THE UNION
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER NINETY ONE:91*
*THE UNION*
*JIDDAAH BARKUM*
——-
(Cigaban labari)
Dare ya yi sosai, Arman Mansion ta yi shiru, kowa ya koma ɗakinsa, fitilun hallway ɗin kaɗai suke haske a hankali, yayin da gidan ya shiga cikin wannan irin nutsuwar da dare ke kawowa. A ɗakin Zayd kuwa, yana zaune a gefen gadonsa, laptop ɗinsa a gabansa, yana duba wasu documents da suka shafi harkokin kamfani, fuskarsa a nutsaye take, idanunsa a kan screen, hannunsa yana flipping pages ɗin da ke gabansa lokaci zuwa lokaci, sai aka kwankwasa ƙofar, Zayd ya ɗaga kansa, “Come in,” ƙofar ta buɗe a hankali, Ummie ce.
Zayd ya ɗan gyara zamansa, ya ajiye abin da ke hannunsa gefe, “Ummie,” ta shigo cikin nutsuwa, ta rufe ƙofar bayanta, sannan ta ƙarasa zuwa inda yake, “Ba kayi barci ba ne?” “Yess,” Ummie ta kalleshi na ɗan lokaci, sannan ta zauna a kusa da shi, “Na zo ne mu yi magana,” Zayd bai ce komai ba, ya kalleta kawai, yana jiran ta ci gaba, Ummie ta sauke ajiyar zuciya, “Zayd… yanzu ka girma.” “Ba wai ina magana da kai kamar ƙaramin yaro bane, kai yanzu namiji ne, miji ne, kuma kai ne mutumin da ake kallon reflection na gidan nan a tare dashi,” Zayd ya ɗan sauke idanunsa, Ummie ta ci gaba a hankali, “Saboda haka ina son ka riƙa tsoron Allah a cikin duk abin da kake yi,” ta ɗan dakata, “Musamman wajen matanka,” Zayd ya ɗaga idanunsa ya kalleta, “Seeyama da Raihana…” Ta ambaci sunayen biyun a hankali, “Dukansu amana ne a hannunka,” “Ba za ka iya son ɗaya ka manta da ɗaya ba, ba za ka iya fifita ɗaya har ɗayan ta fara jin kamar ba ta da wani matsayi a gidanka ba.”
“Adalci ba yana nufin zuciyarka dole ta ji daidai ga kowacce ba saboda zuciyarka ba a hannunka take, amma abin da yake hannunka, lokaci, kulawa, abinci, sutura, matsuguni, mutunci, da duk abin da shari’a ta ɗora maka, dole ka yi adalci a ciki,” Zayd ya ɗan ja numfashi a hankali ya tattara dukkan nutsuwar shi gareta, Ummie ta kalleshi sosai, “Ka sani, habibi… aure ba abin wasa bane,” muryarta ta ɗan yi ƙasa, “Idan mutum ya cutar da mace, musamman matar da Allah ya ba shi amana, sannan ya fifita wata saboda son zuciya, akwai ranar da zai tsaya ya amsa tambaya a gaban Allah,” Zayd ya sunkuyar da kansa kaɗan, Ummie ta ɗan taɓa hannunsa, “Kar ka bari fushi, sha’awa, son rai ko wani yanayi ya sa ka manta da wannan,” ta yi shiru na ɗan lokaci, “Ko Seeyama ce, ko Raihana ce,” “Dukansu matanka ne,” Zayd ya ɗaga idanunsa ya kalleta, Ummie ta yi masa murmushi kaɗan, amma fuskarta har yanzu cike take da seriousness, “Ni ba zan gaya maka ka so ɗaya fiye da ɗaya ba, zuciya ba a hannun mutum take ba,” “Amma ina gaya maka ka yi musu adalci,” Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci, “In Shaa Allah Ummie,” ta gyada kai, “Allah Ya sa ka fahimta,” sai ta yi ɗan murmushi, sannan ta ƙara da wata magana da ta zo masa ba zato, “Gobe kuma, in Allah Ya kaimu…” “Za ka ɗauki matarka Raihana,” “Ku tafi gidanku,” Zayd ya kalleta amma baice komai ba, Ummie ta yi murmushi, “Za ku tafi da ita can, Allah Ya ba ku zaman lafiya, Ya sa wannan auren ya zama alheri a gare ku, Ya haɗa kawunanku, Ya sa soyayya da fahimta su shiga tsakaninku,” “Allah Ya kare ku daga duk wani abu da zai kawo fitina tsakaninku,” Zayd ya yi shiru, kafin ya amsa a hankali da amin, kalmomin Ummie suka zauna masa a zuciya, ba wai saboda bai san abin da take faɗa ba, amma saboda ya san cewa a yanzu, nauyin da ke kansa ya fi yadda yake son ya yarda, Ummie ta mike a hankali, ta kalleshi, “Allah Ya tashe mu lafiya,” “Ameen,” Ummie ta juya ta nufi ƙofa, ƙofar ta rufe a hankali, Zayd ya rage shi kaɗai, ya kalli ƙofar na wasu seconds, daga nan ya mayar da idanunsa kan documents ɗin da ke gabansa, amma a wannan karon… bai iya ci gaba da karatun ba, kalaman Ummie sun riga sun mamaye masa tunani, “Dukansu amana ne a hannunka.”
Washegari da yamma, bayan sallar Asr, Raihana da Suhaila suna zaune a ɗakin Suhaila, Suhaila ta kwanta a kan gado, yayin da Raihana ke zaune a kan sofa, sanye da wata doguwar rigar material mai lemon green, sai dark green veil da ta ɗaure a kanta, suna ɗan hira lokaci-lokaci, Suhaila tana jefa magana, Raihana kuma tana amsawa a hankali, amma gabanta? Sai uban bugu yake, ta kasa gane dalilin da ya sa zuciyarta ta ƙi nutsuwa, wani irin nervousness ne kawai yake yawo a jikinta, har ta kai ga idan za a yanka ta a wannan lokacin, wallahi ba za ta iya cewa me yake damunta ba, tana amsa Suhaila, amma ba wai saboda hankalinta yana nan gaba ɗaya ba, kamar rabin tunaninta yana wani wuri daban, har Suhaila ta fara lura, ta ɗaga kanta daga kan pillow ɗin, sannan ta miƙe ta zauna sosai a kan gadon, “Anty Rayy…” Raihana ta ɗago kai, manyan fararen idanunta suka kalli Suhaila, lashes ɗin da suka cika idonta suka ƙara bayyana, har suka yi kamar ta sa artificial lashes, Suhaila ta ɗan kalle ta na ƴan seconds kafin ta ce, “Na ji kin yi wani iri ne… ko akwai abin da yake damunki?” Raihana ta sauke idanunta ƙasa, ta ɗan kakalo murmushi, kamar tana son ta tabbatar mata cewa babu komai, “Ba komai, ina jin headache ne kawai… amma ba wani abu,” Suhaila ta bata fuska, “Headache kuma kike zaune haka? Ba ki ce na ba ki magani ba,” Raihana ta sake murmushi a hankali, “A’ah, ai it’s not that serious,” Suhaila ta ɗan girgiza kai, “Duk da haka…” Ta sauka daga kan gadon ta miƙe, “Kin fi so yau a kai ki gidanki baki da lafiya ai sai Akhie yayi holding ɗina accountable,” Raihana ta yi shiru, amma kalmar gidanki ta sake sa gabanta faɗuwa, ta kasa cewa komai, Suhaila kuwa ba ta lura da abin da ya faru a fuskarta ba, ta je ta ɗauko magani ta haɗa da ruwa ta dawo ta miƙa mata, “Ga shi, sha,” Raihana ta karɓa, ta kalli maganin na ɗan lokaci, sannan ta sha ba tare da musu ba, ba wai don kanta tana jin ciwon kan sosai ba, kawai dai ba ta son Suhaila ta ƙara tambayarta, kafin su sake cewa wani abu, aka buɗe ƙofar, Ummie ce.
Nan take Raihana ta gyara zamanta, Suhaila ma ta kalli mahaifiyarta, Ummie ta shigo a hankali, ta kalli Suhaila sannan ta ce, “Suhaila, ki ba ni waje kaɗan, ina son in yi magana da Raihana,” “Okay, Ummie,” Suhaila ta tashi daga wurin, ta bar su biyu, da ta fita, Ummie ta zauna a gefen Raihana, Raihana ta ɗan matsa jikinta gefe, kamar yadda ɗabi’ar kunya ta sa ta yi duk lokacin da ta samu kanta ita kaɗai da Ummie, Ummie ta lura, ta yi murmushi a hankali, ta ɗaga hannunta ta shafa gefen fuskar Raihana cikin tsananin kauna, Raihana ta sauke idanunta, har yanzu akwai wannan kunyar a tare da ita, ba wai tana jin tsoron Ummie ba, sai dai har yanzu zuciyarta tana ɗaukar Ummie a matsayin mahaifiyar mijinta, duk da yadda Ummie take ƙoƙarin nuna mata cewa ba haka kawai take ganinta ba.
Ummie ta ɗan yi shiru kafin ta ce, “Raihana, ina son in yi miki magana ne kamar uwa da ɗiyarta,” Raihana ta ɗago idanunta a hankali, sannan ta sake sauke su, “Hmm…” Ummie ta ci gaba, “Na san zama da kishiya ba abu ne mai sauƙi ba, kuma ba zan taɓa ce miki ki yi kamar ba komai bane ba, sai dai akwai abu ɗaya da nake roƙonki…” Ta ɗan dakata, “Ki yi haƙuri,” Raihana ta yi shiru, “Ki yi haƙuri, ki ɗauke kai idan abin bai kai ga komai ba, ba duk abin da aka faɗa ba ne ake bukatar a amsa shi,” Raihana ta gyada kai a hankali, Ummie ta ci gaba, “Idan akwai wani abu da ya shige miki duhu, ko wani abu da yake damunki, kada ki zauna ki riƙe shi a zuciyarki,” ta matse hannunta a hankali, “Ki kira ni kai tsaye, ko ki ce ya kawo ki, kar ki ji saboda ni uwar mijinki ce sai ki kasa magana da ni,” Raihana ta kalleta, “Ki ɗauke ni a matsayin uwa, ba kawai uwar mijinki ba,” maganar ta shiga zuciyar Raihana sosai, ta yi saurin sunkuyar da kanta, kunya ta sake bayyana a fuskarta, Ummie ta yi murmushi, “Kin ji ni?” Raihana ta gyada kai, “Ehh Ummie,” ta amsa cikin sanyin murya, “Good,” Ummie ta ɗan ja numfashi, “Sannan Seeyama…” Nan take Raihana ta sake yin shiru, Ummie ta kalle ta sosai, “Idan ta neme ki da fada, don Allah kar ki soma biye mata, kada ki bari fushinta ya jawo ki cikin abin da ba zai amfane ki ba, ki yi haƙuri, ki ɗauke kai, idan abin ya yi yawa, sai ki kira ni,” Raihana ta sake gyada kai a hankali, “In Shaa Allah,” Ummie ta shafa kanta, “Allah ya sa ku zauna lafiya da juna, wannan gidan ba gidan tashin hankali ba ne, ina son ku duka ku zauna lafiya,” Raihana ta yi murmushi mai rauni amma bata ce komai ba, Ummie ta sake kallonta na ɗan lokaci, sannan ta ce, “Sannan anjima za ku wuce gidanku, ke da shi,” ta ɗan murmusa, “Ki zama cikin shiri, kin ji ko?” Raihana ta ɗaga idanunta gare ta na ɗan lokaci, amma maimakon ta yi magana, sai kawai ta gyada kai, kunyarta ta hana ta cewa komai, Ummie ta yi murmushi, ta sake shafa fuskarta a hankali, “Allah ya muku albarka gaba daya,” Raihana ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, sannan ta sake gyada kai, “Ameen.”
Bayan fitar Ummie, sai Raihana ta ji kamar mashashshara ta kama ta, kamar zazzabi-zazzabi take ji a jikinta, ta ɗan zauna tana kallon inda Ummie ta fita, zuciyarta na ta bugawa ba tare da ta san dalili ba, maganganun Ummie suna ta maimaituwa a kanta, ta sauke ajiyar zuciya a hankali, sai kawai ta kwanta a kan sofa ta kudundune jikinta, tana son ta ɗan samu nutsuwa, ba daɗewa Suhaila ta dawo, amma a zatonta dai ciwon kan ne ya dawo, shi ya sa ba ta dameta ba, ta bar ta a kwance, ita kuma ta fara haɗawa Raihana ƙananan abubuwanta a waje ɗaya, kamar yadda Ummie ta bata umarni, Raihana na jin komai, tana jin motsin Suhaila, tana jin yadda take ɗaukar kayan tana ajiyewa wuri ɗaya, amma sai ta yi pretending kamar tana bacci, ba ta motsa ba ko kaɗan, ta rufe idanunta sosai, tana yin kamar ba ta ma san abin da ke faruwa ba, har aka kira Magrib, sai da ta ji lokacin ya yi sannan ta tashi a hankali, ta ɗauki hijab ɗinta, ta shiga yin alwala, ta fito ta shimfiɗa sallaya, ta yi sallah, a lokacin da take tahiyar ƙarshe ne Ummie ta sake shigowa, ta shigo da wata babbar atamfa mai kyau sosai, burgundy color, wadda ta haɗa da wani cream ɗin lafiyayyen lafayya material mai azabar laushi, ta zo da kayan a hankali ta ajiye su a gefen Raihana, kayan kuwa sai kamshi, azababben kamshin kabbasa mai mugun class, kamar an kwashe watanni ana turara su.
Raihana ta sallame sallarta, Ummie kuwa tana tsaye tana kallonta, kafin tace, “Ki shiga wanka, idan kin fito, ga kaya nan ki saka,” ta nuna kayan, “Yana shiri ne, za ku wuce,” a hankali Raihana ta gyada kai, muryarta ta fito a sanyaye, “Toh…” Ummie ta jinjina kai, ta juya ta fita, amma maimakon ta mike nan take, sai ta zauna a wajen na kusan minti goma, tana kallon waje ɗaya, tana zaune shiru, ta sake kallon agogo, ta fahimci lokaci na tafiya, tana bata lokaci ne, ba ta son kuma Ummie ta sake zuwa bata tashi ba, Raihana ta sauke ajiyar zuciya, ta ɗan zauna na wasu seconds again kafin ta miƙe a sanyaye ta shiga toilet, ta yi wankan tare da ɗauko alwala, bayan kusan minti goma sha biyar da shigarta, ta fito, ta ɗaure jikinta da babban towel, a daidai lokacin ne Suhaila ta shigo da gawayi wanda yake ta fitar da hayaƙi, “Anty Rayy, zauna,” ta nuna mata wata kujera da ta shigo da ita, Raihana ta kalleta, ba yadda ta iya, sai ta je ta zauna a kan kujerar, Suhaila ta ajiye kaskon a gabanta, ta kara turaren sosai, sannan ta rufe Raihana da wata babbar aba kamar riga, kanta kawai ne ya fito, “Ki zauna nan, let the perfume enter your body,” Raihana ta yi murmushi a hankali, “Suha…” “Shhh,” Suhaila ta rufe bakin ta da hannu, “Today you are not allowed to complain,” Raihana ta yi dariya a hankali, kamshin turaren ya fara shiga jikinta, hayaƙin na kewaye ta, bayan ɗan lokaci Suhaila ta buɗe abun da ta rufe ta, ta taimaka mata ta tashi, “Now let’s get you ready,” Raihana ta kalleta, “Suhaila kawai…,” Suhaila ta kalle ta da wani irin kallo, “Anty Rayy, please, don’t start,” ta ɗauko kayan makeup ɗinta, Raihana kuwa ta fara kallon kayan da idanunta a tsorace, “Wallahi Suhaila, kunya nake ji, kar Ummie ta ce har kwalliya na yi, don Allah ki bar shi,” Suhaila ta tsaya, sai ta fashe da dariya, “Why are you acting like this?” Raihana ta sunkuyar da kai, “Wallahi kunya nake ji,” Suhaila ta ƙara dariya, “Mijinki kika yi wa kwalliyar ai, common, Anty Rayy,” Raihana ta ɗago kai da sauri, “Suha!” Suhaila ta riƙe ciki tana dariya, “Me ne wai? Ba dai mijinki kika yi wa ba? Common!” Raihana ta kalle ta, wlh kunya take ji, “Don Allah ki bari,” “Okay, okay,” Suhaila ta ɗaga hannayenta sama, “But you are still doing this makeup,” Raihana ta yi shiru, Suhaila ta ja ta zuwa wajen dressing mirror, da ƙyar dai ta zauna a kan stool ɗin, Suhaila ta tsaya a gefenta, ta fara shafe-shafe a fuskarta a hankali, light makeup kawai, ba wani abu mai yawa ba, ta gyara mata brows kaɗan, ta shafa mata abin da ya dace da fuskarta, ta ƙara mata ɗan haske a lips, sannan ta tsaya tana kallon yadda kyan Raihana ke ƙara bayyana, Raihana kuwa ta kasa kallon kanta sosai, idan ta ɗaga ido zuwa mirror, sai ta sake sauke shi, “Suhaila…” “Hmm?” “Ya isa,” “Not yet,” “Please,” Suhaila ta yi murmushi, “Anty Rayy, just relax,” ta ɗauko turaren, ta fara zuba mata, sannan ta ɗauki wani ta shafa mata a wuyanta da hannuwanta lungu da sako ko ina, Raihana ta lumshe idanunta, zuciyarta na cigaba da bugawa, daga ƙarshe dai aka gama makeup ɗin, ba mai yawa ba ne, amma ya yi kyau sosai, Suhaila ta taimaka mata ta saka kayan, dinki ya zauna a jikinta da kyau, lafayyar kuwa ya ƙara masa class, ta gyara mata rufin lafayyar, ta saka mata sarka da sauran kayan ado a hankali, daga ƙarshe Suhaila ta ja baya, ta tsaya kawai, tana kallon Raihana, Raihana ma ta ɗago kai zuwa mirror, na ɗan lokaci ta kasa cewa komai, Suhaila kuwa ta kafe idanunta a kanta, kamar ita ma ba ta shirya ganin final result ɗin haka ba, “Anty Rayy…” Raihana ta kalleta ta mirror, “Hmm?” Suhaila ta yi shiru, sai kawai ta girgiza kai a hankali, murmushi ya bayyana a fuskarta, “Wallahi…” Ta sake kallonta daga sama har ƙasa, “You look so beautiful,” Raihana ta sake sunkuyar da kai, kunya ta mamaye fuskarta, kawai sai tayi murmushi, Suhaila ta yi dariya, “Look at you,” Raihana ta yi ƙoƙarin kar tayi murmushin da ke son bayyana a fuskarta, amma ta kasa, sai ta ɗan yi murmushi cikin kunya, Suhaila kuwa har yanzu tana kallonta, kamar tana ƙoƙarin fahimtar yadda ita da ta kasance a yau cikin nervousness da ciwon kai ta koma wannan kyakkyawar amarya mai kamshi da natsuwa, “Anty Rayy…” “Hmm?” “Akhie is definitely going to notice,” nan take Raihana ta juya mata ido, “Suhaila!” Suhaila ta fashe da dariya, “Okay! I said nothing,” Raihana ta sunkuyar da kanta, amma murmushin da ke fuskarta ya kasa ɓoyuwa.
Inno ce ta buɗe ƙofar, ta tsaya a bakin ƙofar tana kallonsu daga inda take, ta kalli Suhaila daga sama har ƙasa, sannan ta ce, “Suhaila, ko canja mata halitta kike yi dai? Yaci ace kin fito da ita,” ta ɗan girgiza kai, “Haba! Kun bar shi a zaune tun dazun yana jira, ya kamata ta fito su zo su tafi,” Suhaila ta ɗago kai da sauri, “Gamu nan zuwa,” Inno ta jinjina kai, ta juya ta fita, da ta fita, Suhaila ta kalli Raihana, sai ta kama hannayenta biyu ta taimaka mata ta miƙe, kafin su fara tafiya, Suhaila ta janyo ta zuwa jikinta, ta rungume ta sosai, “Anty Rayy… I will miss you so much,” muryarta ta ɗan yi laushi, “I really enjoyed staying with you these past few days,” “Allah ya sa ki shiga gidanki a sa’a, kuma In Shaa Allah, yadda kika shiga, Allah ya sa sai dai a cire gawarki,” Raihana ta lumshe idanunta, maganar ta taɓa wani wuri a zuciyarta, nan take ta ji hawaye na son zubowa, amma sai ta dake, ta ɗan ja numfashi, ta haɗiye abin da ke son fito mata, sannan ta ce cikin rawar murya, “Thank you, Suhaila,” ta ɗan yi murmushi, duk da yadda idanunta suka fara cika da kwalla, “You are such a precious angel… down to earth,” “Thank you for everything,” Suhaila ta janye kanta daga jikinta tana murmushi, amma da ta kalli fuskar Raihana sosai, sai ta ga kwalla ta cika idanunta, murmushin Suhaila ya ɗan dusashe, “Noo… please, don’t cry,” ta ɗaga yatsanta a hankali, ta fara share mata hawayen da suka taru a gefen idonta, “Please, Anty Rayy…” Ta yi mata murmushi mai taushi, tana ƙoƙarin kada ita ma ta nuna yadda maganar ta ta taɓa zuciyarta, “Don’t cry,” Raihana ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin riƙe hawayen, Suhaila ta sake goge mata ɗayan gefen idonta, sannan ta ɗan ja numfashi, “Let’s go,” ta sake kama hannun Raihana.
Suhaila ba ta sake sakin hannunta ba, a haka ta riƙe hannun Raihana har suka sauko downstairs, suna tafiya a hankali tare, har suka sauko ƙasa, hannayensu a manne da juna, Ummie da Inno suna zaune a kan sofa, yayin da Mr Armaan yake zaune a kan two-seater, ƙafa ɗaya a kan ɗaya, sanye yake da wata falleliyar shadda mai launin cream, sai maiko take kamar yanzu yanzu aka qeeraa ta, kansa ya sa hula tangaran wadda take ta zuba sheki, a hannunsa kuwa akwai ubansun wristwatch — Rolex Day-Date, mai tsananin kyau da ɗaukar ido, sai black leather sandals ɗinsa masu masifar kyau, kamshin da yake fitowa daga jikinsa kuwa? Kamar yana zaune ne a cikin factory ɗin turare, fuskarsa a dinke, tsaf, babu wata hayaniya a tare da shi, wannan irin sanyin fuskar da yake ƙara masa kamala, fatarsa kuma tana ta kyalli a ƙarƙashin hasken ɗakin, hannunsa ɗaya yana sarrafa wayarsa, kamar babu wani abu da yake faruwa a wajen, kawai dai ango sakk!
Amma da Raihana ta sauko, sai kamar zuciyarta ta tsaya na second ɗaya, gabanta ya faɗi nan take, idanunta suka tsaya a kansa na ɗan lokaci, sai ta gane tana kallonsa, nan take ta ɗauke kanta da sauri, kamar wadda aka kama tana yin abin da bai kamata ba, Suhaila kuwa ta kama hannunta, tana shirin zaunar da ita, amma Inno ta yi zumbur, “Wanne zaman kuma za ku yi? Duk wanda kuka yi a ɗaki bai isa ba?” Ta kalli Raihana, sannan ta kalli Zayd, “Tashi ku tafi, gata nan,” ta ɗan gyara zamanta, “Allah ya ba da zaman lafiya,” Zayd ya ɗago kansa a hankali, kallo ɗaya kacal ya yi wa Raihana da Suhaila, sai ya ɗauke kai, ba tare da ya ce komai ba, ya miƙe a hankali, ya zura wayar cikin aljihunsa, sannan ya nufi wajen Ummie, ya durƙusa a gabanta, ya kama hannunta ya sumbata, Ummie ta yi murmushi, ta ɗaga hannunta ta shafa kansa, “Ku je, Allah ya ba ku zaman lafiya,” can ƙasan muryarsa ya amsa, “Ameen,” sai ya miƙe, ya wuce ta gefen Suhaila ba tare da ya ce komai ba, sannan ya fice, Ummie ta miƙe, ta kama hannun Raihana, Raihana ta sake sunkuyar da kai cikin kunya, ta bi ta, har suka isa gaban Inno, Inno ta ɗaga hannunta ta shafa kan Raihana, “Allah ya ba ku zaman lafiya,” Raihana ta yi murmushi cikin ladabi, Suhaila dake gefe ta amsa, “Ameen,” sannan Ummie ta kamo hannunta, Suhaila na binsu a baya, har suka fita zuwa compound.
Zayd ya riga ya isa wajen motar, yana tsaye kusa da ita, ya buɗe motar amma bai kai ga shiga ba, Ummie ta kai Raihana har wajen motar, ta buɗe mata front seat, “Shiga,” Raihana ta shiga a hankali, Ummie ta gyara mata lafayyar da ta ɗan sauko kasa, sannan ta rufe mata ƙofar a hankali, Zayd ya shiga, ya kunna motar, ya yi reverse, sannan ya daidaita motar, Suhaila ta tsaya a wajen tana waving Raihana, murmushi dauke a fuskarta, “Bye, Anty Rayy!” Raihana ta ɗago hannu tana mayar mata da waving ɗin, murmushi ya bayyana a fuskarta duk da nervousness ɗin da kuma uban bugun dake cikin zuciyarta, gateman ya buɗe ƙofar compound a hankali, motar ta fara tafiya, a hankali ta fice daga compound ɗin.