ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 9

by @ibtisamwrites01

………………..
                    ZAREN ZUMUNCI 
            (The thread of family bond)


                        WRITTEN 

                
                             BY


                IBTISAMWRITES ✍️
    

PAGE 9
 
Wasu ma ba su da aure a cikin budget dinsu a yanzu. Sun fi so su yi rayuwarsu kafin wata ta shigo ciki.
 
Haka dai kowa ya tafi yana ta tunani kala-kala.
 
A can ɓangaren gidan Alh. Lawal kuwa, ’ya’yan na komawa ɗakunansu suka rinka tsalle suna murna cewa za su yi aure.
 
Kuma waɗanda suke crushing akai, su aka ce za a aura musu, shi yasa suke cikin farin ciki da annushuwa.
 
A kwana a tashi, a cikin wannan yanayi aka yi sati biyu da yi musu maganar aure.
 
Sannan a cikin kwanakin nan, mafita ɗaya ya samu ita ce ya je wajen Abba ya faɗa masa abin da ke ransa. Kawai ya san zai goyi bayan shi.
 
Haka gari na wayewa, bayan sun dawo daga mosque, ya ce,
 
“Abba, ina da maganar da nake son mu yi da kai.”
 
Abba ya ce,
 
“Toh, Moddibo.”
 
He sometimes calls him Moddibo because he has his name.
 
“Mu shiga daga ciki tukunna, then we can talk.”
 
Bayan shigarsu ciki, sun shiga cikin palon Abba ɗin. Anan ne Aliyu ya faɗa masa maganar Amna da yadda ya faɗa wa Inne, amma ta ƙi karɓar zance.
 
Alhaji Aliyu yayi shiru. Sai can ya ce,
 
“Ta shi ka je, Aliyu. I will talk to her, and if she still doesn’t agree, I know what to do.”
 
Sai Aliyu ya tashi ya tafi, yana mai farin ciki saboda ya samu an goyi bayan shi.
 
Bayan sun gama maganar da Aliyu, Abba ya je ya samu Inne yayi mata magana, amma ba ta yarda da maganar ba.
 
Ta ce,
 
“Ai babu wannan aure, tun da ita yarinyar ma ba a ƙasar take ba. so zancen ma is cancelled.”
 
Ran Daddy in yayi dubu ya ɓaci.
 
Ya ce,
 
“Haka kika ce?”
 
Ta ce,
 
“Eh, Alh., haka na ce.”
 
“Haka ne? Shikenan. Tun da haka kika ce, to nima bari kiji me zance miki. Ki buɗe kunnuwanki ki jini da kyau.”
 
Ya ce,
 
“If kika ga Aliyu bai auri yarinyar nan ba, to bana da rai ne. In kuwa ina da shi, kamar an yi auren an gama ne.”
 
Ya tashi ya fita ya barta baki sake, ta kasa cewa komai.
 
Haka nan bakin Inne a hangame, saboda ba ta taɓa kawo wa a ranta cewa mijinta ba zai goyi bayan ta ba.
 
Tun da tun farko ya riga ya san tsarin ta, not her yin la’akari da shi ma cewa yana da nasa tsarin. Yana dai bin bayanta ne for peace to reign.
 
Amma tun da haka ta zaɓa, shikenan.
 
ABBA yana gama wannan maganar da Inne ya fito daga ɗakin nata. Ran shi ba ce ya ce bari ya kira Alh. Lawal su yi maganar, kar ta yi nisa, bayan ya san ana can ana ta shirye-shirye.
 
Alh. Aliyu called his friend, Alh. Lawal, and said,
 
“I have something to tell you, and I want you to understand me.”
 
Alh. Lawal said,
 
“Okay. Where will we meet?”
 
Alh. Aliyu sai ya ce,
 
“We should meet in the restaurant we usually go.”
 
And Alh. Lawal agreed to it. They agreed to meet in the evening.
 
Lokaci yayi da za su haɗu. Bayan sun haɗu suka gaisa sannan suka samu wuri suka zauna.
 
Anan ne Alh. Aliyu ya faɗa masa me ke faruwa.
 
Ya ce,
 
“Alh, na san ka san cewa you are my friend since childhood, kuma kasan ’ya’yanka ’ya’yana ne. Ba zan so wani abu ya cutar da su ba, ko kuma ni in cutar da su.”
 
Alh. Lawal ya kasa gane inda maganar ta dosa, sai ya ce,
 
“Alh, wace magana kake yi ne? Ni ban gane akan me yasa kake wannan magana ba.”
 
Sai Alh. Aliyu ya ce,
 
“Akan yaran nan ne. Kasan an yi maganar za a yi auren su. So sai shi Aliyu ya zo min da wata magana, na ce ya kamata na samu na zo wurin ka mu tattauna ta.”
 
“Aliyu ya ce min yana da wadda yake so ya aura, mai suna Amna, amma ba anan suke ba. A India suka haɗu. Ya ce ba ya son ace sai dole an haɗa aurensa da Maryam, saboda ba zai taɓa samun farin ciki ba, ita ma ba za ta taɓa samu ba.”
 
Shi ne na ce wannan zance na wai a ji shi kuma a ƙi ɗaukan mataki ne kawai ba. Saboda ko da an yi auren, ba za su yi farin ciki ba.”
 
Alh. Lawal yayi shiru. Sai can ya ce,
 
“Gaskiya ne abin da ka faɗa, kuma hakan shi ne daidai. Don kar a zo saboda abin da muke so, su kuma su zo su cutu.”
 
Ya ce,
 
“Wannan magana ta Maryam da Aliyu an kashe ta anan har abada.”
 
Alh. Aliyu ya ce,
 
“Ba wai na faɗi wannan da wani abu bane. Naga kamar ka ɗau zafi.”
 
Sai Alh. Lawal ya ce,
 
“A’a, ba zafin da na ɗauka ba. Haka abin ya kamata ya kasance.”
 
Alh. Aliyu yayi murmushi ya ce,
 
“Toh shi kenan.”
 
Anan suka yi order ɗin abinci suka ci cikin raha da farin ciki.
 
 
 
Ibtisamwrites✍️