YAR MAULA

5-6

by @mamanteddy

"Karar motoci da Dana Mutanen da ya Karo yasakata fahimtan cewa" Alh.Abubakar maloniya ya sauka". Wanda cike da isah da Aji ta mike,Sauran matan na bin da kirari,Uwar gida Ta Alh.Maloniya. Tuni falon ya rikice da guda na Mata,Murmushi kawai take binsu dashi,wanda a hakan ta nufi Farfajiyar gidan,yan Uwanta da ma'aikatan ta na Mara mata baya". Farfajiyar gidan Babu masaka tsinke....domun ko ta koinah Mutane ne kye Bulbulowa". Wanda basu San ma daga inda suke ba". Nufo Mai gidan Nata tayi,a yau duk wani Annuri ya bayyana a saman fuskanta". Hayaniya ne ya karcame,yayin da Masu maulah da Maroka,suka Fara kirari da cewa" Allahu Akbar....Uwar gida Rangida,mata Tauraruwa mai Haskawa ta wajen Alh. maloniya uban B'ull...... Maganan Marokan ne ya datse,tuno da Abun dake faruwa,wurin kam duk yawan biladam nan,tsit kakeji,sai dai saukar numfashi. Cike da Dakiya da sanin Famin dasuka Dago masa,ya Fara Kitsawa hadi da nifan Bangaren shi". Wanda tuni idon Hjy. Latifah ya kawo Ruwa". Kasa bin bayan mijin Nata tayi,kawai sai ta juya hadi da nufar Part din ta". Aminan tane da Yan Uwa sukayo bayan ta,don Tabbas a yau sun San An debo mata Abun da ta mantashi,tayo hakuri ta kuma Dangana". Duk damuwar da Maryam ke ciki,awannan karon nufan Hajiya Latifah tayi don Rarrashin ta". Duk da taasan itama Nata damuwar duk akan wannan Yarinyar ce B'ul-b'ul.

"Maryam yana kejin kaman muryanki na cikin wata damuwa"?.Hmm Laylah kenan,aini dama Kullum indai damuwa ne a cikin ta nake". Wlh har nagaji da itah,Amma Yaya xanyi tunda Damuwar ta xama jinin jikina,dole sai Hakuri". Hajiya Layla dake kishin Gide ana yarfa mata Lallaen Zane ne,ta mike daga Zaune,tana Fadin" Hmmm ban gane ba??. Meke faruwa ne,badai har Yanxu Safwan Ranshi da koman shi na kan wannan Shegiyar yarinyar ba?". Daya bangaren ne Maryam tace" Layla kenan,tom ya zanyi,na Auri wanda yake mawa tsohuwar matarsa Kaunar daukar rai,Sakaci nane tun baya Dana Bari So da Kaunar Safwan suka taru sukayi mun yawa". Har takai ma na Amince duk da baya sona!!!, na Aure shi. amma Sam bansan Yaya Allah zaiyi Dani ba,tabbas nasan ina hakuri,kuma ina kokarin cinye Jarabtar da Allah yayimun". Tab". Ikon Allah!!!. Layla ne mai fadin wannan maganar tana,Kara jajanta mawa Maatan Abokin mijin Nata". Hmmm duk naji Abun da kkce,Amma ki sani ki ajiye wannan Hakurin naki a gyefe,domun ko Hakuri shi ya kashe Jaki!!. Kya macace mai bukatan ana nunawa so da Tattali....Don ki ajiye maganar matacciya a gyefe,don a yanxu matar Safwan,ko nace matar da akayi masu baiko ta mutu,kyece dai matar,kuma dole ki rage Son Safwan ki Fara Nina masa kyema din Macace kamar kowa....ko yanuna maki so,ko kuma ya jingine Son Wannan Yarinya watake....? Bull...waye oho dao". Hmmm nisawa Maryam tayi don duka maganar Layla taji babu na Dauka". Tom Layla Zan yi tunanin akan maganan ki!. Kwarai kam...gsky kiyi tunani,Ya kwanan Bby na?!. Dariya Maryam tayi tana shafa Litsetsen Cikin ta da ya turo sannan tace" Bby ki na lfy....? Yaushe ne Zaki Bamu naki Bbyn???.

Hmmm kye Maryam rabani!!. Inahh,gsky ban shirya Haihuwa yanxu ba". Shuru Maryam tayi,kan tace" Hmmm amma kinsan Omar na Da Son yara ko??. Kuma ai ma yy maki hakuri shekara 5 fah Yabarki yana biye maki??.

Tom Maryam,ba dole ya kyaleni ba". Ai yasan bashi kye nakudar ba!. Hmmm Amma bakya tunanin ya gaji da Wannan Jan ajin naki??. Gajiya tom me kke nufi kenan??? At any time Omar zai iyah yi maki Kishiya,yana bala'in son yara,tun kan kuyi Aure kksan da Haka!!. Tom don nasan da hakan sai mene?? Ina fada maki wlh wargi wuri ya samu. Omar bazai tabs gigun Aure ba,shi baya ma da Irin wannan kalle²n ko son Hakan.don No baba Damuwa Wai don naji Omar na Waya da mace,babu mai iya jure masa saini,Omar tamkar gogawa ne,mai turkanan sa idan ya daga,sai wanda yasan Gabansa da Bayansa!!. Hmmm Maryam ba wani magana ba,nice dai Matar Omar Amarya kuma Uwar gida". Babu mahalin wani ko Wata a cikin zuciyar miji na, sai dai ni dai Layla!.

Dariya Maryam tasaka,tana cewa" Wow gsky K'awata kinyi dace". Inama nine kye??. Hmmm kyema ai kinyi dacen...don Safwan miji ne,wannan Yarinyan itace tayi maki Katanga da Soyayyar mijin ki,sai kiyi ta Neman hirji da itah". A haka dai sukayi sallama. Kan Hajiya Layla ta kalli Asabe cike da Masifah tace" kehhh Wata kalon Dabba Ce??. Sau nawa ne zanyi ta maki mgn akan Abu daya. Jiki na Rawa Asabe tafara cewa" Tuba nake Hjy.Don Allah kiyi hakuri". Dogon tsaki Tajah Kan ta kauda kai.....tana cigaba da Danna tafkeken Wayar ta".

"Yau a cikin gidannan babu inda Zakuje,Wlh na gaji da Zubar mun da mutuncin da kkyi na Wannan Maulan!. Baba Jume ne mai wannan maganan yana yi yana daga makoshi". Lalubar sandar ta Oumma tayi tana lalube da cewa" Haba Malam,idan bamuje Maulah munyi bara anbamu ba,da yunwa ne zamu zauna?? Kaifa ba nemo wa kk ka bamu ba".

Banyarda ba wlh....ko kye xaki je sai dai kye daya,ba da y'ata ba. Na fada maki. Yana fadin haka ya juya hadi da ficewa daga kuntacaccen gidan yana Dada sababi har waje". Idon Safiyyatu ne ya ciko da Kwalah,zaunar da Makauniyar Mahaifiyar Nata tayi,tana aikin rarrashin ta kaman kullum,don Allah Oumma kiyi hakuri,ki kyale Baba". Tom Safiyyatu yaya zamuyi yau?. Gashi bama da Abincin da zamu ci?!. Oumma kar ki damu da Akwai Naira Hamsun,sai yanxu nayi Sauri naje shagon niga na sayo Gari da siga".

Nisawa Oumma tayi cike da hamdllah da gode maww Allah tace" Yowa maza tashi kije ki sayo......kamin ya dawo,shuma yace zaisha shi!. Tom Oumma.

Fitan Safiyyatu ke da wuya ne tafita layin su hadi da Tsallaka titi,bayan ta sayo garirogon ne,Ta nufo titin ta Zumar ta Tsallako....Wanda sabd yunwa bata ko kallon gabanta". Karar birki taji anjah shi da karfin gaske....Wanda nan take jikin ta ya hau rawar kyarma". Jikakke kuuuuuu.....Tayar tana gogar Kwaltah.........

Share to another grps

Mmn teddy🧸 [7/18, 6:13 AM] Maman Teddy🧸: *Loading.....*

*YAR MAULAH🦯*

_Written by: Mmn teddy🧸_

*SADAUKARWA* °°°°°°°Wannan littafin sadaukar wane ga Teddyna🧸. Allah yayi ma Rayuwar ki Albarka,d'iyar Mmn tah".

*TUKWICI* Tukwici ne gareku mutan kungiya ta, Wato Alheri Writers association,baxan manta daku ba,har ilah yau inai maku son so fisabillah!!!.

*ABIN ALFAHARI* Mahaifiyata Abin Alfahiri na,ina kara godiya a bisa ga tarbiyar, da kulawar da kk bani,Allah ya karemun ke daga Sharrin mai sharri...Allah kuma yaka wanxar maki da xamar lafy,kwanciyar hankali mai Dorewa Ameen".

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ALHERI WRITER ASSO.📘🖊️*

*A.W.A*

©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©

_____________________________________

```Kungiya daya tamkar da dubu,masu rubutu don fadakarwa,da nishadantar da Al'ummah,Alheri sai d'an Alheri```

***

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

Da Sunan Allah mai Rahma mai jinkai!!.( In the name of Allah...)

Plz don Allah Hjy indai kinsan baxaki rinka sharhi ( Comment) ba,karki karantamun labari final". Masu comment ina matukar godiya,Allah yabar kauna...❤️