ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 21

by @ibtisamwrites01

…………………ZAREN ZUMUNCI 
              (The thread of family bond)

                     
                              WRITTEN 

                                      BY

                          IBTISAMWRITES ✍️


PAGE 21
 
 Abhie ya dawo gida shima a wannan time din da Aleeshbah ta zo.Yace wa Ammi “yana bukatar ya watsa ruwa tukunna kafin komai ya biyo baya”.Haka Ammi ya tafi din hada masa ruwan wanka.

Ko da Ammi ta gama hada masa ruwan wankan,Ya ta shi ya shiga yai wanka kafin nan ta sama masa abinci mara nauyi da zai iya ci .
 
    Amman kafin ta fita sai da ta gyara masa dakin ta fess freshener me sanyi kamshi,sannan ta tafi hada masa abinci.
 
 
Tana fita daga dakin,ta samu Aleeshbah zaune a kan kujera, “Aleeshbah na tambayar ta Ina Abhie din Ammi”, “sai Ammi ta ce yana fitowa yanxu.Ni Abinci zan girka masa ,ko zaki taya ni girkin ne”.
 
 
     Aleeshbah ta zare ido ta ce Ammi girki kuma, bana cikin mood din girki ni,sai dai zan taya ki hira ne kawai in kina so.
 
     Ammi ta kalle ta ,ta ce  ,” ko dai ba ki iya girkin ba ne Aleeshbah ?Na ga duk sanda na ce ki zo ki tayani girki sai kin kawo wani excuse kin fada”.
 
 
   Aleeshbah ta ce Ammiii ta ja sunan kafin ta ce;”If I cook my food you will be surprised and daga nan zaki ce na din ga yin girki a gidan ni kuma I am not fond working in the kitchen ko wane lokaci.”
 
 
     Ammi ta saki baki tana kallon ta ,” ta ce Anya kuwa ‘Yar nan,Toh naji kin iya yin girki amma baki cika yi bah sai kin so ko,Toh in kin yi aure wa zai na yi muku girkin ke da mijin?Ammi ta tambaye ta”.
 
 
 
    Aleeshbah ta kalli Ammi sai ta ce “well that’s not a problem,zan ce masa ban iya girki bane , ya samo me yi masa girki don ni ba girkin kowa nake ci bah  and abincin ma bai dame ni bah,ko kuma yana yi mana order shikenan,problem solved ta fada tana murmushi.”
 
 
      Ammi ta juyo daga girkin da ta ke ,kawai don ta tabbatar da abin da ta ji ya fito daga bakin Aleeshbah din.
 
 
    Ta kura mata ido , sai ta juya tana aikin nata ta ce mata ,”waye ya ce miki wannan tsari ne da kowa ma zai dauka?Ammi ta kuma yi mata wata tambayar.”
 
 
   Sai Aleeshbah ta dago da kanta ta ce” well ni dai shi ne nawa and ko wa zan aura ma zan gaya masa in ya ji ya gani fine if not yayi gaba .”
 
    Sai Aleeshbah ta kuma cewa  “Ammi why are you asking all this bayan ma ni ai ba wani aure da zan yi yanzu,baya cikin agenda na.”
 
 
     “Ni buri na bai wuce na gama internship nawa na fara aiki bah sannan sai a fara tunanin marriage but not now.”
 
 
     Ammi ta kalleta,ta kuma juyawa tana ci gaba da girkin nata da ta kusan gamawa ,duk suna cikin hirar ta je girkin ga shi ta kusan  kammala wa , “tana tunanin wannan buri na Aleeshbah tun tana karama ta ke da shi ga shi har yanxu bai canzu bah.Ya za ayi in wani abun zuwa ya zo unexpectedly ya faru,ba fata ba dai.”
 
 
 Bayan Ammi ta gama girkin, Aleeshbah ta taya ta fito da flask din tana kai wa dining.
 
  Bayan sun kammala shirya dining din,Abhie ya fito daga daki,Aleeshbah ta je ta yi hugging na shi tana ce wa welcome back Abhie with smile on her face.
 

     Abhie was surprised da ya ga Aleeshbah a gidan bayan ya San be San da zuwan ta ba,but yayi murna sosai.

  Suka karasa dining din suka zauna don cin abinci,Amma Aleeshbah juice kawai ta zuba shi ne don kar ace me yasa bata cin komai.
 
 
    Haka suka gama cin abinci,maids suka zo suka kwashe kwanukan da aka bata da sauran flasks din da suke wajen.
 
Palour suka dawo suka zauna,suna dam hira da Ammi ,don ita Aleeshbah tuni ta yi musu sallama ta ce sa hadu gobe .
 
    Abhie ne ke tambayar Ammi yau she beta ta dawo ne  , sai Ammi ta ce rana daya suka dawo da yayunta.sai Abhie ya dago kai ya ce ta dade da dawo wa kenan ,amma ta je ta gaida inne ne?
 
    Ammi ta ce aa ,na yi nayi ta je ,ta ce zata je amma sai ranar da babu kiwa a gidan,saboda bata son in ta je a sa ta a gaba bayan ba lokacin da ta tsara haduwa da su ne yayi bah.
 
      Ta ce ka San tun da ta dawo a cikin yaran nan ba Wanda ya dawo gidan nan ,suna can gidan inne dukan su ,sun mana Hijra.
 
     Ita kuma wai ta fi son kafin su hadu da sisters da brothers din nata da cousins din sai ta fara zuwa wajen inne ita kadai sun gaisa har ma ta yinan mata.
 
 
    Abhie ya dago Kai ya ce “sam wanna be dace bah,na San halin ta na taurin kai,ba in ta ce abu babu canji sai in ta saka kanta ,amma dai ya kamata ko ma mene ta je ta gaishe da inne din.”
 
 
     Before wannan ma tun da ta dawo ta kirawo inne ta fada mata ta dawo?

   Ammi ta girgiza kai ta ce “ta kirawo ta amma bata ce mata tana nan Nigeria bah.kawai dai ta ce mata ta kusa ta dawo Nigeria and tana ta murna da hakan.”
 
 
    Abhie ya ce kin gani bah,” ita tana murnar jikar ta zata dawo amma ita ta dawo amma ba ta je inda ta ke bah.Me yasa hakan?”
 
 
      Ammi ta ce” sorry nasan an yi laifi and ni ma da nawa laifin na biye mata da nayi am an tursasa mata akan dole sai ta je bah.we are so sorry kaji Abhie .”
 
 
   Haka ta yi ta lallaba shi har ya hakura,amma ya ce gobe ta fada wa Aleeshbah ta zo ya same shi in ta shi daga barci.
 
 
Ibtisamwrites ✍️