ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 18

by @ibtisamwrites01

…………………ZAREN ZUMUNCI 
              (The thread of family bond)

                     
                              WRITTEN 

                                      BY

                          IBTISAMWRITES ✍️



PAGE 18
 
   A cikin wannan rayuwa da ake yi, sai Allah ya do ra wa inne son jikokin nan nata,especially ma ‘ya’yan yaya Aliyu,sam bata ba ri wani Abu ya sa me su.
 
       Haka ta ke ririta su kamar Kwai ,ko da iyayen su mata ne suka yi musu fada ,haka zata yi kicin kicin ta hana su wai yara ne.
 
   Amma ita ma din ba ta bar su haka ba, ta na yi musu fada amma ba da tsawa kamar yadda iyayen nasu suke musu ba wani lokaci,in da su ma sai in sun yi maganar da yawa kuma suka ki ji ne suke musu tsawa.
 
 
     A  bi sa wannan dalili ne inne ta sauko,ta ke amsawa wa Amna wadda aka ce wa (Ammi) yanxu cikin kulawa da so.
 
 
     A haka weeks passed,months ma ya zo ya shige ,and shekaru ,makaranta ma sun kusa shiga jami’a .
  
     A wannan shekaru ne aka kuma samun karuwa a cikin gidan nan,in da ko wane hutu,suna tafiya gidan kakanni su don yin hutu .
 
      Haka za su hadu ,ayi fada a shirya,kullum dai haka .
 
    A cikin yaran akwai masu rashin kunya da tsoro,akwai kuma masu tsoro,da kuma Wanda ‘yan kan ta kife ne.komai ta fanjama fanjam.
 
     A wannan shekaru ne aka kara haifar wasu ,in da aka haifi su Najma,Nihal su ‘ya’yan baba Yusuf ne ,Su kadai Allah ya ba shi  Sai Khairat ,Anwar da Tasleem ‘ya’yan baba kabir ne kannen Aliyu junior (moddibo).
 
 
                Ayan ,Khalid,Amina,Aliya,Ashna,Aleeshbah,Asad,Arshad su kannen Khalil da Nihla ne sannan ‘ya’yan Abba Aliyu ne.
 
      
          Nafisa ita kadai ce ‘ya a wajen abbu(Isma’il) kenan,haka suke kiran shi.
 
      Dada(kamal) haka yaran suke kiran shi , shi Allah be ba shi haihuwa bah .
 
 
     Toh haka suaj ta so , sun shaku da juna.Alan a cikin su Aleeshbah bata ta so cikin su bah,saboda tun da aka yaye ta mutanen india suka dauke ta.
 
     So ita kadai ce bata ta so cikin su bah ,amma kuma suna kiran juna a waya suna magana so ta Saba da su a haka.
 
      Har group ma suka bude saboda a ringa zumunci,a nan ne ma aka samu sabani sosai a tsakanin Najma da Aleeshbah.
 
   Wanda sai da aka yi zaman sulhu online in da duk rashin son magana yaya Aliyu sai da ya rufe group din nan,yayi dogon voice yana musu fada.
 
       A lokacin da aka yi wannan dogon voice Aleeshbah ta kwana wajen biyu bata online saboda ita ba ma abociyar hawa online ba ce,sai da ma Arshad ya yi mata magana akan ta hau ta duba sannan ta hau,anan ta saura ra ta ji me aka ce.
 
 
   Ina ita fah wannan hukunci da aka yi be yi mata ba ,taya za ayi bayan yaya Najma ce da laifi a ce wai sai kowa ya zo ya bada hakuri,and wai ita ce zata fara bayarwa,ta girgiza kai ta ce “No” this will never happen.
 
 
     A nan Aleeshbah ta samu wuri ta zauna , ta fara voice ta in da ta shiga bata nan ta je fita bah, sai da ta kai karshen voice din hankalin ta ya kwanta sannan ta tura musu ,ta sauka a online din.
 
 
        Haka kowa ya hau ,ya ji wane sako voice din ke Kunshe da shi sai ya sauka,A haka a haka kowa ya gama ji amma ban da shi Wanda aka yi wa martani na voice din da yayi.
 
 
 
     For almost a week da yin abin ,ya shiga group din ya ji me take fadi,shi ma kuma sai da yaji labarin da ake yi nan ne ya tafi tunanin wane voice yayi anan ne ya tuna .shi ne dalilin shi na shiga group din ya ji me ta fada ake magana akai.
 
 
     Ran shi in yayi dubu ya baci, shi yasa fah baya shiga harkar yaran nan saboda shi ko kadan baya son ayi masa rashin kunya.
 
     
         Ga shi yanxu a wani dalili yarinya ta samu damar yi masa rashin kunya.
 
 
 
        A saboda wannan voice da Aleeshbah ta yi wa Yaya Aliyu sai da abin ya kai ya kawo sai da iyaye suka shiga lamarin, conference aka hada na wadanda fada ya faru a tsakanin su aka yi sulhu.
 
   Tun daga nan kuma ,ya kuma daure fuskar nan ta shi , dama kuma ba wani fara’a ya ke musu bah.
 
    In kaga yayi fara’a ko dariya to da iyayen shi yake ,ko kuma cikin sa’annin shi,sai kuma wajen grand parents na shi.
 
 
 
Ibtisamwrites ✍️