ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 13

by @ibtisamwrites01

……. ……..  ZAREN ZUMUNCI 
               (The thread of family bond)

                        WRITTEN 

                            BY

                  IBTISAMWRITES ✍️



PAGE 13
 
Sai Alh. Aliyu ya ce,
“Ai ita ma Fauziyya da zu ta zo tana kuka, ta ce ita ma tana da Wanda ta ke so, kuma shi take so ta aura.”
 
Alh. Lawal ya ce,
 
“Ai shikenan ma. komai ya zo da sauki, tunda both parties ne ba su amince ba.”
 
    Anan su ma suka ce wa Fauziyya ta fada wa Ibrahim din, cewa idan a shirye yake, shi ma ya turo magabatan sa a daura musu auren tare.
 
   Haka shi ma yayi na’am, don baya son abin da zai raba shi da Fauziyya.
 
  Shi yasa da ya fada wa babansa, Alh. Yunus Galadimawa, aka yi kasa a gwiwa ba wajen zuwa neman auren.
 
    Alh Yunus Galadimawa shi ne mahaifin Ibrahim saurayin Fauziyya,yana da mata guda daya Haj Bilkisu ,mutuniyar Kirki ce me ji da ado.she is calm and she supports her children in everything they want ,sai dai abin ya Saba wa addini ko wani abin shi ne kawai ta ke taka musu burki ,shi yasa su ma ba sa yin abin da bata so.sun haifi ‘ya’ya guda 4,Babban su shi ne Ibrahim sai Hajara,sumayya sai kuma Ramadan.Sun taso cikin so da kaunar Junan su,abu ba zai faru da daya bah ace dan uwan shi abin be taba shi ba .They are so close da ba a iya Jin kan su sai dai in abin ne yafi karfin su shi ne ma parents nasu zata ji.
 
     Haka su ka kasance cikin so da kaunar junan su, da girmama juna don cikin su Ibrahim ya bawa Hajara 2years and Hajara ta bawa sumayya 1 and half year sai sumayya kuma ta ba wa Ramadan 3years ne.So zance ace babu girmama wa be ta so bah and iyayen su sun basu tarbiyya daidai gwargwado.
 
    Bayan da Haj zuwairah ta ji zance cewar an fasa auren Fauziyya da Abdulahad,hankalin ta ya ta shi , tana ta kiran Alh Aliyu ta ji wane magana ce ta je ji haka nan ne ba dadin ji.
    
    Ya ce ta Bari ya dawo zai fada mata duk abin da ya faru.Da ya dawo bayan ya huta ,ya fada mata duk yadda aka yi amma sam bata yi na’am da zancen bah , sai cewa ta yi ai Alh “ni ban gane me yasa kuke biye wa wadannan yaran bah,su da ba hankali suka gama bah ,sannan ba wai sun San abin da zai yi musu bane.”Alh Aliyu was shocked sosai don be yi tunanin zata Fadi wannan magana bah.
   
    Amma ganin cewar ita ta kawo wannan shawara ,dole ne ayi mata uzuri ganin kamar abin  ta ke son hada wa ne ya ke rugujewa.Duk yadda ya so yi mata bayani kin yadda ta yi.
  
   Anan ne aka samu rikici tsakanin Hajiya Zuwairah da Alh. Aliyu.Da yaga abin na neman sa su samun sabani sai kawai ya fara yi mata bayanin cewa;
 
   “Abdulahad ne ya ce ba ya so.”
 
     Nan ne ma ta dan sauko,amma duk da haka dai, Inne ta ce ita tana ganin a hada Fauziyya da Lamin.
  
Alh. Aliyu ya ce,
“That is impossible.”
 
    Ya gaya mata abin da za a yi, don har iyayen yaron sun so kuma sun amince. Ba za ta mayar da su kananan mutane ba.
Haka dai ta hakura,aba don ta so bah.
 
    Sai kuma ya ke  gaya mata sunan mahaifin yaron da Fauziyya ta ke so, sai hankalinta ya dan kwanta, tun da babansa shahararren mai kudi ne an Africa gaba daya.
        
         Ya samu ya fito daga falon,ganin ta sauko ba kamar loakcin da ya dawo bah, amma duk da haka bata son har yanxu maganar Aliyu da yayi ta na nan bah , shi yasa ko maganar bata yi bah,a ganin ta ai ta huce tun da ta yi wa tufkar hanci.
     
     Haka Alh Aliyu da Alh lawal suka hadu suka kuma tattaunawa akan al’amuran da ke faruwa a cikin rayuwar su.
 
   Da ga nan dai suka gama maganganunsu, har suka yanke cewa next week, insha Allah, za su tafi India nema wa Aliyu auren Amna.
Inda zai yi dai-dai, dama saura four weeks kenan a daura auren.
 
    Bayan komawar Alh. Aliyu gida, ya kira dansa Aliyu.
Ya fada masa yadda suka yi da Alh. Lawal akan za a je nema masa aure a gidan su Amna.
Amma ya gargade shi,
“Kar ka sake kowa ya ji wannan maganar har sai an daura auren.”
Ya ce,
“Toh, Daddy.”
Daddy ya ce,
“Ka fada mata ta sanar da su zuwan su gidan nasu, don su ma su san da za su zo.”
Ya ce,
“Toh.”
Sannan ya tashi ya tafi.
Da farin ciki ya dauki wayarsa ya kira Amna.
Ya fada mata yadda suka yi da Daddy.
Tana ta murna ta ce yanzu nan za ta je ta fada wa Maa dinta, sai ta sanar da Daddy.
And they communicated in English, tunda bata jin Hausa.

 
Ibtisamwrites✍️