YAR MAULA

3-4

by @mamanteddy

A inda ta bar Oumman Nata ta ganta,saurin nufan ta tayi,hadi da daukar Sandar Ta tana fadin,Oumma na dawo ga sandar". Yowa Safiyyatu mu tafi gida ko?. Ehh Oumma,tace hadi da Shiga gaban ta Oumman ta Dafata suka Fara nufar Hanyar gidan su". Tafiya ce mikakkiya kunsan dai idan sun tafi yawon Maulan su,sai inda Allah yakai su,kuma a haka da kafaffun su suke dawo wa, duk kuwa nisar Inda suke Da Zama". A dai dai wani gidan Jarkasa naga sun tsaya,hadi da kutsa Kai suna shiga daga ciki,Zauren kam Na gab da Fadowa,Wannan nace inda lokacin damuna ne ,da kam tuni ya Dade da Rushewa". Bin gidan nake da kallo,wanda gidan dukan sa Ginin Yammine,Babu siminti bare kuma dabe". Ba wani girma ne dashi ba,don Daku na guda biyu ne a cikin gidan,sai kuma bayi da madafi". A tsakar gidan Oumma ta Zauna a kan tuebayan,tana Fadin Safiyyatu Kafin na shiga daga ciki,bani buta na Fara Alola,sannan sai na shiga gaba daya". Tom Oumma". Ta fadi hadi da kitsa,kan ta cikin kunta taccen Dakin,da ko inah Tsummoki ne,kulle,sai Wata Yar filangyen tabar mansu guda biyu,da suke kwana a Kai". A bayan kofan Langa² ta dauko butan hadi da fitowa tana baimawa Oumma. Dafata Oumman tayi hadi da nufan bandaki don tayi tsarki". Da takaita ne ta fito,bayan ta gama ta kuma kirar ta sannan ta Shiga hadi da dafota sukayo waje.sai da Oumma ta kammala Alwalan sannan ta kamata tana lalubar sandar ta sukayi cikoin soron ta". Da ta tayarda da Sallan ne,Safiyyatu ta fito hadi da Dauro Nata Alwalan ta nufo Dakin". Idarwan Su ba wuya suna zaune suna Laximi ne,sukajiyo muryan Malam Jume". Nan take kirjin Safiyyatu ya buga,Jikkn ta sai Rawa yakeyi,banjo labulan Dakin yayi,yana kirar sunan da Cewa" Safiyyatu..."Safiyyatu". Na'am Baba!!". Maza mikomun kudin Maulan naku nan,nima nasamu na cin Abinci". Shiru tayi tana Rarraba idanuwa cike da Tsoro da Zullumin koyaya zai fahimci Zan can Nata". Wani irin tsawa ya Daka mata". Kan yace" Ba mgn nake dake ba??!. Ehh..ehh Baba". Iskan ci ne da Rani yasako mun shiru kenan?!. A'ah kayi hakuri Baba!!". Munafuka!!! Mai taushi da lafaxin karya,A gida kiringayin kaman bai war Allah,nasan ma tayaya Akya samo kudin Maulan!!?. Maza bani nan na fice kan nayi kasa-kasa dake". Cike dajin dacin maganganun sa ga Diyar Nata,Oumma tace" Ai Malam ba kullum ne akye kwana a gado ba,mun Saba yo Maula mu kawo maka,tom kasan da yake Allah ne mai bayarwa,yau bamu samu ba'. Cike da Hayaniya da Hargogowa Yafara cewa" Ehhh Ramatu Dama nasan kece kk Hana yarinyan tayimun Alheri,kifah sani badon makantanki ne yasa ake baki Sadakar Maulahn nan ba,A'a Saboda wannan Yarinyan ne Safiyyatu'. Tom malam,na gode ma a hakan,nasan haihuwa tayimun Rana!!!". Tayi maki Rana,ko tayimun Rana!!. Ai da ninake jidali dake da lallurar ki,yanxu ne Allah yakawomun sauki,da har yanxu nine me dawainiyya dake". Yana kananun maganganu ya Saki labulan ya juya". Itakam Safiyyatu banda share Hawaye babu Abun da takeyi,ace kullum mahaifin ta tsakanin ta dashi,sai zagi kyara hantara,yayi ta zagin Oummanta,yana mawa Allah galatsi da makantan ta". Kuka takeyi sosai,a ranta tana kuma cewa" Shi a,kulum baida aiki daga ya zauna karkashin wannan bishi yayi bacci,sai in yagiji ya koma wata yasha Inuwa". Sune in sun nemo a wurin Maulan suke cida Kansu da Shi ma,ranar da basu samu ba,yy masifah yacimasu mutunci yayi ficewar sa". "Safiyyatu kuka kkyi ne??. Cikin Sauri cike da son Ta daidaita natsuwarta kar ta daga mawa Oumman Nata hankali ta yi saurin saka taffan hannun ta tana goge hawayen fuskar ta da cewa" A'a Oumma ba kuka nakeyi ba". Sai kawai Oumman tayi murmushi hadi da cewa" Safiyyatu Uwar Yan Amana,Safiyyatu har ilah yau ina Kara baki hakuri,kiyi hakuri da dik yanda Rayuwa take dake,wata Rana sai Labari...." Hmmm Oumma kibar wannan Maganar,wlh bakomai fa'. Murmushi oumman tayi bata ce mata komai ba ta cigabada da Zan caxbihan ta,tana mawa Kansu Addu'a".

*******************

ADAMAWA

Gidan Alh. Abubakar barau ne,wanda Akafi sanin sa kuma ake kiransa da (Alh. Habu Maloniya....)tun daga farkon sa har karshen sa mutane yayyame,yan Uwa da Abokan Arxiki duka Ana cikin farin cikin Dawowar Alh. Abubakar maloniyan,bisa ga jinyan da yayi na tsawon shekaru uku baya.....wanda alhmdllh a wannan Rana ne jirgin sa zai sauka gida Nigeria. Kowa a familyn farin ciki yake matuka da Dawo wans,wannan shahararran Attajirin,da duk fadin Nageria babu wanda baisan shi ba". Ko inah ne ya rikece,don har Hutu aka Saka,na babu aiki A gaba daya kasar,na jimamin ranar da Diyar sa ta mutu tsawon shekaru uku Baya,wanda wannan shine musabbabin kamuwar sa da ciwon Zuciya,da yadade yana jinya,a kasar China". Wannan kuma Rana shine ranar da ta zagayo shekaru uku kenan da mutuwar diyar tasa". Gaba daya fannin sadarwa ko inah amsa kuwa yake na Kara dadin ta'aziyar Yarinyan tasa Daya tilo da yayi,da kuma farin cikin samuwar lafiyan sa". Duk girman gidan nasa,sai da ya kasance babu masaka tsinke. Manyan mutane kusoshin gomnati da yan kasuwa,kowa Ya halitta gidan Alh. Maloniya don Tarbansa,banda Wanda Suke a Airport suna Zaman jiran saukan sa". Omar" Omar".... Cikin dajin Ba dadi da kuma fara fusata Omar din ya kalli Safwan da cewa" Ehemm Oga Inajinka". Safwan ne ya sunkuyar da kansa kasa". Kawai sai Hawaye ya Fara bin kun cinsa,wanda cikin sauri Omar yafara masa magana cike da Taushin murya da cewa" Haba Safwan,yaushe ne kuma a watta rana,zakayi hakuri ka rungumi kaddara na Rashin Bul-bul a Rayuwar ka??!. Tsawon shekaru uku ya kamata ka sani kayi hakuri kuma ka mance dakomai,Addu'a Zakayi mata". Kai Hannun sa Safwan yayi gami da daukar Hankie yana Goge hawayen kan fuskan sa,cikin Dauriya yace,Omar na dade da hakurin Rashin Little bul-bul,Amma Zuciyata takasa Juremawa Rashin Ta kusa Dani". Da soyayyar Ta na taso,kuma na girma,kuma dashi Zan mutu". Maryam da Sakkowanta kenan daga Step tana karakowa duk maganar Sa ya sauka a kunnen ta,cike da Dauriya ta nufesa tana cewa" Yah Safwan na Tafi". Kasa bata amsa yayi kawai sai dai daga mata kai". Omar ne yayi saurin cewa" Okay Maryam sai mun karaso". Tom Allah ya kawoku lfy!!". Kan ya bata amsa tayi saurin ficewa daga Dakin,Tana jin babu dad I,don tuni idon ta ya kawo ruwa". A cewanta itah da mijin ta,baya Nuna mata kulawa da kauna,sai dai Kanwar sa matansa ta baya,wanda ta Dade da isah gidan Gsky??!. Tuni hawaye ya jika fuskar ta,da Sauri ta shiga moto yayi da Driver ya rufo ta yana zagayawa yana Jan ta don nufar gidan Alh. Abubakar Maloniya". Da fitan ta ne Omar ya kalli Safwan yana cewa" Haba Safwan kayi hakuri ka ringa daure mawa Rashin bul-bul kodon matarka,mata fa da kishi a kasansu,bazata ringa jin dadI ba". Nisawa Safwan yayi gami da tabe baki,cike da Nuna ko ajikin sa,don shi a ko inah zai Nuna soyayyar Bul-bul,don baiki ya rabu da kowa a kan ta ba,duk da ta Mutun,cike dajin ma zafin maganar Aminin nashi yace"Bai dameni ba,Tun Kaminn na Auri Maryam,na fadeta cewa" Bazan sota kaman Nanah ba". Kuma bazan hada soyayyar wata ya mace da itah ba,wannan alkawari ne nayi mata tun tana a Raye". Baki sake Omar yake bin sa da kallo,Har Ya mike yana mayarda hularsa da cewa" Zamu iyah tafiya don yanxu Daddy ya Sauka suna airport". Hmm babu magana Oamar ya mike hadi da ficewa kowannen su moton sa ya hau hadi da nufan gidan Alh. maloniya". Zaune take Tasha Ado na mata masuji da Aji,cikakkiyar mace wanda a shekaru zata kai Arba'in da biyar". Matace dattijuwa maiji da Karfin dukiya ga Hutu,Wanda sanye take cikin Dinkin Shadda Yar galila mai kyaun gaske". Wanda yake dauke da Launin Coffee brown". Hannun ta kam Tasha Jan lallae wanda yake dauke da Awarwaron Gold. Fuskan nan babu wani make Powder sai lipglow tasaka....amma abun ka ga farar fata tuni ta haskaka,hadi da haskaka Wurin". Daurin Ture kaga tsiya tayi,yyn da tayi parking din kwantaccen Gashun ta mai tsantsi da sulbi ta kasa,daurin yayo sama. Saman wuyan ta kam ta Zuma masa sarkar zinare,da sai walwali takeyi". Hajiya Latifah kenan,mata kuma Uwar gida ta Wurin Alh. Abubakar Maloniya". Sunan mutanen ta na kyewaye da itah ne,amma hankalin ta na kan Hoton diyar tata,da ta mutu shekaru uku baya,yarinya mai shiga rai,wanda kallo daya nayi mata na fahimci baxata haura shekara Sha Bakwai a shekarun ta na haihuwa ba".

Tom fah!!!!

Chakwakiyar nannadaddiya kenan..

Ko wacece wannan yarinyar Alh. Maloniya??.

Kuma wacece wannan yarinyar da shi kansa Safwan Abokin Omar ke mata irin wannan Zababban son???...

Shikam Baba Jume wani irim mataccen Zuciya ne yake dashi haka,ace sai dai Makauniya da Yar ka suje Maulah sinemo su baka,ka kuma am she kaci???

Muje xuwa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Domun samun Cigaban labarin Littafin Yar Maulah zaki turo katin #100 MTN,normal kenan.

Idan VIP da VTU ne #200

SPC kuma #300 Duka ta wannan number ***.

Idan kuma Bank Account ne ta wannan👇 7782217014 Mohammed Hassana Fcmb.

Sai kiyi screen shorting ki turo shaidar biyarki ta wannan Whatsaap numbern👇 ***.

Naji comment naku ina godiya Allah yabar kauna. Ku tura zuwa wasu grps👏🏻

Mmn teddy🧸 [7/17, 12:38 PM] Maman Teddy🧸: Typing.......

*Y'AR MAULAH🦯*

Story and Written by: Mmn teddy🧸teddy🧸

*Alheri writers asso.*

*A.W.A*

```K'ungiya daya tamkar da dubu,masu aiki da ilimin su.Alheri sai Dan Alheri```

______________________________________