THE THRONE OF THORNS

THE WEIGHT OF INFLUENCE

by @maryam730

‎Kano state
‎
‎KB
‎
‎Ganin kamar raina musu hankali yake,yasa suka kira masa ƴan sanda.Nan da nan ƴan sandan suka kwashe shi suka yi police station dashi.
‎
‎
‎Tunda suka je station ɗin yake ihu yana iface -iface kamar wani zararre.Wani ɗan sanda ne a cikin su ya daka mai wata muguwar tsawa,nan da ya shiga hankalinsa  aka garƙameshi a cell.sai sambatu yake yana cewa wallahi ina da kuɗi sai kuka rus-rus yake.
‎
‎Bayan ya gama jigata a cell ne, kuma ƴan sandan sunga ba abincin daza'a ba shi yasa suka tambaye shi ya bada number wani nashi,da ƙyar ya iya karanto number ƙanwarshi.
‎
‎
‎Kiran farko number ta shiga amma sai data kusa tsinkewa kafin a ɗaga.Bayani ɗan sanda yayi mata kafin daga can tace "malam nifa ina da abinyi,may be idan naga da sarari zan shigo".
‎
‎Sakin baki ɗan sandan yayi kafin kuma yaji kit an kashe kiran.Girgiza kansa yayi yana faɗa a ransa " Allah ya bamu ƴan uwan da suke son mu suka damu damu".(Nima na amsa da Ameen ya rabbi)
‎
‎
‎Sai wajen 10 na dare,kafin wata yarinya wacce ba tafi shekara 23 ta shigo sai taunar cingum ta ke ƙas-ƙas,taci uban no respect baƙi,wanda  ya cinye rabin fuskarta,ga gashin doki.

Wata shegiyar fitted gown ce a jikinta ta wani fabric mai kwanciya a jiki sosai.Ga ta dai kamar muciya amma haka ta saka kayanan da suka tona asirin duk wani lungu da saƙo na jikin ta.
‎
‎
‎
‎Wani irin kamshin turare ta ke na tashin hankali amma hakan bai dusasar da ƙarnin bleaching ɗin da take ba. 
‎
‎
‎Duk idanun kurtun dake tsaye a gurin ne ya dawo kanta har ta ƙaraso.Kafin ta musu wani kallon banza tana ce musu,"ji mana 
,nace KB nazo beli",wani ɗan sanda ne wanda da ya keji da zafin kai yace " ke an gaya miki nan gurin wasan yara ne da zaki shigo kina tauran cingum".Wani yatsine fuska tayi tana cewa "kai dalla rufe mana wani bakin ka mai hamami" ta kara sa faɗa tana toshe hancin ta .

Habawa ay sai yayo kanta yana cewa "ke ɗan uwarki nine mai warin bakin,ke ni sa'an ki ne dan baban-baban ki",da sauri sauran ƴan sandar suka riƙo shi suna "Ba girmanka bane mutumi na".
‎
‎
‎Shi kuwa sai hura hancin sa yake yana cewa "ay da kun ƙyale ta na nuna mata ni ɗan ganye ne,ƙaramar mara kunya".
‎
‎DPO ɗin dake ciki ne ya ɗaga murya yana cewa,"wai hayaniyar mai nake ji ne". Wanda aka gama rigimar da shi ne yana murmushin mugunta ne yace "Sir,wata ce tazo zata nuna mana rashin ɗa'a".DPO ne yace a shigo da ita.
‎
‎
‎Nuna mata hanya yayi yana cewa ƙaramar karuwa muje mana.Haka ta shiga gaba tana tafiya sai murguɗe-murguɗe take.(ko ina abun murguɗawae ohoo🤣🤣)
‎
‎
Lokacin da suka ‎shiga DPO ɗin ya shiga toilet,yarinya sai wani baza ido take tana huhhura hanci.Shikuwa ɗan sandar yaƙi fita ya tsaya sai ya ga ƙwal uwar daka.
‎
‎
‎Fitowa yayi yana gyara wando sa, tsaya yayi DPO ɗin yayi a ƙofar yana wani washe baki yace "ah ah dagirman kujerar ki,kece yau a gari,ashe rai kanga rai" ya ƙarasa faɗa yana karasa kujerar dake facing ɗin ta ya zauna.
‎
‎Wani murmushi tayi tana cewa "Ashe ma harkar gida ce,abin yazo da sauƙi",shi kuwa DPO da kamar an mai albishir da aljanna  ne yake cewa "REZA manyan ƙasa,wace tace ƴar iska ce ita ga uwar ta,iyayen ƙana nan ƙwari",Ita kuwa jin ana famfa ta sai ƙara ji take irin wata shegiya ce ita "DPO nawa",Saurin cewa DPO yayi "ah ay mu yanzu ki yadamu kin manta da asali,ke yanzu manya harkoki kike".
‎
‎
‎Murmushi tayi kafin tace " Ni dai yanxu ba wannan ba,haka yaran ku saka zama gaba ɗaya basu da da'a",nan ta fara bashi labarin ƙarya da gaskiya.Shikuwa ɗan sandan nan tunda ya ga sun fara magana alamar sun san juna ya ƙame guri ɗaya,kamar wanda yayi suman wucin gadi.
‎
‎
‎Tsawar da DPO ya daka mai ne ya dawo dashi hayyacinsa,yana cewa "Yes sir",Inda DPO ya fara kai dan abu ta kaza-kazan ka wannan tama kala da sa'ar ka ne" nan ya balbale shi da faɗa kamar zai ari baki.Har sai da REZA ta ga dama tace "ƙyale shi haka kasan yaro bai san wuta ba sai ya taka,na mai uzurin rashin sanin ni wacece".
‎
‎
‎DPO ne yace "je ka Allah yacece ka ba dan halinka ba mutumin banza mutumin wofi",Shikuwa ba abinda ya ke cewa sai sorry sir,har ya fita zuciyar na mai wata suya da tiririn cin mutuncin da wulakancin da mutanen nan suka yimai,tare da ɗaukan alƙawarin har dai kere na yawo zabo na yawo WATARAN ZASU HAƊU.
‎
‎
‎
‎Sai a sannan DPO ya kalleta yacce,"Ranki ya daɗe ay da da sai ki kira a waya ba sai kinzo da kanki ba har gurin nan,ba girmanki bane".
‎
‎Taɓe baki tayi tana cewa "Wallahi KB wai aka kama kuma ban san nan station ɗin kake ba ,shine nazo nayi bailing shi".
‎
‎
‎Subhanallahi DPO yace yana cewa bari kuwa yanxu da kaina in je in sa a fito da shi.Fita yayi yaje bakin kanta sai ihu yake musu ya bada umarnin a fito da shi kafin ya koma sai rawar ƙafa yake.
‎
‎Bayan mintuna kaɗan sai ga wani ɗan sandan daban ya shigo yace "Sir an fito da shi".

Tashi REZA tayi tana jan wayar sa da ke kan tebur ɗin sa.Number ta tasaka ajiki,kafin ta ɗago ta kalle shi ta kashe mai ido ɗaya tayi mai alamar ya kira ta da hannun ta 🤙 ta juya ta fara wannan tafiyar.Shikuwa DPO bin bayanta yayi da wani ɗan iskan kallo kamar maye,kafin ya buɗe bakinsa da ƙyar yana cewa "Toh sai mun haɗe tawaje na",yana lashe bakinsa.
‎
‎
‎Haka ta ta fice tana haɗuwa da KB an gama bashi kayanshi jikin sa yayi laƙwas,ko magana bayayi sai dai giɗa kai.
‎
‎
‎Haka su REZA da KB suka fice ko sisi ba su bayar ba balle suyi sign ko takardar tsire.......
‎
‎
‎
‎
‎
‎Lagos state
‎Grand CREST
‎
‎
‎
‎
‎Sabuwar duniya kenan,babu wani mahaluƙi da zai yi tunanin akwai irin wannan gurin a ƙasan GRAND CREST.Gurin da suka shiga kamar reception haka yake,wani jan haske ya haska gurin gaba ɗaya luxury furnitures da decor ɗin gurin Black ne.......end of chapter 14........ written by Muraimaa Naabba ✍️✍️
‎
‎
‎
‎
‎
‎