ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 8

by @ibtisamwrites01

………………….
                   ZAREN ZUMUNCI
            (The thread of family bond)
   
                      WRITTEN 

                           BY

               IBTISAMWRITES ✍️

    

PAGE 8
Toh, bayan ya je ya haɗu da Alh. Lawal ɗin, sun tattauna akan batun. 

   Shi Alh. Lawal ɗin yayi na’am da zance, sai dai ya ce zai samu yaran na shi yayi magana da su, duk da ya san duk abin da ya ce musu shi za su yi ba musu.
 
Haka nan bayan ya koma gidan, ya samu matansa duka ya ce yana da magana da su.
 
Suka ce,
 
“Toh Alh., ba matsala.”
 
Suka zazzauna suna jiran su ji da me ya zo.
 
Bayan sun zauna, ya ke ce musu yanzu nan suka gama magana da Alh. Aliyu. Ya zo wurinsa da maganar yana son a haɗa ’ya’yansu aure don a ƙara dankon zumunci.
 
Dukkan su ba a samu matsala da su ba. Sun yi na’am da zancen, suna farin cikin haɗa zuri’a da Alh. Aliyu da Hajiya Zuwairah.
 
Hakanan suka samu ’ya’yansu da batun. Duk su ma cikin kunya suka amsa, suna sunkuyar da kai ƙasa.
 
Amma ba ta haƙura ba sai da ta saka shi ya zama ya yarda da abin da take so. Sannan ta sauko suka shirya.
 
Hakanan ta sa shi ya kira Alh. Lawal ɗin, akan idan yana gida ne yana son ya zo su tattauna akan wani batu.
 
Ga shi yanzu an ɗauko musu maganar suna zaman-zaman su hankali kwance.
 
Wasu ma ba su da aure a cikin budget dinsu a yanzu. Sun fi so su yi rayuwarsu kafin wata ta shigo ciki.
 
Haka dai kowa ya tafi yana ta tunani kala-kala.
 
A can ɓangaren gidan Alh. Lawal kuwa, ’ya’yan na komawa ɗakunansu suka rinka tsalle suna murna cewa za su yi aure.
 
     Ga shi yanzu an dauko musu maganar suna zaman zaman su,hankali kwance.
 
Ibtisamwrites✍️