ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 22

by @ibtisamwrites01

…………………ZAREN ZUMUNCI 
              (The thread of family bond)

                     
                              WRITTEN 

                                      BY

                          IBTISAMWRITES ✍️




PAGE 22
 
    Washegari, sai da Shaɗaya na safiya ta yi sannan Aleeshbah ta tashi daga bacci, a wannan lokacin shine lokacin da ta saba tashi a koda yaushe.Sai dai in tana da wani uzuri da ya kamata ace ta ta shi da wuri shi ne ta ke ta shi,amma dai tun da ta gama zuwa school shikenan sai abin da ya karu.

     Tana tashi wanka ta shiga,  ta yi kusan 2hrs  sannan ta fitowa ta shirya.  A duk sanda ta fito sai  ta yi kusan  awa biyu kafin ta kammala komai nata,  haka al'adar take, sai de kuma a duk sanda ake neman ta, ana tashin ta ne kafin lokacin tashinta ya yi.
 
     Ammi da kanta ta je ta kirawo ta, ta ce ta  zo Abhie na kiranta,  haka ta taso ta bi bayan Ammi zuwa bangaren Abhie.
 
     Da shigar su cikin bangaren, suka yi sallama , ta samu waje ta zauna a kusa da shi kafin ta ce, "Good morning Abhie".
 
ya amsa mata da kulawa yana kallon ta. Kafin ya ce.
 
"Tun da kika dawo kin je wurin Inne kin gaishe ta?
 
 Ta ce,"A'a amma mun yi waya da ita".
 
   Ya ce, "Da kuka yi wayar ta san da cewar kin dawo Nigeria?
 
Sai ta girgiza kai tare cewa, "a'a".
 
Yaa ce,"Toh kin gani, yanxu kin kyauta kenan,ko da ba zaki kirawo kowa ki fada masa kin zai ba ai Kya fada wa Inne ko? ita da ta ke ta murnan zaki dawo amma bata san kin dade a nan din bah".
 
 
    Ta dago da kai ta ce, "sorry Abhie I will make it up to you, yau insha Allah after isha zan je in gaishe da ita".
 
Ya ce" after isha kuma? Ai dare yayi lokacin".
 
Ta ce," Abhie wannan ranar ce bana son shiga tana da zafi sosai".
 
 
   Ya ce"Shikenan, zan fada wa driver zai kai ki in anjiman".
 
Ta dago ta ce” Abhie ni zan yi driving kai na ai,ya ce kin san gidan ne sai ta girgiza kai ya ce to taya zaki je da kanki?ta ce kwatance za a min in tafi ni kadai.”
 
 
  Kawai girgiza kansa yayi ya ce aa ,”driver zai kai ki and that’s final.Ta shi ki je ki fada wa Ammi ta kawo min tea.Ta ta shi ta ce toh sannan ta fita.”
 
 
    Tana fita ,ta jiyo motsi a kitchen,tana lekawa sai ta ga Ammi ce a ciki sai ta ce mata “Ammi ,Abhie ya ce ki kai masa tea”.Ta juya zata ta fi sai Ammi ta ce” ya kuka yi da shi din”.
 
  “  Sai ta ce ya ce min na je gaida inne ne ko na fada mata na dawo amma dai na ce masa zan je after isha”.Ammi kawai ta juyo ta kalle ta ta ce “sai isha zaki je gidan?To wane irin zuwa kika yi kenan,mene amfanin zuwa daren.”
 
 
   “ Aleeshbah ta ce Ammi it’s normal fah ,and ta fi dadi fita da daren nan,babu hayaniya and na fi son fita da daren ne.”
 
 
     Ammi zata kuma magana “ Aleeshbah ta ce Abhie is waiting for his tea and ni zan je nayi wanka bye.”Ta juya tana murmushi ta tafi,Ammi ta girgiza kai ta ce “ this girl bah komai aka ce mata sai ta yi opposing na shi,sai ta san ta yadda aka yi dole ita ta zama me final word din.”
 
 
     Aleeshbah ce ta fito sa ye da black Abaya,ta yi rolling din mayafin in da ta fito ta yi kyau abin ta kamar a sace ta.Ta je dakin ammin ta yi knocking aka ce ta shigo, ta bude amma bata shiga duka bah sai ta zura kanta ta kofar,ta ce i am ready zan tafi yanxu ,sai na dawo.Ammi ta ce a dawo lafiya ki gaishe min da inne din.
 
 
  Bayan tafiyar Aleeshbah amma ta tuna wani abu sai tayi murmushi ta ce rayuwa kenan da fah ba irin abin da inne bata yi mata bah amma yanxu kamar ba a yi ba albarkacin wadannan ‘ya’yan.
 
  Sai ta tafi tunani na yadda ta ke zuwa gidan Inne amma bata fitowa su gaisa sai dai in Abba yana gidan shi ne ta ke fitowa,amma in baya nan haka zata karaci zaman ta a nan saman ta yi tafiyar ta bata ga ko gilmawar Ammi bah.
 
 
    Sai watarana da Ammi ta zo gidan ,ta yi sallamar ba a amsa ta bah,saboda in ta zo gidan masu aikin na ansa mata Amma wannan karin sai ta ji wani irin shiru ya mamaye gidan gaba ki daya.
 
 
   Ta ji dai shirun bai kwanta mata bah,ta ta shi ta tafi dakin inne,shi ne tana shiga taga duka masu aikin suna nan a ciki ,inne ta gani kwance kan gadon nata amma kana ganin ta bata Jin dadin jikin ta sosai.
 
 
   Ta karasa ciki da sauri tana tambayar me ya faru da inne din ,why is she like this,me ya same ta and me yasa ba su kai ta asibiti bah ?duk a lokaci daya ta yi wannan tambayoyi.”
 
 
     Ta ce wa masu aikin su taya ta su fito da ita zata kai ta hospital in ya so a kirawo ka wa ye ma a waya ,yan priority na su shi ne a samu lafiyan inne ba wani abu bah.
 
    Duk wannan abin da ake yi inne na kwance ,ba halin ta yi magana , jikin ta duk ya saki saboda rashin kwarin jiki.
 
 
Ibtisamwrites ✍️