ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 17

by @ibtisamwrites01

…………………ZAREN ZUMUNCI 
              (The thread of family bond)

                     
                              WRITTEN 

                                      BY

                          IBTISAMWRITES ✍️
PAGE 17
 
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yau dadi gobe ba dadi.
 
    Amna ta je gaida inne kusan sau ba adadi amma babu wani canji da aka samu.Tana dai samu Abba suna gaisawa,ya zamana kusan in dai zata je gidan Abba na nan don ya debe mata kewa,sannan kar abin da inne ta ke mata ya ringa damunta.
 
    Haka za su zauna tare,yana Jan ta da hira don ta sake da shi sosai sannan ya na yi yana kara tunasar da ita mahimmancin hakuri.
 
  Ya kan ce mata ,shi komai na duniyar nan dan hakuri ne ,don haka hakurin da ta ke da shi to ta kara a kai wata rana zata ci ribar hakan.
 
 
    Haka rayuwar dai ya ci gaba da tafiya.Ta bangaren su yaya kabir ma duk Ana zaman lafiya,kuma sa’I da lokaci suna zuwa ziyara wajen su inne.
 
 
       A haka a ka yi 5 years da auren ma su duka.A cikin wannan shekarun,abubuwa da dama sun faru har da karuwa da aka samu a gidajan duka.
 
     Hayaniya ce ta je ta shi a cikin farfajiyar gidan, yara ne kusan su shida a wajen, wasu na wasa,wasu guje guje,sai guda daya da ya ke gefe kadan da su a zaune yana kallon su.
 
    A cikin yaran guda biyu mata kansu daya don za su kai shekaru daya,sai mazan ma guda biyu sunan za su iya kai wa shekara daya,sai ragowar biyun kuma sun ba wa juna shekara guda.
 
 
     Ina cikin lissafi sai na ji Ana ,Khalil Ina kuka shiga ne kai da ‘yan uwan naka,Toh duk ka tattaro ku ,ku shigo ciki,inne ta ce a fada muku ku dawo duka.
 
 
      A cikin Wanda shi ne aka kira da khalil din,ya amsa da cewa gani nan inna(mai aikin inne),yan zu zamu shigo.
 
 
     Haka ya tattaro su duka amma shi wannan da yake a gefe ko motsawa be yi bah,Sai da me shekaru kamar shi ya zo, naji yana cewa me sunan Abba(Aliyu) ka taso mu tafi Ana kiran mu, anan ne na gane cewar shi wannan da ya zo wurin Wanda ya je zaune tun dazu dan Abba ne,kafin in gama wannan tunani naji Ana ,Ayaan ka tafi ni ba yanxu zan shiga bah.matan kuma sunan su Nafisa fada Nihla.
 
 
    Kawai sai na kura wa yaran ido, dududu be fi shekara uku bah and yadda yayi maganar ba zaka ce haka shekarun sa suke bah.
 
       Yana da girman jiki,kuma Allah ya zuba masa wayo,don a yadda yayi maganar za ka yi  tunanin ya gi haka a shekaru.
 
   
        Da kyar dai ya ta shi ,Su ka shiga parlor din tare.
 
 
   Suna shiga sai na ji inne na magana, cewar me kuka tsaya yi ba ku shigo tare bah, sai ta kuma cewa au ashe tare kuke da Mara maganar nan.
 
    Aliyu Wanda shi ta ke cewa Moddibo ya dago kansa ya kalleta, amma ko Kala be ce mata ba ,ya mai da kan sa kasa ya jingina kansa da kujerar.
 
 
 
    Duk maganar da ta chigaba da yi mi shi da tsokanar, ko kula be kuma yi bah,daga kar she dai ta chigaba da yi wa sauran yaran wasa.
 
 
      Da dare yayi kuma duk yaran suka ta shi suka shiga dakunan su na gidan.
 
    Don tun da aka haifi yaran ,inne ta sa aka gyara mata wani bangare a gidan ,kawai saboda in sun zo Hutu,suna da inda za su zauna.
 
Ibtisamwrites✍️