Page 6
by @mamanteddy
*Writting by* Aysha maman teddy🧸
*ALHERI WRITERS ASSO.*📘🖊️
***
*Bismillahir rahamanur rahim*
____________________________________
Cike da jin haushin xibewar nonon ga ƙwaryan data rabe biyu yasa mairo xubewa tana wani irin kuka don tasan yau ta shiga uku a wajen umma hausi. Bai ko tsaya bi ta kanta ba, balle yasan halin da take ciki yajah moton shi haɗi da kama hanyan nufan rugar kidandan. Ganin har sun fara nisa ne yasa abun kaga hauka ta fulani ta ɗauki sandar da take tare da itah ta nufesu.
Shikuwa Muhammad Adnan da yake can yagama ƙulewa da jin haushin mairo. Yana aikin huci kaman xaki. Yayin da khamis ke aikin bashi baki, akan yy haƙuri su haka mutanen ƙauye suke, balle kuma fulanin ruga, ae a kansune hauka tagama ƙarewa. Maganan sune ta datse sakamakon saukar sandar da sukaji akan glass ɗin su tagaba. Wanda sam ba suga xuwan taba sai dai saukar sandan haɗi da ganin ta kamal aljana a gaban su, gashin kanta gaba ɗaya ya rufe mata fuska. Ga fuska ya koma ya rine yy jah saboda kukan da tayi kuma abunka ga farar fata... Cike da tsoron ganin ta a gaban su khamis bakin shi yasoma rawa don a tunanin shi ba mutum bace mairo. Cikin makekƴartan murya ya hau cewa wa'innahu sulaimanu wa'inahu bisimillahir rahamanur rahim. Ganin yanda khamis ya birgice yasa muhammad Adnan ƙara ƙuluwa, wanda cikin ɓacin rai ya fito daga motan haɗi da ɗaga murya cikin xafin rai yace mawa mairo"kehhh dabban ina ne? Xaki matsa kibamu wuri ko sai na gwada maki halina. Masu halin dabbobi. Cikin jin hausan tasa data tsinci wasu da ƙƴar tace"kai dabba. Sai kuma tayi shiru don bata iya hausa can ba, balle ta rama abun da yy mata, duk da ta fahimci xagin ta yayi. Jin furucin dabban da ta kirashi yasa shi cike da ɓacin rai fara ƙoƙarin nufan ta. Ganin haka yasa khamis jiki na rawa yaxo haɗi da jawo shi yana cewa " plz Adnan ka rabu da itah, yanxu kuma fushin naka har da irin wannan wanda basa da ilimin kobo. Plz ka shiga mu tafi.... Haka dai da ƙƴer khamis yasaka shi a mota yayin da mairo ke a tsaye tana bin su da kallo bb ko tsoro a tare da itah. Haka cike da ƙunar rai Muhammad Adnan yaja motan. Wanda ita kuma mairo duk abun da tayi masu bai ishe ta ba, nan takuma bin bayan su haɗi da ɗaukan sandar takuma buga ma glass ɗin baya, wanda nan take shima ya rotse. Cikin tafarfasan zuciya ya fito haɗi da yaga rigar shaddan gexnan jikin shi saboda zuciya nan take singilate ɗin jikin shi ta sojoji ta bayyana. wanda ganin singelete ɗin jikin nasa yasa mairo tsorata don tabbas tasan waye sojah. cikin daujin wurun ta faɗa tana gudu, wanda cike da ƙunar rai Muhammad Adnan yafara shirin mara mata baya. Don gani ya keyi ma yanxu ne mairo takuma rainashi.
Muryan wata bafullatana ce Da ta ƙaraso taga abun da ke faru yasata tsorata haɗi da bin bayan mairo tana kwaɗa kiranta Mairo.. .. "Mairo...... "
Tsayawa yayi yana nanata sunan mairo. Kan daga bisani ya dun ƙule hannun sa ya nosa sauran glass ɗin da sukayi saura. Rinan nun idon sa ya ɗago wanda suka rine lokaci guda. Nan ya sauke su kan khamis da abun duniya ta ishe shi. Cikin wani irin murya Adnan ya fara cewa", khamis baxan bar yarinyan nan ba. Sai na azabtar da itah, sai na dasa mata baƙin ciki kaman yanda ta dasaun. Khamis gayamun ya xanyi na rama abun da tayi mun.? Cikin rashin sanin mafita khamis yace" bansani ba Muhammad.. Cije laɓɓa yy haɗi da firxar da wata irin numfashi, sannan yace"Auren ta xanyi, xan axabtar da itah, sai na ɗanɗana ma wannan yarinyan azaba. Kuma baxan bar cikin rugar nan ba sai da Auren ta. Xata san tayi da sojah mai zuciya da naci. Cike da mmki khamis yace"Wai Ban fahimce ka ba, amaimakon niman magani da mukaxo, yanxu kuma ka koma Auren manufah xakayi da BAFULLATANAN RUGA. .. .?
🤔🤔🤔🤔toh ko yayuwuwan Auren manufar da Muhammad Adnan xaiyi.? Shin xai yiwu ko baxai yuwu ba Allahu ma sani🤗💃💃💃
Plz kuyi manage wlh kwana biyu i'm to busy.
*#share to another groups*
Maman teddy 🧸 [3/6, 8:51 PM] Husnah: 🎪🎪🎪🎪🎪🎪🎪 🎪🎪🎪🎪🎪🎪 🎪🎪🎪🎪🎪 🎪🎪🎪🎪 🎪🎪🎪 🎪🎪 🎪 *BAFULLATANAN RUGA* 🎪🎪🎪🎪🎪🎪🎪 🎪🎪🎪🎪🎪🎪 🎪🎪🎪🎪🎪 🎪🎪🎪🎪 🎪🎪🎪 🎪🎪 🎪