ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 14

by @ibtisamwrites01

………………..ZAREN ZUMUNCI 
               (The thread of family bond)
                           
                              WRITTEN 

                                       BY


                    IBTISAMWRITES ✍️


PAGE 14
 
Weeks in , rana bata karya,sai gashi date din da su Abba suka sa za su tafi india ya zo.
 
 Haka satin ya zagayo suka tafi kasar India, inda suka samu tarba mai kyau daga dangin Amna din.
 
    Kuma sun yaba da karamci irin na su, sannan sun yi farin ciki da gidan da dan su ya je neman aure.
 
      Haka aka gama magana aka tsaida komai da komai, sannan sun yarda za ayi daurin auren a lokacin da aka ce za ayi din tare da sauran.
 
      Sun taho gida suna farin ciki sosai da irin tarbar da suka samu a can.
 
   Da dawowarsu, gadan-gadan, lokaci ya riga ya yi. Saura sati biyu a fara shagulgulan biki.
 
     Ana ta gyara amare, an dauko masu gyaran jiki, suna na su aikin events, ma an kama inda za ayi shi. Ana ta hada-hada dai.
 
     Su Amna ma sun dawo Nigeria.
 
     Dama Abbanta yana da gida a nan, so anan ne za ayi duk shagulgulan bikin nasu tare da family nata.
 
    Duk da su aka taho, sun ce ba za ayi biki babu su ba. Don haka da su za a fara komai, in da wasu kuma sai in bikin ya zo gab da za a fara su karaso Nigeria din.
 
      A haka kusan duk Ahalinta sun hallara, sai farin ciki take yi ita kadai.
 
    A bangaren su Amna, za su yi bukukuwan al’adar India irin su mehendi, sangeet, da dai sauran su.
 
   Rana bata karya, lokaci ya zagayo, inda anan ne za a fara gudanar da bikin.
 
     An fara bikin ne tare da Daurin aure,in da dubban mutane suka halarta ,Ana ta gaiggaisa wa Ana nuna farin ciki da wannan aure.
    
    Maroka ne suka fara busa suna fadin an daura aure lakadan ba ajalan bah.
 
      Inda aka daura auren:
Kabir Aliyu Guruntum da amaryarsa Aina’u Lawal Shu’aibu, a sadaki naira 500k.
Isma’il Aliyu Guruntum da Zuhra Lawal Shu’aibu.
Yusuf Aliyu Guruntum da Asma’u Lawal Shu’aibu.
Kamal Aliyu Guruntum da Khausar Lawal Shu’aibu.
Sai suka ji an ce an daura auren Aliyu Aliyu Guruntum da amaryarsa Amna Anwar Tafida, a sadaki naira 500k.
 
    Anan kowa ya tunanin ana yi kuwa? Liman din nan daidai yake?
 
  Amma kafin su gama wannan tunani, sai suka ji an ce an daura auren Ibrahim Yunus Galadimawa da amaryarsa Fauziyya Aliyu Guruntum.
 
   Nan dai aka yi ta maganganu saboda babu wanda ya san an canza amaryar Aliyu da kuma angon Fauziyya sai yanzu da aka daura aure.
    
    Kowa ya na tunanin ya hakan ya faru bayan katin da aka tura musu ba haka sunayen ya ke bah ,amma ba Wanda ya ce komai a ka chigaba da yi musu congratulations na auren.
 
   Su ma dai brothers din Aliyu da Fauziyya were surprised sosai, amma kuma sun taya su farin ciki sosai.
 
    A nan ne ma suka samu labarin ya aka yi aka canza groom din Fauziyya da kuma yadda aka nemo wa Aliyu aure an india.
 
    Shi ma in-law din nasu Ibrahim, sun taya shi farin cikin samun kanwarsu da yayi, duk da ba su san da zancen ba, but they are happy for them.
 
     Toh, a can bangaren gidan Alh. Aliyu kuma, labari ya  iso wa Hajiya Zuwairah cewar ga abin da ya faru a wajen daurin aure.
 
     So duk inda kuke tunani, tashin hankali fa ya tashi a lokacin.

   Hajiya Zuwairah kuwa na tunanin,”How can all this happen without her knowledge?”
 
    And to think that it happened under her nose terrified her so much.
 
     Haka ta tashi ta tafi daki ita kadai, tana ta kiran Alh. Aliyu saboda tana son ta san me yasa yayi mata hakan.
Why?
 
 
Ibtisamwrites✍️