ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )
PAGE 10
……………….
ZAREN ZUMUNCI
(The thread of family bond)
WRITTEN
BY
IBTISAMWRITES ✍️
PAGE 10
Daga ɓangaren Fauziyya kuma, tun maganar da suka yi da Inne ta rage walwala da duk wani abu da take yi a cikin gidan, don kawai ta nuna ita fa wannan hukunci be yi mata ba.
Ko da Inne ta ga haka, sai ta ƙi ta nuna cewa ta kula da abin da take, ta ci gaba da harkokin ta.
Duk damuwa ta yi mata yawa. Tana zaune tana saka da warwara sai kawai wani tunani ya faɗo mata ta ce,na San me zan yi kawai.Ta ce :
Yes, Abba zan je na faɗa wa na san in ya ji zai yi wa Inne magana.”
In her own thoughts tana cewa, in an yarda sai ta ce har Yaya Aliyu ma ba ya son auren, not knowing shi matter ɗin shi tuni ya kai gaba. Jira kawai take ya ga abin da zai faru.
A can bangeren su Alh Aliyu da Alh lawal kuwa,bayan sun gama cin abincin sun fito, sai Alh. Lawal ya ke cewa,
“Yaushe ne za su je nema wa ɗan nasu auren Amna?”
Alh. Aliyu was shocked, amma bai nuna a fuska ba.
Sai yake cewa wa Alh. Lawal ɗin ya fara zuwa ya faɗa wa matansa abin da ke faruwa. Daga nan sai su daura daga inda suka tsaya.
A nan suka yi sallama, kowa ya shiga motarsa aka ja su zuwa gida.
Washegari, Alh. Lawal ya kira matansa ya ce yana da maganar da zai fada musu.
Suka ce,
“Toh, ga su nan zuwa.”
Haka suka gama abin da za su yi suka tafi wajen sa.
Anan ne yake fada musu what transpired between him and Alh. Aliyu yesterday.
There was this silence that followed after Alh. Lawal had finished saying what he was supposed to say.
Then his wife, Hajiya Lubna, said,
“Allah yasa haka shi ya fi alkhairi.”
Hajiya Zainab ta biyo baya da addu’a irin tata.Duk da a cikin ransu sun ji babu dadi ko kadan.
A nan zaman ya zo karshe, suka tashi kowa ya koma sashensa.
Bayan ya gama magana da matayen nasa, sai ya kira Alh. Aliyu ya ce ya fada musu, kuma sun karba hannu bibbiyu, sun yi addu’a.
Alh. Aliyu ya ce,
“To, Alhamdulillah. Abin da ake fata kenan.”
Sai Alh. Lawal ya kuma tambaye shi,
“Yaushe za su je nema wa Aliyu auren?”
Sai ya ce da ya fi son in aka gama wannan bikin sai aje nema masa aure.
Sai Alh. Lawal ya ce,
“A’a, gwara dai aje a nemo masa auren. In yaso sai a hada auren tare da ’yan uwan.”
Sai Alh. Aliyu yayi na’am da zancen.
Ya ce,
“Shikenan, hakan za a yi.”
A haka suka tsaida ranar da za su tafi can India neman auren.
Ibtisamwrites✍️