Page 2
Cikin sauri Salim ya taimakawa Hajja Kaka suka dauki Jazzeelah, wato Fatima.
Fatima ita ce suke kira Jazzeelah saboda sunan Hajja Kaka tace suke kiranta haka. Tun tana karama, tun tana yarinya karama da bata san komai ba, Hajja Kaka ce ta ce sunan ta za a saka mata. Sunan da ke dauke da ma'ana mai zurfi. Sunan da ke dauke da soyayya ta kaka da jika.
Shi kuma Baba da Daddy da Baffa suna kiranta da Ummi. Ummi... Sunan da yake dauke da daraja a gidan. Sunan da yake nuna cewa ita ta mussaman ce a gidan, saboda yarinya ce mai hankali, tana da kunya. Kowa a gidan ya san Ummi yarinya ce mai mutunci. Ba ta fita, ba ta shiga, kullum daga makaranta sai daki take. Saboda haka ne ma abin da ya faru ya fi ba kowa mamaki.
Cikin dakinta suka kai ta. Dakinta mai kyau, mai tsafta, ga kamshi da yake fitarwa duk da zuwa yanzu bata son kamshin dakin kwata-kwata. Salim ya dauketa. Jikinta yayi laushi kamar ba ta da kashi a jiki. Kanta ya kwanta a kafadar shi. Hajja Kaka na shafa kanta tana kuka a hankali, tana fadin kalmomin addu'a.
Abidah tana biye dasu a baya, kamar inuwa. Tana kuka, amma tana kokarin boye kukanta. Idanunta sun cika da hawaye, hancinta ya yi ja. Hannunta na goge hawayenta, amma hawayen na ci gaba da zuba. Tana jin zafin abin da ya faru da 'yar uwarta. Fatima da ta sani tun suna kanana, Fatima da suke wasa tare, Fatima da suke kwana daki daya, yanzu ta zama haka? Ta rasa duk wannan gatan?
Salim ya kwantar da ita a hankali kamar ana kwantar da karamar yarinya. Hajja Kaka ta gyara mata kwanciya. Ta gyara mata hijabin da ya karkace. Ta gyara mata hannunta. Ta lullube ta da bargo.
Hajja Kaka tana magana cikin tausayi. Muryarta na rawa. Ta san halin da jikan ta ke ciki. Ta san yadda mace mai ciki ke wahala. Ta san yadda jiki ke yin laushi. Ta san yadda mutum yake a zabtuwa.
Ya fita da sauri ya dauko akwatin magani na gida. Ya dauko paracetamol. Ya dauko ruwa a jug da cup. Ya ajiye su a gefen gado. Ya san idan ta farka, zata bukaci ruwa. Zata bukaci magani don ciwon jikin da Bilal ya daura mata.
Abinci, Abidah ta so kawo mata, amma tasan kota kawo mata bazata ci ba. Ta san halin Fatima yanzu. Ta san yadda cikin ya mayar da ita. Tun farkon cikin, kwata-kwata Abidah tana kallon wahalar da take sha.
Saboda kwata-kwata cikin baya barinta cin komai. Duk abin da aka kawo mata sai ta ji kyama. Sai ta ji kamar zata yi amai. Kamshin mai kadai na sa ta gudun kitchen. Hakama kamshin albasa na sa ta rufe hanci. Bata iya cin komai. Duk jikinta ya rame. Fuskarta ta sauya. Idanunta sun shiga ciki. Gaba daya ta dashe kamar bata da jini duk da fatan jikin ta mai duhu ne, amma zuwa yanzu gaba daya tayi fari tas. Abu biyu ne kawai suke da auki a jikin ta, daga hips sai cikan kirji da take da shi duk da dama tana dasu tubarkalla masha Allah. Cikin nan ko a shafe kamar ba shine ake fadin akwai yaro a cikin sa ba.
Sai dai kunun tsamiya. Shi kadai, da aka saka kayan kamshi kadan. Shi kadai ne take iya sha. Idan ta sha shi, sai ta ji dadi a cikinta. Sai ta ji karfi kadan. Shi kadai ne ke sauka ba tare da ya dawo ba. Hajja Kaka ce ta koya mata hada shi.
Hakan yasa Abidah ta nufi kitchen din saboda ta samarma ta da kunnu. Ta tashi da sauri ta nufi kitchen din. Tana gudu a cikin corridor. Hawayenta na zuba. Tana so ta hada mata kunun kafin ta farka. Tana so ta ga ta sha ta samu karfi.
Duk da shima wani sa'in takanyi amanshi, amma ita tasan ko kadan ne zai shiga cikinta, zai bata karfi. Ko rabin cup ne, ya fi ta zauna haka nan.
Amma fir! Mommy tace baza a taba dama mata wannan kunnun a kitchen dinta ba.
Abidah ta tsaya cak. Ta kasa motsi. "Mommy dan Allah..."
Amma Mommy ko kallon ta bata yi ba.
Dawowa Abidah tayi, Hajja Kaka ta tambaya, "Ina kunnu?"
Abidah ta fada mata abin da ya faru.
Nan fa Hajja Kaka ta hau fada! Fushinta ya tsananta! Idanunta sun yi ja! Jikinta ya fara rawa saboda bacin rai!
Ta kama hannun Jazzeelah tare da fadin, "Tashi mu koma bangarena! Sai su karata da bakin halin su! Wannan gidan ya riga ya lalace! Wane irin gida ne wannan? Tashi nace, mu koma bangarena inda zakiyi abin da kike so!"
Abidah ta kamata suka nufi bangaren Hajja Kaka...