki bane, grown ne mai duhu, farin ciki fatar kuma ƙar, yadda kasan ruwan madara.
Ya subuhanallah, leɓansa......leɓansa madaidaici, wanda ya banbanta da hasken fatarsa, dan yayi launin light pink, kaman ya shafa janbaki, kuma haka Allah ya yi shi. Idan fa ana maganar ƙyau, to Yarima Laith karshe ne, ta kowani fuska.
Yana da cikar haiba, kamala, nasaba, da kuma Izza, wanda yake wayo a cikin jinisa. Babban matsalar da kowa ke ganin yana da shi, shine rashin fara'a, baya ko murmushi, dan wahala yake mai, idan kuwa ka ga yayi murmushi to tabbas ba ƙaramin abu bane.
Sanye yake da classic black suit mai kyau, wanda ya ƙara fito da siffar shi. A ƙarƙashin suit ɗin akwai farar shirt mai haske sosai. Ƙafafunsa kuma sanye suke cikin takalmin masu rufe, sai ƙyalli suke yi.
Manyan bayanai ne suke bayyana a screen, yayin da yatsunsa suke motsawa cikin sauri a kan keyboard, idanunsa kuma suna kan screen ɗin.
A hankali ya jingina da kujerarsa, ya karanta wani bayanin da ya bayyana a gabansa.
Sai ƙofar office ɗin ta buɗe.
Wata kyakkyawar baƙar fata ta shigo.
A kallo ɗaya za ka ce ƴar africa ce, duba da launin fatarta da kuma shigar dake jikinta. Sanye take da kayan Hausawa masu matuƙar kyau, doguwar riga mai ɗaukar ido, an yi musu ado cikin tsari. Ta saka mayafi a kanta wanda ya yi mata kyau sosai, yayin da fuskarta take ɗauke da nutsuwa ta musamman.
A hankali take tafiya kai kace kaman ba za ta taka ƙasa ba, tana tafiya cikin jan aji da natsuwa.
Laith kuwa yana zaune a gaban system ɗinsa, idanunsa a kan screen, hannunsa yana motsa mouse a hankali.
Ta tsaya kusa da shi.
“Breakfast is ready.” ta furta da muryata mai daɗi.
“Give me five minutes.”
Ta girgiza kai, duk kuwa da tasan baya son gardama.
“No.”
Laith ya ɗago kai a hankali ya kalleta.
“No?”
“Yes. You said five minutes ten minutes ago.” ta ɗaga mai kirarta ɗaya.
Laith ya shafa gashin kansa ba tare da yace komai ba, na tsawon minti 2, ita kuma tana tsaye ko motsi bata yi.
“I have something to finish.” ya faɗa da ƙyar kamar wanda aka yi ma dole.
“You have something else to do.”
Ya ɗan daure fuska.
“What?”
Ba tare da ta yi wata magana ba, sai ta miƙa hannunta zuwa akan system ɗin gabanshi, ta danna wani abu, take screen ɗin ya ɗauke.
Laith ya tsaya yana kallonta bai ce komai ba.
“You just turned off my system.”
“Yes.”
“Why?”
Ta kalli agogon hannunta, sannan ta ɗago idanu ta kalle shi.
“You have twenty-one minutes before your meeting at the Grand Meridian Conference Hall.”
Laith ya ɗan yi shiru.
Sai ya gyada mata kai a hankali.
“Fine.”
Ta juya a hankali.
“Good.”
Ya bi ta da kallo na ɗan lokaci kafin ya ɗau dogon lokaci ya miƙe sannan ya rufa mata baya.
Bayan ya yi breakfast, ta tattara kayan da ya ɓata, already Laith ya shirin office amma yau a privet office ya fara aiki kafin ya fita.
Bayan ta gama ta nufa office ɗin. Ta iso gaban Laith sannan ta tsaya mai a kai.
Laith bai ɗago kai ya kalleta ba, ya ce.
“You’re late.”
Ta amsa cikin nutsuwa.
“By thirty-seven seconds.”
Sai Laith ya ɗago kai ya kalle ta.
“You counted?”
“I always count.”
Laith ya jinjina kai.
“Of course you do.”
Sai ta miƙa masa wayarsa.
“Your phone.”
Laith ya karɓa daga hannunta.
“Thank you.”
Ta gyada kai.
“You have three missed calls. Two from your office and one from an unknown number.”
Laith ya duba wayar.
“Anything important?”
“The first two are work-related. The unknown number called twice.”
Laith ya ɗan kalli fuskarta.
“And you answered none of them?”
“You instructed me not to answer unknown calls.”
Laith ya ɗan lumshe ido.
“Good.” Har za ta juya sai kuma tace.
“Your meeting starts in ten minutes.”
Laith ya koma kan system ɗinsa.
“Cancel it.”
Ta ɗan dakata.
“Do you want me to give them a reason?”
“Tell them I'm busy.”
“That is not a reason.”
Laith ya ɗago ya kalle ta.
“For them, it is.”
Ta gyada kai.
“Understood.”
Ta juya domin fita.
Laith ya sake kiran ta.
“Maya.....Wait.”
Ta tsaya, sai kuma ta ɗan juyo tana haɗe fuska.
“Yes?”
Laith ya kalli fuskarta na ɗan lokaci, sannan ya ce:
“Come here.”
Ta dawo ta tsaya kusa da teburinsa.
Laith ya kai hannu ya kama nata hannun, sannan cikin kulawa yace.
“Maya, what’s bothering you?”
Maya ta girgiza kai.
“Nothing, Sir.”
“No, tell me... what’s wrong?”
Baki ta ɗan tura gaba.
“Nothing, Sir.”
Sai ya ce.
“Are you sure?”
“Yes, Sir.”
“Then why are you acting like something is wrong?”
Maya ta yi shiru na ɗan lokaci.
Sai ya ƙara cewa.
“Maya, you can tell me.”
Ta ɗago kai ta kalle shi.
“There’s really nothing wrong, Sir.”
Ta kalli Laith na ɗan lokaci, sannan ta ce.
“I think I should leave now, Sir.”
Ta miƙa hannu domin ɗaukar key ɗin motarsa, amma Laith ya yi saurin hana ta.
“Wait.”
Maya ta tsaya, ta kalle shi cikin ladabi.
“Yes, Sir?”
Laith ya sake fuskarsa, ya yi shiru na ɗan lokaci.
“Take the key and leave. But be careful.”
Maya ta ɗan tsaya.
Sai kawai ta saki jikinta, murmushi ya bayyana a fuskarta.
“Thank you, Sir.”
Ta ɗan matsa kusa da shi, ta sumbaci goshinsa cikin gaggawa, sannan ta juya ta fita.
Yasan inda za ta je, shi yasa bai hanata ba, yana dai fatan ta dawo lafiya ba tare da dauko mai magana ba, dan tsaf za ta iya faɗa da kowa.
Hannunsa mai haske, wanda yake ɗauke dogayen yatsu, a jere cikin tsari da ƙudurar Ubangiji, ga farcensa farare da su kuma a yanke, hakan yasa hannun ya ƙara ƙyau.
Ya buɗe folder ɗin dake gefansa.
PROJECT: A.I. HUMAN ASSISTANT
STATUS: FINAL TEST PENDING
Laith ya jingina da kujerarsa.
Sai ya yi murmushi kaɗan.
Domin matar da ta shigo office ɗinsa ba kawai mataimakiyarsa ba ce.
Ta fi haka.
Ita ce mafi girman ƙirƙirar da ya taɓa yi.
Ta iya magana.
Ta iya fahimtar umarni.
Ta iya gane yanayin fuskar mutum.
Ta iya yin murmushi.
Ta iya nuna damuwa.
Ta iya girki, ta iya komai da duk abinda ya shigar ma na'urarsa. Ya sake kallon ƙofar da ta fita.
“Let's see how human you've really become.”
Sai ya lumshe ido, ita ce babban abinda zai gabatar nan da ɗan lokaci, so yake ya tashin kowa da Maya, dan kuwa abubuwan da ta iya, ko mutane dari ba za su kai ta ba, hakan yasa ta za ba Best ɗin sa ta kowani fanni.
Maya ba mutum bace, robot ce, amma ba kowa yasan da haka ba..............
★★★★★★★★★★
Mama ta ce,
“Alhaji, barka da zuwa gidan Garkuwar Mata. Ga mu da ƴammata wayayyu, ƴan harka, sai wanda ka zaɓa.”
Alhaji Naira ya gyara zaman babbar rigarsa, sannan ya jingina da kujerar yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.
“Ina so kowacce ta gabatar min da kanta. Ina son wacce za ta fi kowacce burge ni.”
Mama ta musu alama da kai.
Take, kowacce ta fara gyara zaman ta, wasu suka ɗan saki murmushi.
Daga nan sai ta farko ta tako a hankali ta tsaya a gabansa, cikin ranƙwaɗa da iyayi, ta tsaya gabansa tana cewa.
“Sunana Raliya. Amma a nan ana kirana da Raliya Beauty. Na shafe shekaru ina wannan harkar, kuma duk wanda ya zo nan ba ya mantawa da ni, dube Ni Alhaji daga sama har ƙasa.” ta juya ta koma wajen zamanta tana girgiza jiki.
Ta biyu ta tako gaba.
“Ni kuma sunana Hadiza. Ana kirana Haddy. Ina son kyau, ado da kwalliya, kuma ina da iya mu'amala da mutane sosai.” ita cikin na ta salon iyayin ta yi magana.
Ta uku ta matso da ƙarfin hali.
“Sunana Samira. Kowa a nan ya san ni da Samira Sweet. Saboda zaƙi da garɗi na ake kirana da wannan sunan.”
Wata ta huɗu ta fito tana murmushi.
“Sunana Rufaida, haka kuma banci sunan a banza ba, akwai abubuwan.” ta girgiza ƙirjinta tana wani banƙara makar kaza.
Ƴam matan suka yi dariya.
Sai ta biyar ta fito. Ta tsaya gabansa tana kallonsa kai tsaye.
“Sunana Nafisa. Amma an fi sanina da Nafisa Gold. Ni sabuwa ce a nan, amma Garkuwar mata ta ce idan na fara harkar nan, ba zan yi nadama ba, sabuwar jini ce, sabuwa fil” ta kashe mai idanunta.
Alhaji Naira ya yi ɗan murmushi, yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.
Amrah wacce ta sha fitted gown itama ta fito, ta gabatar da kanta, ta koma ta zauna, haka Hawanzeey, Rukky, Zee-Zee, Ayusha.
Ina daga ɗaki nake leƙe ta window, wani na kwashe da dariya, wani na zaro ido. Dariya na fara yi ina toshe baki, ganin Beasty (Dan daudu) ya fito.
Sanye yake da doguwar rigar atamfa, ya kashe ɗauri, sai wani fari yake yi.
Mama ita kanta dariya ta ɗan yi.
“Alhaji muna da ƴan daudau, suma ba baya ba wajen harka.”
Beasty ya tafa hannu.
“A hayye casss, Garkuwars faɗa masa dai, Nima kamar su nake, zamzam, ciki da waje ba ƙyarya, na sha gyara, dube Ni da ƙyau.” ya jujjuya, yana buɗe hannu kaman tantabara.
Alhaji Naira yayi dariya.
“To shike nan, koma baya.” Beasty ya juya ya ci gaba da tafiya mai cike da jan hankali.
“To Alhaji, Hausawa sun ce, Kuturu da kuɗinsa, Alkaki sai na ƙasan ƙwano. Dan haka ka zaɓa ka dirje.” ya jinjina kai, yana sake duban matan ɗaya bayan ɗaya.
Ganin Mama ta nufo inda nake sai na bata hanya ta shigo ciki dan a bayan labulen ƙofa nake.
“Ki kawo mai abinci da drinks ɗin yanzu.....”
“To Mama.” na faɗa ina kokarin juyawa baya.
“Ke.”
“Na'am Mama.” na kalleta da sauri.
“Ƙarfe 8pm, Alhaji Sani zai zo wajenki....wallahi Sakeenat kina da farin jini, a iya yau, kin samu customer 13, sai na basu kowa kwana ɗaya, kafin ki saba, da kin saba ma, a rana kina iya gamawa da maza biyar, dan haka dole sai kin dage da shan maganin ƙarin ni'ima, dana infection.” na jinjina kai cikin takaici da ƙyama.
Mama ta juya ta fita.
Na riga na tsara, duk wanda Mama za ta haɗa Ni da shi, zan je, amma da zarar an bar mu tare, zan roƙe mutum, na yi kuka sosai, nasan za su ƙyaleni, hakan yasa na rage damuwa.
Na gyara hijabin jikina na ɗauki tray na fita.
Na isa wajen na yi sallama, sannan na aje tray ɗin gaban Alhaji.
“Ina wuni.” na furta kaman mai jin tsoron wani abu.
Ban jira ya amsa ba, na juya da sauri jikinsa kuwa yana ta uban rawa, wai haka ma hijabi na sanya.
Taku ɗaya, biyu, uku.
“Ke.” na tsaya cak jin Muryar Alhaji Naira, a saitina.
Na juyo a hankali, dan ƙyaryata bani yake kira ba, sai dai ba shi kaɗai ba, kusan gaba ɗaya mutanen wajen Ni suka zuba ma ido.
Jikina ya fara rawa saboda ban san abinda na yi ba..
Na yi sauri na dawo kusa da shi, na tsugunna cikin ladabi, ina cewa.
“Alhaji kayakuri idan na yi maka wani abu, kuskure ne, kayakuri....” na faɗa a hankali, take kuma na ɗaga idanuna farare masu ƙwantaccen ruwa a ciki, na kallesa.
“Ba ki yi komai ba ƴam mata, ya sunanki!?.”
“Sakeenat.” na faɗa ina wasa da yatsun hannuna, jin ya yi magana da sanyin murya.
“Garkuwar Mata, wannan na zaɓa ta yi min dari bisa dari....ko nawa ne farashin ta zan dinka gomansa.” ya kai nan yana ci gaba da murmushi, idanunsa kuwa a kai na.
Karo na barkatai gabana ya sake faɗi, na sake kallonsa, Ni ɗin dai yake kallo, na kasa cewa komai.
“Ki Turo min ita waje yanzu.” yana faɗin haka ya fiddo maƙudan kuɗi ya aje ma Mama wacce mamaki ya kusa sumar da ita.
Kaman jira ake yi, Alhaji na fita, ƴam matan nan suka yi kaina da sunan za su duke Ni. Wasu sun fara zane-zane.
Garkuwar mata ta daka musu tsaya.
“Mai ta yi muku!? Kar wani ya kuskura ya taɓa ta......Zo nan Sakeenat.” na share hawayen idanuna, na isa kusa da Mama.
“Ki je waje yana jiran ki, duk abinda yace karki mai musu, idan tafiya zai yi da ke, ki bishi kawai, wallahi Sakeenat idan kika bashi haɗin kai sosai, za ki ci riba.......” Na fashe da kuka mara sauti ina girgiza kai.
“Ke zan ci kumar uban can, bansan iskanci, tashi ki bani waje, Allah yasa ki mai hauka sai na karya ki, banza shashasha.” ta dungure min kai.
Ba musu na tashi na yi hanyar fita.
Daidai nan *wata ƙaddarata ta sake sallama.*
Na gaishe da Aunty Duwais, ta amsa cikin sakin fuska, ta wuce ciki, Ni kuma na yi waje.
Wata babbar baƙar mota na iske gefen gidan mu, na isa wajen, take aka buɗe min ƙofa.
Karo na farko da na shiga cikin mota irin wanan kenan, sai dai bana cikin yanayin jin daɗi gaba ɗaya.
Take na ji ya sanya lock, sai kawai na ji hannunsa akan fuskata, ban yi kokarin ture shi ba, na kalla fuskarsa.
“Karo na farko da na ga mace ta burge Ni, idanunki suna da matukar jan hankali, wayyo Allah, leɓan nan zai yi taushi sosai.” na rintse ido jin hannunsa akan leɓena.
Alhaji Naira ya kasa leɓansa na kansa sannan yace.
“Zan yi magana da Garkuwar mata, gaskiya Ni na samu ta hannun dama, za ki zama min inuwa, dan daga yanzu duk inda zan kasance kema za ki zama a wajen.......zamu fara more rayuwa kafin na aureki, dan ba zan bar wannan zazzafar ta wuce Ni ba.” ya ciza leɓensa sannan ya figa mota.
Na yi saurin rintse ido ina karanto duk addu'ar da ya zo bakina, ga tunanin inda zai kai Ni nake, dan tafiya kawai muke yi akan titi, lokaci zuwa lokaci muke haɗa ido, sai ya kashe min ido ɗaya, ko ya kama hannuna ya matsa cikin shauƙin giyar huɗubar shaiɗan...........................
★ Aunty Duwais ta zauna kusa da Garkuwar mata, ta aje baƙar jakkatar gefe guda.
“Akwai labari mai zafi Ƙawatah.” Garkuwar mata ta gyara zama, ta kalleta ba tare da mamakin abinda ya faru ya sake ba.
“Shafamin mana.”
“Ina wannan aikin da muka taɓa magana dake akan za ki tura Sakeenat!?.” Garkuwar mata ta ɗan yi tunani kaɗan sannan ta ce.
“Na tuna.”
“Yauwa, yanzu wannan ƙawartawa ta kira Ni, tace sun fara ɗaukan sabbin ma'aikata, duk wata ana biyan kuɗi masu yawan gaske, tunda Sakeenat taƙi harka, kawai ki tura can, ki dinga samun kuɗi.” Garkuwar mata ta zaro ido.
“Hmmm kin kawo babban shawara kam, dan haka na miki alƙawarin 20% na aikin na ki ne, 80% na wa ladan raino.........to wani gudu ba sauri ba, ya zanyi da Alhaji Naira.” Garkuwar mata ta bata labarin abinda ya faru yanzun nan.
Aunty Duwais ta yi murmushi.
“Ki ce lokacin da za ki girba wahalar da kika yi ya zo, ki bari kawai ya mora ƙuruciyarta sosai kafin lokacin tafiyar ta su ta yi, Kinga riba biyu kenan.” suka yi shewa harda tafawa.
“Wani ƙasa ce ma!?.”
“Bara na duba, dan manta sunan nake yi.” Aunty Duwais da buɗe wayarta, ta duba cikin Whatsapp, sannan ta saki murmushi ta ce.
“JORDAH......” Sai suka sake yin dariya........
Abinda ba su sani ba shine, tsarin da Allah ya yi ma Sakeenat ya sha bambam da rayuwar da suke hange.
Duk kuwa da Sakeenat wannan shine mataki na gaba da za ta ƙara ɗanɗanar wata ƙaddarar mara daɗi, ƙaddara mai wiyar fassara, ƙaddarar da za ta yi kuka ta gode ma Allah, sai dai ku sani.....duk bayan wiya akwai.......DAƊI...........
★Tabbas yanzu zamu fara littafi, yanzu wasan zai soma, yanzu sabon shafi zan buɗe, ba sai na ce komai ba, mu je, mu haɗu kawai, SAKEENAT BAMBANCIN RA'AYI 😍 tashin kai over🥹
🔥📚 SAKEENAT — BAMBANCIN RA’AYI 📚🔥
Kin kai CHAPTER 26 kuma kin ga abin da ya faru… 😭🔥 Yanzu fa WASAN YA SOMA! 👀💥
Idan kina son ki ci gaba da samun sabbin pages/chapters ba tare da jira ba, ki shiga PAID GROUP ɗin littafin. 🔐📖
💰 JOIN NOW — ₦300 kacal!
📌 Bayan an kammala littafin gaba ɗaya: ₦700
💳 PAYMENT: Sakina Abdullahi OPay: ***
📲 Bayan kin biya, ki turo proof of payment domin a tabbatar da shigar ki group.
🔥 SAKEENAT — BAMBANCIN RA’AYI Yanzu wasan zai soma… 😍📖✍️
PRETTY SK CE ❤️